Jarabawowin da Amiril Mu'uminin Imam Ali (AS) ya fuskanta |
Written by administrator | |||
Thursday, 22 August 2024 12:54 | |||
Alhamdu lillah bayan kawo Tarihi da kuma wasu daga cikin darussa na rayuwa mai albarka na A'imma (AS) wato tun daga Imam Ali (AS) Har ya zuwa Imam Mahdi (AS) Haka nan an kawo Tarihi na Manzon Allah (S) Da Sayyida Zahra (AS) Da kuma wasu daga rayuwar su mai albarka, dukkansu dai an kawo bayanan ne a takaice, to yanzu insha Allah a wannan sashe za'a juya zuwa ga Jarabawowin da kowane Imami ya fuskanta a zamaninsa ta fuskacin masu tafi da iko, da kuma jarabawowin da ya fuskanta daga mutanen gari, bayan haka kuma daga jarabawowin da ya fuskanta daga mabiyansa da dai sauransu. Zamu fara insha Allah daga Imam Ali (AS) Har ya zuwa Imami na Karshe, saboda haka abin zai dauki lokaci tun da za'a bisu daya bayan daya har a kammala, kasantuwar Jarabawowin da A'imma (AS) suka fuskanta a zamunnansu sun kasu kashi biyu, akwai jarabawar da dukkansu sun yi tarayya a ciki sune kamar guda ukku: 1-Kwace tafi da iko daga hannunsu a zahirance saboda sune Manzon Allah (S) Ya ayyana ma wannan al’umma da su khalifance shi a bayansa. khudubar da Manzon Allah ya yi a Ghadir hujja ne akan haka saboda haka kowane Imami a zamaninsa shine yake da hakkin ya tafi da iko, akasin haka kwace ne, wani tambihi a nan kasantuwar basu suka tafi da iko ba, ba yana nufin wannan matsayi na su ya canza a wajen Allah bane wato suna nan a matsayin na khalifofin Manzon Allah sun yi shugabanci ba su yi ba. 2- Sun yi musharaka na ganin zaluncin da ake yi ma al’umma amma basu da ikon yin komi akai, mutum ya bibiyi Tarihi ya ga kowane irin zaluncin da Azzaluman zamaninsa suka yi ma Jama’a misali a lokacin Imam Zainul Abidin (AS) Dubi abinda Yazidu (LA) yasa aka yi ma Mutanen Madina da dai sauransu. 3- Sun yi musharaka wajen ganin jirkita wasu ababe na Masulunci da aka yi kuma aka gina mutane akan jirkitaccen wasu ma sun wanzu har ya zuwa wannan zamani namu misali a watan Muharram yadda aka kago hadisai na cika-ciki da kuma yelwata ma iyali a ranar Ashura da dai wasu Hadisai wadanda aka kirkiresu kuma aka gina mutane a kai. Idan mutum ya yi bincike zai ga wadannan ga sunan birjik, misali lokacin da tafi da iko a zahirance ya dawo wajen Amiril mu'uminin Ali (AS) ya nemi ya hana sallar Asham wanda mutane suke yi a watan Azumi tun da bidi’a ce, hatta wanda yasa ayin wato Umar da yake ana yi ya ce madalla da wannan bidi’ar saboda a lokacin Manzon Allah ba'a yi haka ba. to da Imam Ali ya nemi ya hana mutane kusan tawaye suka yi kasantuwar mutane sun gini akai kasa da shekaru hamsin bayan wafatin Manzon Allah (S) To ina gamu a wannan zamanin, wasu ababe da aka kirkira aka gina mutane akai sama da shekaru dubu. Shi yasa daga cikin jarabawowin da Imam Mahdi (AF) Zai fuskanta akwai wannan saboda zai dawo da Addinin Musulunci kamar yadda yake a lokacin Manzon Allah kuma a Duniya baki daya wato da kasashen Musulmi da wadanda bana Musulmi ba. Baya ga wadannan jarabawowi da suka yi tarayya akai to kowane Imami akwai nau’in jarabawar da ya fuskanta a zamaninsa misali nau’in jarabawar da Imam Hassan (AS) ya fuskanta tana da banbanci da wadda Imam Husain (AS) ya fuskanta, Kuma kowannensu da zamanin dayan yake to haka zai yi, misali matsayar da Imam Hassan ya dauka na sulhu da Mu'awiya in da Imam Husain ne a zamanin to shima matsayar da zai dauka kenan haka nan in da Imam Hassan ne a lokacin Imam Husain to abinda Imam Husain ya dauka na yaqi shima shi zai yi. Bayan wannan ‘yar shinfida yanzu insha Allah za'a fara da Imam Ali (AS). Imam Ali (AS) Ya fuskanci jarabawowi masu yawa a rayuwarsa kai har ma da bayan rayuwarsa saboda akwai wasu ababe sai bayan shahadarsa aka kago su aka jingina masa. Da farko dai bayan rasuwar Manzon Allah ko mako guda ba'a yi ba, aka zo za'a kona gidansa da sunan wai dole yazo ya yi bai’a shi da wadanda ke tare dashi a gidan, alhali hakkinsa ne kuma Manzon Allah ya bayyanar da haka kasa da kwana 100 da zuwa gidansa za'a kona, saboda idan mutum ya yi lissafi tsakanin Ranar Ghadir da rasuwar Manzon Allah kwana saba’in ne ba wai shekaru aka dauka ba, a takaice dai abubuwan da suka faru sun faru a lokacin, mutum ya tambayi Tarihi mi ya faru zai bashi amsa. Bayan haka Imam Ali ya tattara Alkur’ani mai girma wadanda suka amshe iko suka ce basu son nashi, saboda bayan rasuwar Manzon Allah abinda Imam Ali ya soma yi shine shirin jana’izar Manzon Allah (S) Bayan jana‘izar Manzon Allah abu na biyu da Imam Ali ya yi shine tattara Alkur’ani waje guda, domin har Manzon Allah ya bar Duniya Alkur’ani ba an tattara bane waje guda, to suka ce basu son wadda Imam Ali ya tattara to haka abin ya cigaba a wajen sai lokacin kalifancin Usman dan Affan suka tattara shi waje guda. Mu a i'itikadinmu Alkur'ani tsararrene wato Allah ya tsare shi babu ragi babu kari wato duk irin tasarrufin da masu tafi da iko suka yi akan Hadisai to shi Alkur’ani Allah ya tsare sai dai mutum ya kago Hadisi ko ya jirkita shi ta hanyar ragi ko kari amma ba dai Alkur’ani ba shi Allah ya kare shi, kamar yadda Allah Ta’ala yake cewa a cikin Alkur’an, “Mune muka saukar da Ambato-Alkur’ani- mune kuma masu kare shi” Shi yasa masu surutan cewa wai ‘yan shi'a na da wani Alkur’ani dabam dana sauran musulmi to mai irin wannan tunanin ko maganar to kamar bai yadda da abunda Allah ne ya ce ba wato na kare shi Alkur’ani, kuma masu irin wannan tunanin, ‘yan shi’a sun sha yi masu kule, akan to su kawo Alkur’ani aga ni, na san ko ni ma a shekarun baya mun hadu da wani dan kungiya to sai yake ce man ai ‘yan shi'a na da Alkur’ani dabam, na ce masa duk ba gaskiya ba ne, to a lokacin akwai Alkur’ani tare dani kuma bugun Iran sai na fito dashi na mika masa, na ce ya duba daga ina aka buga shi sai ya ga ansa Qum-Iran na ce, to ya bude ya karanta duk Surar da yake so ya ga ta yi dai dai da yadda ya sani ko ta saba, ya bude nan, ya bude nan daga karshe da bakinsa ya ce lalle yadda ya karanta haka ya sansu shi bai ga wani bakon abu ba, amma duk da haka ya ce to su dai haka ake ce masu wai ‘yan shi'a na da Alkur’ani dabam, to sai na ce in zaka hukunta mutum ko mutane zaka hukunta sune da abunda ka gani ba abinda aka ce maka na karyayyaki ba akansu. Dawowa ga maudu’in to haka Imam Ali ya kasance a kebance in kaga an neme shi to wasu ababe ne suka cukurkude musamman a fagen ilimi basu san mafita ba sai akawo masa domin ya warware, idan mutum ya bibiyi zantukan wadanda suka yi kalifancin zai ga haka misali wata magana ta Umar da yake cewa, “Allah ya tsare Kada na kasance cikin wata matsala wato ta ilimi wanda baban Hassan bai ciki wato domin ya war ware". Akwai kuma lokacin da yake cewa ka da wani ya ba da fatawa a cikin masallacin Manzon Allah alhali Ali yana nan. A kwai fadin Usman dan Affan da yake cewa, “Ba domin Ali ba to da Usman ya halaka.” To haka dai Imam Ali ya kasance har lokacin da khalifanci a zahirance ya dawo a hannunsa, kuma jama’a ne suka ce shi suke so, sabanin wadanda suka gaba ce shi na khalifofin, misali Abubakar mutum ya binciki yadda zabensa ya kasance a Saqifa, baki daya a cikin sahabbai muhajirin su ukku ne a wajen wato daga Abubakar sai Umar sai kuma Abu ubaida sai kuma wasu daga cikin Ansarawa su suka zabe shi. Shi kuma Umar, Abubakar ne ya zabe shi ba tare da shawarar kowa ba, ta nan mutum idan yai tunani tun da sun ce Manzon Allah bai zabi kowa ba wai ya bar wa Al'umma ta zaba, to mi ya sa shi Abubakar bai bi wannan sunna ta Manzon Allah wato ya bar jama’a su zaba? To shi kuma Umar sai ya kafa kwamiti na mutum shida cewa wai su zabi khalifa to shine suka zabi Usman. To shi Ali mutum ya karanci Tarihi jama’a ne suka ce shi suke so, saboda idan mutum ya duba zai ga cewa Imam Ali shi ka dai ne yake da Nassi daga Manzon Allah da kuma zabin mutane amma daga karshe, to lokacin da yayi wannan khalifanci na Zahiri, wadansu wadanda basu su suka haifar da matsaloli masu yawa wanda har ya kai ga yaqoqi har guda ukku sune: 1-Yaqin Jamal. 2- Yaqin Siffin. 3- Yaqin Nahrawan. Ga bayaninsu a takaice. YAQIN JAMAL A- Abinda ya sabbaba wannan yaqin. B- Wadanda suka jagoranci wannan yaqin. C- Yaushe wannan yakin ya auku. A- Abinda ya sabbaba wannan yaqin: Bayan kashe Usman sakamakon yadda ya tafi da Mulki da kuma Fifita Bani Umayya kan sauran sahabbai da kuma sauran ababe da ya aikata ta kai ga wasu daga cikin Sahabbai suka ce a kashe shi tun da sunyi-sunyi ya canza bai canza ba, daga cikin masu cewa a kashe shi akwai Aisha, Dalha da Zubair, kai ta kai Dalha da Zubair suka je gidansa da nufin aiwatar da wannan kisa, Lokacin da wadannan al’amura suke faruwa Imam Ali ya nisanci wannan kwamacala. A gefe guda kuma lokacin da wadannan ababe ke faruwa ita Aisha ba ma ta Madina tana Makka ne, amma tana goyon bayan abubuwan da ake so ayi. YAQIN SIFFIN YAQIN NAHARAWAN
|