Darussa daga waki’ar Ashura. Print
Written by administrator   
Sunday, 09 October 2016 14:05

Kasantuwar wannan wata da muke ciki na Muharram wata na juyayi da kuka ga mabiya Ahlul bayt a sassan duniya dabam dabam.A irin wannan munasaba akan tunasar da juna kan janibobi masu yawa na wannan wa}i’a ta Ashura.A nan insha Allah za a tunasar da juna ne kan Darussa daga wannan wa}i’a ta Ashura,kuma wa]annan darussa suna da yawa saboda haka wasu daga cikinsu ne za a kawo domin su kasance darasi garemu da zamu darastu dasu musamman ma a wannan lokaci da muke ciki na jarabawa na wa}i’ar Zariya,wanda idan muka kwatanta zamu ga cewa tarihi ne ya maimaita kansa.Ga wasu daga cikin darussan.

          1. MUHIMMANCIN KYAKKYWAN A{IBA: A cikin rayuwar mutum babu abin da ya fi muhimmaci a kan a}ibarsa, wato }arshensa. Shi ya sa da za a yi tambayar cewa, a cikin rayuwar mutum menene ya fi muhimmanci? Amsa ita ce yadda ya bar duniya a addinance, wa]anda suka yi wannan aika-aikar, inda mutum zai bi tarihin rayuwar wa]ansunsu abin zai ba shi mamaki. Domin wasunsu sun kasance tare da Imam Ali (AS) har ma sun yi ya}i a bayansa, amma yau ga shi sun dawo suna ya}ar ]ansa da mutanen gidansa, har ma daga }arshe suka karkashe su, tare da kuma sun san matsayinsu, ba wai sun jahilta ba ne. Saboda haka wannan akwai abin ban tsoro a ciki, a ce mutum ya zauna da Ma’asumi, ya rayu tare da shi har ya koma ga Allah (T), shi kuma daga baya ya zo ya canza. Allah ya yi mana kyakkyawar a}iba.

          2. ILLAR SON DUNIYA DA ABIN DUNIYA: Da yawa daga cikin wa]anda suka yi wannan mummunan aiki, babban abin da ya kai su ga aikata wannan aiki shi ne tunanin abin da za a ba su na duniya. To, abin tambaya a nan, yau ina abin da aka ba su na duniyar yake? In ma an ba su kuma ina wa]anda suka ba su suke? Suna ina yau? Wanda su da abin da aka ba su ba su kai shekara 100 ba. Amma ga shi sun jefa kawukansu a wahala da azaba ta dindindin.

          3. {ARANCIN ADADI BAI HANA FUSKANTAR MA{IYA: Idan mutum ya dubi adadin jama’ar da ke tare da Imam Husain (AS) ya kwatanta da adadin da ke gefen ma}iya, zai ga cewa bambancin ba ka]an bane, amma duk da }arancin adadi, haka Imam Husain (AS) da jama’arsa suka fuskanci wa]annan dubban ma}iya. Tabbas Imam Husain (AS) da jama’arsa su suka samu nasara a kan wa]annan ma}iya. Da yake nasara iri biyu ce, akwai babbar nasara wadda ita ce nasarar lahira, akwai kuma }aramar nasarar wadda ita ce nasarar duniya, ita kuma iri biyu ce, akwai ta zahiri wadda ita ce samun nasara kan ma}iyi, da kuma ta ba]ini wadda ita ce dakewa a kan gaskiya, wato tafarki har mutuwa ta zo a kashe mutum a kai, ko kuma samun galaba kan ma}iyi.

          4. {IYASTA ABIN DA YA SAME SU GA MUTUM A KANSA: Duk lokacin da abu ya samu mutum a hanyar addini ko kuma saboda ri}onsa ga Ahlul Baiti (AS), to ya kwatanta wannan abin da ya same shi da abin da ya samu Imam Husain (AS) da Sahabbansa da kuma abubuwan da suka biyo bayan shahadarsu. Wannan tunani sai ya kashe masa zogi ko ra]a]i na abin yake samunsa,ko kuma yasa ya ga rashin }imar abin da yake samunsa sakamakon bin sa ga tafarkin Allah (T) da kuma ri}o da Ahlul Bait (AS).

          5. MUHIMMANCIN DAKEWA DA SADAUKAR DA KAI DOMIN [AUKAKA ADDINI DA KUMA WANZUWARSA: Dakewa da sadaukar da kai da Imam Husain (AS) ya yi tare da Sahabbansa shi ya wanzar da wannan addini zuwa yanzu. Domin da ba don wannan sadaukar da kai da kuma dakewa ba, da idan an ce yau babu addinin Musulunci, to ba za a yi musu ba. Saboda haka wannan darasi ne babba gare mu.

          6-MUTUM BAI DA TABBAS:Wannan wa}i’a ta Ashura ta koyar da mu cewa lalle mutum bai da tabbas,saboda idan muka dubi wa]anda suka ya}i Imam Husain akwai wa]anda tabbas sun rubuta masa takarda na kan yazo amma kuma da yazo suka bashi baya,mu kuma duba tarihin wanda ya jagoranci shi ya}in wato Umar ]an Sa’ad sun taso tare da Imam Husaini ne ma’ana sun yi yarinta tare,lokacin suna yara duk abunda Imam Husain ya samu to yakan bashi,ko dabino Manzon Allah[S] ya bashi to ya ka kan raba shi biyu ya bashi rabin amma mu duba shi ya jagoranci kashe shi.Mu kuma a yanzu mu duba wannan wa}i’a ta Zariya,mu dubi Gwamnan Kaduna lokacin da aka kashe ‘ya’yan Sayyid[H] har gidan Sayyid ya zo ta’aziyya haka nan ma da rasuwar mahaifiyar su Sayyid ya zo ta’aziyya zuwa gidan,haka nan ranar da wa}i’ar nan ta fara,a ranar ya bugo ma Sayyid waya amma mu duba rawar da yake takawa a wannan wa}i’a da muke ciki,saboda haka duk yadda mutum ya kusance ka ko yayi ala}a da kai to bai da tabbas zai iya canza maka ko ya baka baya.

          7-JURIYA DA KUMA HA{URI:Wannan wa}i’a ta Ashura ta koyar damu cewa duk wanda yake akan tafarkin Ahlul bayt to dole ne fa ya kasance mai juriya da kuma ha}uri saboda mutum zai fuskanci cutarwa da kuma musgunawa dabam dabam wanda bai da wani magani in ba dauriya ba.Mu duba wahalhalu dabam dabam dasu Imam Husain suka sha a wannan wa}i’a ta Ashura,sai da ya kai abinci da ruwan sha basu dashi haka suka kasance cikin yunwa da kuma }ishi na kwanaki,ga kuma isgili da cin mutunci dabam dabam da ma}iya suka yi masu a ranar Ashura amma haka suka daure.Mu kuma duba abubuwan da aka yi ma su Sayyida Zainab bayan wa}i’ar Karbala na }ona tantunansu da kuma kwashe masu kayayyaki da cutar dasu misali dukansu da ]aure hannayensu da sar}o}i da kuma yawo dasu ana nuna ma mutane da hana su abinci sai sau ]aya a yini da dai sauran ababe na cutarwa da kuma gallazawa da aka yi masu kamar rushe gidajensu dake Madina.Mu kuma a yanzu mu dubi wannan wa}i’a ta Zariya yadda aka gallaza ma ‘yan uwa aka cutar dasu ta fuskoki dabam dabam bayan kisa da aka yi da makamai dabam dabam,aka yi amfani da wuta aka }wana wasu da ransu,aka kama wasu aka je aka azabtar dasu ta fuskoki dabam dabam,aka }wace masu dukiyoyinsu da dai sauran nau’oin zalunci dabam dabam da aka yi.

          8-BABU MATSAYI DA MUTUM ZAI KAI WANDA ZAI WUCE JARABAWA:Wannan wa}i’a ta Ashura ta koyar damu cewa babu wani matsayi da mutum zai kai wanda zai wuce a jarabta shi misali mu duba matsayin Imam Husain wanda a I’iti}adinmu shi Ma’asumi ne,sa’annan mu duba matsayi irin ta nasabarsa cewa babansa Ma’asumi ne,mahaifiyarsa Ma’asumiya ce,kakansa Ma’asumine,]ansa Ma’asumi ban da kuma Hadisai masu yawa da aka ruwaito wa]anda suke bayanin matsayinsa a duniya da lahira amma duk da haka mu duba irin jarabawar da ya fuskanta na kashe shi da aka yi aka sare kansa,haka aka dunga yawo da kan gari-gari ana nuna ma jama’a,haka nan tufafin da ke jinsa bayan kashe shi aka ]ebe, aka sa dawakai suna sukuwa kan jikinsa da kuma sauran na wa]anda suka yi shahada tare dashi,wato dai darasin shine mutum ya fahimci cewa zai iya fuskantar kowane cin mutumci da kuma zarafi yana raye da kuma bayan an kashe shi. Komin matsayinsa ko a fagen addini.Mu kuma a yanzu mu dubi wannan wa}i’a ta Zariya mu dubi matsayin Sayyid[H] a cikinmu amma mu duba abinda ma}iya suka yi masa na cutar dashi da kuma nuna ma duniya,haka nan kuma mu dubi wasu ‘yan uwa da suke da matsayi da daraja a cikin zukatanmu amma bayan an kashe su aka je aka ha}a rami a ka binne wato ba tare da yi masu jana’iza yadda shari’a ta shinfi]a ba kamar yi masu wanka,likkafani,sallah da dai suransu.Saboda haka mutum zai iya fuskantar jarabawa ta kowace fuska yana raye ko baya raye.

          9-GODIYA GA ALLAH DA KA ZAMO MAZLUMI BA AZZALUMI BA.Idan mutum ya dubi wannan wa}i’a ta Ashura zai ga cewa ~angarori ne guda biyu sune:Azzalumai da kuma wa]anda aka zalunta.An ruwaito daga Imam Ali[AS] ya ce, “Ka kasance wanda aka zalunta amma kada ka kasance azzalumi.” Kuma in ka dubi rayuwar mutane ko da wane lokaci a kuma kowane zamani zaka samu cewa mutum ko dai ya kasance azzalumi ko wanda ake zalunta.Yanzu idan muka dubi wannan wa}i’a ta Zariya zamu ga cewa akwai azzalumai akwai kuma wa]anda aka zalunta,saboda haka mutum ya dun ga godiya ga Allah Ta’ala da bai sa ya kasance cikin azzalumai ba ko cikin karnukan azzalumai sai ya sanya shi cikin wa]anda ake zalunta.Saboda shi zalunci yana da illoli masu yawa a nan duniya da kuma lahira dama addinin mutum,misali wanda ya bada umarni aje a kashe wani ko wasu da kuma wa]anda suka je suka aiwatar da umarnin kisan to ga illolin haka a gobe }iyama.Allah Ta’ala yana cewa a cikin Suratu Nisa’i aya ta 93, “Duk wanda ya kashe Mumini da gangan to sakamakonsa Wutar Jahannama ne,zai dawwama a cikinta,kuma Allah yayi fushi dashi,kuma Allah ya tsine masa,kuma Allah yayi masa tattalin azaba mai girma.” To mu dubi wa]annan ababe da aka ambata wa]anda zasu sami azzalumi gobe }iyama.Anan gidan duniya kuma in ka zalunci mutum to duk irin addu’ar da ka yi masa to sai ta kama shi ko ba jima ko ba]e,Manzon Allah[AS] yana cewa, “Kuji tsoron addu’ar wanda aka zalunta domin kar~a~~iya ce wajen Allah.” Illar zalunci ga addinin mutum shine duk wanda ka zalunta to za a kwashi ladar wani aiki da kayi mai kyau sai a baiwa wanda ka zaluntar,in kuma azzalumin bai da wata lada to sai a kwaso zunubin wanda aka zalunta amai dashi ga wanda ya zalunce shi,shi yasa a wajen bayin Allah azzalumai abin tausayi ne.Yazo akan cewa a ranar Ashura bayan da Imam Husain ya yi duk abinda zai yi na ya dawo da ma}iya kan hanya da kuma kada su aiwatar da wannan mummunan aiki da suke so su yi amma haka bai yiyu ba sai aka ga yana kuka,aka tambaye shi sai ya ce yana tausayinsu domin zasu tafi wuta ne kuma su dawwama a cikinta saboda wannan aiki da zasu yi.Domin shi azzalumi idan yayi zalunci in yana ganin a wajensa ba komi ko abin ya wuce to a wajen Allah fa abin ba haka yake ba wato bai wuce ba har sai ya fidda ha}}in wa]anda aka zalunta.Shi yasa in mutum ya dubi abubuwan da aka yi a Zariya zai ga cewa wa]anda suka bada umarnin da wa]anda suka aiwatar dashi sanadiyyar wannan mummunan aiki da suka yi sun halakar da kansu wato sun janyo makansu fushin Allah da kuma la’anarsa kamar yadda wannan aya ta yi bayani,a lokaci guda sun ]aukaka darajojin wa]anda suka karkashe ko cutar a wajen Allah Ta’ala,kuma abinda suke fa]a dashi wato Harka sun bun}asata amma su basu sani ba,domin a tarihin wannan Harka ba a ta~a wata wa}i’a wanda ta tambatsa wannan Harka kuma ta bun}asa ta kamar wannan wa}i’a da ta auku a Zariya,Saboda yanzu ko mutum yaso ko ya}i ko ya yarda ko kada ya yarda wannan Harka Islamiyya da Sayyid yake jagoranta ta zama ta duniya baki ]aya wato ta shiga lungu-lungu na duniya sakamakon wannan mummunan abun da aka yi,kuma duk wannan jinkiri da ake yi na sakin Sayyid da sauran ‘yan uwa yana da]a tambatsa Harka ]in ne da kuma sa mutane su da]a fahimtar zaluncin da aka yi.Saboda haka lalle mutum ya goda ma Allah da bai yo shi cikin azzalumai ba ko masu taimaka ma azzalumai ko kuma masu goyon bayan abunda azzalumai suka yi.Imam Sadi}[AS] ya ce, “Wanda yayi zalunci da wanda ya taimaka aka yi zaluncin da kuma wanda ya yarda da zaluncin da aka yi to duka sun yi tarayya cikin zunubi.” A wani Hadisi Imam Ali[AS] yana cewa, “Kashedinka da zalunci domin babban zunubi ne,a wata ruwaya ya ce,Mafi hasararku shine mafi zaluncinku.”

          10-DOGARA GA ALLAH TA’ALA:Wannan wa}i’a ta Ashura ta koyar damu muhimmancin dogara ga Allah ga dukkan al’amuranmu,mu dubi yawan rundunoni da kuma kayan ya}i da ma}iya suka yi tanadi a wa}i’ar Ashura wanda a wata ruwaya an ce maya}a sun kai su 30,000 amma su Imam Husain da jama’ar sa basu wuce mutum 100 ba,sai ya zamanto su babban makamin su shine dogaransu ga Allah Ta’ala.Haka nan idan muka dubi wannan wa}i’a ta Zariya lalle Sayyid[H] ya koyar damu wannan babban darasi na dogaro ga Allah,alal misali jawabinsa na }arshe wanda duniya taji na wata tattaunawa da aka yi dashi a ciki yake cewa shi ya dogara ga Allah ne,kuma ai mun ga abun da ya faru an zo da nufin a kashe shi kuma aka harbe shi a makisa amma Allah Ta’ala ya kare bayansa,kuma bayan da aka hahharbeshi aka barshi domin jininsa ya tsiyaye nan ma Allah ya kare bawansa,a wata ruwaya kisan ma sun yi amma Allah bisa ikonsa ya dawo masa da ransa domin ya nuna masu cewa dun kana da iko da makami baya na nufin zaka iya yin duk abinda ka dama ne ba.In ma mutum bai fahinmci haka ba to ya dubi miyagun makamai da suka yi amfani dasu don wai su ruguza wannan Harka Islamiyya sai ya zamanto yanzu sun bun}asa Hakar ne.Ina gab da zan kammala wannan rubutu wani labari ya bayyana cewa wai jahar Kaduna ta soke Harka Islamiya a jihar,wannan mu bai bamu mamaki ba sai dai su sun ]auka mu }ungiya ne wato basu ]auka cewa mu musulmi ne da muke }o}arin ]abba}a Musulunci a ]ai-]aikunmu da kuma al’ummar da muke ciki ba,shi yasa ko a zantukanmu sai dai kaji ko an ce ‘yan uwa Musulmi ba wai }ungiya ba.Yanzu misali zaman makoki da muke yi wanda shi ya firgita su suka ]auki wannan matakin }ungiya ne, addini ne kuma yana da ala}a da a}idar da muke akai ko kuma Arba’in dake tafe ko kuma munasabar ranar Ghadir da aka yi watan Zul-hijja,saboda haka munasabobi da sauransu duk suna da ala}a da fahimtar da muke ta addini ne ba wai muna yi a matsayin }ungiya bane,yanzu wa]annan munasabobi da na bada misali dasu a matsayinka na mabiyin Ahlul bayt kana bu}atar in zaka yisu kaje kayi rajista da gwamnati daman ai a cikin dokokin }asa an baka damar kayi addinin da kake so ko kabi fahimtar daka za~a.Kuma ai a cikin wannan Harka akwai cibiyoyi wa]anda suke bu}atar rajista ai suna dashi.Kuma kashe fahimta da muke akai wani abune wanda ba zai ta~a yiyuwa ba, ina nufin fahimta ta Ahlul bayt kamar yadda na farko basu iya ba to ballatane na }arshe.A ta}aice dai wannan matakin ba zai yi nasara ba kamar yadda matakin }arfi da suka yi amfani dashi bai yi nasara ba,kuma su bibiyi tarihin wannan Harka ai akwai Gwamnatocin da sun gwada haka amma basu yi nasara ba misali ta Abaca a lokacin duk ranar ta’alimi sai an zo an yi harbebe amma yanzu gashi ya zama tarihi.Saboda haka a wannan zamanin mutum yayi mafarkin wai ya kashe fahimta ta Ahlul bayt lalle yana ru]ar kansa ne,lokacin da Allah yake nufin ya tabbatar da fahimtar a doron }asa baki ]aya a lokacin wasu suke ganin zasu iya hanawa saboda haka su bada }o}ari su gani har ya zuwa lokacin da zasu fidda rai cewa lalle wannan abu ba zzasu iya kauda shi ba,sun ma gano matakan da suke ]auka yana da]a ha~aka abun ne.Ga ‘yan uwa musamman ma wa]anda suke jahar Kaduna a da]a daurewa da kuma dogara ga Allah Ta’ala na wannan sabon salo na cutarwa da kuma musgunawa da za a fuskanta,insha Allah wa]annan abubuwa zasu zo su wuce kuma zasu zama tarihi,kyakkyawan misali mu dubi abubuwan da suka auku ga ‘yan uwan mu a wa}i’ar Sokoto amma yanzu gashi ya zama tarihi,to haka ma wannan zai zo ya wuce Allah Ta’ala yana tare da masu dauriya.Wamakaru-wamakarallah-wallahu-kairul-makirin.