Thursday, 19 September 2024
Email
Make My Homepage
RSS
Register
Hada Salloli Print E-mail
Written by administrator   
Monday, 19 August 2024 19:40

Wannan sashe na Shi'a-Sunna damar manufarsa shine kawo wasu sassa na addinin Musulunci wadanda aka samu sabani tsakanin Sunna da Shi'a da kuma bayyana hujjojin kowa, musamman ma wasu ababe da ‘yan shi’a suke akai ko kuma suke aikatawa da kuma kawo hujjojinsu a littafan ‘yan uwanmu Ahlus Sunna, saboda ya kasance an dada fahimtar juna da kuma samun kusanci da juna domin rage kaifin gaba da kiyayya. Idan mutum ya yi bincike zai ga cewa mafi yawan abinda ‘yan Shi'a suke akai ko kuma suke aikatawa to zasu iya tabbatar dasu a littafan Ahlus sunna amma yawanci saboda jahilci, wani abin idan ‘yan shi'a sun aikata sai a ga kamar sabon abune a addini, kuma wannan ya shafi fannoni dabam-dabam na ilimi, misali a fannin fiqihu, Hadisi ko Tarihi da dai sauransu. Yanzu insha Allah zamu juya ga wasu sassa na Fiqhu wato mas’alar Hada Salloli, akan wannan asasi bayani zai gudana kamar haka:

A- Hada Salloli.

B- Hadisan Ahlus sunna kan hada salloli.

C-Hadisan Shi'a kan hada Salloli.

D- Lokutan Sallah
A- Hada Salloli: Dukkan Mazahabobi na Sunna da Shi'a sun yi ittifaki akan halaccin hada sallar Azuhur da Asar a lokaci guda da kuma sallar Magariba da Isha’I a lokaci guda in da kawai suka saba shine dalili ko sabab din da zai sa a hada Salloli misali a wasu mazahabobi na Ahlu sunna kamar Malikiyya inda yake halatta a hada sallar shine kamar idan akwai uzuri na ruwan sama wato kamar da damuna yamma ta yi ga hadari ya taso to a wannan yanayi ana iya hada sallolin, kuma a halin tafiya mutum zai iya hada Sallar Zuhur da Asar shima ya halatta da dai sauransu amma haka kawai babu wani uzuri bai halatta mutum ya yi ba. Amma a mazhaba ta shi'a mutum ya samu ya hada salloli na Magariba da Isha’i ko Zuhur da Asar ba tare da wani uzuri ba kuma suna da hujjojin yin haka a littafansu da kuma littafan Ahlus sunna kamar yadda zamu gani nan gaba insha Allah. Amma abin ban takaici saboda jahilci sai a ga kamar ‘yan Shi'a sun zo da wani sabon abu ne.
B- Hadisan Ahlus sunna kan hada salloli: Idan mutum ya duba a cikin fitattun littafan Hadisai na Ahlus sunna misali littafin Sahih Muslim a littafin sallah idan a ka duba za'a ga babi da yai bayanin hada salloli, mutum yana zaune a gida ba wai a halin tafiya ba, ga wasu daga cikin Hadisan 1- An ruwaito daga ibn Abbas ya ce, “Manzon Allah (S) Ya yi Sallar Zuhur da Asar a tare, haka nan ya yi sallar Magariba da isha’i a tare ba da wani uzuri na tafiya ba ko tsoro – kamar tsoron hadari- 2- A wata ruwaya a dai cikin sahihi Muslim Abdullah dan Abbas ya ce, “Manzon Allah ya hada sallar zuhur da Asar haka nan Magariba da Isha’i a Madina babu wani uzuri na ruwan sama to shine aka tambayi Abdullahi dan Abbas cewa mi yasa Manzon Allah ya yi haka? Sai ya ce saboda kada ya takura ma al'ummarsa.” 3- An ruwaito daga Mu'azu dan Jabal Ya ce, “Manzon Allah (S) A yakin Tabuka ya hada sallar Zuhur da Asar tare haka nan ya hada Sallar Magariba da Isha’i tare. Shima sai wani ya tambayi Mu'azu to miyasa ya yi haka? Ya ce saboda kada ya matsa ma al’ummarsa” Haka nan an ruwaito daga Abdullahi dan Mas’ud ya ce, “Manzon Allah (S) A Madina ya hada Sallar Azuhur da La'asar ya kuma hada Sallar Magariba da Isha’i. Sai aka tambayi Abdullahi dan Mas’ud to miyasa ya yi haka ya ba da amsa da cewa saboda ka da ya matsa ma al’ummarsa.” Wannan Hadisin yana cikin “Mu'ujamul Kabir na Dabrani” Haka nan an ruwaito daga Abdullahi dan Umar ya ce, “Manzon Allah ya hada Sallar Magariba da Isha’i.” Shi kuma wannan Hadisi yana ciki Sahih Buhari a littafin Sallah. A takaice dai akwai Hadisai masu yawa da aka ruwaito daga Manzon Allah (S) na cewa ya hada Sallar Azuhur da Asar da kuma Magariba da Isha’i ba da wani uzuri ba kuma ya hada sallolin a lokutan da wasu uzurori suka bijiro kamar halin tafiya ko kuma ruwan sama, kuma idan mutum ya lura da Hadisan da aka ruwaito zai ga an tambayi wadanda suka ruwaito to miyasa Manzon Allah ya yi haka amsar da suke bayarwa ita ce saboda kada ya matsa ma al’ummarsa. To tambaya a nan shine minene laifin ‘yan Shi'a idan sun hada Sallolinsu? Ashe ba sun yi aiki da wannan Sunna ta Manzon Allah ba kenan! Bllantana kuma suma Shi'a suna da ruwayoyin Hadisai da aka ruwaito daga Ai'mma (AS) dangane da hada salloli ga kuma kari daga ruwayoyin Ahlus sunna a kuma cikin Buhari da Muslim.
C- Hadisan Shi'a kan hada Salloli: Akwai Hadisai masu yawa akai amma ga wasu daga ciki an ruwaito daga Imam Sadiq (AS) Ya ce, “Manzon Allah (S) Ya hada Sallar Azuhur da Asar, tare da yi masu kiran Sallah biyu da iqama biyu – Wato ko da mutum zai hada sallolin to mustabbi ne kowace Sallah yai mata kiran Sallah da Iqama amma idan bai yi ba sallar ta yi amma ya rasa ladar kiran sallar- Haka nan a wata ruwaya ya ce, “Manzon Allah (S) Ya yi Sallar Zuhur da Asar a waje guda ba tare da wani uzuri ba, to shine Umar dan Kaddab ya tambayi Manzon Allah wani sabon hukunci na sallah ya auku ne – Wato ya ga sabanin yadda aka saba yi ba tare da yinsu a hade ba- Sai Manzon Allah ya ce masa A’a ina son in yalwata ma al'umma ta ne.” -Wato zasu iya rarraba sallolin kuma zasu iya hadawa- Ga mai son gani wadannan Hadisan yana iya duba littafin Wasa’ili Shi'a Juzu’i na ukku.
D- Lokutan Sallah: Idan mutum ya duba cikin littafan Fiqihu na Sunna da Shi'a zai ga cewa Malamai sun yi bayani sanka-sanka na kowace Salla ga lokacin ta, wato tun daga Sallar Asuba har ya zuwa Sallar Isha’i to mutum yana da zabi kodai ya yisu a rarrabe kamar yadda galibin Ahlu suuna suke yi sai ya kasance lokuta biyar kenan a yini. Ko kuma ya yi Sallar Asuba ita kadai ya hada Sallar Azuhur da Asar sa'aanan ya sake hada Sallar Magariba da Isha’i sai ya kasance lokuta ukku ke nan a yini. Duk wanda mutum ya yi, yayi ko kuma ya kasance wani lokaci mutum ya yi su a rarrabe wani lokaci kuma ya hada, a takaice dai zabi yana ga mutum, saboda yana yin lokutan mutane ya ban banta, amma idan mutum ya je kasashe na Shi'a zai ga cewa lokuta ukku suke yin sallolin saboda suna hada salloli ne wato Asuba sai sallar zuhur da Asar da kuma Sallar Magariba da Isha’i
Daga karshe daga wadannan Hadisan da aka kawo daga bangaren Sunna da kuma Shi'a zamu ga cewa ‘yan Shi'a da suka lizimci hada Salloli abu ne wanda bai saba ma shari’a ba, ga hujja a littafansu ga kuma hujja a cikin littafan Hadisai na Ahlus Sunna misali cikin Buhari da Muslim da sauransu. Allah Ta’ala ya dada hada kawukanmu da zukatanmu.

 
Home Shia/Sunnah Hada Salloli
Copyright © 2024. www.tambihin.net. Designed by KH