Thursday, 18 April 2024
Email
Make My Homepage
RSS
Register
Bayani kan fannin ilimin Akhla{. Print E-mail
Written by administrator   
Friday, 06 September 2013 03:13

Akhla} ~angare ne na ilimin irfani,wato misali kamar  yadda ilimin fi}hu,yake da manyan ~angarori guda biyu,wato Ibadat da Mu’amalat, ilimin A}a’id  kuma yake da manyan ~angarori guda biyar,Tauhid,Adl,Nubuwwa,Imama da kuma Ma’ad,to shima ilimin  irfani yana da manyan ~angarori guda biyu,sune AKHLA{,wanda wani lokaci ake cewa IRFANIL-AMALIY,da kuma MA’ARIFA,wanda ake cewa IRFANIN-NAZARIY.                                                                                                                                            Wannan janibi na akhla} wasila ne,wato tsanine zuwa ga ma’arifa,wato sanin Allah[T] akan asasin zau}i ko shu’uri,wato mutum da farko ya samu tsarkakuwa daga munanan ]abi’oi,bayan haka ya siffantu da kyawawan ]abi’oi,to wannan shine zai taimaka wa mutum ko kuma samun hanya wajen ala}antuwa da Allah [T] da kuma damfaruwa da shi.Akan wannan  asasin ne insha Allah, za’a soma gabatar da darussa akan Akhla}.Wanda }ila zai iya ]aukan lokaci ana  gabatarwa.                                                Amma gabanin  shiga cikin shi wannan darasin na Akhla}, zai yi kyau da kuma muhimmanci yin bayani ko da a dun}ule dangane da illmin irfani.Ilimin irfani kamar yadda ake ce masa a madrasah ]inAhlul bait [AS].A madrasah ]in Ahlus  sunna, ana ce masa ilimin Tasawwuf,wannan ilimi na irfani,ilimi ne mai zaman kansa,wato yana da is]ila-hohinsa da littafan sa da kuma malaman sa.Alal misali ga wasu daga cikin fitattun malaman sa da suka kasance a wannan zamani.Ayatullah Bahjati,Ayatullah sayyid Ali Al-}adiy,Ayatullah sheikh Hasan Ali Al-isfahaniy,Ayatullah mirza Jawad malakiy  Attab-riziy da kuma Ayatullah Sayyid Abdul-Aa’la Assib-ziwary.Dukkan wa]annan malaman da aka ambata, bawai kawai malamai ne a fannin ba,a’a sun fitar da malamai masu yawan gaske a fannin ilimin irfani,wato urafa’u.Ban da malaman da suka yi fice, a wasu fannonin wanda in ka bincika tarihin rayuwar  su, za kaga sun yi fannin ilimin irfani a ]aya daga cikin wa]annan malaman.Misali anan shine ,Allama Taba-taba’I,wato wanda yayi tafsirin almizan,yayi karatun irfani ne awajen Ayatullah sayyid Aliy Al-}adiy,har ma yana yawan cewa wannan uslubin tafsirin sa daga Ayatullah }adiy ne.misali kuma,Imam khumaini yayi karatun ilimin irfani a wajen,Ayatullah Mirza Jawad Attab-riziy da dai sauran wasu malamai fitattu, a wannan zamanin da suka yi karatun irfani a wajensa.                                                                                                          insha Allah wani lokaci za’ayi rubutu dangane da wa]annan malaman  da aka ambata, domin sanin tarihin su da rayuwar su da karamomin su, da dai makamantan su.Haka nan shi ilimin irfani  ba wai kawai ilmi ne da yake cin gashin kansa bane.A’a ilimi ne da yake taimaka wasu fannoni ilimi wajen kamalar su.Alal misali  fannin  ilmin fi}ihu,zamu  ga  a fi}ihu an koyar da mutum yadda zai yi sallah.sharu]]an ta, da abubuwan dake ~atata,  amma abin da ya shafi ba]inin,ita salla ]in,wato ruhin ta,kamar khushu’i  aciki,halartar da zuciya acikin salla,ta’azimin Allah[T] da tsoronsa  aciki,to duk wa]annan dama wasun su, da ba’a ambata ba na ruhin sallah.shi ilimin irfani ne yake bayanin su,haka ma sauran ibadodi kamar su Azumi,Hajji da dai sauransu,ruhin wa]annan ayyukan,to ilimin irfani ne ke bayanin su.To kaga ke nan a nan ya taimaka wa ilimin fiqhu wajen kamalar sa, a dun}ule abin da ake nufi idan fiqhu yayi bayani dangane da zahirin wa]annan ayyuka na ibadodi,shi irfani sai ya kammala da bayani dangane da ba]ininsu.Haka nan kuma mu ]auki ilimin A}a’id,misali Tauhid,za kaga ya koyar da mutum sanin Allah[T] ta hanyar siffofin sa,sunayen sa, da dai makamantan su,Amma za kaga galibi wannan yakan tsaya wa mutum a matsayin ii’ti}adi,ga misali  guda ]aya, a tauhidi,za’a koyar da mutum Allah  mai jine,kuma mai gani ne.Amma samun zau}in shu’urin cewa Allah[T] na ganin mutum, kuma yana jinsa wanda wannan zai iya kai wa ga shamakance mutum daga sa~a wa Allah[T].To anan ilimin irfani ke taimakawa wajen samun haka.Kaga anan ya taimaka wa ilimin A}a’id, wajen samun kamalar sa.Wato in shi ya gina akan ii’ti}adi,shi kuma irfani sai ya gina yadda zaka samu zau}i da shu’urin wannan ii’ti}adin.To haka nan ma a Nubuwwa,wato shi irfani zai taimaka maka wajen kyautata ala}ar ka da Manzon Allah [S] a ba]inance,ba wai kawai a matsayin ilti}adi ba.Haka nan Ma’ad,yadda zaka dun ga shu’urin lahira  kamar kana ganinta.Bawai a matsayin ilti}adi ba.A ta}aice dai a nan samun wannan shu’uri da kuma zau}i, ya taimaka wa ilimin A}a’id, wajen kamalar sa.saboda haka kamar yadda aka ambata a baya cewa ilimin irfani, ilimi ne mai zaman kansa,kuma mai taimaka wa wasu fannonin ilimi domin kamalar su,

Manufa da kuma gayar wannan ilimi na irfani shine ya kai mutum matsayin insa-niyyah da kuma ubu-diyya.Abin da ake nufi da insa-niyyah anan shine, mutum ya zama insan[mutum] a ruhinsa,bawai hayawan ba,wato[dabba] ba, domin mutum zai iya zama a zahirinsa shi insan ne, amma a ba]ininsa ba insan bane, hayawan ne.To anan mutum zai fahimce yadda Imam khumaini a littafan daya rubuta dangane da irfani yana yawan magana akan mutum ya zama insan,har ma yakan ce zama insan yana da wahala.Akwai  ma wani waje a cikin littafinsa na jihadul Akbar, yana cewa zama malami yafi sau}i kan zama insan,wannan magana ce ta Arifai.wato mujahadar da mutum yake bu}ata wajen zama malami,bata kai mujahadar da mutum yake bu}ata wajen zama insan ba,wato mujahadar zama insan tafi wahala,insha Allah a darasin Akhla}, za’a ]an fa]a]a bayani dangane da zama insan a ruhi.Hadafi na biyu na ilimin irfani,wato kai wa ga matsayi na ubudiyyah,wato mutum ya zama Abd[bawa] na Allah[T],ba Abd na nafs ]insa ba ko kuma Abd na shai]an,kuma idan mutum ya kai wannan matsayin na ubudiyya,to ya kai matsayin da shai]an be da sul-]a akansa,kamar yadda Allah[T]  yake fa]i acikin littafinsa,wato yake cewa shai]an ‘’bayina  baka da sul-]a akansu’’,wannan kenan dai a ta}aice dangane da ma’anar ilimin irfani da abin daya }unsa da kuma hadafinsa.

Dawowa gashi darasin Akhla} ]in.Amma gabanin  shiga cikin darasin Akhla} ]in, zai yi kyau yin bayani dangane da muhimmancinsa da kuma hadisai da aka samo daga Manzon Allah[S] da kuma Ahlul bayt[AS] da suke nuni ga matsayinsa da kuma falalarsa.muhimmancin Akhla} bai ta}aita ga  mutum shi }ashin kansa ba,ko kuma rayuwarsa tsakanin mutane,a’a,hatta  dabba in  ka  kyautata  mata ko ka munana mata zai iya kasancewa sanadiyyar shiga mutum Aljannah ko wuta.Alal misali }issar wani mutum da yazo akan cewa yana jin }ishi sai yaje wata rijiya ya ]ebo ruwa ya sha,bayan yasha  sai ya juya  zai  tafi sai ga wani kare yazo yana lallagi na alamun }ishi,sai wannan mutum daya ga haka sai ya ]ebo ruwa a rijiyar ya baiwa  karen yasha.bayan wuce warsa, sai Allah[T]  ya yi wahayi ga Annabin   zamanin  cewa ya fa]a wa wannan mutumin,Allah ta’ala ya gafarta masa saboda wannan aiki da yayi, kuma zai shigar dashi Aljannarsa.Haka }issar wata mata  wadda ta kasance  tana da mage,amma sai ta ]aure magen bata ba ta abinci,ba ta kuma sake ta ba domin ta nemi abinda zata ciba.to bayan rasuwar matar,yazo akan cewa Allah[T]  ya saka ta a wuta.to mu duba wa]annan }issar da tazo a hadisan na mutanen  biyu,wannan sanadiyar  kyakkyawar  akhla}, ga kare ya shiga aljannah,ita kuma sanadiyyar mummunan  akhla} ga mage ta shiga wuta,idan wannan sakamakon  akhla} ya  kasance  ga dabba’ to ina  ga sakamakon Akhla}, kyakkyawa  ko mummuna  ga mutum ]an uwanka ,wannan ka]ai ya isa ya nuna muhimmancin Akhla}.

Kuma  ga  wanda yake ma’abocin addini,kyakkyawan Akhla} babbar  hanya ce  tayin da’awa,domin  tafi  yin  tasiri ga ruhin mutum,in mutum ya duba tarihin Manzon Allah[S] lokacin da ya soma da’awa a makka,da yawa sun musulunta ne sakamakon Akhla} ]in Manzon Allah[S].akwai misali da yawa,amma  ga  guda ]aya,yazo akan cewa lokacin da manzon Allah[S] yana makka,to hanyar da yake bi zuwa ka’aba, sai wani mutum ya ]aukar wa kansa  zuba }ayoyi a hanyar,in Manzon Allah[S] yazo wucewa sai ya kaudasu,wa she gari ya }ara sawa,Manzon Allah[S] ya kawar,haka yayi tayi har  lokaci mai tsawo,wata rana Manzon Allah[S] zai je ka’aba domin yayi da’awa, kamar yadda ya saba ,sai bai ga }ayoyin ba,kwana ]aya,kwana biyu haka,sai ya bincika  aka  ce masa ai bai da lafiya ne,shine Manzon Allah[S] ya tafi har gidansa da nufin ya gaishe shi,shine  daya isa gidan yake ce masa,Abin da nasaba  gani akan hanya  kwana biyu ban gani ba,sai na tambaya aka ce  baka da lafiya ne, shine na zo domin in gaishe ka,jin haka  mutumin nan take yayi kalmar shahada na shiga musulunci,mu duba yadda  kyakkyawar Akhla} ya canza shi,

 

Haka nan kyakkyawar Akhla}, yakan mai da ma}iyi ya zama masoyi,shima wannan akwai misali da yawa daga rayuwar Aimma na Ahlulbayt [AS],amma ga  guda uku,wata rana Imam Hasan[AS] yana  tafiya sai wani mutumin  sham ya ganshi,kawai sai ya kama zaginsa da kuma la’antarsa[Wa’iyazubillah].Da yake mutanen  sham haka aka ginasu,wato zagi da kuma la’antar Ahlulbayt [AS] musamman ma ga Imam Ali [AS],domin ta kai ga cewa a hu]ubar juma’a, liman ba zai }areta ba sai yayi wannan la’antar ga Imam Ali[AS] .Haka wannan mummunan  aikin  ya kasance  tsawon shekaru 70,zuwan umar ]an Abdul-aziz ya hana wannan la’antar,ya maye wajen wannan  la’antar da wata  aya,[ga mai son ganin ayar  ya duba cikin suratu-Nahal ayata 90,wato Inna-llaha-ya’amuru bil-adli…….]wanda har yanzu masu khutbah na juma’a, a duniyar sunna  zaka ji suna biya ta.shi yasa idan mutum ya dubi jawabin da sayyida Zainab [AS] tayi a kufa na wa}i’ar karbala,zai ga tana da bambanci akan wadda tayi a sham.Domin su mutanen kufa sun san Ahlulbait[AS] da matsayinsu,sa~anin mutanen sham,basu san Ahlulbayt [AS] ba,ballantana sanin matsayinsu.Mu dawo ga shi wannan mutumin da yayi zagi da la’anta ga Imam Hasan [AS],yana tayi,Imam Hasan [AS] bai ce masa komai ba sai da ya gama,Imam Hasan [AS] ya dube  shi, yayi murmushi yace ,ya kai wannan Dattijo! Ina tsammanin kai ba}o ne, ina  zaka je,in baka san wajen ba, ka fa]i akaika? In kuma ba inda zaka sauka  kazo a baka masauki,in kuma kana da bu}ata ka fa]i a biya maka.yace in ma zai yiwu kazo ka ba}uncemu mana,ka zauna wajenmu kafin ka koma sham.jin wa]annan kalmomi na Imam Hassan [AS] nan take, sai wannan mutumin ya fashe da kuka,sai yace wa Imam Hasan [AS],lallai na shaida kai khalifan Allah [T] ne a doron }asa,kai da babanka,ada  babu wanda nafi }i kamarku,amma yanzu kai kafi soyuwa gare ni akan kowa a duniyar  nan,yace wajenka nake so in sauka.Haka ya zauna wajen Imam Hasan [AS] har lokacin da zai koma sham.yazo akan cewa tun daga lokacin ya shiga cikin shi’a ]in Imam Hasan [AS].Na biyu yazo akan cewa wata rana Imam Zainul Abidin [AS] ya fito sai wani mutum ya bishi yana zaginsa,nan take mabiyansa da kuma bayinsa suka yun}ura zasu auka wa mutumin,sai Imam Zainul Abidin [AS]yace masu a’a,sai Imam Zainul Abidin [AS] ya dubi mutumin yace masa,Al-amarinmu ya ~oyu a gare ka,kana da wata bu}ata mu taimaka maka akai? Jin haka sai mutumin yaji kunya,Imam Zainul Abidin[AS]  ya mi}a masa abayarsa,yace kuma abashi Dirhami dubu,to tun daga lokacin duk in da yaga Imam Zainul Abidin [AS] sai yace lallai na shaida  kai ]an Manzon Allah[S] ne.Na uku yazo akan cewa akwai wani a madina,ya kasance yana cutar da Imam kazim [AS] gayar cutarwa,domin duk  in da yaga Imam kazim [AS] sai ya zage shi,ya zagi Imam Ali [AS],sai sahabbansa suka ce masa kabarmu mu kashe wannan fajirin mutumin,sai Imam kazim [AS] ya hana su,ya kuma tsawata akan haka gayar tsawatawa.sai wata rana Imam Kazim  [AS]  ya tambayi mutumin aka ce ya tafi gona,sai Imam Kazim [AS] ya bishi gonar da kansa,lokacin daya shiga gonar  da dabbar da yake kai,mutumin na  ganinsa,yace kada ka taka mani shuka cikin fushi,Imam Kazim [AS] yayi taka-tsantsan bai taka masa shukar  ba,har ya isa wajensa,sai Imam Kazim [AS] ya sauka daga kan dabbar yana jansa da maganan da kuma murmushi.Daga }arshe yace masa,nawa  ka kashe a wannan shukar  taka?yace dinari 100, yace to nawa kake tsammanin zaka samu in ka girbe?yace ni bansan gaibi ba.sai Imam Kazim [AS] yace masa,ai nace ne nawa kake tsanmani zaka samu,yace,to ina tsammanin dinari 200.Sai Imam Kazim [AS] ya mi}a masa jaka, acikinta akwai dinari 300, yace masa wannan shuka taka Allah yasa mata albarka,abinda kake tsammani zaka  samu na dinari 200 in ka girbe,Allah yasa haka.jin haka sai wannan mutumi ya sun baci Imam kazim [AS] yace masa ka yafe mani duk abinda nayi maka,sai Imam kazim [AS] yayi murmushi yace masa ba komai.sai ya juya ya tafi.Bayan haka  In da  Imam kazim [AS] yake zama a masallaci shi da sahabbansa,mutumin na komawa gida,sai yatafi masallaci ya zauna wajen,shine su sahabban Imam kazim [AS] da suka ganshi sukace masa kai ya akayi haka? Sai yace musu Allah [T] shine mafi sanin in da yake sa sa}onsa,Daga nan ya juya ya shiga addu’a, yana Allah ka saka wa Abul Hasan [AS][wannan kinaya ne na Imam Kazim] da alheri,to lokacin da Imam Kazim [AS] ya koma gida,sai yace ma wa]anda suka nemi damar ya basu izini su kashe shi, baku ga yadda na gyara al-amarinsa ba,kuma na tsaru daga sharrinsa,ga mai bu}atar ganin wa]annan }issoshi dama }ari yana iya duba littafi mai suna A’IMMATUNA,mu duba yadda wa]annan kyawawan Akhla} na Imaman da aka ambata suka canza ma}iya suka koma masoya.

Last Updated on Tuesday, 29 October 2013 19:26
 
Home Darusan Akhlaq Bayani kan fannin ilimin Akhla{.
Copyright © 2024. www.tambihin.net. Designed by KH