Wannan maudu’i na Iklasi yana da gayar muhimmanci saboda shine ruhin ko wane aiki da mutum zai aikata a addini na Musulunci. Duk wani aiki da mutum zai aikata idan babu iklasi a ciki to misalinsa kamar gangar jiki ne ba Ruhi, kuma aikinsa ba zai samu karbuwa ba wajen Allah (T) ba komin yawan aikin. Bayanai a taqaice insha Allah zasu gudana kan wadannan ababe:
1- Ma’anar Iklasi.
2-Iklasi a cikin Alqu’rani da Hadisai.
3- Muhimmanci da kuma fa’idodin Iklasi.
4- Ababen da suka taimakawa wajen samun Iklasi.
5- Ababen da suke hana samun Iklasi.
6- Matakan Iklasi.
7- Bayani kan Niyya.
8- Qissoshin masu Iklasi.
9- Dawwama kan Iklasi.
1- Ma’anar Iklasi: Shine tsarkake niyya ga kowane aiki wato mutum duk aikin da zai aikata to ya aikata saboda Allah da kuma neman yardarsa amma ba ya gina aikin nasa kan neman yardar mutane ko yabawarsu ko domin yin suna misali yin kyauta ko sadaka akan asasin wadannan manufofi. 2- Iklasi a cikin Alqur’ani da Hadisi: Idan mutum ya bibiyi Alqur’ani mai girma zai ga cewa akwai ayoyi masu yawa da suke Magana dangane da Iklasi, Haka nan idan mutum ya bibiyi Hadisai da aka ruwaito daga Manzon Allah (S) da kuma A'imma na Ahlul bait (AS) zai ga cewa akwai Hadisai masu yawa da aka ruwaito dangane da Iklasi, ga wasu daga ciki: 1- Manzon Allah (S) ya ce, “ Allah (T) baya duban jikkunanku da ayyukanku amma yana dubi ne ga zukatanku da kuma Niyyarku.” Wato abinda ya shafi Iklasi saboda muhallinsa a zuciya yake. 2-Manzon Allah (S) Ya ce, “ Iklasi Sirri ne daga cikin Sirrorina ni kan sashi a cikin zuciyar wanda naso daga cikin bayina.” Wato in ji Allah (T). 3- Manzon Allah (S) Ya ce, “ Da Iklasi ne Darajojin muminai yake banbanta.” Wato ko da suna aiki iri daya misali Gwagwamarya a tafarkin addini, ko wajen neman ilimi ko yada shi da dai sauran ayyuka na ibadodi to a wajen Allah Ta’ala ko a ranar qiyama darajar da kowanne zai samu gwargwadon Iklasinsa ne ga aikin. 4- Manzon Allah (S) Ya ce, “ In zaka aikata wani aiki to ka yi aikin saboda Allah saboda baya karbar aiki daga bayinsa sai wanda aka aikata shi akan asasin Iklasi.” Da dai sauran Hadisai masu yawa da aka ruwaito kan Iklasi. 3- Muhimmanci da kuma fa’idodin Iklasi: Iklasi kamar yadda aka ambata a baya cewa shine Ruhin kowane aikin, kuma duk aikin da babu Iklasi a ciki komin yawan shi to ba karbabbe ba ne a wajen Allah. Imam Ali Ya ce, “ Tsarkake aiki yafi muhimmanci kan aikin.” Wato mutum ya aikata aikin kan a sasin Iklasi to yafi aihairi kan aikin saboda in da zai aikata aikin ba akan Iklasi ba to bashi da lada, ladar sa tana ga wadanda ya yi dominsu misali idan ya yi aikin domin a yaba masa ne to in an ya ba masa to shine sakamakonsa. Imam Sadiq (AS) Ya ce, “ Aiki mai Iklasi shine wanda baka nufin wani ya yaba maka face Allah (T) Aikata kowane aiki akan asasin Iklasi yana da gayar muhimmanci da kuma fa’idodi masu yawa alal misali mutum bai da tabbas yana iya baka baya wani lokaci amma idan saboda Allah ka yi masa abubuwan alhairi da ka yi sai ka ga cewa ba zaka damu ba damu ba saboda ba don shi ka yi ba, saboda Allah ka yi. Ko kuma kana yi masa shi kuma bai yi maka saboda haka ko bai yi maka ba zaka damu ba tun da saboda Allah kake yi masa. Akwai wani Hadisi mai wahalar dabbaqawa amma in akwai Iklasi bai da wahalar aikatawa, wato da ya zo akan cewa ka ba wanda ya hana maka, ka sadar ga wanda ya yenke maka, ka kyutata ma wanda ya munana maka. Wato wannan ga ‘yan uwa na jini ko na Addini ko maqwabta da dai sauransu. Daga cikin fa’idodin Iklasi an ruwaito daga Imam Sadiq (AS) Ya ce, “ Idan mutum ya kasance mai Iklasi to Allah zai sanya komi ya kasance yana tsoronsa hatta qwarin qasa.” Wato duk wani maqiyin Allah ko qwarin qasa masu cutarwa zai kasance suna tsoronsa. Rashin Iklasi a ayyuka ba wai kawai yana haifar da rashin samun ladar aikin ba, a’a yana iya kai ga mutum ya yi Hasarar duniyarsa da lahirarsa kamar yadda aka ruwaito daga Imam Ali (AS) Ya ce, “ Ya yi Hasara duk wanda ya kasance manufarsa wanin Allah a ayyukansa.” 4- qissoshin masu Iklasi: Da farko qissar wani da ya gina aikinsa ba kan a sasin Iklasi ba. Abinda ya faru shine ya tashi da tsakar dare domin yin Sallar Tahajjud a cikin Massallaci, to yana cikin Sallar Tahajjud sai ya ji motsi a cikin Masallacin sai ya dauka ko wani ne ya shigo cikin Massallacin sai ya dada kyautata Sallar, can bayan wani lokaci da ya sallame sallar sai ya waiwayo baya ya ga ashe Mage ce ta shigo cikin Massallacin tana kai komo, shine a ransa ya ce kaito na yanzu duk wannan kyautata Sallar da na yi ashe saboda Mage ne. To mu duba mu gani irin wannan tabewa. A taqaice Iklasi yana da fa’idodi masu yawa a wannan gida na Duniya da kuma Lahira, akwai wata qissa na wani shima daga cikin magabata da na taba jin Sayyid (H) Ya kawo a wani Imams week da aka yi a ABU Zaria 1990 cewa wani Malami dannin gidansa ya fadi cikin dare kuma a lokacin damuna – a wannan zamanin misali a ce katangar gidansa - to sai cikin almajiransa da ya farka cikin dare ya ga dannin gidan Malam ya fadi, shine ya ga bai dace da safe a ga gidan Malam qwaye ba, cikin daren sai ya tafi daji ya samo karare wanda ya yi ma Malamin nasu sabon Danni, Malamin da safiya ta yi yaga lalle Dannin gidansa ya fadi amma gashi har an yi sabon Dannin, sai ya tambayi almajiran nasa ya ce Dannin gida na ya fadi, ya ce wani ko wasu cikin almajirai an yi sabo wane ne ya yi wannan aikin? Wannan dalibi da ya yi aiki bai ce Uffan ba, wanda in da wani ne nan take zai ce Malam ai nine. To shine Malamin tun da ba wanda ya ce shine cikin Almajiran ya ce ai yi ma wanda ya yi wannan kyakkyawan aiki Addu’a, Ya ce ya Allah duk wanda yai wannan aiki ilimin da ya zo nema Allah (T) ka bashi da dai sauransu, aka ce wannan dalibi da yai wannan aiki ya samu ilimin da kuma shahara fiye da sauran dalibansa to mu duba wannan tun a gidan Duniya Kenan sakamakon Iklasi to ina ga gidan Lahira. Haka nan mu dubi wanda ya rubuta littafin Mafatihul Jinan wato Shaikh Abbas Alqummiy, mu dubi yadda wannan littafin nasa na mafatihu ya samu karbuwa da kuma shahara ta yadda a yau kusan kowane gida na dan Shi’a za ka samu akwai wannan littafi a wajensa, haka nan idan mutum ya je qasashen shi’a zai ga duk Masallatai baya ga Alqur’ani zai ga cewa akwa litafin mafatihu, to tambaya minene sirrin da wannan Bawan Allah ya samu wannan tagomashi? Amsa shine gayar Iklasinsa da sauransu. 5- Ababen da suke taimakawa wajen samun Iklasi: Daga cikin ababen da suke taimaka ma mutum wajen samun Iklasi shine ko da wane lokaci mutum ya dun ga tunanin neman yardar Allah ga dukkan al’amuransa wato ya kasance Allah (T) kadai yake tunani kan duk wani aiki da zai aikata da kuma kwadayin abinda ke wajensa. Imam Ali (AS) Ya ce, “ Duk wanda ya kasance mai kwadayin abinda ke wajen Allah to zai kasance mai Iklasi a ayyukansa.” Daga cikin ababen da suke taimakawa wajen samun Iklasi shine mutum ya debe tsammani ga abinda ke hannun mutane, wato bai kwadayin abin hannunsu ko kuma neman matsayi a cikin zukatansu. Ya zo a wani Hadisi da aka ruwaito daga Imam Ali (AS) Ya ce, “ Asalin Iklasi shine debe tsammani daga abinda ke hannun mutane.” Daga cikin ababen da suke taimaka ma mutum wajen samun Iklasi shine mutum ya yi mujahada har ya kai matayin da yabo da suka na mutane basu da Tasiri a cikin zuciyarsa wato ya kasance bai damu da yabonsu ba ko sukarsu da dai sauran hanyoyi da zasu taimaka wajen samun Iklasi. 6- Ababen da suke hana samun Iklasi: Shima ababe ne da yawa suke sabbaba shi, babba daga ciki shine bin son rai. Amiril Muumini (AS) Ya ce,” Ya ya mutum zai samu ikon yin Iklasi alhali bin son rai ya samu galaba akansa.” Daga cikin abin suke hana samun Iklasi akwai son Duniya da kuma neman matsayi a zukatan mutane ko son yabonsu da dai sauransu. 7- Matakan Iklasi: Iklasi yana da matakai guda biyu ko martabobi guda biyu, mataki ko martaba na farko shine bautata ma Allah ko yin ayyuka saboda tsoron wuta ko kwa]ayi Aljanna, wannan abu ne mai kyau amma ga bayin Allah wadanda suka kai mustawa Aliya na kusanci ga Allah (T) Suna ganin wannan a matsayin Hijabi. Mataki na biyu shine bautata ma Allah saboda sonsa ko godiya gareshi ko kuma akan asasin shi ya cancanta a bautata ma. Imam Ali (AS) Ya ce, “ Wasu Mutane suna bautata ma Allah saboda kwadayi – Aljannarsa- To wannan bautar ‘yan kasuwa Kenan. Wasu mutane kuma suna Bautar Allah saboda tsoro –Wutarsa- To wannan bautar bayi Kenan. Wasu mutane suna bautata ma Allah saboda godiya –Ga ni’imominsa- To wannan bautatar ‘ya’ya Kenan.” A wani munajati na Imam Ali yana cewa, “ Ya Ubangiji na ban bauta maka saboda tsoron wutarka ko kwadayin Aljannarka, na bauta maka ne saboda kai ne macancancin a bautata masa.” Wannan yana buqatar dogon sharhi amma saboda gudun tsawaitawa sai dai wani lokaci Insha-Allah. 8- Bayani kan Niyya: Idan mutum ya yi bincike a littafan Aklaq zai ga cewa a babin Iklasi akan kawo bayani kan Niyya, da yake shi Iklasi ya assasu ne kan Niyya wato kyakkyawa niyya ita ke haifar da Iklasi haka nan mummunar Niyya ita ke haifar da Riya, saboda haka duk abin da mutum zai aikata to ya gina shi kan kyakkyawa Niyya. 9- Dawwama kan Iklasi: Abinda ake nufi a nan shine ko bayan mutum ya aikata aiki akan Iklasi to ana son ya dawwama akan Iklasi har ya zuwa saukar ajalinsa, saboda mutum zai iya aikata aiki akan asasin Iklasi amma daga baya sai ya bata aikin nasa sakamakon suma’a wato jiyarwa misali ya yi ma wani ko wasu abu na al-hairi sai ya zamo matsala ko wani abu ya shiga tsakanin su daga ba ya, Shaidan sai ya ingiza shi ya ba da labarin duk abubuwan alhairi da ya yi a baya, alhali gabanin haka qila ba wanda ya san ya yi sai Allah (T). Akwai wani Hadisi da aka ruwaito daga Imam Baqir (AS) Ya ce, “ Dawwama kan Iklasi ya fi tsanani akan aiki- sai wani ya tambaya- Minene dawwama kan Iklasi? Sai Imam Baqir ya ce, Mutum ne zai sadar da, zumunci ko ya yi wani infaqi saboda Allah sai a rubuta ladarsa a sirrice, sai ya ba da labarin aikin da ya yi, sai agoge a rubuta shi a bayyane, wani lokacin ya sake ba da labarin aikin sai a rubuta aikin nasa a mtsayin Riya.” Saboda haka yana da gayar muhimmanci mutum ya kiyaye Iklasi gabanin aiki ko lokacin aiki ko kuma bayan aiki, musamman ma bayan aiki saboda Shadan zai ta qoqarin ya ga cewa ya bata aiki daga baya, saboda haka mutum ya yi mujahada wajen Dawwamar da Iklasin. Saboda shi Shaidan ko da wane lokaci yana sa’ayi ne ya ga cewa mutum bai aikata aikin alheri ba, in kuma har ya samu ya aikata to zai yi sa’ayi wajen bata aikin ta hanyar Riya da sauransu. Kuma idan har mutum ya yi mujahada ya shiga cikin ajin masu Iklasi to ya kai matakin da Shaidan ya debe tsammani da shi wato ba yadda zai yi da shi. Kamar yadda shi kanshi Shaidan ya ke ce ma Allah (T), “ Zan batar da su baki daya face bayinka masu Iklasi.”
|