Friday, 29 March 2024
Email
Make My Homepage
RSS
Register
Bayani kan Azumi 2. Print E-mail
Written by administrator   
Friday, 06 September 2013 03:35

Kamar yadda ya gabata a darasin baya a wannan babi na Azumi, wasu fasaloli guda hu]u. Yanzu za a tashi a fasali na biyar. Bayani dangane da wanda ya yi abin da yake karya Azumi. a darasin da ya gabata a fasali na hu]u, in za a duba, an kawo abubuwa guda 10, wanda ya wajaba mai Azumi ya kame daga gare su. To shi wannan fasali na biyar, yana bayani dangane da hukuncin mai Azumin da ya aikata ]aya daga cikin wa]annan ababe guda 10, ko kuma wasu daga cikinsu.

A cikin littafin Tahrirul Wasila na Imam Khumaini ({S), yana cewa aikata abubuwan da aka ambata guda 10, kamar yadda yake wajabtar da ramuwar Azumi, to haka nan kuma yana wajabtar da kaffara. In an aikata su da gangan da kuma za~i, wato ba a kan tilas ba. Amma a cikin goman, Imam Khumaini ({S) ya fitar da amai da gangan daga ciki. Ya ce shi bai wajabtar da kaffara. To a cikin wa]annan abubuwa guda 10, inda mutum zai aikata wani daga cikinsu, a kan asasin mantuwa, wato ba da gangan ba, misali yana Azumi, sai ya manta ya ci abinci ko ya sha abin sha. To a Imamiyya da Hanafiyya da Shafi'iyya da kuma Hambaliyya, babu komai a kansa, wato ba zai yi ramuwa ba, ko kuma kaffara. Amma a Malikiyya zai rama Azumin. Akwai kuma wasu abubuwa idan mutum ya aikata su, abin da ya wajaba a kansa shi ne rama Azumin, ban da kaffara. Sune:-

1- Idan mutum ya ci abinci a kan asasin dogaro da fa]in mai fa]i cewa akwai sauran dare, sai ta bayyana masa daga baya ashe Al-fijir ya keto. To abin da ya hau kansa a nan shi ne rama Azumin, bayan watan Ramadan.

2- Idan mutum ya ci abinci a kan asasin dogaro da fa]in mai fa]i cewa, Al-fijir ya keto, sai ya ci gaba da cin abinci da tunanin wasa yake yi masa ko kuma isgili, sai daga baya ta bayyana masa, ashe da gaske ne Al-fijir ya keto. To nan shi ma ramuwa zai yi.

3- Yin bu]a baki a kan asasin dogaro da fa]in mai fa]i cewa dare ya shiga, wato lokacin bu]a baki ya yi, sai daga baya ta bayyana masa ashe lokacin bu]a bakin bai yi ba. To a nan shi ma ramuwa ne mutum zai yi, amma da shara]in, shi wanda ya fa]i maganar, irin wanda ake dogara da maganarsa ne. In ko ba haka ba, wato wanda ba a dogaro da maganarsa ne, a nan Imam Khumaini ({S) ya ce kaffara da ramuwa sun hau kansa.

4- Idan mutum ya yi bu]e baki da ya}inin cewa dare ya shiga, saboda yanayi na duhu, sai daga baya ta bayyana masa ashe lokacin bu]e baki bai yi ba. To a nan ramuwa ce zai yi. Amma fa sai idan babu wata illa a sama. Misali hadari, hazo, girgije da dai sauransu. Amma idan akwai illa a sama, sai ta bayyana masa daga baya ashe kuskure ne. To a nan ko ramuwa ma ba ta wajaba masa ba.

5- Idan mutum ya yi abin da yake karya Azumi, misali ya ci abinci, gabanin ya bincika cewa Al-fijir ya keto, ko bai keto ba, sai ta bayyana masa ashe ya keto alhali yana da ikon bincikawa ]in, to shi ma zai yi ramuwa.

6- Idan mutum ya manta da wankan janaba a watan Ramadan, sai bayan kwana ]aya, ko kwanaki sai ya tuna. To a nan zai rama Azumin kwana ]aya ko kwanakin ne.

7- Idan mutum ya sa ruwa a bakinsa domin samun sanyi ta hanyar kuskurar baki, ko makamancin haka, sai ruwan ya wuce ma}ogoronsa. To shi ma nan ramuwar Azumi zai yi. Amma da a ce da ya sa ruwan a bakinsa, sai ya manta ya ha]iye. To ko ramuwa babu a kansa. Haka nan yana kuskurar baki a wajen alwala, sai ruwan ya wuce ba da nufi ba, shi ma wannan ba ramuwa kansa, kamar yadda Imam Khumaini ({S) ya yi bayani. Wannan ke nan dangane da fasali na biyar.

6- Bayani dangane da sharu]]an ingancin Azumi, da kuma wajibcinsa. Sharru]]an ingancin Azumi sune. 1- Musulunci, wato dole ya kasance Musulmi. Domin Azumi bai inganta ga kafiri. Saboda haka da Musulmi yana Azumi sai ya yi ridda (wal iyazubillah), to Azuminsa ya lalace ko da ya dawo daga riddar a ranar, wato kafin bu]e baki. Duk da haka Azuminsa bai inganta ba.

2- Balaga, Azumi bai wajaba ba ga wanda ba baligi ba. Amma wanda ba baligi ba, in ya yi Azumi ya inganta daga gare shi. Kuma za a ba shi lada a kai.

3- Hankali, Azumi bai wajaba ba ga mahaukaci. In kuma ya yi Azumin, to bai inganta ba. Haka nan Azumi bai inganta ba ga wanda ya suma ko ya bugu da maye. To da a ce mutum na Azumi sai ya suma, to in ya farfa]o daga baya zai iya ci gaba da Azuminsa. In ko har lokacin bu]e baki ya yi bai farfa]o ba, to zai yi ramuwa ne.

4-  Tsarki daga jinin haila ko nifasi. Shara]i ne na ingancin Azumin mace ya zamanto tana da tsarki na haila da nifasi. Saboda haka Azumin mai haila ko nifas bai inganta ba. Ko da a ce tana Azumi sai gab da za a yi bu]e baki jinin haila ya zo mata, to Azumin ranar bai inganta ba. Ko kuma jinin hailar ya yanka mata bayan ketowar Al-fijir da ka]an, duk da haka Azumin ranar ba zai inganta mata ba.

5- Rashin Tafiya. Yana daga cikin ingancin Azumi mutum ya kasance ba matafayi ba, tafiyar da take wajabtar da Sallar }asaru. Kuma wannan haka hukuncin yake ko da a Azumin nafila ne. Amma akwai wurare uku inda matafiyi zai iya yin Azumi. [aya daga ciki shi ne Azumin da aka yi alwashi. kuma an shar]anta ingancin Azumin nafila, ya kasance ba ramuwar Azumin wajibi a kansa. Misali a ce bayan watan Ramadan akwai Azumin ramuwa a kan mutum, To ba zai yi Azumin shida na Shawwal ]in nan ba na nafila. Sai bayan ya rama Azumin da ake bin sa na wajibi.

5- Rashin Lafiya. Yana daga cikin sharu]]an ingancin Azumi ya kasance mutum bai da rashin lafiya. Amma a nan a lura, ba kowace rashin lafiya ba. Ana nufin rashin lafiya mai tsanani, wanda in da a ce mutum zai yi Azumin, to zai iya }aro masa tsananin ciwon ko jinkirtuwar warkewarsa, ko kuma ma ya haifar masa da wani ciwon.

7- Yana daga cikin sharu]]an ingancin Azumi, ya kasance mutum bai da wani uzuri na barin Azumin. Da yake a shari'a akwai wa]anda aka yi masu rukhsa (sau}i) daga yin Azumi. Sai dai su yi kaffara ta ciyarwa. Sune: Dattijo da Dattijiwa, wato wa]anda suka tsufa sosai, wanda inda za su yi Azumi zai kasance ya tsananta ko wuyata gare su. Haka nan wanda yake da ciwon }ishi, wato wanda yin Azumin zai wuyata gare shi. Haka nan da mace mai ciki wadda ta kusan haihuwa, wanda inda za ta ce ta yi Azumin, to zai cutar da ita, ko abin da yake cikinta. Haka nan mace mai shayarwa wadda take da nonon shayarwa ka]an, wanda inda za ta ce ta yi Azumin, to zai cutar da ita ko ]an nata. Dukkan wa]annan da aka ambata, an halatta masu cin abinci. Sai dai tambihi a nan shi ne, wajibi ne ga mai cikin da kuma mai shayarwa daga baya su rama Azumin da suka sha.

Haka nan Imam Khumaini ({S) ya ce ihtiya]i ne, ga Dattijo ko Dattijiwa ko mai ciwon }ishi, in sun samu iko daga baya, wato za su iya yin Azumin. Su ma su rama Azumin, sai dai a lura a nan wannan ihtiya]i da Imam Khumaini ({S) ya ce, ihtiya]i ne istihbabi. Saboda haka ko da ba su rama ]in ba, wato su Dattawan ko mai ciwon kishin, in sun sami ikon daga baya, to ba matsala. Wannan ke nan a ta}aice dangane da fasali na shida.

7- Bayani dangane da ramakon Azumi watan Ramadan:- Ba wajibi ne ga yaro ya rama Azumin da ya sha zamanin yarintarsa ba. Haka nan mahaukaci wanda ya sha a zamanin ciwon haukarsa. Haka nan kafirin da ya musulunta, ba zai rama abin da ya sha ba na zamanin kafircinsa ba. Amma da a ce mutum shi Musulmi ne sai ya yi ridda, bayan wani lokaci ko shekaru, sai ya dawo Musulunci. To a nan duk Azuman da ya sha, wajibi ne ya biya. Ba wajibi ba ne gaggauta ramakon Azumin. Sai dai kuma bai halatta a jinkirta shi ba har wani Ramadan ya zo ba. Haka nan ba wajibi ba ne yin tartibi a ramakon Azumi, wato yin su biye da juna. Saboda haka da a ce yana da ramakon Azumin na kwanaki, zai yi niyyar ramakon kwanakin ne, ba wai ya tsaya ya duba ya ga cewa misali na wacce rana ya soma sha, haka-haka. A'a zai rama adadin kwanakin ne kawai. Haka hukuncin yake da a ce Azumin Ramadan biyu ne a kansa ko sama da haka, inda hukuncin yake canzawa shi ne, da a ce akwai Azumin ramuwa na Ramadan guda biyu a kansa, sai bai rama ba har wani Ramadan ]in ya zo, kuma lokacin da ya rage ba zai isa ya yi Azumin watan Ramadanonin ba, to a nan zai rama Azumin shekarar bara ne, na ]aya shekarar kuma daga baya sai ya rama. Haka nan kuma da a ce Azumin watan Ramadan zai ku~uce masa ko wasu kwanuka daga ciki saboda wani uzuri, kuma uzurin sai ya kasance bai gushe ba, har wani Ramadan ]in ya zagayo. To hukunci a nan shi ne idan uzurin rashin lafiya ne. To a nan ramuwa ta fa]i a kansa, abin da ya hau kansa shi ne kaffara, wato ba da mudun abinci kowace rana, bayani kan mudin zai zo a fasali na gaba insha Allah.

To, amma da a ce uzurin ba rashin lafiya ba ne, misali tafiya ne da makamantansu. To a nan abin da ya wajaba a kansa shi ne ramuwa kawai. Haka nan ma ramuwa kawai zai yi idan ya kasance abin da ya janyo ku~ucewar Azumin rashin lafiya ne. Amma abin da ya jirkintar da ramuwar, wani uzuri ne daban. To da a ce Azumin watan Ramadan ya ku~uce wa mutum da gangan ko kuma saboda wani uzurin, amma sai uzurin bai ci gaba ba, kuma wani uzurin bai gitto ba. Mutum ya yi sakaci a haka, har wani Ramadan ]in ya zo, to a nan baya ga ramuwar da zai yi, sai ya yi kaffara ta wannan sakaci da ya yi. In ko Azumin da ya sha ba a kan asasin uzurin ba ne, a'a da gangan ne, to a nan abin da ya hau kansa, baya ga ramuwar Azumin, akwai kaffara guda biyu, kaffara ta farko ta shan Azumi da gangan. Kaffara ta biyu ta jinkirin ramuwa. Ya halatta mutum ya karya Azumin ramuwar Ramadan gabanin Zawal, amma da shara]in lokaci bai }ure ba. Misali mutum ana bin sa Azumi biyar, kuma yanzu saura kwana biyar a fara Azumi. To a irin wannan yanayin bai halatta mutum ya karya Azumin ramuwar ba. To, amma da a ce bayan Zawal ne a nan mai Azumin ramuwa, haramun ne a gare shi ya karya Azumin. In ko ya karya, to akwai wata nau'in kaffara da ta hau kansa, ita ce zai ciyar da miskinai 10, kowane miskini zai ba shi mudu ]aya. In ko bai da ikon ciyarwa. To zai yi Azumin kwana uku.

Wani tambihi a nan shi ne, shi wannan mai Azumin ramuwa da ya karya, to ba wajibi ba ne ya kame bakinsa ba a sauran yinin, wato ma'ana zai iya ci gaba da cin abinci. Sai dai kuma ya ja wa kansa irin wannan kaffara da aka ambata.

Mas'ala ta }arshen wannan fasali, ita ce Azumi kamar Salla yake, wato na cewa kamar yadda ya wajaba ga babban ]a namiji na uba, ]an ya biya masa Sallar da ke kansa, to haka shi ma Azumi wajibi ne ya rama masa Azumin da ke kansa in akwai. Wannan ke nan a ta}aice dangane da fasali na bakwai.

8- Bayani dangane da kaffara da kuma fidya, kaffara tana da nau'o'i daban-daban. Misali akwai kaffarar kisan kuskure, kaffarar rantsuwa, kaffarar zihari, kaffarar karya Azumin watan Ramadan da dai sauransu, wanda bayanan su, ya zo a wasu babobi na Fi}hu. Abin da yake da ala}a da wannan fasali shi ne kaffarar karya Azumin watan Ramadan, da kuma yadda ake yin kaffarar. Da yake kaffarorin da suke da ala}a da Azumin Ramadan suna da yawa.Saboda haka a nan za a ambaci wasu daga ciki ne. kamar yadda aka ambata a baya, wanda ya aikata abubuwan nan guda goma da suke karya Azumi da gangan, to ramuwa da kaffara ya hau kan mutum.

Yadda ake kaffara shi ne mutum zai yi ]ayan abu uku. 1- 'Yan’ta bawa. 2- Yin Azumi wata biyu biye da juna. 3- Ciyar da miskinai 60. Da yake yanzu babu bayi, za~in da mutum yake da shi ]ayan biyu ne; ko dai ya yi Azumn, ko kuma ya ciyar da miskinai. Amma a nan Imam Khumaini ({S) ya ce ihtiya]i istihbahi, shi ne in ba zai iya ba ne, sai ya ciyar. Amma da a ce wannan Azumi da ya karya da gangan, ya karya shi ne da abin da yake haramun ne, misali giya, ko ya sato abu ya ci, da dai makamantansu. To a nan kaffarar da zai yi a na ce mata 'kaffaratul-jam'i'. Wato abubuwan nan guda uku da aka ambata, duka sai ya yi su. Zai 'yanta bawa, Azumi 60, ciyar da miskinai 60.

Wata mas'ala kuma ita ce da a ce mutum zai sadu da matarsa a watan Ramadan alhali suna Azimi. To idan matar ta biye masa, to kowannensu kaffara da ta'azir ya hau kansu. Ta'azir Imam Khumaini ya yi bayani cewa, kowannen su za a yi masa bulala 25, in ko ba ta biye masa ba, ya tilastata ne, to a nan zai yi kaffara biyu ne. Nasa da kuma nata. Sannan kuma za a yi mai ta'azir guda biyu nasa da nata. Wato bulala 50 ke nan.

To tambaya a nan ya ake kaffarar ciyarwa? Yadda ake yi shi ne ciyar da su miskinai ]in, imma ta }osar da su, wato kowanne ka ba shi abinci ya ci ya }oshi, ko kuma kowannensu ka ba shi mudu na shinkafa ko masara ko gero da dai sauransu.

Mudu a nan shi ne wanda mutanenmu suke cewa Mudin-nabiy, wato ba ana nufin mudu na kasuwa ba. Shi Mudin-nabiy yana daidai da ¾ na kilo. Wato in ka kasa kilo kashi 100, to 75 ]insa shi ne Mudin-nabiy ]aya. In mutum zai ciyar ta hanyar ba da mudun abubuwan da aka ambata a sama na hatsi ne. To Imam Khumaini ({S) ya ce ihtiya]i istihbabi, mutum ya ba da Mudun-nabiy biyu-biyu, wato maimakon ]aya, in ko kaffarar ta Azumi ce zai yi, wato Azumi 60 biye da juna. To a nan akwai sa~ani tsakanin Imamiyya da sauran mazahib na Ahlus Sunnah wajen wannan kalma ta biye da juna. Wato a Imamiyya ya wadatar wajen yin sa, shi Azumi 60 ]in, biye da juna. Idan mutum ya yi Azumin wata ]aya, ya yi kuma Azumi ]aya a wata na biyun. To sauran yana da za~i, wato ya halatta masa ya yi su  a rarrabe. Wato in dai ya samu kwana 31 a jere yana Azumi, to sauran 29 yana da za~i, ko dai ya ci gaba da yin su a jere, ko kuma ya rarraba. Amma su a mazahib na Ahlus Sunnah dole ne ya yi su 60 a jere.

Sai kuma kaffarar wa]anda aka yi masu rukhsa daga yin Azumi, wato mai ciwon }ishi da kuma tsofaffin da ba su iya yin kaffarar ita ce, a wani wajen ana ce mata fidiya. Shi ne Mudin-nabiy ]aya kowace rana, na abin da ya za~a ya bayar. Wannan ke nan a ta}aice dangane da fasali na takwas.

9- Bayani dangane da hukunce-hukuncen Azumin matafayi. A nan ma akwai sa~ani tsakanin Imamiyya da sauran mazahib na Ahlus Sunna. A mazahib na Ahlus Sunna in mutum ya yi Azumi a tafiya, Azumi na wajibi ne ko nafila. To Azuminsa ya yi. Wato wannan mas'ala ta Azumi a tafiya, su a wajensu rukhsa ce, ba Azima ba.

A Imamiyya idan mutum yana zaune a inda yake, to sai zai yi tafiya. In tafiyar gabanin Zawal ne, to wajibi ne ya aje Azumi. In kuma bayan Zawal ne zai yi tafiyar, to wajibi ya wanzu a kan Azuminsa.

Haka nan da zai kasance a tafiyar, sai ya dawo garin da yake, ko kuma garin da ya yanke zai yi kwana 10, in gabanin zawal ne ya iso, kuma bai yi wani abu da yake karya Azumi ba. To a nan Azumi ya wajaba a kansa. In ko bayan Zawal ya iso, ko gabanin Zawal, amma ya yi wani abu da yake karya Azumi, misali ya ci abinci. To a nan ba wajibcin Azumi a kansa. Haka nan kuma kamar yadda yake a Sallar }asaru, mutum ba zai soma yin ta ba tun daga gida, in zai yi tafiya, sai ya isa inda ake soma yin ta, wato 'haddu-tarakkus'. To haka nan hukuncin yake ga Azumi, wato ga wanda yake zai yi tafiya ne gabanin Zawal, a nan ba zai soma cin abinci daga gidansa ba ne, sai ya kai inda ake soma }asaru, wato haddu-tarakkus. In ko ya ci abinci daga gidansa, to ramuwa da kaffara sun hau kansa. A bisa ihtiya]i wujubiy, kamar yadda Imam Khumaini ({S) ya yi bayani.

Haka nan makaruhi ne ga matafiyi a watan Ramadan dama dukkan wanda ya halatta ya ci abinci a watan Ramadan ]in, kamar masu uzurori da su yawaita cin abinci ko abin sha. Wato ko da mutum na da uzuri na rashin yin Azumi, to makuhi ne gare shi ba haramun ba, ya yawaita cin abinci ko abin sha. Wato ana so ya ta}aita su saboda girmama watan Ramadan. Da yake wata ne mai daraja, kuma shi ne Shugaban watanni. Wannan ke nan a ta}aice dangane da fasali na tara.

 

Sai dai wani tambihi a nan shi ne; a Imamiyya wa]anda suke tafiya ita ce aikinsu, wato sana'arsa, kamar mai tu}in mota, ko tu}in jirgin sama, ko na }asa, ko na ruwa da dai makamantansu. To su hukuncinsu shi ne za su cika Salla, za su kuma yi Azumi, wato a irin wannan tafiye-tafiye nasu. To haka nan hukuncin yake ga wanda yake tafiya mu}addima ne ga aikinsa. Misali yana zaune a gari kaza, kuma yana aiki a gari kaza. To in dai a duk kwana 10 ya kan je aikin a}alla sau ]aya, to zai cika Salla kuma zai yi Azumi. Haka nan mai yawon tijara na kasuwanci, wato mai tafiya daga wannan gari zuwa wancan garin, shi ma zai cika Salla, kuma zai yi Azumi.

Last Updated on Tuesday, 29 October 2013 19:38
 
Home Darusan Fiqh Bayani kan Azumi 2.
Copyright © 2024. www.tambihin.net. Designed by KH