Falalar Ziyarar Arba'in na Imam Husain (AS) |
Written by Administrator | |||
Wednesday, 06 September 2023 18:03 | |||
20 ga watan Safar ita ce Ranar Arba’in din Imam Husain (AS) wato da shahadarsa. Rana ce wadda take da muhimmanci, musamman ma ga mabiya Ahlul bayt (AS), Saboda ma muhimmancinta mabiya Ahlul bait daga sassan Duniya dabam-dabam suke zuwa Karbala domin ziyarar Imam Husain. kuma daga cikin falalar ziyara ranar yana daga cikin alamomin mumini kamar yadda aka ruwaito daga Imam Hassan Al-askari (AS), in da ya ce, “Alamomin mumini (wato dan shi’a) guda biyar ne. 1.Yin salla raka’a 51 ko wace rana. 2.Ziyarar arba’in. 3. Sa zobe a dama. 4. Sa goshi a qasa (ta’afir). 5. Bayyana karatun bismillah a sallah.” Insha Allah a wannan rubutu dai-dai gwargwado za’a yi bayani ko sharhi ga wannan Hadisi da aka ruwaito daga Imam Hassan Al-askari (AS) da nufin mu aikata su wato mu siffata da su. Amma kafin bayani dangane da wannan hadisi da kuma ranar arba’in din, zai yi kyau a dan yi bayani a taqaice dangane da matsayin adadin arba’in a addinin musulunci. Adadin arba’in yana da wani asrar gaibiyya a wajen Allah (T) da kuma tarkizi na musamman a wasu ayoyi na Al-qur’ani mai girma, da kuma wasu hadisai da aka samo daga Manzon Allah (S) da kuma Ahlul bayt (AS), ga misalin wasu daga cikin wadannan Hadisai, an ruwaito daga Imam Sadiq (AS) ya ce, “ Idan mumini ya rasu, mutane 40 daga muminai suka halarci jana’izarsa, cikin addu’ar da sukayi masa suka ce ‘ ya ubangiji Bamu san komi dangane dashi ba sai alheri, kai ka fimu saninsa, Allah (T) zai ce na zartar da shaidarku, na gafarta masa na abin da na sani da abunda ku baku sani ba.”. Haka nan kuma daga Imam Sadiq (AS) ya ce, “Babu wasu jama’a 40 da zasu hadu su yi addu’a a kan wata buqata tasu face Allah (T) ya karba musu”. Har ila yau daga Imam Sadik (AS) ya ce, “ Duk wanda ya gabatar da muminai 40 gabanin addu’arsa, bayan haka ya gabatar da addu’a ta buqatarsa, to Allah (T) zai karba masa” kuma wannan wani abu ne wanda yake da gayar muhimmanci da falala, na cewa kowannenmu ya sabawa kansa da yin haka, wato na addu’oi ga muminai guda 40, in son sa mune a kowane dare a qunut na witri, ko kuma bayan ya gama sallar tahajjud dinsa, in ba zai iya yi ko wane dare ba to aqalla duk daren juma’a mutum ya lizimci hakan, domin yin hakan ya na da fa’idodi masu yawan gaske, kuma sunna ce daga cikin sunnonin ma’asumai (AS), alal misali yazo akan cewa sayyida fatima (AS) in ta gama sallar tahajjud dinta, takan yi addu’oi ga muminai na kusa da na nesa, shine har Imam Hasan (AS) yake ce mata “ Na kan ji ki kan yi addu’oi ga mutane, amma ban ji kina addu’a gare ki ba ”. shine ta ce masa, “ Maqwabci gabanin gida” Haka nan kuma akwai Hadisi da aka ruwaito daga Manzon Allah (S) ya ce, “ Duk wanda ya kiyaye wa al’ummata Hadisai 40 da suka shafi al’amarin addininsu, baya nufin komai face yardar Allah (T) da kuma gidan lahira, to Allah zai tashe shi ranar qiyama a matsayin faqihi kuma Malami” wannan Hadisin yasa da yawa daga cikin malaman madrasah din Ahlul bayt (AS) da kuma ta Ahlus sunna, suka rubuta littafai na Hadisai 40 domin samun falalar wannan Hadisi, misali a nan shine littafin hadisi 40 na Imam khumaini da kuma littafin hadisi 40 na Imam Nawawi, in mutum ya duba littafin Hadisi 40 na Imam khumaini, zai ga cewa a wajen gabatarwa na littafin yana cewa ya tattara wannan Hadisai ne da fatan ya samu shiga cikin Hadisin Manzon Allah [S] da yazo akan cewa “Wanda ya kiyaye wa al’ummata Hadisai 40 da suke amfana dasu, to Allah zai ta da shi ranar al qiyama a matsayin faqihi kuma Malami”. Da dai Hadisai da dama da suka zo akan Tarkizi kan 40, wanda ba za a iya kawo su ba saboda gudun tsawaitawa. Dawowa ga wannan Hadisi da aka samo daga Imam Askari [AS] na alamomin mumini guda biyar, alama ta farko, kamar yadda yazo a hadisin, shine yin Raka’a 51 ko wace rana, wannan raka’a 51 ya hada da sallolin wajibi da nafilfilinsu da kuma sallar tahajjud tare da shafa’i da witri, a warware ga lissafin adadin raka’oin na sallolin wajibi, wato daga sallar Asuba zuwa sallar Isha’i, in mutum ya ha]a zai ga 17 ne, sai nafilfilinsu, sune raka’a 2 gabanin Asuba, raka’a 8 gabanin sallar zuhur, raka’a 8 gabanin sallar Asar, raka’a 4 bayan sallar maghrib, raka’a 2 a zaune bayan isha’i (watira), amma biyun nan yana matsayin raka’a daya ne, sallar tahajjud raka’a 8, shafa’i 2 witri 1, in mutum ya hada zai ga lissafin ya tashi 34, wato na raka’oi na nafilfilin, in mutum ya hada da wadancan raka’oi na wajibi 17, zai ga ya tashi akan 51, To wadannan raka’oi 51 sune a ke so kowane mumini, wato mabiyin Ahlul bayt (AS) ya tsayu da yinsu kowace rana ba tare da yin fashi ba. ko da za ta kai a ce mutum bai samu yin su nafilfilin ba, saboda wani uzuri, to yazo akan cewa ana son mutum ya rama su. Misali a ce bai samu yin nafilfilin zuhur da asar ba, ya na iya ramka su a cikin yini din, ko kuma da daddare. In kuma bai samu yin nafilfilin dare ba, wato kamar maghrib ko isha’i, ko kuma sallartahajjud dinsa, to ya na iya ramka su a daren, ko kuma washe gari cikin yini. Wato ya tsayu akan yin haka kowa ce rana ba tare da fashi ba. A in da kawai wadannan nafilfilin suka fadi shine a halin tafiya, a nan nafilfilin zuhr da asar sun fadi, amma sauran nafilfilin na sallar maghrib da isha’I da asuba da kuma tahajjud, shafa’i da witri, su basu fadi ba. Wato dai a halin tafiya nafilflin sallolin rana ne suka fadi, amma nafilflin dare basu fadi ba. kuma wadannan raka’oi 51 mutum ya kwatanta su da raka’a dubu daya da Imam Aliy (AS), Imam Husain (AS), Imam zainul Abidin (AS) da kuma Imam Ridah (AS) suke yi ko wace rana, zai ga daya bisa 20 ne. kuma su wadannan raka’oi 51, su ake cewa salloli na yaumiyyah. Akwai kuma salloli na usbu-iyyah, wato na mako, suma an ruwaito sune daga Manzon Allah (S) da kuma Aimma na Ahlul bayt (AS), wato wadannan kwanaki bakwai na mako, misali daga juma’a zuwa Asabar to kowace rana da kuma dare na wadannan kwanaki na da na ta sallolin, littafai da dama sun kawo wadannan sallolin, misali littafin Diya’us Salihin. Ga wanda bai da wannan littafin to ga yadda sallolin suke a Daren juma’a raka’a 2, ko wace raka’a mutum zai karanta qul-huwallahu 70. wannan an samo daga Manzon Allah ne. Sai kuma ranar juma’a raka’a 8, ko wace raka’a qul-huwallahu 1. Daren Asabar raka’a 4, kowace raka’a bayan fatiha, sai kul-huwallahu 7, sai kuma ranar asabar raka’a 4, kowace raka’a bayan fatiha, qul-ya Ayyuhal- kafirun sau 3 bayan sallama ta raka’a 4, sai mutum ya karanta Ayyatul - kursiyu sau daya, sai daren lahadi raka’a 6, ko wace raka’a bayan fatiha, qul-huwallahu sau 7, sai ranar lahadi raka’a 2, raka’a ta farko bayan fatiha, Inna -A’adaina sau 3, raka’a ta biyu bayan fatiha qul-huwallahu sau 3, sai daren litinin raka’a 2, kowace raka’a bayan fatiha, Ayatul kursiyu, qulhuwallahu, sai suratul falaqi da nasi, dukkansu sau daya, bayan sallama sai istigfari sau 10. sai ranan litinin raka’a 4, raka’a ta farko bayan fatiha Ayatul kursiyu daya, raka’a ta biyu bayan fatiha, qul-huwallahu daya, raka’a ta uku bayan fatiha, suratul falaqi, raka’a ta hudu bayan fatiha suratu Nasi, Daren talata raka’a 2, raka’a ta farko bayan fatiha, inna- Anzal-nahu sau 1, raka’a ta biyu bayan fatiha quhuwallahu 7. Ranar talata raka’a 2, kowace raka’a bayan fatiha, wattini, qul-huwallahu, falaqi da nasi, dukkansu sau daya. Daren laraba raka’a 2, bayan fatiha, kowace raka’a Ayatul kursiyu, inna Anzal nahu, iza-ja’a sau dai-dai, sai kuma qulhuwallahu sau 3, Ranar laraba raka’a 2, kowace raka’a bayan fatiha, iza-zul sau 1, sai kuma qulhuwallahu sau 3. Daren Alhamis raka’a 6, kowace raka’a bayan fatiha qul-ya Ayyuhal kafirun sau daya, sai qulhuwallahu sau 3, bayan sallamewa duka, wato raka’a 6 din, sai mutum ya karanta Ayyatul kursiyu sau 3, sai ranar alhamis raka’a 2, bayan fatiha kowace raka’a iza-ja’a da kuma inna -A’adaina ko wace sau 5. To,irin wadannan salloli su ake cewa sallolin usbu’iyyah, wato na mako. in mutum ya duba cikin littafin jamalul-usbu’i, na sayyid Ibn dawus da kuma littafin mir’atul kamal, zai ga duk sun kawo su. Su ma wannan ya na da kyau kowannen mu ya tsayu dasu, wato baya ga wancan raka’a 51 na yaumiyyah. Sai kuma sallah ta shahariyya, wato ta wata, ita kuma yadda take shine; idan ka yi ta a daren farko na ko wane wata, sai kuma wani sabon wata a daren farko, haka nan in ka yi a ranar farko na wata, sai kuma wani wata a ranar farko. shine ake ce mata shahariyya. mutum na iya duba sallolin a littafin Mafatihul Jinan babi na 2 fasali na 11. Ga wanda bai da imkaniyyar dubawa ga yadda sallolin suke. Daren farko na kowane wata raka’a 2, kowace raka’a bayan fatiha, sai ya karanta suratul An’am, idan mutum bai haddace ba yana iya amfani da Al’qur’ani domin karanta suratul An’am din. sai kuma ranar farko ta ko wane wata, shima raka’a 2, raka’ar farko bayan fatiha, qul-huwallahu 30, sai raka’a ta biyu bayan fatiha, Inna -Anzal nahu 30. Suma wadannan sallolin an samo ne daga A’imma na Ahlul bayt (AS), suma wadannan salloli na wata-wata ana son mutum ya tsayu dasu, wato ko wane wata daren farkonsa da kuma ranar farkonsa ya zamo mutum na yi ba tare da fashi ba, sai in da wani uzuri. Sai kuma salloli na sanawiyya, wato shekara- shekara, su kuma yadda suke, in ka yi su misali yau, to sai kuma wata shekara zaka sake yinsu. Irin wadannan salloli sun zo ne jefi-jefi a cikin kwanuka na shekara, wato ba kullum ake yinsu ba. misalin irin wadannan salloli na sanawiyya sune kamar sallar ranar qarshe ta shekara, ko kuma sallar daren Ashura, to ire-iren wadannan salloli sune ake cewa salloli na shekara. misali sallolin da suka zo na daren Ashura, yanzu mutum ba zai sake yinsu ba, sai kuma shekara mai zuwa in Allah (T) ya kai mu wani daren Ashurar na shekara mai zuwa. Yanzu sallah ta sanawiyya dake gabanmu itace ta 17 ga watan Rabi’ul Awwal, wato ranar maulidin Manzon Allah (S), in mutum ya duba mafatihul jinan zai ga sallah din, kuma wadannan watanni 12 na musulunci, in mutum ya bisu daya bayan daya zai ga ba wani wata wanda babu sallar sanawiyya a cikinsa. Shima wannan wato sallah na shekara-shekara ya na da kyau kowannen mu ya tsayu dasu. Saboda haka in muka duba a wannan nizami, wato tsari zamu ga akwai salloli na yaumiyya, Usbu’iyya, shahariyya, da kuma sanawiyya, kuma duk wadannan salloli an ruwaito sune daga Ma’asumai (AS). Saboda haka ya na da muhimmanci tsayuwa da sabati na yin wadannan salloli domin koyi dasu da kuma samun ladar dake cikin su, kuma kamar yadda muka ga wannan nizami guda hudu na salloli, to haka nan ma addu’oi na da nizami wato tsari na yaumiyya, usbu’iyya, shahariyya, da kuma sanawiyya. Haka nan ma shi Azumi yana da wannan nizamin guda hudu, haka nan surori na Alqur’ani suma suna da wannan nizami guda hudu, wato akwai surorin da ake son karantawa yaumiyya, akwai usbu’iyya, shahariyya da kuma surori na sanawiyya. insha Allah dukkansu za’a yi bayanin su a muhallinsu. Abinda yake da gayar muhimmanci shine aikata su har ya zamanto mutum ya saba da yin haka, ta yadda ko da rashin lafiya za ta bijiro ko wadansu shugul da ya sa bai samu yin su ba kamar yadda ya saba to insha Allah ana fatar za a rubuta masa lada kamar ya yi sune, sabanin ko sai jefi-jefi ne yak e yin su to ka ga wannan bai da tabbacin ko za a rubuta masa ladar. Wannan shine bayani a taqaice dangane da alamar mumini na farko. Sai kuma alama ta biyu kamar yadda ya zo a hadisin, wato ziyarar Arba’in din Imam Husain (AS) a 20 ga watan safar, wato kwanaki 40 bayan shahadarsa (AS), ya na daga cikin alamomin mumini wato mabiyin Ahlul Bayt (AS). Kuma ita wannan ziyarar, imma ta kasance daga kusa ne ko daga nesa, wato in mutum ya na da iko da kuma damar zuwa karbala domin ziyara ko kuma yin ziyarar daga garin da yake. A kan wannan asasin ne zamu ga mabiya Ahlulbaiti (AS) daga sassan duniya daban -daban da suke da ikon zuwa karbala, musamman ma wadanda suke cikin kasar iraqi, suke tururuwa zuwa karbala domin wannan ziyarar ta Arba’in, wanda mutum zai iya dukan qirji a wannan zamanin namu, ya ce babu wani taro da yake tara mutane a doron qasa kamar wannan ziyarar ta Arba’in a karbala. Ta yi wu mutum ya yi tunanin taron aikin hajji.To, duk shekara taron bai kai wa miliyan biyar, galibi miliyan biyu ne zuwa uku. To, amma mu duba taron jama’a na ziyarar arba’in din Imam Husain (AS) a karbala na shekarun bayan nan da suka wuce, akan samu jama’a sama da miliyan 15, kuma ko wace shekara adadin qaruwa ya ke yi, wannan aya ce babba ga masu tunani. Kuma wani abin lura shine wasu dake cikin qasar Iraqi sukan tako ne da qafa daga garuruwansu, har ya zuwa karbala domin wannan ziyarar. Za ka gansu maza da mata yara da manya da ma dattijai. kuma a irin wadannan hanyoyi na zuwa karbala za ka ga akwai bayin Allah [T] daban daban da suke gabatar da hidima ta fuskoki daban daban ga wadannan matafiyan zuwa karbala, kuma dukkan wadannan hidimomin kyauta suke gabatar dasu wato fi-sabi-lillah. Akwai masu bada abinci a hanyoyin, akwai masu bada masaukai, misali mutum ya yo tafiyan kwanaki daga garinsu, ya na son ya huta kafin ya cigaba da tafiya, to, ga masauki fisabilillah. Akwai likitoci, ga masu gyaran takalmi, ga masu hanyoyi na sadarwa, wato tarho shima duk kyauta ga wadannan matafiya zuwa karbala, da dai abubuwa da yawa da ba a ambata ba na hidimomi, da wasu bayin Allah ke gabatarwa fisabilillah, Allah taala ya saka wa kowa da alhairi. Ita ziyarar Imam Husain (AS) ta kasu kashi biyu, akwai ziyara mud laqa, wato ita ce ziyara wadda ba ta kebanta da wani zamani ayyananne ba. Akwai kuma ziyara mak susa, wato ta ke banta da wani zamani ayyananne .To,ziyarar Arba’in ta na daga cikin ziyara mak susa. A wata ma’ana ziyara mak susa, ana ce mata ziyara sanawiyya, wato ta shekara-shekara. Domin idan ka yi ta sai kuma wata shekara. Misali wannan ziyara ta Arba’in. Ziyarar Imam Husain (AS) mak susa, kuma sanawiyya guda 10 ne sune: 1.Ziyarar Ashura,wato 10 ga muharram. 2.Ziyarar Arba’in, wato 20 ga watan safar. 3.Ziyarar ranar farko, ta watan Rajab. 4.Ziyarar 15 ga watan Rajab. 5.Ziyarar 3 ga watan sha’aban, wato ranar haihuwar Imam Husain (AS). 6.Ziyarar daren 15 ga watan sha’aban. 7.Ziyarar daren lailatul qadr 19, 21, 23 na watan ramadan. 8.Ziyarar daren idi qarama da kuma daren idi babba. 9.Ziyarar rana kun idi qarama da babba. 10.Ziyarar ranar Arfa, wato 9 ga zul hijja. To dukkan wadannan kwanaki da aka ambata, mustahabbine ga mutum ya ziyarci Imam Husaini (AS) a cikin su daga kusa ko nesa. Ba ya ga wannan ziyara ta shekara ta Imam Hussain (AS) Akwai kuma ziyar usbu’iyya wato mako mako. Itace duk ranar litinin. Ga mai buqatar ganin wannan ziyara dama sauran ziyarori na Manzon Allah (S) da kuma Ahlul bait (AS) na mako, ya duba cikin littafin mafatihu, babi na daya fasali na biyar. Baya ga wadannan ziyarori mustahabbi ne yin ziyara a rana kun wilada da kuma wafati na Ma’asumai (AS), wato Manzon Allah (S) da kuma Ahlul bayt (AS), musamman ma rana kun wafatinsu, wato ya na da kyau mutum ya sunnanta ma kansa wannan sunna din, ya kasance duk ranar wilada ko wafati na daya daga cikin ma’asumai, mutum ya kasance ya ziyarce shi ziyara ta kusa ko ta nesa. Domin yin haka yana daya daga cikin hanyoyin kyautata alaqa da Manzon Allah (S) da kuma Ahlul bayt (AS) da kuma dan faruwa dasu qal- biyyan wato a zuci. A taqaice dai kiyaye wadannan rana ku na wilada da wafati na ma’asumai (AS) a matsayi na dai-dai ku da kuma jama’a, yana da gayar muhimmanci. Ga wata da kuma ranar wafatin ko wanne daga cikin ma’asumai (AS): 1.Manzon Allah (S) 28 ga watan safar. 2.Sayyida fatima (AS) 3 ga watan jimada-sani. 3.Imam Aliy (AS) 21 ga watan ramadan. 4.Imam Hasan (AS) 7 ko 28 (a wata ruwayar) ga watan safar. 5.Imam Husain (AS) 10 ga watan muharram. 6.Imam zainul Abidin (AS) 25 (a wata ruwaya) 12 ga watan muharram. 7.Imam Baqir (AS) 7 ga watan zulhijjah. 8.Imam Sadiq (AS) 25 ga watan shawwal. 9.Imam Kazim (AS) 25 ga watan Rajab. 10.Imam Ridha (AS) 23 ga watan zulqidah (a wata ruwaya) a watan safar. 11.Imam Jawad (AS) qarshen watan zulqidah. 12.Imam Hadi (AS) 3 ga watan Rajab. 13.Imam Askari (AS) 8 ga watan Rabi’ul Awwal. Wadannan sune rana ku na wafatin su, wato rasuwarsu. Sai kuma na wiladar su, wato haihuwar su kamar haka: 1.Manzon Allah [S] 17 ga Rabi’ul Awwal. 2.Sayyida fatima [AS] 20 ga watan jimada sani. 3.Imam Aliy [AS] 13 ga watan Rajab. 4.Imam Hasan [AS] 15 ga watan Ramadan. 5.Imam Husain [AS] 3 ga watan sha’aban. 6.Imam Zainul Abidin [AS] 5 ga watan sha’aban. 7.Imam Baqir [AS] 1 ga watan Rajab (a wata ruwaya 3 ga watan safar). 8.Imam Sadiq [AS] 17 ga watan Rabi’ul Awwal. 9.Imam Kazim [AS] 7 ga watan safar. 10.Imam Ridha [AS] 11 ga watan zulqidah. 11.Imam Jawad [AS] 10 ga watan Rajab. 12.Imam Hadi [AS] 2 ga watan Rajab. 13.Imam Askari [AS] 10 ga watan Rabi’us sani. 14.Imam Mahdi [AS] 15 ga watan sha’aban. Haka nan baya ga ziyara a wadannan kwanaki na wafati ko wilada na ko wannensu, akwai yin juyayi, in na wafati ne, da kuma yin murna, in na wilada ne, da kuma miqa ta’aziyya ga Manzon Allah (S) da kuma Ahlulbayt (AS) in na wafati ne, in kuma na wiladar ma’asumai ne, sai ya miqa murnarsa ga Manzon Allah (S) da kuma Ahlul bayt (AS) duk sai bayan mutum yayi musu sallama. Idan mutum ya duba ko kuma ya yi bincike zai ga cewa Imam Husain (AS) ya fi yawan ziyarori a cikin watannin shekara wato in ka kwatanta da sauran Ma’asumai(as), wato wannan yana nuna wata kususiyya ce ta musamman gareshi. Alama ta ukku ta mumini kamar yadda yazo a wannan hadisi da aka samo daga Imam Hassan Al-askari ita ce: Sa zobe a hannun dama, duk da cewa ta yi yu mutum ya ci karo da wasu hadisai da suke nuna cewa za a iya sawa a hannun hagu. To akwai malamai na imamiyya da suka yi bayanin cewa irin wadannan hadisai sun doru ne kan asasin taqiyya, saboda an yi zamanin da musamman ma zamanin Bani Umayya da sa zobe a hannun dama an mai da shi fitina babba, domin da an ga zoben mutum a hannun dama sai a ce to wannan dan shi’a ne, kuma wani abun mamaki har yanzu akwai gwuggubin haka, a tsakankanin wasu musulmi musamman ma qasashen larabawa. Domin sa zobe a hannun hagu kawai Muawiya ne ya sunna ta shi kuma ya gina jama’a a kai, wato saboda ya saba ma Imam Ali (AS) da kuma mabiyansa. Akwai ma wani da ya tambayi Imam Kazim (AS) cewa mi yasa Imam Ali yake sa zobe a hannun dama? Sai ya ba shi amsa da cewa: Yana sa zobe a hannun dama ne saboda shine shugaban ma’abuta dama bayan Manzon Allah, kuma Allah ya ya bi ma’abuta dama, ya kuma soki ma’abuta hagu. Kuma Manzon Allah ya kasance yana sa zobe ne a hannun damansa, kuma alama ce ta shi’armu da ake gane su da shi.” A taqaice dai sa zobe a hannun dama ita ce sunna ta Manzon Allah (S), sa shi kuma a hannun hagu sunna ce ta Mu’awiya. Wani abun mamaki in mutum ya duba tarihi zai ga cewa akwai wasu daga cikin Malaman Ahlus sunna da suka ba da fatawar cewa, Na’am sun san cewa sa zobe a hannun dama shine sunna ta Manzon Allah, to amma tun da ya zama alama ta ‘yan shi’a, to a saba masu a mai da shi hannun hagu. Alama ta hudu ita ce: Ta’afir wato sa goshi da kumatu na dama da hagu a lokacin sujudu shukur. Kamar yadda aka sani idan mutum ya yi ko wa ce sallah daga cikin wadannan salloli wajibai to mustahabbi ne bayan ya yi abin da ake ce ma Ta’aqibat na Amma da kuma kassa, ya yi sujudi shukur. Yadda a ke yi shine zai sa goshinsa da hancinsa akan abin da ake sujuda a kai ya yi addu’a, bayan haka sai yasa kumatunsa na dama ya yi addu’a, bayan haka sai ya sa kumatunsa na hagu ya yi addu’a, sa’annan kuma sai ya mai da goshinsa ya yi addu’a. Addu’oin da ake yi a lokacin wadannan ababe, addu’oi ne da aka ruwaito daga Ma’asumin, mutum na iya duba littafin Misbahul-Mutahajjid ko Mafatihul jinan zai ga wadannan addu’oi, idan kuma mutum bai san wadannan addu’oi ba ko kuma bai hardace su ba, to a lokacin da yake wadannan ababe da aka ambata ana son aqalla ya ce “Shukran Lillah” sau ukku wato a sujudar da kuma lokacin da yasa kumatunsa na dama da hagu. Kuma wannan Sujuda ta shukur ba ta taqaita ga salloli na wajibai ba, a’a hatta salloli na nafilfili ana yi masu musamman ma sallar Tahajjud. A taqaice dai wannan Ta’afir na sujuda ta godiya ana so mutum ya lizimci yin su ga dukkan al’amuran sa na yau da kullum, wato ya kasance duk lokacin da Allah Ta’ala ya yi maka wata ni’ima, ko ya tunkude maka wata musiba sai mutum ya yi wannan sujuda ta shukur. Domin yin ta ya na da fa’idodi masu yawa ga duniyar mutum da addininsa da kuma lahirarsa, alal misali daga cikin fa’idodin yin ta akwai qaruwar ni’imar da Allah ya baka, da kuma dada tsare mutum daga dukkan musibu. Haka nan daga cikin fa’idodinta idan mutum ya yi ta bayan sallarsa to idan ruhin sallar ta shi na da naqasu, to wannan sujuda ta na cike gurbin naqasun. Kuma in muka duba tarihin rayuwar Aimma na Ahlul bayt zamu ga misalan masu yawa na sujudu shukur daga rayuwarsu misali yazo cewa, Imam Zainul Abidin ya kasance duk ni’imar da Allah ya yi masa ko ya tunkude masa wata musiba to sai ya yi wannan sujuda ta shukur. Haka nan ya zo a tarihin Imam Kazim (AS) cewa ya kwashe shekaru masu yawa ko wace rana ya kan yi wannan sujuda ta shukur tun daga hudowar Rana har ya zuwa Zawal. Akwai kuma hadisi da aka ruwaito daga Imam Sadiq (AS) ya ce, Babu wani mumini da zai yi sujuda ga Allah, sujuda ta godiya kan ni’imar da ya yi masa, to za a rubuta masa lada, a goge zunubinsa a kuma daukaka darajojinsa. Alamar mumini na biyar shine bayyanar da Bismillah wato a sallah: Shima wannan yana daga cikin mas’alolin da mabiya Ahlul bayt suka kebanta da shi. Domin idan mutum ya bibiyi mazhabobi na Ahlus sunna zai ga cewa sun saba a tsakaninsu kan wannan mas’ala ta Basmala, alal misali sun saba akan cewa Bismillahir-Rahmanir-Rahim shin aya ce cikin fatiha ko kuma aya ce ta ko wace sura? Saannan kuma sun saba akan cewa a bayyane ake karanta ta ko a boye? Saannan kuma sun saba akan cewa karanta ta wajibi ne ko mustahabbi? Da dai sauran sabani da suka yi kan wannan mas’ala. Akwai ma Malamai daga cikinsu da suka rubuta littafi kan wannan al’amari na Basmala, saboda akwai zamanin da aka yi kace-nace tsakanin Malamai kan wannan al’amari. Amma idan mutum ya bibiyi mas’alar a mazhabar Ja’afariyya zai ga cewa baki dayan Malamanta sun tafi akan cewa Bismillahir-Rahmanir-Rahim juz’i ne na ko wace sura, saboda haka wajibi ne a cikin sallah duk surar da mutum zai karanta sai ya hada da ita, domin ita sashen surar ne, in da kawai ba a karanta ta a farkon sura sai a suratu Tauba. To kan kuma mas’alar bayyana ta ake a karatun sallah ko boyewa? To a Ja’afariyya sallolin da ake bayyana karatu a ciki misali sallar Asuba ko Magriba to mutum zai bayyana ne, haka nan kuma a raka’oi biyu na farko na sallar da ake boye karatu wato sallar Zuhur da Asar shima bayyanawa zai yi, bilhasali ma ita wannan alamar mumini na biyar wato bayanna Bismillahi khususan kan raka’oi biyu na farkon sallar Azuhur da Asar ake nufi. Amma a raka’oin biyu na qarshe, kamar yadda aka sani mutum na da zabi ko ya yi tasbihi wato Subhanallah-Walhamdu Lillah-Wala’ilahaillallah-Wallahu Akbar sau ukku ko kuma ya karanta Surar Fatiha, to anan in mutum ya zabi ya karanta fatiha to zai boya karatun Basmalar ne wato ba bayyanawa zai yi ba, haka nan ma a raka’oin biyu na qarshen Isha’i da raka’ar qarshe ta Magriba. Wata mas’ala kuma ita ce wannan bayyana karatun Basmala a raka’oin farko na sallar azahar ko la’asar matsayin wajibi yake ko mustahabbi? Matsayin mustahabbi yake, saboda haka da mutum zai yi sallarsa sai bai bayyana Basmalar ba to sallarsa ta yi sai dai ya rasa ladar wannan mustahabbi. Daga qarshe wannan wata addu’a ce da Imam Sadiq (AS) ya kasance yana yi ga masu ziyarar Imam Husain (AS) Saboda haka yana da muhimmanci ga mutum idan zai iya ko wace rana ya dun ga karanta wannan addu’ar ga Zuwwar na Imam Husain (AS) Musamman ma a cikin watan Safar. Ga addu’ar, “Ya Allah ka gafarta mani, ka gafarta ma ‘yanuwana, ka gafarta ma masu ziyarar Imam Husain wadanda suka ciyar da dukiyar su, suka kuma fito da gangar jikinsu saboda biyayya garemu, da kuma kwadayin ladarka, haka nan kuma domin sa farin ciki ga Manzon ka, ba dun komi ba face saboda neman yardar ka. Ya Allah ka tsare su dare da rana. Ka kiyaye iyalinsu da ‘ya’yansu da suka baro. Ka tsare su daga dukkan sharrori na mutane da aljannu. Ya Allah ka basu fiye da abun da suke fata da buri a wajenka a wannan baqunci na su. Ya Allah maqiyanmu suna aibanta wannan fita tasu, amma haka bai hana su fita ba.Ya Allah ka tausaya ma wadannan fuskoki da rana ta yi butu-butu dasu. Ya Allah ka tausayawa ma wadannan idanuwa da suka zubar da hawaye saboda abun da aka yi mana. Ya Allah ka tausayawa ma wadannan zukata da suke jin zafi da zogi saboda mu. Ya Allah ka tausayawa ma wannan sauti dake kururuwa saboda mu. Ya Allah ka tsare kuma ka kiyaye wadannan rayuka har mu hadu da su ranar qiyama.” Ga mai buqatar ganin wannan addu’a cikin larabci yana iya duba littafi mai suna “Mir’atul-Kamal” Juz’i na ukku.
|
|||
Last Updated on Wednesday, 06 September 2023 18:06 |