Thursday, 19 September 2024
Email
Make My Homepage
RSS
Register
Shahidan Ahlul-Bait a waki'ar Karbala Print E-mail
Written by administrator   
Saturday, 27 July 2024 19:52

Kasantuwar wannan wata da muke ciki na juyayi da baqin ciki dangane da abubuwan da suka faru a waqi’ar Karbala, kuma kamar yadda aka saba a irin wannan munasaba akan dauki wani maudu’i da yake da alaqa da wannan waqi’a ta Karbala domin tunasar da juna akai. Insha Allah a wannan shekara maudu’in da zamu tunasar da juna a kai shi, Shahidan Ahlul Bait a waqi’ar Karbala, saboda wadanda suka yi shahada a Karbala za ka iya kasa su kashi biyu ko ukku, kashi na farko sahabban Imam Husain, kashi na biyu jinin Ahlu bait, na ukku Imam Husain (AS) kamar yadda ya zo a ruwayoyi da kuma tarihi bayan shahadar sahabban Imam Husain (AS) baki daya sai ya rage jinin Ahlul bait wato ‘ya’yan Amiril Muuminin, Imam Hassan, Imam Husain da sauransu kamar ‘yayan Aqil dan Abi dalib da Ja’far dan Abi dalib. Wani tanbihi muhimmi a nan shine idan mutum ya bibiyi tarihi zai ga cewa duka jinin Ahlul bait da suka yi shahada a waqi’ar Karbala idan mutum ya bibiyi nasabarsu zai ga cewa tana tuqewa ga Abu dalib ne, wannan aya ce babba wato idan mutum ya dubi irin gudunmawa da Abu Dalib ya baiwa Manzon Allah (S) Lokacin da yake Da’awa a Makka, muka dubi irin gudummawa da jikokinsa suka bayar a waqi’ar Karbala. An samu sabani a Malaman Tarihi kan adadin jinin Ahlul bait da sukayi shahada a waqi’ar Karbala akwai wadanda suka tafi akan cewa su 16 ko 17, wasu kuma suka tafi akan sama da 20, saboda yadda zai yi sauqin fayyacewa za a kawo su kamar haka.

A- Ya’yan Amiril Muuminin dan Abu Dalib da suka yi shahada a waqi’ar Karbala.

B- Ya’yan Imam Hassan (AS).

C- Ya’yan Imam Husain (AS).

D- Ya’yan Aqil dan Abu Dalib.

E- Ya’yan Ja’afar dan Abu Dalib.
A- Ya’yan Amiril Muuminin da suka yi shahada a waqi’ar Karbala: Idan mutum ya bibiyi tarihi zai ga cewa ‘ya’yan Imam Ali (AS) da suka yi shahada a waqi’ar Karbala su bakwai ne ga sunayensu: 1-Imam Husain (AS). Yazo a Tarihi cewa bayan shahadar dukkan sahabban Imam Husain da kuma Ahli baitinsa, ya zamanto saura shi kadai wanda wannan babbar jarabawa ce wato shahidai har 72 ga jikkunanan su yana kallo kuma babu wani namiji sai shi, to shine Imam Husain yai sallama da iyalinsa domin zai je ya fuskanci maqiya, Imam Husain ya dubi Hemarsu yai kira ya ce, Ya Zainab, Ya Sukaina, Ya Fadima inai maku sallama da kuma bankwana. Duka musibobin da suka sami Imam Husain suna da qona zuciya da zub da hawaye amma musibar ta bankwana tafi sosa rai da tada hankali musamman kasantuwar wadanda suka rage mata ne da yara kuma zasu kasance a hannun azzalumai masu busassun zukata babu wani tausayi tare dasu face gallazawa, mutum ya dubi abubuwan da suka yi bayan shahadar Imam Husain na kwashe masu kayayyaki da kuma qona hemominsu da dai sauran abubuwan da suka yi na rashin Imani da tausayi. 2- Abul Fadal Abbas. Kamar yadda aka sani a ‘ya’yan ummu banin guda hudu Abbas shine babbansu, kuma shine ke riqe da tutar Imam Husain, ya zo akan cewa a daren Ashura ya tara jinin Ahlul bait da ke tare da Imam Husain a Karbala ya ce masu gobe ya kasance su za su fara mubaraza, jin haka sai Habib dan muzahir shima ya tara sahabban Imam Husain ya nuna masu muhimmancin gobe ya kasance sune zasu soma fuskantar maqiya kafin Ahlul bait har yake ce masu da wace fuska zasu dubi Manzon Allah ranar qiyama ana kashe Ahlu baitinsa suna kallo, haka ko aka yi sahabbansa daya bayan daya suka yi shahada, ya zo a a tarihi cewa cikin sahabban Imam Husain da sukayi shahada a Karbala akwai sahabban Manzon Allah wajen guda takwas a ciki, akwai cikin sahabban Manzon Allah da ya fito mubaraza sai da Imam Husain yai kuka, saboda kasancewarsa dattijo saboda a lokacin yana shekaru 95 a duniya. Abul Fadal kafin shahadarsa ‘yan uwansa ukku sai da ya kirasu domin yin mubaraza da maqiya kuma daya bayan daya haka suka fito suka fuskanci maqiya har suka yi shahada. Lokacin da suka yi shahada ya zo wajen Imam Husain ya bashi izini ya fuskanci maqiya, jin haka Imam Husain yai kuka sosai ya ce ai kai ne ma'abocin tuta na, sai Abbas ya ce zuciya ta tayi qunci ne. To shine a lokacin Imam Husain ya ce masa amma kaje ka samo ma wadannan yara ruwa ko da kadan ne, sai Abbas ya tafi ya samu an girke maqiya wajen dubu hudu domin gadin ruwan Furat din, to shine Abbas yai masu wa'azi amma wa'azin bai amfane su ba, ya dawo ya fada ma Imam Husain, sai ya ji yara suna kuka suna qishi-qishi, jin haka Abbas ya hau dokinsa ya dauki makaminsa da kuma tulu wato abin zuba ruwa suna ganinsa ya doso su, suka kama harbinsa da masu amma haka ya fuskance su ya keta su har ya isa ga ruwan an ce a wajen sai da ya kashe maqiya 80 wato cikin masu gadin ruwan, lokacin da yai nufin ya sha ruwan sai ya tuna halin da Imam Husain da Ahli baitinsa suke ciki na qishi sai bai sha ba ya ciki tulun kawai, ya kamo hanya domin kawo masu, maqiyan suka sake taso masa duk wanda ya fuskance shi gaba da gaba ya kashe shi to daga qarshe suka yi masa abinda ake cema kwantan bouna wato suka labe a wasu wajaje akan hanyar daga qarshe dai bai samu dawowa ba, yai shahada. 3- Abdullahi dan Ali. Wannan qanin Abul fadal Abbas ne, lokacin da ya yi shahada yana da shekaru 25 ne 3-Ja’afar dan Ali ya fito bayan shahadar Abdullah wanda shima yai yaqi sosai har yai shahada. 5- Usman dan Ali. Bayan shahadar ja’afar dan Ali sai qaninsa Usman dan Ali ya fito shima ya fuskanci maqiya ya kashe wasu daga ciki har yai shahada lokacin yana da shekaru 21 a Duniya. Wani tanbihi a nan shine irin wadannan sunayen da A'imma suka sa ma ‘ya’yansu yana da alaqa da wasu daga cikin sahabbai ne misali Usman da Imam Ali ya sa ma dansa yana da alaqa da sunan Usman dan Maz’un ne yana daga cikin manyan sahabban Manzon Allah, yazo a tarihinsa cewa Manzon Allah yana son sa sosai. Kuma ya rasu tun lokacin Manzon Allah yana raye bayan komawarsa Madina ba da jimawa ba, ya ma zo akan cewa shine sahabi na farko da ya rasu a Madina, saboda shine sahabin farko da aka binne a Maqabarta Baqi’a da ke Madina. 6- Abubakar dan Ali. 7- Muhammadul Asgar dan Ali.
B- Ya’yan Imam Hassan da suka yi shahada a waqi’ar Karbala: Idan mutum ya binciki tarihi zai ga cewa Ya’yan Imam Hassan da suka yi shahada a waqi’ar Karbala su ukku ne, ga sunayensu: 1- Abdullah dan Hassan. Ya zo a tarihi cewa bayan da aka kashe Qasim dan Hassan sai Abdullahi dan Hassan ya fito domin mubaraza, kafin shahadarsa ya kashe maqiya 14. 2- Abubakar dan Hassan. Shine mijin Sukaina ‘yar Imam Husain, a wata ruwaya ya zo akan cewa mahaifiyar su daya da Qasim dan Hassan wato shaqiqai ne 3- Qasim dan Hassan. Lokacin da Qasim ya nemi izinin Imam Husain domin fitowa sai bai bashi izini ba kasantuwarsa yaro amma yai ta magiya ga Imam Husain, sai ya bashi izini,to zai fita an ce Imam Husain ya yi kuka sosai. Ya fuskanci maqiya har ya kashe wasu daga cikinsu daga qarshe yai shahada, lokacin da Imam Husain ya zo wajensa ya ce, “ Tir da mutanan da suka kashe ka, kuma kakan ka zai yi husuma dasu ranar qiyama. Sai Imam Husain ya ce, ya girmama ga Amminka ka kira shi bai amsa maka ba, ko kuma ya amsa maka amma bai yi maka amfani ba. Da yake lokacin da wanda ya shahadantar da shi ya sare shi a wuya sai qasim ya ce “YA AMMA” Wato yana kiran Imam Husain ya kawo masa agaji to shine da Imam Husain yazo wajensa yake yi masa wannan jawabi.
C- Ya’yan Imam Husain da suka yi shahada a waqi’ar Karbala: Wadanda suka yi shahada a cikin Ya’yansa su biyar ne, ga sunayen su: 1- Aliyul Akbar dan Husain, shine babban da na farko na Imam Husain, kuma yazo a kan cewa ya yi kama da Manzon Allah sosai a halittarsa kai ma har da maganarsa tafiyarsa, bayan wafatin Manzon Allah da an ganshi sai a tuna da Manzon Allah, shi yasa lokacin da ya fito fagen daga domin mubaraza a ranar Ashura, Imam Husain yai kuka ya daga kan sa zuwa sama ya ce, “ Ya Allah ka yi shaida akan wadannan mutane, yaro wanda ya yi kama da Manzon Allah a halitta da dabi’u da magana ya fito domin mubaraza da su, mun kasance idan mun yi shauqin Manzon Allah mu kan dubi fuskarsa, a taqaice dai saboda gayar kamar sa da Manzon Allah har laqabi ake yi masa da Ahmadus sani. Akwai wani abu da ya taba faruwa bayan wafatin Manzon Allah, sahabban Manzon Allah wata rana sai suka ga wani banasare wato kirista ya zo Masallacin Manzon Allah, sai suka ce masa mi ya shigo da kai masallaci alhali kai banasare ne, sai ya ce masu ai ya Musulunta, shine ya ce masu ya yi mafarki da Isa dan Maryam tare da Manzon Allah sai Annabi Isa ya ce masa ka Musulunta a hannun Manzon Allah domin shine Manzon wannan zamanin kuma cikamakin Manzanni, to shine na Musulunta, to yanzu na zo a nuna min zuriyyarsa in musulunta a bayyane a hannunsu, to shine aka kai shi wajen Imam Husain, sai ya sake Musulunta a hannunsa, bayan haka sai Imam Husain ya aika a ce Ahmadu sani ya zo lokacin yana qarami sosai, to da ya zo banasaren yana ganin sa nan take ya suma, sai Imam Husain yasa a yayyafa masa ruwa, da ya farfado ya tambaye shi wanda ka gani a mafarki ya yi kama da wannan yaron, to shine ya ce tabbas kamar su daya sosai wato da ya ganshi ya dauka Manzon Allah ne shine har ya suma. Ahmadu sani yazo a Tarihi cewa shine shahidi na farko wato jinin Ahlulbait da aka kashe a filin Karbala duk da wata ruwaya ta nuna shahidin farko cikin jinin Ahlul bait shine Abdullah dan Muslim dan Aqil, amma dai ruwayar da tafi shahara ita ce cewa Aliyul Akbar shine ya fara shahada, kuma in mutum ya karanta ziyarar shahidan Karbala zai ga cewa ta fara da cewa “ Assalamu alaika ya Awwala qatilin min nasli khara salilin ma'ana Sallama gareka ya farkon wanda aka kashe daga tsatso, mafi alhairin tsatso. Lokacin da ya yi shahada yana da shekaru 25 a duniya ne. Kuma ya kasance Jarumi sosai saboda kafin shahadarsa sai da ya kashe mutum 120 cikin rundunar maqiya. 2- Abdullah dan Husain. Sauran guda ukkun duka Jarirai ne amma wanda sunan sa ya fi shahara a cikinsu shine Abdullahi-Radi’i. A dukkan shahidan Karbala Abdullahi Radi’i shine wanda Imam Husain ya haqa qabari ya binne shi, amma saboda gayar bushewar zukata na wannan Makiya sai da suka tona kabarin suka sare masa kai, wato lokacin da suke bin jikkunan shuhada’u suna sare kawukansu, to shine wani ya ce cikin wadanda suka kashe akwa wani jariri, kuma sun ga Husain ya tona rami ya binne shi, to shine suka ce shima a tono shi domin a sare kansa, haka ko suka yi, wadannan kawuka na shahidai haka suka kama hanya dasu har zuwa Sham, kowane kai a goshinsa aka sa sunansa, to lokacin da suka isa gaban Yazidu (LA) da kawukan sai ya ce su kwashe su duka amma su bar kan Imam Husain da na Abul fadl Abbas da kuma na Ahmadu sani, wanda wannan yana nuna gabarsu da qiyayyarsu ga Ahlul bait.
D- Ya’yan Ja’afar dan Abu Dalib:Ya’yansa da suka yi shahada a waqi’ar Karbala su biyu ne, ga sunayensu: 1- Aun dan Abdullahi dan Ja’afar. 2- Muhammad dan Abdullah dan Ja’afar. Abdullah dan Ja’afar shine mijin Sayyida Zainab kuma Aun da Muhammad ‘ya’yanta ne, saboda haka ‘ya’yanta biyu suka yi shahada a Karbala. Yazo a tarihi cewa abin da yasa Abdullahi dan Ja’afar wato mijin Sayyida Zainab bai fita da su Imam Husain ba daga Madina lokacin bai da lafiya ne, a wata ruwaya kuma Imam Husain ne ya ce masa ya tsaya domin kula da sauran Bani Hashim dake Madina. Aun ya kashe Maqiya 21 kafin shahadarsa, shi kuma Muhammad ya kashe maqiya goma.
E- Ya’yan Aqil dan Abu Dalib: Idan mutum ya binciki tarihi zai ga cewa wadanda suka yi shahada a cikin ‘ya’yansa a waqi’ar Karbala su hudu ne, ga sunayensu: 1- Muslim dan Aqil. Shine farkon wanda ya fara shahada a jinin Ahlul bait, kamar yaddda muka sani shi ya yi shahada a Kufa ne wato tun gabanin ma waqi’ar Karbala da wajen wata guda domin yai shahada a ranar 9 ga watan Zul-hijja wato ranar Arfa shekara ta 60 bayan Hijira. Kuma ‘ya’yan Muslim dan Aqil guda hudu suka yi shahada a waqi’ar Karbala biyu a filin Karbala ne suka yi shahada, biyun kuma bayan waqi’ar Karbala suka yi shahada. Wadanda suka yi shahada a filin Karbala sune 1-Abdullah dan Muslin dan Aqil, a wata ruwaya kamar yadda aka ambata cewa Abdullah dan Muslim dan Aqil shine ya fara mubaraza a jinin Ahlul bait kuma shine aka fara kashewa, amma akasin haka shi yafi shahara na cewa Aliyul Akbar shine ya fara shahada, Abdullahi dan Muslim shine na biyu a Shahada wato a jinin Ahlul bait kamar yadda Shekh Abbas Alqummiy ya yi bayani. kafin shadarsa Abdullahi dan Muslim ya kashe maqiya 98. Wani tambihi anan shine Muslim dan Aqil yana auren Ruqayya ne ‘yar Imam Ali saboda haka wadannan ‘ya’ya na Muslim da suka yi shahada a waqi’ar Karbala dukkansu ‘ya’yan Ruqayya ne ‘yar Imam Ali. 2- Ja’afar dan Aqil. Ya kashe maqiya 15 gabanin Shahadarsa 3- Abdurrahaman dan Aqil. Ya kashe maqiya 17 gabanin shahadarsa. 4- Abdullahil Akbar.
Daga qarshe kamar yadda aka yi bayani tun farko cewa shahidan Ahlul baiti da suka yi shahada a Karbala dukkansu nasabarsu tana tuqewa ne ga Abu Dalib, wannan yana daga cikin dalilan da yasa Bani umayya suke da gayar gaba da qiyayya ga Abu Dalib har ma suka sa aka qirqiro Hadisai wai bai Musulunta ba wal iyazu billah.

 
Home Maudu'oi daban-daban Shahidan Ahlul-Bait a waki'ar Karbala
Copyright © 2024. www.tambihin.net. Designed by KH