Thursday, 19 September 2024
Email
Make My Homepage
RSS
Register
Tarjamar Ziyarar Ashura Print E-mail
Written by administrator   
Friday, 21 July 2023 22:04


أَلسَّلاَمُ عَلَيْكَ يَا أَبَا عَبْدِ اللّٰهِ، أَلسَّلاَمُ عَلَيْكَ يَا بْنَ رَسُولِ اللّٰهِ، أَلسَّلاَمُ عَلَيْكَ يَا بْنَ أَمِيرِ الْـمُؤْمِنِينَ، وَابْنَ سَيِّدِ الْوَصِيِّينَ،أَلسَّلاَمُ عَلَيْكَ يَا بْنَ فَاطِمَةَ سَيِّدَةِ نِسآءِ الْعالَـمِينَ،
Aminci ya tabbata a gare ka Ya Aba Abdillah; Aminci ya tabbata a gare ka Ya dan Manzon Allah; Aminci ya tabbata a gare ka Ya dan Sarkin Muminai kuma dan Shugaban Wasiyyai (na Annabi); Aminci ya tabbata a gare ka Ya dan Fatimah, Shugabar matan dukkan talikai.

أَلسَّلاَمُ عَلَيْكَ يَا ثَارَ اللّٰهِ وَابْنَ ثَارِهِ وَالْوِتْرَ الْـمَوْتُورَ، أَلسَّلاَمُ عَلَيْكَ وَعَلىٰ الأَرْوَاحِ الَّتِي حَلَّتْ بِفِنَآئِكَ،
Aminci ya tabbata a gare ka Ya wanda aka kashe kuma ba'a dau fansar jininsa ba, wanda kuma Allah ne zai dau fansar jininsa, kuma dan wanda aka kashe shi, amma ba'a dau fansar jininsa ba (Imam ‘Ali b. Abi Talib), Aminci ya tabbata a gare ka wanda yake shi kadai, kuma aka kashe shi shi kadai. Aminci ya tabbata a gare ka da ruhin wadanda aka kashe su a farfajiyarka.

عَلَيْكُمْ مِنِّي جَمِيعاً سَلاَمُ اللّٰهِ أَبَداً مَا بَقِيتُ وَبَقِيَ اللَّيْلُ وَالنَّهارُ،
A kan ku daga gare ni dukkaninku amincin Allah har abada, tsawon wanzuwata da wanzuwar dare da rana.

يَا أَبَا عَبْدِ اللّٰهِ، لَقَدْ عَظُمَتِ الرَّزِيَّةُ وَجَلَّتْ وَعَظُمَتِ الْـمُصِيبَةُ بِكَ عَلَيْنَا وَعَلىٰ جَمِيعِ أَهْلِ الإِِسْلاَمِ، وَجَلَّتْ وَعَظُمَتْ مُصِيبَتُكَ فِي السَّمٰوَاتِ عَلىٰ جَمِيعِ أَهْلِ السَّمٰوَاتِ،
Ya Aba Abdillah! Haqiqa wannan qiyayya ta girmama, ta daukaka kuma ta girmama wannan musiba da ta same ka a kanmu da dukkan ma’abota Musulunci, kuma ta daukaka, ta girmama musibarka a sammai da dukkan mazowa sammai.


فَلَعَنَ اللّٰهُ أُمَّةً أَسَّسَتْ أَسَاسَ الظُّلْمِ وَالْـجَوْرِ عَلَيْكُمْ أَهْلَ الْبَيْتِ
Tsinuwar (la’anar) Allah ta tabbata ga al’ummar da ta assasa tushen zalunci da danniya a gare ku iyalan gidan Annabi (Ahlul Bayt).

وَلَعَنَ اللّٰهُ أُمَّةً دَفَعَتْكُمْ عَنْ مَقَامِكُمْ وَأَزَالَتْكُمْ عَنْ مَرَاتِبِكُمُ الَّتِي رَتَّبَكُمُ اللّٰهُ فِيهَا،
Tsinuwar Allah ta tabbata ga wadanda suka tunkude ku daga muqaminku, suka gusar da ku daga martabarku da Allah ya martaba ku da shi.

وَلَعَنَ اللّٰهُ أُمَّةً قَتَلَتْكُمْ، وَلَعَنَ اللّٰهُ الْـمُمَهِّدِينَ لَـهُمْ بِالتَّمْكِينِ مِنْ قِتَالِكُمْ،
Tsinuwar Allah ta tabbata ga makasanku, kuma tsinuwar Allah ta tabbata ga wadanda suka yi shinfida gare su ga samun damar kashe ku.

بَرِئْتُ إِلىٰ اللّٰهِ وَإِلَيْكُمْ مِنْهُمْ وَأَشْيَاعِهِمْ وَأَتْبَاعِهِمْ وَأَوْلِيَآئِهِمْ˛
Na barranta zuwa ga Allah da kuma ku daga gare su, da qungiyarsu da mabiyansu da masoyansu.

يَا أَبَا عَبْدِ اللّٰهِ، إِنِّي سِلْمٌ لـِمَنْ سالَـمَكُمْ، وَحَرْبٌ لـِمَنْ حَارَبَكُمْ إِلىٰ يَوْمِ الْقِيَامَةِ،
Ya Aba Abdillah! Ni mai zaman lafiya ne da wanda ya zauna lafiya da ku, kuma ni mai yaqar wanda ya yaqe ku ne har zuwa ranar qiyama.

وَلَعَنَ اللّٰهُ آلَ زِيَادٍ وَآلَ مَرْوَانَ، وَلَعَنَ اللّٰهُ بَنِي أُمَيَّةَ قَاطِبَةً،
Tsinuwar Allah ta tabbata kan iyalan Ziyad da iyalan Marwan, kuma tsinuwar Allah ta tabbata kan Bani Umayya baki daya.

وَلَعَنَ اللّٰهُ ابْنَ مَرْجَانَةَ، وَلَعَنَ اللّٰهُ عُمَرَ بْنَ سَعْدٍ، وَلَعَنَ اللّٰهُ شِـمْراً،
Tsinuwar Allah ta tabbata kan dan Marjana, kuma tsinuwar Allah ta tabbata kan Umar bin Sa’ad, kuma tsinuwar Allah ta tabbata kan Shimr.


وَلَعَنَ اللّٰهُ أُمَّةً أَسْرَجَتْ وَأَلْـجَمَتْ وَتَنَقَّبَتْ لِقِتَالِكَ،
Kuma tsinuwar Allah ta tabbata kan al’ummar da ta aiwatar, ta gani, kuma ta yi shiru kan kisanka.

بِأَبِي أَنْتَ وَأُمِّي، لَقَدْ عَظُمَ مُصَابِي بِكَ، فَأَسْأَلُ اللّٰهَ الَّذِي أَكْرَمَ مَقَامَكَ، وَأَكْرَمَنِي بِكَ، أَنْ يَرْزُقَنِي طَلَبَ ثَارِكَ مَعَ إِمَامٍ مَنْصُورٍ مِنْ أَهْلِ بَيْتِ مُحَمَّدٍ صَلَّى اللّٰهُ عَلَيْهِ وَآلِهِ.
Ubana da Uwata su zama fansa gare ka! Haqiqa ya girmama baqin cikin da nake ji kan abin da ya same ka, ina roqon Allah wanda ya daukaka matsayinka, ya daukaka ni da kai, da ya azurta ni da neman fansarka tare da Imami Mai nasara daga Iyalan gidan Annabi Muhammad (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da Alayensa).

أَللّٰهُمَّ اجْعَلْنِي عِنْدَكَ وَجِيهاً بِالْـحُسَيْنِ ˛ عَلَيهِ السَّلاَمُ فِي الدُّنْيَا وَالآخِرَةِ،
Ya Allah! Ka sanya ni a gun ka mai matsayi saboda Husain, aminci ya tabbata a gare shi a duniya da lahira.

يَا أَبَا عَبْدِ اللّٰهِ، إِنِّي أَتَقَرَّبُ إِلىٰ اللّٰهِ، وَإِلىٰ رَسُولِهِ، وَإِلىٰ أَمِيرِ الْـمُؤْمِنِينَ، وَإِلىٰ فَاطِمَةَ، وَإِلىٰ الْـحَسَنِ، وَإِلَيْكَ بِـمُوَالاَتِكَ، وَبِالْبَرَاءَةِ مِـمَّـنْ أَسَّسَ أَسَاسَ ذٰلِكَ وَ بَنىٰ عَلَيْهِ بُنْيَانَهُ، وَجَرىٰ فِي ظُلْمِهِ وَجَوْرِهِ عَلَيْكُمْ وَعَلىٰ أَشْيَاعِكُمْ،
Ya Aba Abdillah! Haqiqa ina neman kusanci zuwa ga Allah, da Manzonsa da Sarkin muminai da Fatima da Hasan da kuma gare ka ta hanyar soyayyarka, da bara’a daga wanda ya assasa asasin wannan, ya kuma yi gini a kansa gininsa, ya kuma ci gaba da zaluncinsa da danniyarsa a kanku da magoya bayanku.

بَرِئْتُ إِلىٰ اللّٰهِ وَإِلَيْكُمْ مِنْهُمْ، وَأَتَقَرَّبُ إِلىٰ اللّٰهِ ثُمَّ إِلَيْكُمْ بِـمُوَالاَتِكُمْ وَمُوَالاَةِ وَلِيِّكُمْ، وَبِالْبَرَاءَةِ مِنْ أَعْدَائِكُمْ، وَالنَّاصِبِينَ لَكُمُ الْـحَرْبَ، وَبِالْبَرَاءَةِ مِنْ أَشْيَاعِهِمْ وَأَتْبَاعِهِمْ،
Na barranta zuwa ga Allah kuma gare ku daga gare su, ina neman kusanci zuwa ga Allah, sannan gare ku da soyayyarku da soyayyar ma’abocin al’amarinku da bara’a daga maqiyanku da wadanda suka nassaba yaqi a kanku, da bara’a daga magoya bayansu da mabiyansu.


إِنِّي سِلْمٌ لـِمَنْ سَالَـمَكُمْ، وَحَرْبٌ لِـمَنْ حَارَبَكُمْ، وَوَلِيٌّ لـِمَنْ وَالاَكُمْ، وَعَدُوٌّ لِـمَنْ عَادَاكُمْ،
Ni mai zaman lafiya ne da wanda ya zauna lafiya da ku, kuma ni mai yaqar wanda ya yaqe ku ne, kuma majibincin al’amarin wanda ya jibance ku, kuma mai adawa da wanda ya yi adawa da ku.

فَأَسْأَلُ اللّٰهَ الَّذِي أَكْرَمَنِي بِـمَعْرِفَتِكُمْ، وَمَعْرِفَةِ أَوْلِيَآئِكُمْ، وَرَزَقَنِي الْبَرَاءَةَ مِنْ أَعْدَائِكُمْ، أَنْ يَـجْعَلَنِي مَعَكُمْ فِي الدُّنْيَا وَالآخِرَةِ، وَأَنْ يُثَبِّتَ لِي عِنْدَكُمْ قَدَمَ صِدْقٍ فِي الدُّنْيَا وَالآخِرَةِ
Ina roqon Allah wanda ya karrama ni da sanin ku, da sanin majibintanku, ya azurta ni da bara’a daga maqiyanku, ya sanya na kasance tare da ku a duniya da lahira, kuma ya tabbatar da ni a gun ku da kafafuwa na gaskiya a duniya da lahira.

وَأَسْأَلُهُ أَنْ يُبَلِّغَنِي الْـمَقامَ الْـمَحْمُودَ لَكُمْ عِنْدَ اللّٰهِ، وَأَنْ يَرْزُقَنِي طَلَبَ ثَارِي مَعَ إِمَامِ هُدىً ظَاهِرٍ نَاطِقٍ بِالْـحَقِّ مِنْكُمْ،
Kuma ina roqon sa ya kai ni ga matsayin abin godiya gare ku a wajen Allah, kuma ya azurta ni da neman fansar ku tare da Imamin shiriya na zahiri, mai furuci da gaskiya daga gare ku.

وَأَسْأَلُ اللّٰهَ بِـحَقِّكُمْ وَبِالشَّأْنِ الَّذِي لَكُمْ عِنْدَهُ أَنْ يُعْطِيَنِي بِـمُصَابِي بِكُمْ أَفْضَلَ مَا يُعْطِي مُصَاباً بِـمُصِيبَتِهِ، مُصِيبَةً مَا أَعْظَمَها وَأَعْظَمَ رَزِيَّتَهَا فِي الإِسْلاَمِ وَفِي جَمِيعِ السَّمٰوَاتِ وَالأَرْضِ.
Kuma ina roqon Allah don haqqinku da sha’anin da ke gare ku a gun sa, ya ba ni saboda damuwata da musibar da ta same ku, abin da ya fi wanda ake ba wanda ya damu da musibar da ta shafe shi, wannan musiba da ba wadda ta fi ta da radadinta a Musulunci da dukkan sammai da qassai.

أَللّٰهُمَّ اجْعَلْنِي فِي مَقَامِي هٰذَا مـِمَّنْ تَنَالُهُ مِنْكَ صَلَواتٌ وَرَحْمَةٌ وَمَغْفِرَةٌ،
Ya Allah! Ka sanya ni a inda na tsaya din nan cikin wanda yake samu daga gare ka aminci da rahama da gafara.

أَللّٰهُمَّ اجْعَلْ مَـحْيَايَ مَـحْيَا مُحَمَّدٍ وَآلِ مُحَمَّدٍ، وَمَـمَاتِي مَـمَاتَ مُحَمَّدٍ وَآلِ مُحَمَّدٍ.
Ya Allah! Ka sanya rayuwata irin rayuwar Muhammadu da Alayen Muhammad kuma mutuwata irin wafatin Muhammadu da Alayen Muhammad.

أَللّٰهُمَّ إِنَّ هٰذَا يَوْمٌ تَبَرَّكَتْ بِهِ بَنُو أُمَيَّةَ وَابْنُ آكِلَةِ الأَكْبَادِ، اللَّعِينُ ابْنُ اللَّعِينِ عَلىٰ لِسَانِكَ وَلِسَانِ نَبِيِّكَ فِي كُلِّ مَوْطِنٍ وَمَوْقِفٍ وَقَفَ فِيهِ نَبِيُّكَ.
Ya Allah! Wannan rana ce da Banu Umayya da dan magatsiyar hanta suke neman tubarrakinsa, Tsinanne dan Tsinanne a bisa zancenka da harshen Annabinka a kowane wuri da matsayar da Annabinka ya tsaya a cikin sa.

أَللّٰهُمَّ الْعَنْ أَبَا سُفْيَانَ وَمُعَاوِيَةَ وَيَزِيدَ بْنَ مُعَاوِيَةَ عَلَيْهِمْ مِنْكَ اللَّعْنَةُ أَبَدَ الأَبِدِينَ، وَهٰذَا يَوْمٌ فَرِحَتْ بِهِ آلُ زِيَادٍ وَآلُ مَرْوَانَ بِقَتْلِهِمُ الْـحُسَيْنَ صَلَواتُ اللّٰهِ عَلَيْهِ. أَللّٰهُمَّ فَضَاعِفْ عَلَيْهِمُ اللَّعْنَ مِنْكَ وَالْعَذابَ الأَلِيمَ.
Ya Allah! Ka tsine wa Abu Sufyan da Mu’awiyah da Yazid bin Mu’awiyah – a kansu daga gare ka, tsinuwa ta har Abadan abada. Wannan rana ce da suka yi farin ciki da ita, Iyalan Ziyad da Iyalan Marwan, saboda kisan da suka yi wa Husain, tsiran Allah ta tabbata a gare shi. Ya Allah ka nunka a kansu tsinuwa daga gare ka da azaba mai radadi.

أَللّٰهُمَّ إِنِّي أَتَقَرَّبُ إِلَيْكَ فِي هٰذَا الْيَوْمِ، وَفِي مَوْقِفِي هٰذَا، وَأَيَّامِ حَيَاتِي بِالْبَرَاءَةِ مِنْهُمْ، وَاللَّعْنَةِ عَلَيْهِمْ، وَبِالْـمُوَالاَةِ لِنَبِيِّكَ وَآلِ نَبِيِّكَ عَلَيْهِ وَعَلَيْهِمُ السَّلاَمُ.
Ya Allah! Ina neman kusanci zuwa gare ka a wannan rana, a wannan wuri da na tsaya, da ranekun rayuwata ta hanyar bara’a daga gare su da tsinuwa a gare su da jibintar al’amari ga Annabinka da Iyalan Annabinka, amincin Allah ya tabbata a gare shi da kuma su.

أَللّٰهُمَّ الْعَنْ أَوَّلَ ظَالِمٍ ظَلَمَ حَقَّ مُحَمَّدٍ وَآلِ مُحَمَّدٍ وَآخِرَ تَابِعٍ لَهُ عَلىٰ ذٰلِكَ. أَللّٰهُمَّ الْعَنِ الْعِصَابَةَ الَّتِي جَاهَدَتِ الْـحُسَيْنَ وَشَايَعَتْ وَبَايَعَتْ وَتَابَعَتْ عَلىٰ قَتْلِهِ، أَللّٰهُمَّ الْعَنْهُمْ جَمِيعاً.
Ya Allah! Ka tsine wa farkon wanda ya zalunci haqqin Muhammad da Alayen Muhammad da na qarshen da ke bin sa a kan wannan. Ya Allah ka tsine wa gungun jama’ar da ta yi fada da Husain, kuma ta yi taimako, ta yi mubaya’a, ta yi biyayya a kan kashe shi, Allah Ka la’ance su dukkan su.

أَلسَّلاَمُ عَلَيْكَ يَا أَبَا عَبْدِ اللّٰهِ وَعَلىٰ الأَرْوَاحِ الَّتِي حَلَّتْ بِفِنَآئِكَ، عَلَيْكَ مِنِّي سَلاَمُ اللّٰهِ أَبَداً مَا بَقِيتُ وَبَقِيَ اللَّيْلُ وَالنَّهَارُ، وَلاَ جَعَلَهُ اللّٰهُ آخِرَ الْعَهْدِ مِنِّي لِزِيَارَتِكُمْ، أَلسَّلاَمُ عَلىٰ الْـحُسَيْنِ، وَعَلىٰ عَلِيِّ بْنِ الْـحُسَيْنِ، وَعَلىٰ أَوْلاَدِ الْـحُسَيْنِ، وَعَلىٰ أَصْحَابِ الْـحُسَيْنِ.
Aminci ya tabbata a gare ka Ya Aba Abdillah da ruhin wadanda aka kashe a farfajiyarka, a gare ka daga gare ni amincin Allah har abada, matuqar rayuwata da wanzuwar dare da rana. Kada Allah ya sanya shi qarshen alqawari daga gare ni na ziyartar ku. Aminci ya tabbata ga Husain da Aliyu dan Husain da ‘ya’yan Husain da Sahabban Husain.

أَللّٰهُمَّ خُصَّ أَنْتَ أَوَّلَ ظالِمٍ بِاللَّعْنِ مِنِّي، وَابْدَأْ بِهِ أَوَّلاً، ثُمَّ الْعَنِ الثَّانِيَ وَالثَّالِثَ وَالرَّابِعَ. أَللّٰهُمَّ الْعَنْ يَزِيدَ خَامِساً، وَالْعَنْ عُبَيْدَ اللّٰه ِبْنَ زِيادٍ وَابْنَ مَرْجَانَةَ وَعُمَرَ بْنَ سَعْدٍ وَشِـمْراً وَآلَ أَبِي سُفْيَانَ وَآلَ زِيَادٍ وَآلَ مَرْوَانَ إِلىٰ يَوْمِ الْقِيَامَةِ.
Ya Allah! Ka kebanci farkon azzalumin da la’ana daga gare ni, ka fara da shi a farko, sannan ka la’anci na biyu, da na uku da na hu]u. Ya Allah ka la’anci Yazidu na biyar, ka la’anci Ubaydullah bin Ziyad da Ibni Marjana da Umar bin Sa’ad da Shimr da Iyalan Sufyan da Iyalan Ziyad da Iyalan Marwan har zuwa ranar qiyama.

أَللّٰهُمَّ لَكَ الْـحَمْدُ حَمْدَ الشَّاكِرِينَ لَكَ عَلىٰ مُصَابِهِمْ. أَلْـحَمْدُ لِلّٰهِ عَلىٰ عَظِيمِ رَزِيَّتِي. أَللّٰهُمَّ ارْزُقْنِي شَفَاعَةَ الْـحُسَيْنِ يَوْمَ الْوُرُودِ، وَ ثَبِّتْ لِي قَدَمَ صِدْقٍ عِنْدَكَ مَعَ الْـحُسَيْنِ وَأَصْحَابِ الْـحُسَيْنِ الَّذِينَ بَذَلُوا مُهَجَهُمْ دُونَ الْحُسَيْنِ˛ عَلَيْهِ السَّلاَمُ.
Ya Allah! Godiya ta tabbata gare ka, godiyar masu shukura gare ka kan abin da ya same su. Godiya ta tabbata ga Allah kan girman baqin ciki na. Allah ka azurta ni da ceton Husain ranar da ake komawa zuwa gare ka, ka tabbatar da dugadugai na da gaskiya tare da Husain da Sahabban Husain wadanda suka sadaukar da rayukansu gaban Husain, aminci ya tabbata a gare shi.

Last Updated on Friday, 21 July 2023 22:19
 
Home Maudu'oi daban-daban Tarjamar Ziyarar Ashura
Copyright © 2024. www.tambihin.net. Designed by KH