Tuesday, 23 July 2024
Email
Make My Homepage
RSS
Register
Darussa daga rayuwar Imam Khumaini (QS) Print E-mail
Written by administrator   
Friday, 21 July 2023 21:26

Kasantuwar wannan wata da muke ciki na June wanda a cikinsa ne rasuwar Imam Khumaini (QS), ta kasance wato 3 ga watan June shekara ta 1989, amma a qidaya ta Hijiriyya ya rasu ne a 28 ga watan Shawwal shekara ta 1409 bayan Hijira. Kuma kamar yadda aka saba a irin wannan munasaba ta wafatinsa akan tunasar da juna kan abinda ya shafi wani sashe na rayuwar sa mai albarka, to a wannan shekara insha Allah za'a tunasar da juna ne kan abinda ya shafi rayuwarsa tare da iyalinsa da ‘ya’yansa da kuma maqwabtansa da dai sauransu, saboda su kasance darussa garemu da zamu aikata su a rayuwarmu ta yau da kullum musamman ma alaqarmu tare da iyalanmu da kuma maqwabtanmu.
Da farko Auren Imam Khumaini: Sunan matarsa Khadija, mahaifinta babban malami ne lokacin a birnin Tehran wato babban birnin Iran, Sunansa Ayatullah Mirza Muhammad At-Tehraniy. Wannan Aure mai albarka an yi shine lokacin ita Sayyida Khadija tana da shekaru 15 shi kuma Imam Khumaini yana da shekaru 20 da wani abu a lokacin yana dalibi a birnin Qum. Amma kafin aurensu akwai ababe da suka faru da suke nuna karama na Imam Khumaini, alal misali mafarkin da Sayyida Khadija ta yi da Ashabul kisa’i baki dayansu wato Manzon Allah (S) da Sayyida Zahra, Imam Ali, Imam Hassan, Imam Husain (AS). Wanda a cikin mafarkin Manzo Allah (S) Ya ce mata ki amsa ma dan mu, saboda abinda ya faru shine ita Khadija ba ta son auren kasantuwar idan an yi auren za ta bar birnin Tehran zuwa Qum wanda a lokacin kamar a matsayin qauye take kuma ba ta da abubuwan cigaban zamani kamar Tehran ga kuma yanayinta na zafi sabanin Tehran mai yanayin sanyi to akan wannan asasi taso ta qi amsa auren, ana gobe za ta ba da amsa to a daren sai tai wanannan mafarki wanda ya canza mata tunani kuma ta sallama, da safe sai ta shaida ma kakarta wannan mafarki da ta yi, da yake kakarta ita ma ba ta goyon bayan al’amarin amma mahaifinta da mahaifiyarta suna goyon bayan al’amarin aurenta da Imam Khumaita, da ta shaida ma kakarta mafarkin sai ta ce mata lalle wannan ya nuna wannan – wato Khumaini- salihi daga cikin salihan bayin Allah saboda haka ki amince da auren. Ta ce tun da ta yi wannan mafarki duk wadannan ababen sun gushe a tunaninta saboda haka ita ta yarda a daura masu aure. Bayan daurin aurensu suka zauna a Qum na shekaru masu yawa sama da shekaru 50 wato har ya zuwa lokacin da Imam Khumaini yai Hijira zuwa Iraq amma gabanin nan ya dan zauna a Turkiyya na wani lokaci daga nan ya wuce zuwa Birnin Najaf wanda ya zauna ciki wajen shekaru 15.
Ya’yansa: Imam Khumaini yana da ‘ya’ya takwas maza ukku, mata biyar, mazan sune 1- Ayatullah Sayyid Mustafa. 2- Hujjatul- Islam Sayyid Ahmad. 3- Sayyid Ali shi ya rasu tun yana da shekaru 4. Sayyid Mustafa ya yi shahada ne a 1977 a birnin Najaf wato lokacin Imam na gudun Hijira, lokacin da ya yi shahada yana da shekaru 47. Sayyid Ahmad kuma ya rasu a 1995. Sunayen ‘ya’yansa mata sune: 1-Sayyida Farida. 2- Sayyida Siddiqa. 3- Dr Sayyida Zahra. 4- Sayyida Sa’ida. 5- Sayyida Ladifa.
Idan kuma muka juya rayuwar Imam Khumaini tare da iyalinsa akwai misalai da kuma darussa masu yawa ga wasu daga ciki: Matar Imam Khumaini tana yawa cewa, “ Tsawon zaman da muka yi da Imam Khumaini sama da shekaru sittin ban taba ganin ya aikata wani zunubi go da ko sau daya ne, kuma ya kasance yana yawan yi mana nasiha koda wane lokace cewa mu yi qoqari mu nisanci sabo, idan mun kasa aikata ayyuka na ibada to mu yi qoqari wajen ganin cewa bamu saba ma Allah (T) ba.” Haka nan a wani waje tana cewa, “ Imam yana yawan yi masu wasiyya da su kyatata dabi’oinsu su kuma nisanci girman kai.” Sayyida Farida tana cewa, Idan muna gaban Imam babu wani daga cikinmu wanda zai iya yin giba, saboda mun san Imam bai son haka, ya nai mana nasiha da nisantar zunubi musamman giba, kuma yana qarfafawa ga mata cewa idan sun hadu su tattauna kan matsalolinsu wato saboda gudun fadawa cikin giba. Haka nan Imam Khumaini yana qarfafawa ga iyaye musamman idan ‘ya’yansu sun kai shekaru na Taklif wato sun balaga su qara kula da Tarbiyyarsu da kuma sa masu ido a mu’amalolinsu da kuma kai komansu. Haka nan ya kasance yana qarfafa ma yara girmama iyayensu da kuma kyautata masu musamman Uwa. Ya kasance ma a ranar mata ta Duniya wato maulidin Sayyida Zahra (AS) ya kan ba jikokinsa kyautar kudi yace masu suje su sai wani abu su ba mahaifansu mata albarkacin munasabar. A taqaice dai idan mutum ya bibiyi Tarihin Imam Khumaini zai ga cewa yana son ‘ya’ya mata, yama zo a Tarihinsa cewa ‘yan uwansa mata na jini in sun buqaci Addu’a daga wajensa idan suna da juna biyu ya kan ce ki yi Addu’a Allah ya baki ‘ya mace. Alhamdu lillah in muka dubi adadin ‘ya’yan Imam guda takwas zamu ga guda biyar mata ne. Haka nan Imam Khumaini ya kasance yana qarfafa ‘ya’yansa maza da mata da kuma jikokinsa wajen karatu na boko da Hauza-Isilamiya- misali babban dansa Sayyid Mustafa kafin shahadarsa ya kai matsayin Ayatullah, haka nan ‘yarsa Sayyida Zahra tana da PhD a fannin da take na karatun Boko, a taqaice dai cikin ‘ya’yansa akwai wadanda suka yi karatun Hauza akwai kuma wadanda suka yi karatun Boko, akwai kuma wadanda suka hada guda biyu wato na Boko da Hauza. Sayyida Zahra ta ce Imam ya kasance duk ranar Idi na babbar Sallah ko qaramar Sallah yana baiwa ‘ya’yansa kyauta ta kudi tun suna yara kuma dukkansu yake basu har da mahaifiyarsu ta ce yara yana basu Toman 100 manya kuma ya basu Toman 300, har ma lokacin da yake Najaf yana bamu. Ta ce a wata Idin sai dai ba zan iya tuna shekarar ba muna jiran ya bamu wannan kyautar kamar yadda ya saba sai ya ce masu kyautar Idi da na saba baku daga kudi na ne, ba na dukiyar Jama’a ba ne to wannan Idi ban da kudin da zan baku. Haka nan Imam Khumaini ya kasance yana gayar girmama matarsa, akwai ma lokacin da take ba ‘yar ta wato Dr Zahra labari cewa wata rana ta ce ma Imam, “ Haqiqa na kasance tare da kai a tsawon gwagwarmayarka kuma na yi tarayya da kai ga dukkan abubuwan da suka same ka, abinda nike buqata daga wajen ka shine idan zaka shiga Aljanna ka shiga tare dani, to shine Imam ya ba ta amsa da cewa, Allah (T) ya saka maki da alkhairi ga dukkan gudummuwar da kika bayar a wannan fage na gwagwarmaya, Amma a ranar lahira bani da ikon haka saboda kowa yana jingine akan aikinsa.” Akwai kuma wani lokaci bayan rasuwar Imam Khumain aka tambayi ita Sayyida Khadija wato matar Imam Khumaini cewa ko ta yi mafarkin Imam, sai ta ce, “ Bayan rasuwar sa ina yawan mafarkinsa, mafarki na qarshe da nayi dashi shine na ganshi a cikin tufafi masu kyau yana zaune cikin natsuwa, sai na ce masa, ya ya kake? Ya ce Alhamdu lillah, Hisabi anan akwai tsanani kuma zuzzurfa ne saboda haka ku lizimci Ihtiyadi cikin al’amuranku, ya fadi haka har sau ukku.”
Idan kuma muka juya dangane da Mu’amalar Imam da maqwabtansa, ita zamu ga kyakkyawa ce kuma akwai misalai da yawa, misali zamansa a qasar Faransa, kamar yadda aka sani lokacin da Imam yake gudun Hijira a Birnin Najaf to akwai lokacin da Saddam Husain ya buqaci Imam Khumaini da ya bar qasar, ya doshi qasar Kuwait da yake Iraq tana da boda da Kuwait ta wajen Basra, da su Imam suka iso Bodar Kuwait aka hana su shiga, haka suka sake dawowa Bagdad daga qarshe suka yenke su tafi Fransa, da suka isa to garin da Imam ya zauna kasantuwar mafi yawansu bama musulmi ne ba kiristoci ne, amma duk da haka wadanda ya yi maqwabta dasu, suka ce basu ta~a ganin irin wannan kyakkyawan mu’amala ba, ta kai ga hatta a Bikin kirsimeti Imam ya bada Kudi a sawo Furen-Fulawa a raba ma maqwabtan nasa wato domin taya su murna na bikin da suke yi. Haka nan lokacin da Imam zai dawo Iran daga gudun Hijirar da ya ke yi to ana gobe zai bar qasar Faransa to maqwabta da ya zauna dasu haka ya aika wakili ya shaida masu yana yi masu bankwana, to da suka ji haka cikinsu akwa wadanda har kuka sai da suka yi wato na jin zafin rabuwa dashi. To shine suma maqwabtan suka wakilto wasu daga cikin su akan su kawo ma Imam Khumaini kyauta, Kyautar ko itace ta qasarsu wato su a al’adarsu idan an baqunce su, to babban abun da za su ba ma baqon shine su dibi turbayar garinsu su bashi ya tafi dashi, to shine suka dan dibi qasar suka saka cikin kwalba suka kawo ma Imam Khumaini. A taqaice dai saboda kyakkyawan mu’amala da suka gani daga wajen Imam akwa wadanda suka Musulunta.

Daga qarshe da yake wannan munasaba ce ta rasuwar Imam Khumaini za a kawo wasu ababe da suke da alaqa da rasuwarsa. Idan mutum ya bibiyi ababen da suka faru a jinya ta qarshe da Imam Khumaini ya yi a Asibiti daga zantukansa mutum zai fahimci lalle Imam yana da yaqini a lokacin cewa wafatinsa ya kusa, ga wasu misalai daga cikin zantukansa: 1- Matar Imam Khumaini tana cewa, wata biyu gabanin rasuwar Imam Khumaini akwai mafarki da ya yi cewa ya rasu, bayan ya rasu Imam Ali (AS) ne ya yi masa wanka, yasa masa likkafi kuma ya yi masa Sallah saannan yasa shi cikin qabarinsa. Imam ya shaida mata wannan mafarki amma ya ce mata ka da ta fada ma kowa wannan mafarki sai bayan rasuwarsa, to shine bayan rasuwarsa ta shaida ma danta Sayyid Ahmad. 2- Daya daga cikin makusantan Imam ya ce, gabanin rasuwar Imam da kimanin watanni biyu ya ce man, “ Ina gab da rasuwa, lalle na kusan tafiya.” 3- Sati biyu gabanin a yi ma Imam Khumaini tiyata na aikin da aka yi masa da likitoci suka zo suna auna shi, to shine yake ce masu komi yana da qarshe wannan shine qarshe na. 3- A daren qarshe da Imam Khumai ya kasance a gidansa to a daren an kawo masa abincin dare sai aka ga baici ba sai iyalinsa ta ce ya ci abincin mana sai Imam ya ce mata ai wannan shine darena na qarshe kuma dare na bankwana, an ce a cikin yini wani daga cikin jikokinsa mai suna Ali dan Sayyid Ahmad, Imam ya ce masa zo mu taka da kai ta qarshe, da yake ya zo a tarihin Imam cewa ya kasance kowace rana yana kai komo cikin gida na tsawon wasu mintuna wato a matsayin motsa jiki, to shine Imam ya ce ma wannan jika nasa ya zo su yi wannan tattaki amma shine na qarshe. 4- Asibitin da aka yi ma Imam Khumaini aikin Tiyata kusa da gidansa ne yake, in mutum ya taba zuwa zai ga cewa suna kusa ne, To zuwa Asibitin Imam da qafarsa ya taka zuwa Asibitin to kafin su isa Asibitin sai yake ce ma wadanda suke tare dashi, “ Zan tafi ayi min aikin Tiyata amma wannan karon ba zan dawo ba. Sai suka ce a’a za a dawo, sai Imam ya ce masu ku baku sani ba.” 5- Gabanin Imam ya wuce Asabitin da zai fita daga gida ya dubi matarsa ya ce mata “ Fi Amanillah ba sai kin sha wahala wajen zuwa duba ni ba.” Da yake ita ma lokaci ba ta da lafiya tana fama da ciwon baya. 6- Ana sauran awowi Imam ya rasu yasa a ce ma iyalinsa duk wanda yake da dama ya zo to a ranar duka ‘ya’yansa da suke raye da wasu jikokinsa sun zo Asibitin, da suka zo Imam ya dube su ya gaisa da su bayan haka kuma ya ce masu wanda yake so ya tafi yana iya tafiya wanda kuma zai zauna ba matsala, ashe kira ne na bankwana. To daga qarshe zantukan da Imam Khumaini sune suka tabbata dake nuna cewa lalle lokacin komawarsa ga Allah (T) Imam Khumaini ya rasu ranar Asabar qarfe goma da minti ishirin da biyu na dare. Ga mai neman qarin bayani dangane da darussa daga rayuwar Imam Khumaini yana iya duba littafi mai suna, “ Qabasat Min Siratil Imam Khumaini” Juz’i biyar ne littaffin, kusan babu littafi da ya kawo rayuwar Imam Khumaini sanka-sanka kamar shi. In mutum ya yi bincike zai ga cewa mafi yawan littafan da suka kawo Tarihi da rayuwar Imam Khumaini to sun ciro ne daga shi wannan littafin.

Last Updated on Friday, 21 July 2023 21:47
 
Home Maudu'oi daban-daban Darussa daga rayuwar Imam Khumaini (QS)
Copyright © 2024. www.tambihin.net. Designed by KH