Bayani kan fannin ilimin Fikhu. Print
Written by administrator   
Friday, 06 September 2013 03:37

Isha Allah saboda muhimmanci da kuma bu}ata daga wasu ’yan uwa na gabatar da darasi kan Fi}hu, shigen yadda ake gabatar da darussa 12 daga rayuwar A’imma (AS), ko kuma darasi kan A}lak ta ~angare na, na yi tunani amsa wannan bu}ata domin  gabatar da shi wannan darasin na Fi}hu gwargwadon iko.

Amma kafin shiga cikin darsin Fi}hun. A nan za a yi shimfi]a dangane da shi ilimin Fi}hu da wasu abubuwa da suke da ala}a da shi. Da farko dai shi ilimin Fi}hu fanni ne mai fa]in gaske, yana kuma ]aya daga cikin fannonin ilimi na addinin Musulunci, wanda ya fitar da Malamai da littafai masu yawa, in mutum ya yi bincike zai ga cewa a dukkan fannonin ilimi na addinin Musulunci babu fannin da ya fitar da Malamai da littafai, kamar fannin ilimin Fi}hu. Kuma wannan haka abin yake a dukkan wa]annan makarantun guda biyu, wato Ahlul Baiti (AS) da kuma Ahlus Sunnah. Kuma ko a wannan nahiyar tamu mutum na iya bincikawa ya gani, in ya bincika zai ga cewa yadda ake karatun fannin Fi}ihu ya fi kowane fanni, musamman ma a cibiyoyin karantarwa na zauruka.

Fi}hu yana da manyan ~angarori guda biyu. Na farko shi ne Ibadat, ~angare na biyu shi ne Mu’amalat. Wannan a dun}ule ke nan. Amma a warware kowane ~angare daga cikin wa]annan ~angarorin guda biyu ya kasu kashi-kashi, misali kamar ~angaren Ibadat ya }unshi abin da ya shafi tsarki Sallah, Azumi, Zakka, Hajji da dai sauransu. Kuma kowanne cikin wa]annan da aka ambata yana da rassa masu yawa a cikinsa. Misali tsarki, akwai maganar ruwa da hukunce-hukuncensa, Alwala, Taimama, Wanka da dai makamantansu.

Misali kuma na Salla, akwai hukunce-hukuncenta, nau’in Salla daban-daban da hukunce-hukuncensu, kamar Sallar Matafiyi, Sallar Ramuwa, Sallar Juma’a, Sallar Idi, Sallar Kusufi na rana da wata da wasu ayoyi, da dai sauran Salloli da suka zo }ar}ashin Salla. To haka nan Azumi, Zakka da Hajji. Duk akwai wa]annan hukunce-hukuncen da kuma rassansu.

|angare na biyu na Fi}hu shi ne Mu’amalat, shi ma a dun}ule, amma a warware ya }unshi cinikayya, auratayya, rabon gado da wa]annan da aka ambata da ma wa]anda ba a ambata ba. Yana da rassa masu yawa, shi ya sa fannin Fikihu kamar yadda aka ambata a baya cewa fanni ne mai fa]in gaske mai yalwa.

Gabatar da Darasin Fikihu yana da usulubi guda biyu. Usulubi na farko shi ne gabatar da shi a kan asasin fatawar wani Mujtahidi daga cikin Mujtahidai ba tare da an kawo na wasu Mujtahidan ba. Misali a nan shi ne Risala ta Imam Khumaini, wato Tahriril Wasila, wanda baki ]aya fatawowin da ke ciki, fatawowi ne na Imam Khumaini. da dai sauran  Risaloli na wasu Mujtahidai. Wannan bai ta}aita ga Fi}ihu na Madrasah ]in Ahlul Baiti (AS) ba, har da na Madrasah ]in Ahlus Sunna. Misali na Malikiyya,Shafi’iyya, Hanafiyya, da kuma Hambaliyya.

Usulubi na biyu na gabatar da darasin Fi}hu shi ne gabatar da shi ta usulubin Mu}arana na fatawoyin Mujtahidai daban-dabn. Wannan mu}arana na fatawowin Mujtahidai zai iya kasancewa dukkansu ’yan makaranta guda ne; misali a ce Mujtahidan dukkansu, ’yan Imamiyya ne, ko kuma Mujtahidai na makarantu ne guda biyu; wato Shi’a da Sunna. Irin wannan Usulubi shi ake ce wa FI{HUL- MU{ARAN.

Insha Allah a wannan darasi na Fikihu da za a ri}a gabatarwa lokaci bayan lokaci zai kasance ta wannan usulubin ne, wato Usulubin Fi}ihul Mu}arana, kuma saboda muhimmanci na Fi}ihul Mu}arana, Malamai na wannan fanni na Fi}hu na wa]annan makarantu guda biyu sun yi littafai masu yawa a kai. Ga misalai na littafai uku-uku na kowannen su a Madrasah ]in Ahlul Bait (AS). Akwai; 1. Al-Fi}ihu alal Mazahibil Khamsah. 2. Kitabul Khilaf na Shaikh [usiy. 3. Durusun Fil Fi}hil Mu}arin na Ayyatullahi Shaikh Jannaty.

A Madrasah ]in Ahlus Sunnah akwai; 1. Al-Fi}hu alal Mazahibil Arba’ah. 2. Bidayatul Mujtahidi wa Nihayatul Mu}tasid na Ibn Rushd. 3. {awaninul-Fi}hiyyah na Ibn Juzayyi da dai sauran littafai na Fi}ihul Mu}arana na Shi’a da Sunna, wa]anda ba za a yi kowa su ba saboda gudun tsawaitawa.

Tun da wannan usulubin za a bi wajen gabatar da wannan darasi na Fi}ihu, wato na shi Fi}ihul Mu}arana, akwai bu}atar bayanin:

1. Menene ma’anarsa?

2. Menene bambancinsa da ilimin Fikihu?

3. Menene maudu’insa?

4. Menene fa’idojinsa?

5. Menene yake sabbaba bambance-bambancensa a tsakanin Mazhabobi?

1. Menene ma’anarsa? Ma’anar Fi}ihun Mu}arana shi ne jam’i tsakanin fatawowi daban-daban wa]anda suka gangaro daga Limaman Mazhabobi ko Mujtahidai ba tare da gudanar da muwazana ba. Wato ta hanyar bincike a kan hujjar fatawar ko rinjayar da wata a kan wata.

2. Menene bambancinsa da ilimin Fikihu? Bambanci tsakaninsu shi ne, shi Fikihu Mu}aran yana koyar da mutum fatawowi daban-daban na Mujtahidai da suka shafi babobin Fikihu, misali kamar babin Alwala, da mutum zai duba zai ga an kawo yadda a Ja’afariyya, Malikiyya, Shafi’iyya, Hanafiyya da kuma Hambaliyya,  za a yi ta. Wani lokaci ma tare da bayani na dalilai ko masadir da kowacce Mazhaba ta yi amfani da shi wajen gina hukuncin. Shi ko Fi}ihu zai koyar da mutum fatawar Mujtahidi guda ]aya, ba tare da bijiro da na wa]ansu Mujtahidai ba.

3. Menene maudu’in Fi}ihu mu}arana? Kamar yadda aka ambata a baya cewa fannin ilimin Fi}ihu, yana da manyan ~angarori guda biyu; ~angaren Ibadat da kuma ~angaren Mu’amalat. Saboda haka maudu’in Fi}ihul Mu}arana shi ne bijiro da fatawowin Mujtahidai daban-daban a wa]annan ~angarori na Ibadata da kuma Mu’amalat, tare da gudanar da muwazana tsakaninsu, ko kuma ba tare da yin haka ba.

4. Menene fa’idodin Fi}ihul Mu}arana? Yana da fa’idodi da kuma amfani masu yawan gaske, ga guda uku daga ciki.

Na Farko, sanin sa zai taimaka wa mutum wajen fa]a]a masa fahimta da ilimi, ta yadda ko da ya samu kansa a wani waje daban, ba zai jahilci abin da ya ga ]an uwansa Musulmi ke aikatawa ba. Misali a ce ya samu kansa a aikin hajji, wanda mutum zai ha]u da Musulmi, wa]anda suka fito daga }asashe daban-daban na duniya, suke kuma a kan Mazhabobi daban-daban.

Na biyu, sanin Fi}ihul Mu}arana zai taimaka wa mutum wurin rage ko kuma kashe ta’asubanci na Mazhaba, wanda galibi yake haifar da gaba da kuma }iyayya tsakanin Musulmi. Wani lokaci ma har yakan kai ga fa]ace-fa]ace wanda yake haifar da asarar rayuka da kuma dukiyoyi.

Na uku, sanin Fi}ihul Mu}arana zai taimaka wajen fahimtar juna da kuma ha]in kai tsakanin Musulmi, ta yadda duk lokacin da Musulmi ya ga ]an uwansa Musulmi yana aikata wani abu na Ibadat ko Mu’amalat sa~anin shi yadda ya sani ko yake aikatawa, sai ya fahimci, to wannan ]an Mazhaba kaza ne. Sa~anin ko in bai da wannan ilimi na Fi}ihul Mu}arana }ila ya yi tunanin wannan ma ba addini yake yi ba, ko kuma ya yi tunanin wannan ya jahilci addini.

5. Menene yake sabbaba bambance-bambance tsakanin mazhabobinmu na Fikihu? Sanin wannan wani abu ne yake da gayar muhimmaci, saboda ma muhimmancinsa akwai Malamai da suka rubuta littattafai a kai. Misali akwai littafi da wani Malami ya rubuta mai suna ASBABU IKHTILAFIL FU{AHA.

Haka nan idan mutum ya duba a cikin littafin BIDAYATUL MUJTAHID WA NIHAYATUL MU{TASID, a mu}addimar littafin zai ga ya kawo sabubba guda shida. A ta}aice dai ga mai bu}ata yana iya komawa ga wa]annan littattafai da aka ambata, ko kuma ya koma zuwa ga littattafan Usul-Fikihu wanda shi ma Malamai na wa]annan makarantu guda biyu duka sun yi littattafai a kai. Amma a nan saboda gudun tsawaitawa, za a kawo sabubba guda uku ne.

Na farko, wani lokaci bambancin yakan kasance daga masadir ]in da shi Fi}ihun ko Mujtahidi ya yi amafani da su, wajen istimba]in hukunci, wato tsamo hukunci ko gina fatawa. Wa]annan masadir ]in sukan bambanta daga makaranta zuwa makaranta. Wato Madrasah ]in Ahlul Baiti da kuma Madrasah ]in Ahlus Sunnah.Akwai wa]anda Ahlus-sunnah suke amfani da su wajen gina hukunci, amma a Madrasah ]in Ahlul Baiti (AS) ba a amfani da su,misali }iyas, istihsan, masalihil-mursala da dai makamantansu na Usulul-Istinba] na Ahlus Sunnah. (Sai dai nan a yi min afuwa, kalmomin da aka kawo is]ilahohi ne na fannin Usul-Fikh, wanda ba zai yiwu a yi bayaninsu ba, saboda ba muhallin hakan ba ne).

Na biyu, wani lokaci bambancin yakan kasance daga yadda Fa}ihi ko Mujtahidi ya fahimci Aya ko Hadisi. A kan wannan fahimta tasa, sai ya gina hukunci a kai, Wato fatawar sa. wadda sa~anin haka kuma }ila shi wani Fa}ihin ko Mujtahidin ba haka ya fahimci Ayar ko Hadisin ba. A kan asasin haka sai ka ga an samu bambanci a fatawowi. Misali wannan Mujtahidin ya ce ya halatta, wani kuma ya ce bai halatta ba, da dai makamantansu na sa~ani.

Na uku, wani lokacin bambancin yakan kasance ne a kan asasin wani Mujtahidin ya ga Hadisin da ya gina fatawarsa a kai, wani Mujtahidin kuma shi bai ga Hadisin ba. Domin su Hadisai ba kamar Ayoyin Al}ur’ani ba ne. Misali mutum zai iya cewa duk Ayoyin Al}ur’ani ya san su, amma ba zai iya cewa duk Hadisai ya san su ba. Shi ya sa ire-iren fatawowi da Mujtahidi bai ga Hadisin da zai gina hukunci a kai ba, yakan gina su ne a kan Ihtiyat. Kuma shi Ihtiyat kamar yadda aka sani akwai wujubiy da istihbabiy. Bayaninsu yana Risala Amaliyyah na Fu}aha. Wannan ke nan a ta}aice dangane da Asbab da suke haifar da sa~ani a fatawowin Fu}aha ko Mujtahidai, kamar yadda aka ambata cewa za a bi Usulubin Fi}hul Mu}arana ne wajen gabatar da shi wannan darasi na Fi}hu. Saboda haka nan za a dinga amfani da littattafai guda biyu ne wajen gudanar da darasin. litattafan sune;

1. ALFI{IHU ALAL MAZAHIBIL KHAMSAH. 2. DURUSUN FIL FI{IHIL MU{ARAN, wanda wa]annan littafai, a duka babubbuka na Fi}ihu sun kakkwo wa]annan fitattun Mazhabobi na Fi}ihu guda biyar, wato Ja’afariyya, Malikiyya, Shafi’iyya, Hannafiyya da kuma Hambaliyya. Baya ga wa]annan Mazhabobi fitattu sun ma kawo wasu Mazhabobin da ba su yi fice ba sosai. Sai dai tambihi a nan shi ne; duk da za a kawo Fi}ihu na wa]annan Mazhabobi za a }arfafa ne kan Fi}ihun Ja’afariyya a darussan, wato fiye da sauran Mazhabobin.

Insha Allah za a ]ora nan gaba a wannan shimfi]a da gabatarwa kafin shiga cikin darasin.

 

Last Updated on Tuesday, 29 October 2013 19:38