Thursday, 19 September 2024
Email
Make My Homepage
RSS
Register
Abubuwan da suka faru a tarihi a watan Shawwal Print E-mail
Written by administrator   
Saturday, 04 May 2024 11:13

Wannan wata na shawwal akwai abubuwa da yawa a tarihi da suka auku a cikinsa ga wasu daga ciki: Idan mutum ya bibiyi yaqoqin Manzon Allah (S) Wato wadanda suka gudana a rayuwarsa zai ga cewa mafi yawan su sun gudana ne a watan Shawwal, abinda da nike nufu a nan shine in ka bibiyi watannani Musulunci tun daga daga watan Muharram zuwa watan Zul-Hijja kowane wata daya bayan daya yaqoqin da suka auku a cikinsa na Manzon Allah zaka samu cewa mafi yawan wadannan yaqoqi sun auku ne a watan Shawwal misali: 1- Yaqin Khandaq ko yaqin Ahzab. 2- Yaqin Hunain. 3- Yaqin Uhud. 4- Yaqin Bani qainuqa. 5-Yaqin Bani Sulaim. Duk sun auku a watan Shawwal ne kamar yadda bayani zai zo a gaba cikin rubutun.
A 3 ga watan Shawwal shekara ta biyar bayan Hijira yaqin Khandaq ko yaqin Ahzab ya auku. A 4 ga watan Shawwal shekara ta 8 bayan Hijira aka yi yaqin Hunain. Wani tambihi a nan shine harin da Iran ta kaima haramtacciyar qasar Isra’ila ya kasance a cikin wannan wata na shawwal ne wato 4 gareshi a dai dai lokacin da ake tunawa da yaqin Khandaq da yaqin Hunain, wanda in mutum ya bibiyi Tarihi zai ga cewa asalin Sahabin da ya kawo wannan shawara ta yin wannan khandaq shine Salmanul Farisiy wanda kamar yadda muka sani asalinsa mutumin Iran ne. A lokacin da ake shawarwarin yadda za a bullo ma Maqiya kan harin da suke so su kawo, sai Salmanil Farisiy ya ce ya Manzon Allah mu mun kasance a Farisa idan maqiya suna so su kawo mana hari to mu kan haqa rami ta fuskacin da muke ganin zasu bullo sai ya zama shamaki tsakanin mu dasu, sai Manzon Allah ya amshi wannan shawara tashi kuma sahabbai suka yi farin ciki da ita har ta kai Ansarawa suka ce Salmun minna, wato Salmanu daga garemu yake, sai suma Muhajirin suka ce Salmun minna, to sai Manzon Allah ya ce masu, “Salmun minna Ahlul bait”. Akwai darussa ta fuskoki dabam dabam da suke da alaqa da yaqin Uhud, Insha Allah wani lokaci za a yi rubutu akai.
Har wala yau a 4 ga watan Shawwal shekara ta 329 bayan hijira farawar Gaibatul-Kubra na Imam Mahdi [AF] -A biyar ga watan shawwal shekara ta 60 bayan hijira Muslim dan Aqil ya isa Kufa, kuma wannan ya nuna waqi’ar karbala ba kamar yadda mafi yawa aka dauka ba cewa waqi’a ce wadda ta faro aka kuma gama ta cikin kwanaki kadan misali kwana goma ko rana guda, a’a waqi’a ce wadda a qalla an kwashe wata shidda wato daga farowar ta zuwa qarshen ta. Domin wannan waqi’a ta faro ne tun watan Rajab shekara ta 60 bayan hijira har ya zuwa 10 ga watan Muharram shekara ta 61 bayan hijira, mu duba tun 5 ga watan shawwal Imam Husain ya aika Muslim dan Aqil zuwa Kufa, wanda in mun lissafa zamu ga wata ukku gabanin shahadar Imam Husain [AS].
1-Daga cikin abubuwa na tarihi da suka auku a watan shawwal akwai cewa a ranar 8 ga watan shawwal shekara ta 1344 bayan hijira wahabiyawa suka rusa ginin qabarin Imam Hassan [AS], Imam Sajjad [AS], Imam Bakir [AS] da kuma Imam Sadik [AS] wato a maqabarta ta Baqi’a dake Madina, idan mutum ya lissafa zai ga cewa yau shekaru dari da daya da faruwar wannan abin baqin ciki wato tun da yanzu muna shekara ta 1445 ne bayan Hijira. Ga wanda ya san tarihi da kuma Aqidu na wahabiyawa wannan ba zai bashi mamaki ba, in ma mutum bai san tarihinsu ba ko aqidunsu to ya dubi masu fahimta irin nasu a wannan nahiya da yake zaune zai ga in sun samu dama suna aiki irin nasu misali sai ka ga gine-gine na qaburbura na wasu sai a wayi gari an rushe gine-ginen. A kan wannan asasi in muka duba zamu ga a yau wajaje masu yawa na tarihi a Makka da Madina an rasa su misali gidan da aka haifi Manzon Allah a Makka, tsawon tarihi wannan gida mai albarka yana nan har massallaci aka yi a wajen, musulmi na ziyartar gidan da kuma massallacin su yi sallah ciki domin neman tabarruki, amma abun baqin ciki a shekarar 1926 mahukunta sa’udiyya suka sa aka rusa gidan da masallacin. Haka nan ma qabarin mahaifin Manzon Allah shima aka rusa aka yi titin mota a wajen, wannan a Madina ke nan domin mahaifin Manzon Allah ya rasu a Madina ne. Dalilin zuwan sa Madina shine lokacin da mahaifiyar Manzon Allah wato Aminatu bintu Wahab tana da cikin sa wata bakwai, sai kakan Manzon Allah Abdul-Mudallab ya tafi Madina tare da mahaifin Manzon Allah wato Abdullahi, saboda su sawo kayan walima idan ta haihu. To bayan isar su Madina ba da jimawa ba sai Abdullahi ya kamu da rashin lafiya, bayan jinya da yayi ta kwana 15 sai ya rasu aka binne shi a Madina, kuma qabarin sa tun wancan lokacin har ya zuwa shekaru 50 da suka wuce yana nan, domin akwai wani malami dana ji yana bayani a wannan munasaba ta rusa ginin qaburburan Aimma [AS] da ke Baki’a yake cewa shekaru 40 zuwa 50 da suka wuce in ya tafi aikin hajji ya kasance ya kan ziyarci kabarin mahaifin Manzon Allah [S] to amma abin mamaki wani zuwa da yayi sai ya ga an rusa kabarin titin mota ya biyo ta wajen. Ire-ire wadannan abubuwa na shafe da kuma kauda ababe na tarihi da mahukumta sa’udiyya suka yi kuma suke kan yi suna da yawa, wato a qoqarinsu na kau da duk wani abu dake tunasar da mutane tarihin addinin musulunci ko kuma hana mutane neman tabarrukinsu.
2- A 14 ga watan Shawwal shekara ta 252 bayan Hijira wafatin Sayyid Abdul Azim Al-hasniy, yanzu haka qabarinsa na Rayyi ne wato a kudancin Tehran kusa da kabarinsa akwai na Hamza dan Imam Musa Al-kazim. Sayyid Abdul Azim yana daga cikin jikokin Imam Hassan shi yasa ake ce masa al-hasni kuma ya yi zamani da Imamai guda biyar sune Imam Kazim, Imam Ridha, Imam Jawad, Imam Hadi da Imam Askariy wato an haife shi a zamanin Imamancin Imam Kazim ya rasu a zamanin Imamancin Imam Al-askariy, yazo a tarihin sa cewa ya kasance mai yawan ilimi wato babban Malami ne har ta kai ga cewa Imam Ali al-hadi ya kan bada umarni ga mabiyansa da suke kusa da Sayyid Abdul Azim cewa tambayoyi na al’amuransu na Addini suna iya gabatar masa ba sai sun zo samarra ba sun same shi, a taqaice dai Imam Hadi yayi kyakkyawan yabo gareshi. Imam Ali al-hadi ya ce wanda ya ziyarce kamar ya ziyarci Imam Husain, shi yasa mabiya Ahlul bait da yawa da suke kewan idan munasabobin ziyarar Imam Husain ya zagayo basu samu zuwa Karbala ba to sukan zo su ziyarci shi Sayyid Abdul Azim. Haka nan ya zo a tarihinsa gab da rasuwarsa in da za a binne shi , sai ma wajen yai mafarki da Manzon Allah cewa za a binne wani jika daga cikin jikokina idan an buqaci sayen wajen ya sayar, da yake lokacin wajen a matsayin gona yake, a lokaci guda kuma wani bawan Allah shima yai mafarkin Manzon Allah yana shaida masa idan wane ya rasu a binne shi a waje kaza, sai mutumin yaje ya samu mai wajen ya ce yana buqatar ya sai masa da wajen domin ga mafarkin da yayi sai ya ce masa lalle shima yai wannan mafarki da Manzon Allah, a taqaice da Sayyid Abdul Azim ya rasu sai aka binne shi a wannan waje, kuma tun daga lokacin har zuwa yanzu wajen ya kasance wajen ziyara.
3-Daga cikin abubuwa da suka auku a watan shawwal na tarihi akwai cewa a 15 ga watan shawwal shekara ta ukku bayan hijira aka yi yaqin Uhud, kuma a wannan rana ce sayyiduna Hamza yayi shahada, a kan asasin haka anai masa laqabi da shugaban shahidai wato na zamaninsa wato kamar yadda Sayyida Maryam take shugaban mataye na zamaninta. Har wala yau a ranar 15 ga watan Shawwal shekara ta biyu bayan Hijira aka yi yaqin Bani qainuqa.
4-Daga cikin abun da suka auku a tarihi a watan shawwal akwai cewa a 17 ga watan shawwal shekara ta 2 bayan hijira aka yi yaqin Bani Sulaim.
5- Haka nan a ranar 25 ga watan shawwal shekara ta 148 bayan hijira Imam Sadiq [AS] ya rasu a Madina. Nan wasu sassa ne na rayuwar Imam Sadik [AS].
1-Haihuwarsa: An haife shi a Madina ranar jumma’a 17 ga watan Rabiul-Awwal shekara ta 83 bayan hijira.
2- Nasabarsa: Sunan mahaifiyarsa Fatimatu ‘yar qasim, sunan mahaifinsa Imam Muhammad Al-baqir [AS]
3-Nash’a dinsa: Imam Sadiq ya tashi a Madina ya rayu a Madina ya kuma rasu a Madina wato baki daya rayuwarsa a Madina ne ta kasance.
4- Laqubbansa: Yana da laqubba masu yawa amma wanda yafi shahara shine Sadiq, kuma ana yi masa kinaya da Abu Abdullahi.
5-Shekarunsa: Imam Sadiq ya rasu yana da shekaru 65 a duniya a wata ruwaya 68, a cikin imamai baki daya in ka cire Imam Mahdi [AF] to Imam Sadik [AS] ne yafi su yawan shekaru a duniya, mai bi mashi a yawan shekaru shine Imam Ali [AS] ya bar duniya yana da shekaru 63 ne.
6-Muddan Imamancinsa: Shekaru 34 ne.
7-‘Ya’yansa: Imam Sadik [AS] yana da ‘ya’ya 10, maza 7, mata ukku.
8-Wafatinsa: Ya rasu 25 ga watan shawwal shekara ta 148 bayan hijira.
9-Kabarinsa: Yana a Madina ne.
6-Haka nan daga cikin abubuwan da suka auku a tarihi a watan shawwal akwai rasuwar Imam Khumaini, domin a lissafi na watannin musulunci Imam Khumaini ya rasu ne a 28 ga watan shawwal shekara ta 1409.
2- Nasabarsa: Sunansa Sayyid Ruhullah, sunan mahaifinsa Sayyid Ayatullah Mustapha, sunan mahaifiyarsa sayyida Hajar, wato shi sayyid ne ta wajen uwa da uba.
3-Shekarunsa: Ya rayu a duniya shekaru 93 ne.
4-Shekarun da ya yi bayan juyin musulunci: Ya rayu kusan shekaru 10 ne.
5-‘Ya’yansa: Yana da ‘ya’ya Takwas maza ukku mata biyar.
6-Kabarinsa: Yana a birnin Tehran ne wato babban birnin Iran.
Daga qarshe kasantuwar bamu jima da fitowa watan Ramadan ba mutane suna ganin watan ya yi gudu wato har ya kama kuma ya fita, idan muka lura sosai zamu ga cewa watannin baki daya haka suke gudu. kuma wannan sakamako ne na zunubai da mutane suke aikatawa kamar yadda Imam Ali yake cewa a wani Hadisi “ Idan al’ummar Manzon Allah sun tozarta Sallah, kuma suka bi sha’awaice-sha’awace, Amana tai qaranci kuma yaudara tai yawa, aka yi algusshu cikin mu’amala, aka yawaita zunubai, aka qaranta kyawawan aiki, cin rashawa ya yawaita, kunya ta qaranta, luwadi da madigo suka waita, zalunci ya yawaita da kuma shaidar zur. To a lokacin shekara za ta zama kamar wata, wata kuma kamar mako,, mako kuma kamar yini, yini kuma kamar sa’a guda, sa’a kuma bai da wani qima”. Saboda haka skamakon wadannan munanan ayyuka lokaci ya zama haka, mai wayau shine wanda ya cika lokutansa da ayyukan alhairi.
Ana ce ma wannan wata shawwal saboda a cikinsa an goge dukkan zunuban mu’uminai. Saboda haka wannan wata, wata ne da mutum ke shiga cikinsa yana tsarkakakke daga zunubai, wato kasantuwar mutum ya fito cikin watan Ramadan wanda ana fata a cikinsa Allah [T] ya gafarta ma mutum dukkan zunubansa. Saboda haka watan shawwal wata ne da ake so mutum ya yi mujahada wajen ganin cewa tsarkakar da ruhinsa ya samu a watan Ramadan daga zunubai, ya yi iyaka iyawarsa wajen ganin cewa bai sake qazantar da ruhinsa ba ta hanyar aikata zunubai na zahiri da badini, domin zunubi guba ne ga ruhin dan Adam. Haka nan tarbiyya da mutum ya samu a watan Ramadan na ibadodi da Aklaq, mutum yayi qoqari ya dore a kai har ya zuwa wani watan Ramadan insha-Allah. Domin idan ya kasance watan Ramadan ya kama ya fita amma mutum bai samu sauyi a ruhinsa ba,wato zuciyarsa ba ta tasirantu da hasken watan Ramadan ba, to lalle duhun zunubin sa ya mamaye zuciyarsa, Shi yasa yana da muhimmanci bayan watan Ramadan mutum ya zauna yayi ma kansa muhasaba, ya tambayi kansa cewa akwai banbanci da ya samu a rayuwarsa a addinance a bayan watan Ramadan da kuma kafin watan Ramadan, in akwai banbanci wato mutum yanzu ya samu ci gaba to alhamdu-lillahi haka ake so, in ko yaga ci baya ma yayi to mutum ya zama mai zaluntar kansa, in ko ba wani banbanci wato bai yi gaba ba kuma bai yi baya ba to mutum ya zama mai taqaitawa wato muq-tasid. Saboda haka wannan haske da kuma tsarkaka na ruhi da mutum ya samu albarkacin watan Ramadan ka da mutum ya sake ya gushe, kuma babbar hanya ta yin haka shine nisantar zunubi. Haka nan kuma tarbiyyar da mutum ya samu da kuma gina shaksiyyar sa da ya yi a watan Ramadan ya dage da mujahada wajen ganin cewa bata rushe ba.

Last Updated on Saturday, 04 May 2024 11:16
 
Home Maudu'oi daban-daban Abubuwan da suka faru a tarihi a watan Shawwal
Copyright © 2024. www.tambihin.net. Designed by KH