Thursday, 19 September 2024
Email
Make My Homepage
RSS
Register
Hukuncin Kudin Kirifto a Makarantar Ahlul-Bait (AS) Print E-mail
Written by administratort   
Wednesday, 31 July 2024 21:03

Ga wasu daga cikin fatawowin Mujtahidai akan kudin Kirifto:

Sayyid Ali Khamene'i:

Samun kudin Kirifto ta hanyar (Not coin), (Hamster Kombat), (Tapswap) da ire-iren su, da kuma mayar da su kudin da aka saba da su, to bayan kiyaye dokoki na Shari'a, to akwai bukatar kiyaye dokokin Kasa, don haka in aka hana mu'amalar a wani kebantaccen wuri, ko canja su zuwa kudi a wasu kebantattun sharudda, to wajibi ne a nisanci yin haka.
Sayyid Sistani:
Saye da sayar da kudin Kirifto muhalli ne da ba ni da fatawa, don haka za'a koma zuwa ga wani Marji'i, tare da kiyaye A'alam sannan mai bi masa.
Haka kuma idan ya zama saye da sayarwa ko fitar da shi (Mining), ya sabawa dokar kasa, to bai halatta ba. 
Ayatullah Shubairi:
Idan kuÉ—in Kirifto za su iya kawo wa tattalin arzikin kasa matsala ko dokar kasa ba ta ba da damar yinsa ba, to bai halatta a bisa Ihtiyadi na wajibi ba.
Ayatullah Safi:
A dunkule a ce Kirifto kudi ne akwai matsala, saye da sayar da shi bai inganta ba.
Ayatullah Makarim:
A bisa la'akari da cewa akwai tambayoyi masu yawa a kan Kirifto, kuma mafi yawan kasashe ba su karbe shi ba, kuma ya zama sanadin yaudarar mutane masu yawa, to saye da sayar da shi bai halatta ba.
Ayatullah Nuri
Shiga irin wannan mu'amalar bai halatta a bisa Ihtiyadi na wajibi ba.
Ayatullah Wahid:
Saye da sayar shi batattu ne, (ma'ana cinikin bai kullu ba).
Irin wadannan Mas’aloli su ake cema “MASA’ILUL MUSTAHADASA” A kwai ma Malaman da suka rubuta littafi akai, Saboda al’murane da suka bijiro na zamani. To idan irin haka ya taso ko suka bijiro to kafin mutum ya aikata to wajibi ne akansa yasan minene fatawar Mujtahidin da yake Taqlidi da shi akai. Idan kuma ya kasance Mujtahidin da yake Taqlidi dashi bai da fatawa akai to abinda zai yi shine sai ya koma ga wani Mujtahidi wanda yake da Fatawa kan al’amarin amma fa ya kasance ya kiyaye Mujtahidin da zai koma gareshi ya zamanto A’alam wato mafi sani.
Wani tambihi muhimmi anan shine a Makarantar Ahlul bait ko a Fikihun Ahlul baiti ba kamar na Ahlus Sunna bane, abinda nike nufi a nan shine misali idan a wata mas’ala a fatawar Malikiyya ka ga ta yi maka tsanani ko baka son ta, to kana iya komawa ga fatawar Hanafiyya ko shafi’iyya idan kaga tafi maka sauki. To a makarantar Ahlul baiti Mujtahidin da kake Taqlidi dashi matukar yana da fatawa akai to ko da tayi tsanani a wajenka haka zaka bi fatawar tasa, in da kawai zaka iya komawa ga wani sai idai shi wanda kake Taqlidin dashi bai da Fatawa akai, to shine zaka koma ga mafi sani, wannan yana da gayar muhimmanci. Atakaice mutum bai da damar ya yi yawo cikin mazahabobi idan wannan fatawa ba ta yi masa sai ya koma ga wannan, amma idan ya kasance Mujtahidan mutum yana ganin dukkansu sun kai mustawa ta A’alamiyya wato mafi sani to a nan mutum na da damar ya kasance wasu sashen fatawowi ya bi wani Mujtahidin wasu kuma ya bi wani Mujtahidin misali sashen Ibadat yabi fatawowin wannan, a sashen Mu’amalat ya bi wani dabam.
A yanzu a wannan Mas’ala da ta bijiro a wannan zamani namu kuma wasu suna ta tambayoyi a kai to mutum zai bi fatawar Mujtahidin da yake Taqalidi da shine.

 
Home Darusan Fiqh Hukuncin Kudin Kirifto a Makarantar Ahlul-Bait (AS)
Copyright © 2024. www.tambihin.net. Designed by KH