Kamar yadda aka sani a cikin Alkur’ani mai girma akwai wajajen yin sujuda idan mutum yana karatunsa ko kuma yana sauraronsa, wani wajen ma yin sujudar wajibi ce, wani wajen kuma mustahabbi ce. Insha Allah bayani zai kasance kan wannan babi na sujudu Tilawa kamar haka:
1- Matsayin yin sujudar karatun Alkur’ani.
2- Wajajen da ake yin sujudar cikin Alkur’ani.
3- Addu’ar da ake son yi cikin sujudar.
4- Falalar yin sujudar.
5- Yadda ake yin Sujudar.
6- Hukunce-hukunce na Sujudar 1-Matsayin sujudar karatun Alkur’ani: Ya kasu kashi biyu akwai in da yin sujudar yana matsayin wajibi ne, wato dole ne mutum ya yi idan ko bai yi ba to yana da zunubi, saboda ga wani abu wajibi akansa amma bai aikata shi ba, wajajen da sujuda na wajibi suke cikin Alkur’ani wajaje hudu ne kamar yadda zamu gani nan gaba insha Allah. Akwai kuma in da yin sujudar yana matsayin Mustahabbi ne, wato ko da mutum bai yi ba ba kome akansa sai dai ya rasa ladar yin sujudar. 2- Wajajen da ake yin sujuda cikin Alkur’ani: Akwai wajaje goma sha biyar da ake yin sujuda a cikinsu, guda hudu daga ciki yin sujudar wajibi ne, sauran kuma yin sujudar Mustahabbi ne. Wajaje da suke yin sujuda wajibi ne sune: 1- Suratu Sajda Aya ta 15. 2- Suratu Fussilat Aya ta ta 37. 3- Suratu Najam Aya ta 62. 4-Surat Alak Aya ta 19. Wajajen da kuma yin sujudar Mustahabbi ne sune: 1- Suratul A’araf Aya ta 206 ita ce karshen Aya a cikin Surar. 2- Suratur Ra’ad Aya ta 15. 3- Suratun Nahl Aya ta 49. 4- Suratul Isra Aya ta 107. 5- Suratu Maryam Aya ta 58. 6- Suratul Hajj a cikin surar akwai wajaje guda biyu wanda mustahabbi ne yin sujuda a cikinsu, na farko ita ce Aya ta 18, na biyu ita ce Aya ta 77. 7- Suratul Furkan Aya ta 60. 8- Suratun Naml Aya ta 25. 9- Suratus Sajda Aya ta 15. 10- Sutatu Sad Aya ta 24. 11- Suratu Fussilat Aya ta 37. 12- Suratun Najm Aya ta 62 ita ce karshen aya a cikin surar. 13- Suratul Inshi-kak Aya ta 21. 14- Suratul Alak Aya ta 19 ita ce karshen aya a cikin surar. Idan mutum ya lissafa wadannan wajaje na sujudar Alkur’ani zai ga cewa guda goma sha biyar ne, kasantuwar a cikin suratu Hajj akwai Karin guda daya. Yana da gayar muhimmanci idan mutum na karatun Alkur’ani duk lokacin da ya zo wajen sujudar ta wajibi ko mustahabbi to ya kasance ya yi sujudar, saboda samun ladar yin hakan da kuma koyi da Manzo Allah da Ahli baitinsa (AS). 3- Akwai zikiri ko Addu’a da ake son karantawa idan mutum ya yi sujudar karatun Alkur’ani, amma idan mutum bai karanta ta ba ba komi akansa, da yake mujarradin sujudar ake bukata ga mutum wato ko da mutum zai yi sujudar amma bai karanta komi ba a ciki to ta yi ko da ko a sujudar wajabi ne, haka nan kuma da mutum zai karanta wani abu dabam ba wadda aka ruwaito ba shima ya yi misali a sujudar mutum ya yi tasbihi wato ya ce subhanallah ko ya ce Alhamdu lillah ya yi, illa dai kawai an fison karanta wanda aka ruwaito shine: لَاإله إلا الله حقا حقا, لا إله إ الله إيمانا وتصديقا, لاإله إلا الله عبو دية ورقا, سجدت لك يا رب تعبدا ورقا, لا مستنكفا ولا مستكبرا, بل انا عبد ذليل خائف مستجير. 4-Falalar yin sujudar: Sujuda kowace iri ce tana da lada da falala babba ballan tana kuma sujuda ta karatun Alkur’ani wadda aka ruwaito daga Manzon Allah (S) da kuma A'imma na Ahlul bait (AS). Yama zo a tarihin Imam Sajjad cewa idan yana karatun Alkur’ani duk in da ake yin sujuda to idan ya zo wajen sai ya yi sujudar shi yasa ma ake ce masa Sajjad wato mai yawan sujuda. An ruwaito daga Imam Sadik (AS) Ya ce “ lokacin da bawa yafi kusa da Ubangiji shine a halin sujuda” A wata ruwaya Manzon Allah (S) Ya ce “ Babu wani Musulmi wanda yai Sujuda saboda Allah face Allah ya daukaka darajarsa ya kuma yafe masa zunubansa.” Da dai sauran Hadisai masu yawa da suke bayani dangane da falalar Sujuda. 5- Yadda ake yin Sujudar: Sujudar karatun Alkur’ani sujuda ce guda daya, idan mutum ya zo dai dai wajen yin sujudar sai ya yi Niyyar sujudar a zuciyarsa, sa'annan sai ya yi sujudar ba tare da yin kabbara ba sai idan zai dago daga sujudar shine zai yi kabbara. Lokacin da mutum yai sujudar ana son ya karanta Addu’ar da aka kawo a sama in zai iya ko ya yi tasbihi ko wata Addu’a, In ma bai karanta komai ba ta yi, domin abinda ake bukata mujarradin Sujudar amma karanta wani abu a ciki yafi falala musamman ma wanda aka ruwaito. Kuma bayan sujudar babu yin Tashahud wato tahiya ko yin sallama, mutum na dagowa daga sujuda sai ya yi kabbara ya cigaba da karatunsa. 5- Hukunce-hukuncen yin sujudar: Idan mutum ya duba cikin littafan Fikihu na Risala amaliyya zai ga an kawo wasu daga cikin hukunce-hukunce na sujudar Tilawa, alal misali ya zo a cikin littafin Muntakabul Ahkam na Fatawowin Sayyid Khamna’i cewa idan mutum ya manta da yin sujudar, to zai yi ta idan ya tuna. Haka nan idan mutum na sauraron karatun Alkur’ani ta TV ko Rediyo da dai sauransu sai ya ji an karanta ayar sujuda to idan sujudar wajibi to wajibi ne ya yi sujudar idan kuma ta mustahabbi ce to mustahabbi ne ya yi sujudar. Haka nan kuma ba sharadi bane fuskantar Alkibla a sujudar wato mutum zai iya fuskantar ko ina ya yi sujudar misali yamma ko kudu amma ya fuskanci alkibla ya fi, haka nan ba sharadi ne ba lokacin sujudar ya zamo yana da Alwala wato mutum zai iya yin sujudar ko da bai da alwala da dai sauran hukunce-hukunce da suka kebanta da ita sujudar Tilawa.
|