Jarabawowin da Imam Hassan (AS) Ya fuskanta musamman lokacin da Imamanci ya dawo kansa Muddan imamacinsa shekaru goma ne wato daga shekara ta 40 bayan Hijira zuwa shekara ta 50 bayan Hijira. To Jarabawowin na kowane Imami, ana maganar jarabawowin da ya fuskanta a muddan imamancinsa ko khalifancinsa saboda mu wajenmu ko wane imami a zamanin muddan imamancinsa shine khalifan Manzon Allah, mutane sun yarda ko basu yarda ba to haka yake a wajen Allah Ta’ala da kuma bayinsa Mu'uminai. Idan mutum ya bibiyi Tarihi zai ga cewa wannan mudda ta shekaru goma da Imam Hassan ya yi a Imamancinsa ya fuskanci jarabawowi masu yawa wanda saboda irin wadannan jarabawowi da ya fuskanta tasa har ya yi sulhu da Mu'awiya kamar yadda zamu ga haka nan gaba insha Allah. Da farko bayan shahadar Imam Ali (AS), Imam Hassan (AS) Ya hau munbari yai khuduba mai tsawo a masallacin Kufa, a hudubar tasa bayan ya yi godiya da yabo ga Allah da kuma salati ga Manzonsa da alayensa, bayan haka ya yi bayanin shahadar Imam Ali da kuma falalolinsa da kuma gudunmawar da ya bayar ga wannan addini da kuma kariya ga Manzon Allah, yana cikin haka ne sai ya fashe da kuka, jama’a dake masallacin suma suka fashe da kuka, bayan haka kuma yai bayani dangane da Ahlul bait da kuma wajibcin yi masu biyayya ya kawo ayoyi da suke nuni da haka da dai sauransu, bayan haka sai Imam Hassan ya zauna, sai Abdullah dan Abbas ya mike da yake yana wajen lokacin, ya ce ya Jama’a wannan shine dan ‘yar Annabinku kuma wasiyyin imaminku saboda haka ku yi masa Bai’a, nan take jama’a suka fara Bai’a ga Imam Hassan, amma Imam Hassan yasa masu sharadin cewa, “Duk wanda na yaka, zaku yake shi, wanda kuma na yi sulhu dashi zaku yi sulhu dashi.” Wannan Bai’a ta kasance a ranar Jumma’a 21 ga watan Ramadan shekara ta 40 bayan Hijira, a lokacin Imam Hassan yana da shekaru 37 a Duniya. Bayan haka sai Imam Hassan ya sauko daga mumbari ya tsara al’amura yadda zasu gudana, ya umarci Abdullahi dan Abbas da komawa Basara da zama saboda a lokacin bayan Kufa kusan babu wani babban gari kamar Basara. Lokacin da labarin shahadar Imam Ali ya samu Mu'awiya, bayan haka kuma Jama’a sun yi ma Imam Hassan Bai’a, to sai Mu'awiya yai farinciki da kashe Imam Ali da bakin ciki da yi ma Imam Hassan Bai’a, saboda haka a lokacin sai ya aika da wani dan leken sa zuwa kufa da kuma Basara da nufin su dunga aiko masa da duk abinda yake faruwa a Kufa da Basara da kuma hanyoyin da zasu kashe Imam Hassan. Imam Hassan ya bayyanar da wannan makirci na Mu'awiya saboda haka Sai Imam Hassan ya ba da umarnin a fitar da wannan dan leken asiri na Mu'awiya daga Kufa da kuma Basara, bayan haka Imam Hassan ya rubuta wasika ya aika ma Mu'awiya a cikin wasikar yake ce masa, “ Ka dasa wasu mutane domin su yi kisan gilla da kuma aika maka da bayanai na ababen dake faruwa ga dukkan alamu kana so ayi yaqi to ka sani ban tsoron haka.” Wannan wasika ta isa ga Mu'awiya, bayan haka wasiku sun gudana tsakanin Imam Hassan da Mu'awiya daga karshe dai Mu'awiya ya aika da mayaka zuwa Iraq wato zuwa Kufa, bayan da labari ya samu Imam Hassan cewa Mu'awiya ya aiko da rundunar mayaka zuwa Iraq, sai ya hau munbari ya kirayi mutane zuwa yaqi da wannan runduna ta Mu'awiya amma abin mamaki sai jama’a suka yi shiru babu wanda ya ce komi, sai wani wanda ake ce ma Adiyyi dan Khatim ya mike tsaye ya ce, Subhannallah wane mummunan matsayi ne haka a ce ba zaku amsa ma shugabanku ba kuma dan ‘yar Annabinku? Baku gudun fushin Allah da azabarsa ta sauka akanku.” Bayan haka aka samu wasu a wajen suka mike suka yi makamanciyar wannan Magana wato ta shajja’a mutane domin tunkarar wannan runduna da ta tunkaro su, domin wata ruwayar ta nuna cewa Muawiya ya aika da mayaka har dubu dari da hamsin domin yakar Imam Hasan. To shine bayan da Imam Hassan yaji zantukan wasu daga cikinsu, sai ya ce masu idan dai da gaske kuke to mu hadu a Nukaila-sunan waje ne kusa da Kufa hanyar da za a bi zuwa Sham- Wallahi nasan ba zaku cika man wannan alkawari ba kamar yadda baku cika shi ba ga wanda ya fini – wato mahaifinshi Amiril muuminin- Bayan da Imam Hassan ya sauko daga munbari ya shirya domin kama hanya a wannan waje da ya ce su hadu a can, da yaje can abun mamaki mafi yawansu basu fita ba wato kadan kawai suka fita. Saboda haka sai da Imam Hassan ya sake dawowa Kufa domin shajja a mutane na su fita yaqin.Wannan ita ce babbar jarabawar da Imam Hassan ya fuskanta a lokacin Imamancinsa wato na rashin tsayayyun mabiya, wadanda kuma suka bishin haka suka dunga yi masa tawaye kamar yadda zamu ga haka nan gaba, alal misali runduna ta farko da Imam Hassan ya fara aikawa to shugaban rundunar sai Muawiya ya aika masa da sakon cewa idan ya dawo sashen sa yai masa alkawarin na da shi a matsayin gwamna a wani yenki na Sham ya kuma hado masa da kudi Dirhami dubu dari biyar, sai shi wannan mutumi ya amshi wannan ta yi na Muawiya, a takiaice dai sai ya bar Imam Hassan ya koma sashen Muawiya. Kuma da zai koma sashen Muawiya aka samu wasu mutane da yawa suma suka bishi, lokacin da wannan mummunan labari ya samu Imam Hassan sai yai jawabi ga wadanda suke tare dashi ya ce masu wanda ya na da a matsayin jagoran yaqin ya yi yaudara ya koma sashen Muawiya, ya ce zan sake na da wani, na san cewa shima zai sake yin abinda wancan ya yi wato na tawaye da komawa sashen Muawiya. Ile ko haka abun ya faru wanda ya na da din, a matsayin sabon kwamandan yaqin shima Muawiya ya saye shi ta hanyar bashi wasu kudade da kuma yi masa alkawarin wani Mukami, bayan haka Imam Hassan yai jawabi dake nuna cewa haka zasu dunga yin yaudara ba za su dake ba to shine daga karshe yasa wani wanda ake ce ma Ubaidullah dan Abbas dan’ uwa ne ga Abdullahi dan Abbas to shima abin mamaki haka ya ba Imam Hassan baya wato ya koma sashen Muawiya, saboda shi wannan Ubaidullahi dan Abbas abubuwan da Muawiya ya bashi da kuma alkawuran da yai masa yafi yawa kan wadancan guda biyun alal misali ya zo akan cewa shi Dirhami miliyan guda ya bashi tare da wasu alkawura wato saboda shi ta wani mahanga yana da alaka ta jini da Imam Hassan. A takaice dai Imam Hassan ya fuskanci jarabawa ta tawaye daga mabiyansa wato misali in ka kwatanta da sahabban Imam Husain (AS) wato yadda suka dake wato har dama Imam Husain ya basu a daren Ashura akan ya basu damar suna iya tafiya amma suka dake suka ce ba in da zasu je koda za a yi gunduwa-gunduwa dasu.. To wannan rashin dakewa na sahabban Imam Hassan yana daya daga cikin dalilan da yasa Imam Hassan yai sulhu da Muawiya saboda bai da mayakan da zai yaki Muawiya dasu, mai son ganin bayani sanka-sanka na irin tawayen da Imam Hassan ya fuskanta daga mabiyansa yana duba littafin Muntahal Amal juz’i na daya wanda sheikh Abbas Alkummiy ya rubuta wato marubucin littafin mafatihul jinan. SULHU DA MU'AWIYA A’amarin sulhu asalinsa bukata ce daga Muawiya wato shine ya aiko wakilai zuwa ga Imam Hassan na cewa maimakon yaqi ayi sulhu saboda Muawiya yasan cewa tabbas da Imam Hassan ya samu mayaka wadanda suka dake komi kankantarsu, idan ya yake shi zai samu galaba akansa to shi yasa shi Muawiya ya dauki matakai na ba za jijita cikin rundunar Imam Hassan da kuma saye wasu da kudade da kuma yi masu wasu alkawurra, alal misali hatta al’amarin wannan sulhu tun gabanin Imam Hassan ya ce ya amince da shi haka wadannan wakilai suka baza jita-jitar cewa wai Imam Hassan Hassan ya amince da sulhun saboda kiyaye jinanan Musulmi. Idan mutum ya bibiyi sharuddan da aka gindiya na sulhun zai fahimci cewa lalle Muawiyan shi ya nuna gayar bukatar sa ga sulhun a matsayin yana ganin kawai shine mafita gareshi na zama kan Mulki shi yasa dukkan sharuddan Imam Hassan ne ya gindaya su wato bashi Muawiyan ba. Ga wasu daga cikin sharuddan da ya gindiya ma Muawiya: 1- Zaka yi aiki da littafin Allah da kuma sunnan Manzon Allah (S). 2- Muawiya dan Abu Sufyan bai da ikon ya na da wani abayansa sai dai ya bar al’amarin ga Musulmi su yi shawara tsakaninsu. 3- Mutane su kasance cikin aminci a duk inda suke ko a Sham ne ko a Iraq ko Makka ko a Madina da dai sauransu wato ka da a zalunce su. 4- ‘Yan Shia da duk wani magoyin bayan Ali su kasance cikin aminci a rayukansu da Matayensu da ‘ya’yansu da kuma dukuyoyinsu wato daga cutarwa. 5- Ka da ayi wani abu na zalunci ga Hassan ko dan uwansa Husain ko wani daga cikin iyalan gidan Manzon Allah (S). Bayan da Imam Hassan ya sa wadannan sharudda wakilan Muawiya suka kai masa ya ce ya amince amma akan asasin yaudara saboda daga baya zamu ga cewa ya saba ma dukkan sharuddan, saboda shi abinda ya dame shi a lokacin Mulki dai ya dawo gareshi ko ta sulhu ko ta yaqi, to tambaya yau ina mulkin ina kuma wadanda aka mulka? Shi Muawiya ya yi Mulki na tsawon shekaru Arba’in ne wato ya yi shekaru ashirin yana matsayin gwamna bayan haka kuma ya yi shekaru ashirin a matsayin wai khalifan Musulmi. Bayan wannan sulhun da wani lokaci Imam Hassan ya bar Kufa ya koma Madina da zama, ya cigaba da zama Madina har ya zuwa lokacin da yai shahada, kuma abin mamaki ta hanyar wata daga cikin iyalan Imam Hassan, Muawiya ya biyo wato ya hada baki da ita ya ba ta guba akan tasa masa a abinci shi kuma yai mata alkawurra daga ciki akwai cewa zai aurar da ita ga Yazidu dansa, lokacin da ta yi wannan aika-aika Muawiyan ya ce mata zai dai ba ta dukiya amma ba zai hada ta aure da Yazidu ba. In muka duba ciikin sharuddan da Imam Hassan ya gindaya masa akwai cewa ba zai yi wani abu na zalunci ga Hassan ko Husain ba. Dama daga cikin dalilan da Imam Hassan ya amince da wannan sulhun shine cewa mutane su fahimci waye Muawiya, wato mutum ne wanda addini bai dame shi ba, shi dai Mulki kawai ko ta halin kaka ko da zai kashe duk wanda suka ja dashi akai bai damu ba, shi yasa bayan sulhun da ya zo Kufa to a cikin jawabin da ya yi wa mutane yake ce masu, “ Wallahi ni ban yaqe ku ba domin ku yi Sallah ko Azumi ko Hajji ba ko kuyi zakka, duk kuna yinsu, ni na yaqe ku ne domin in shugabantu akanku, kuma na samu haka yanzu”. A takaice wannan sulhu ya zama wata babbar jarabawa ga Imam Hassan. saboda tabbas Imam Hassan da ya samu tsayayyun mabiya kuma mayaka da bai yi wannan sulhun ba wato sai dai ayi yaqin domin tun Imam Hassan na Kufa wato gabanin sulhun akwai wasu daga cikin mabiyan Imam Hassan wadanda suka rubuta ma Muawiya wasiku na cewa suna tare dashi kuma zasu iya kama Hassan su mika shi gareshi koma su kashe shi. Saboda a lokacin a cikin Kufa akwai Kawarijawa wato wadanda suka yaqi Imam Ali har daya daga cikinsu shine ma sanadiyyar shahadarsa wato ibn Muljam, Saanan a Kufar akwai magoya bayan Bani Umayya wanda suke tare da Muawiya kai tsaye, akwai ‘yan ba ruwanmu a cikin Kufar wato wanda basu tare da kowa, akwai kuma wadanda ko ina ta fadi sha, sai kuma ‘yan kadan da suke tare da Imam Hassan. Kufa a lokacin bangarorin mutane dabam dabam ne kuma yawancinsu duk makiya ne. Saboda haka bayan wannan sulhu wata sabuwar fitina ta taso tsakan kanin mabiya Imam Hassan wanda da karshe shine Imam Hassan ya koma Madina da zama har ya zuwa wafatinsa.
|