Thursday, 19 September 2024
Email
Make My Homepage
RSS
Register
Bayani kan Ilimi Print E-mail
Written by administrator   
Friday, 16 August 2024 21:26

Bayan kawo Hadisai guda 40-40 da aka ruwaito daga A'imma na Ahlul bait (AS) wato tun daga Imam Ali (AS) har ya zuwa Imam Hassan Al-askariy (AS). Yanzu insha Allah za'a dunga kawo wasu babobi na ilimin Hadisi da aka ruwaito daga Manzon Allah (S) da kuma Ahlu baitinsa (AS) littafin da zamu yi amfani dashi shine “Muntakabu mizanul Hikma” na Sheikh Muhammad Riy Shahariy, littafin yana da dan girma kuma ya kunci Hadisai a babobi dabam-dabam to a cikinsa lokaci bayan lokaci za'a dun ga ciro wasu babobi domin tunasar da juna akai, kuma daga Hadisan da za'a dunga kawowa zamu fahimci dinbin Hadisai masu yawa da A'imma na Ahlul baiti suka bar ma wannan Al’umma ta Manzon Allah (S). Yanzu insha Allah zamu fara da Hadisan da aka ruwaito kan babin ilimi ta fuskoki dabam-dabam kamar yadda zamu gani.
FALALAR ILIMI
Manzon Allah (S) Ya ce, “Neman ilimi wajibi ne kan kowane Musulmi da Musulma, da ilimi ake bauta ma Ubangiji ake kuma yi masa biyayya, da kuma ilimin ne ake sanin Halal da Haram.” Imam Ali (AS) ya ce, “Babu wata taska mafi amfani kamar ilimi.” Haka nan akwai wani lokaci Imam Ali yana ce ma Khumail- wato ma'abocin Du’au Khumail da yake asalin Addu’ar Imam Ali ne ya bashi ita- sakamakon tsawon zamani da ya kasance tare dashi- Imam Ali ya ce masa ya Khumail Ilimi yafi alkairi akan dukiya saboda shi ilimi yana gadinka kai kuma kana gadin dukiya, dukiya tana raguwa ta hanyar ciyarwa amma ilimi yana karuwa ta hanyar ba da shi.” Imam Baqir (AS) ya ce, “Duk zuciyar da babu wani abu na ilimi a cikinta to kamar kangon gida ne wanda babu komi da kowa a cikinsa.” Imam Sadiq (AS) ya ce, “Malamai sune magada Annabawa.” – Wato malamai masu aiki da iliminsu kamar yadda zamu ga haka nan gaba-
FALALAR ILIMI AKAN IBADA
Manzon Allah (S) ya ce, “Ilimi kadan yafi alhairi kan ibada mai yawa – wato wadda aka yi ta ba akan asasin ilimi ba – A wata ruwaya kuma Manzon Allah ya ce, “Barci tare da Ilimi yafi alhairi kan Salla da Jahilci.” Manzon Allah (S) ya ce, “Falalar Malami akan mai ibada kamar falalar rana ne akan taurari. Falalar mai ibada akan wanda bai ibada kamar falalar wata ne akan taurari.” Imam Baqir (AS) ya ce, “Malamin da ake amfanuwa da iliminsa yafi falala kan mai ibada dubu.”
MUTUWAR MALAMI
Manzon Allah (AS) ya ce, “Mutuwar Malami musiba ce babba kuma gibi ne mai wuyar cikewa. Mutuwarsa kamar tauraro ne da ya shafe -wato haskensa –
DUBI ZUWA GA FUSKAR MALAMI
Manzon Allah (AS) Ya ce, “Dubi zuwa ga fuskar Malami saboda son shi ibada ne.” An ruwaito daga Imam Sadiq (AS) Lokacin da aka tambaye shi fadin Manzon Allah cewa, “Dubi zuwa ga fuskokin Malamai ibada ne.” Sai Imam Sadiq ya ce, shine Malamin da idan ka dube shi zai tunasar da kai lahira, wanda yake sabanin haka to dubinsa fitina ne – Wato ba kowane malami ba –
KWADAITARWA A KAN NEMAN ILIMI
Manzon Allah (S) ya ce, “Ku nemi ilimi ko da zuwa Sin ne -Wato kasar China a yanzu – domin neman ilimi farilla ne kan kowane Musulmi, Allah Ta’ala yana son masu neman ilimi.” A wani Hadisi kuma Manzon Allah ya ce, “Duk wanda ba zai yi dauriya na kaskancin neman ilimi ba na wani lokaci to zai kasance cikin kaskancin jahilci har abada.” A wata ruwaya kuma ya ce, “Abubuwa biyu mai nemansu baya koshi da su, neman ilimi da kuma neman Duniya.” Imam Sadiq (AS) ya ce , “Da mutane sun san falalar dake cikin neman ilimi to da sun nemi shi komin wahala da tsanani.”
MAI NEMAN ILIMI
Manzon Allah (S) ya ce, “Mai neman ilimi tsakankanin jahilai kamar rayayye ne tsakankanin matattu.” A wata ruwaya Manzon Allah (S) ya ce, “Idan mutuwa ta zo ma mai neman ilimi alhali yana neman ilimin to ya mutu Shahidi.” Manzon Allah (S) ya ce, “Duk wanda ya kama hanyar neman ilimi to Allah zai saukakake masa hanyar zuwa Aljanna.” A wata ruwaya kuma ya ce. “Duk wanda ya kasance yana neman ilimi to Aljanna za ta kasance tana nemansa.” Manzon Allah (S) ya ce, “Mai neman ilimi komi yana nema masa gafara har kifaye da suke cikin ruwa da sauran kwarin kasa.”
ILIMANTARWA
Manzon Allah (S) ya ce, “Mafificiyar sadaka ita ce mutum ya koyi ilimi sa'anan ya sanar dashi ga ‘yan’uwansa.” A wata ruwaya Manzon Allah yace, “Duk mutumin da Allah ya bashi ilimi sai ya boyeshi – Wato bai sanar dashi ba – To zai hadu da Allah ranar kiyama da linzami na wuta.” Imam Ali (AS) yace, “Kowane abu yana raguwa da ciyarwa amma banda ilimi.” Imam Baqir (AS) yace, “Duk wanda ya koyar da wani babi na shiriya to yana da ladar wanda ya aikata shi kuma ba tare da an tauye ladarsu ba.” Imam Sadiq (AS) yace, “Komi yana da Zakka, to zakkar ilimi shine sanar da shi ga masu nemansa.”
FALALAR MAI ILIMANTARWA
Imam Baqir (AS) yace, “Mai ilimantar da ilimi, Dabbobi dake doron kasa suna nema masa gafara, da kifayen dake cikin koguna, da kuma dukkan wani yaro da babba da suke bayan kasa.”
NEMAN ILIMI SABODA ALLAH DA KUMA BA SABODA ALLAH BA
Manzon Allah (S) ya ce, “Duk wanda ya nemi ilimi saboda ya yaudari mutane dashi to ba zai shaki kanshin Aljanna ba.” A wani Hadisi kuma Manzon Allah ya ce, “Duk wanda ya nemi ilimi ba saboda Allah ba to ya nemi mazauninsa a wuta.” Imam Ali (AS) ya ce “kashedinku da ku nemi ilimi akan asasin manufofi guda hudu, domin kuyi alfahari tsakanin Malamai, ko domin ku yi jayayya da wawaye, ko domin ku yi Riya dashi a wajen zama ko kuma domin ku jawo fuskokin mutane zuwa gareku saboda ku shugaban ce su.” Imam Sadiq (AS) ya ce, “Duk wanda ya nemi ilimi saboda Allah, kuma ya aikata shi saboda Allah, Kuma ya sanar dashi saboda Allah to za'a kira shi a sama da cewa Mai daraja.”
HAKKOKIN DALIBI AKAN MALAMI
Manzon Allah (S) ya ce, “Ku lausasa ga wanda yake koyon ililmi a wajenku.” – Wato kada a tsananta masa ko a kosa da shi –
HAKKOKIN MALAMI AKAN DALIBI
Imam Zainul Abidin (AS) ya ce, “Hakkin Malami akanka shine ka girmama shi, ka da kayi giba a gabansa, ka suturta aibobinsa, ka bayyana kyawawan dabi’unsa, - Da dai sauran Hakkoki – Manzon Allah (S) ya ce, “Wanda ya ziyarci Malamai to kamar ya ziyarce ni, wanda ya zauna dasu kamar ya zauna dani.”
KWADAITAR AKAN AIKI DA ILIMI
Manzon Allah (S) ya ce, “Duk wanda ya aikata abinda ya sani to Allah zai sanar dashi abinda bai sani ba,” Imam Ali (AS) ya ce, “Ilimi ba aiki musiba ne, aiki ba tare da ilimi ba bata ne.”
TSANANIN UKUBA GA MALAMIN DA BAI YI AIKI DA ILIMINSA BA
Imam Sadiq (AS) ya ce, “Wanda yafi tsananin Azaba a cikin mutane shine Malamin da bai amfana da iliminsa ba.” Imam Sadiq (AS) ya ce, “Ana gafarta ma Jahili zunubai saba’in gabanin a gafarta ma Malami zunubi guda.” Daga cikin Addu’oin da Manzon Allah (S) yake yi akwai Addu’ar, “Ya Allah ina neman tsari da ilimin da ba mai amfanarwa ba, da kuma zuciyar da babu khushu’i a ciki, da kuma Addu’ar da ba'a karba.” Da dai sauran Hadisai masu yawa akan wannan babi na ilimi wadanda aka ruwaito daga Manzon Allah da kuma Ahli baitinsa (AS), saboda haka babban abinda ya hau kanmu shine aiki da abunda muke karantawa, domin idan ba haka ba to zasu kasance nauyi da musiba akan mu ranar kiyama, wato za'a tambaye mu kaza da muka sani mun aikata shi, idan mu ka aikata sai ya kasance haske garemu insha Allah a ranar.

 
Home Darusan Hadisai Bayani kan Ilimi
Copyright © 2024. www.tambihin.net. Designed by KH