Monday, 02 October 2023
Email
Make My Homepage
RSS
Register
Bayani kan Isra'i da Mi'iraji Print E-mail
Written by administrator   
Friday, 21 July 2023 21:02

Insha Allah bayani kan wannan maudu’i na Isra’i da Mi’iraji zai gudana kan wadannan ababe:

1-Ma’anan Isra’i da Mi’iraji.

2- Ayoyin Alqur’ani da Hadisai da suka zo da bayanin Isra’i da Mi’iraji.

3-Yaushe ne wannan al’amari na Isra’i da Mi’iraji ya auku.

4- Isra’i da Mi’iraji ya auku ne da Ruhin Manzon Allah kawai ko har da gangan jikinsa.

5- Ababen da suka auku a lokacin Isra’i da Mi’iraji.

6-Manufa ko Hikimar Isra’i da Mi’iraji.


1-Ma’anar Isra’i da Mi’iraji: Isra’i a lugace yana nufin tafiyar dare gabanin ketowar alfijir amma a isdilahi yana nufin tafiyar dare da Allah Ta’ala ya yi da Manzon Allah [S] daga Makka zuwa Baitil Maqadis. Mi’iraji kuma yana nufin tafiyar da aka yi da Manzon Allah [S] Zuwa sama.
2-Ayoyin Alqur’ani da kuma Hadisai da suka zo da bayanin Isra’i da Mi’iraji: Al amarin Isra’i da Mi’iraji yazo ne a surori biyu na Alqur’ani sune a cikin suratul Isra’i wato a aya ta farko da kuma suratu Najam wato a ayata 12 zuwa ta 18. Idan muka dubi aya ta farko cikin Suratul Isra Allah Ta’ala yana cewa, ‘Tsarki ya tabbata ga wanda ya yi tafiyar dare da bawansa, da daddare daga Masallaci mai alfarma zuwa ga Masallaci mafi nisa wanda muka sanya albarka a gefensa domin mu nuna masa ayoyinmu, lalle ne shi Allah mai ji ne,mai gani.” Idan muka yi dubi ga zahirin wannan aya zamu ga cewa akwau darussa masu yawa a ciki misali ga wasu daga ciki: 1-Wannan tafiya da aka yi da Manzon Allah ta kasance ne da ‘Quwwa Gaibiyya’ Wato Allah Ta’ala ne gudanar da ita. 2-Tafiyar baki dayanta tun daga farkonta har qarshenta ta auku ne a cikin dare guda wato daga Makka zuwa Birnin Qudus daga nan kuma zuwa sama har ta bakwai da dai sauran darussa da zamu gansu anan gaba. Wani Tanbihi anan kan wannan aya Kalmar Aq’sa wanda mafi yawan Malaman Tafsiri da kuma Malaman lugga suna fassara ta da mafi nisa, Ayatullahi Sayyid Samiy al-badri ya ce a fahimtarsa wannan kuskure ne kalmar tana nufin abu mai daraja a taqaice dai lokacin da yake yi mana tafsirin wannan aya ya kawo mana misalai masu yawa na in da wannan kalma ta fito a larabci wato da wannan Ma’ana. Idan muka juya zuwa ga Hadisai da suka zo da bayanai dangane da Isra’i da Mi’iraji zamu ga suna da yawa sai dai abin lura muhimmi a cikin wadannan Hadisai shine ba dukkansu bane ingantattu wato wasu Hadisan da suke da alaqa da Isra’i da Mi’iraji suna da rauni wasu ma qagaggune. Allama Dabrasiy ya kasa Hadisai da suka zo da bayani kan Isra’i da Mi’iraji zuwa ga gida hudu: 1-Wadanda aka tabbatar da ingancin su misala asalin Mi’iraji wato babu wani Malami da yake da shakku ko inkarin aukuwarsa. 2-Wadanda ba'a tabbatar da ingancinsu ba kuma ba za a iya yi masu wani tawili ba misali Hadisan da suka zo da bayanin cewa a tafiyar Mi’iraji Manzon Allah ya ga Allah Ta’ala ko ya yi Magana dashi. 3-Hadisan da suka zo wadanda ko da basu inganta ba amma za a iya tawilinsu. 4-Hadisan da suka zo wa]anda hankali zai iya tabbatar dasu kuma basu saba ma Usul ba.
3-Yaushe ne Isra’i da Mi’iraji ya auku: An samu sabani tsakankani Malaman Tarihi kan wannan al’amari wato na a wace shekara ce Isra’i da Mi’iraji ya auku amma abinda yafi shahara shine ya afku ne a 27 ga watan Rajab shekara ta goma bayan aiko ma Manzon Allah da saqo wato shekaru ukku gabanin Hijirar Manzon Allah zuwa Madina, daga cikin Malaman Tarihi da suka tafi akan haka akwai ibn Hisham da ibn Ishaq. Akwai kuma wadanda suka tafi akan cewa ya auku ne a 17 ga watan Ramadan shekara ta sha biyu gabanin Hijira daga cikin wadanda suka tafi akan haka akwai Bai-haqi, akwai kuma wadanda suka tafi akan cewa tun farkon aiko ma Manzon Allah da saqo ne aka yi Isra’i da Mi’iraji a taqaice dai akwai zantukan Malamai da dabam dabam akai. Mutum zai iya hada wadannan zantukan nasu idan aka dubi zancen da yazo cewa Manzon Allah yayi Mi’iraji da yawa a cikin rayuwarsa wato ba guda Ke nan ya yi ba.
4-Isra’i da Mi’iraji ya auku na da Ruhin Manzon Allah kawai ko har da jikinsa: Wannan wata Mas’ala ce wadda Malamai suka samu sabani a tsakaninsu akwai wadanda suka tafi akan cewa Isra’i da Mi’iraji da Manzon Allah yayi da Ruhinsa na kawai ba da jinsa ba suka ba da nasu hujjojin, akwai kuma wadanda suka tafi akan cewa da Ruhinsa da jikinsa ya yi wannan Isra’i da Mi’iraji wannan shine zancen da yafi shahara a tsakankanin Malamai na Sunna da Shi’a. Akwai kuma wadanda suka tafi akan cewa wannan al’amari ya faru ne ta hanyar mafarki, Malamai da yawa sun raunana wannan mahanga da kuma rashin ingancinta. Idan mutum ya dubi zahirin ita wannan aya ta Isra’i zai ga Allah Ta’ala ya ce ne “Subhanallazi asra bi’abdihi” wanda wannan qarara yana nuna da Ruhinsa da Jikinsa ya yi wannan tafiya, inda da ruhinsa ne kawai da zai zo da “Bi Ruhihi”.
5-Ababen da suka auku a lokacin Isra’i da Mi’irajin Manzon Allah: Al’amura da yawa sun faru, akwai ma Malamai na wadannan makarantu guda biyu wato Shi’a da Sunna da suka rubuta littafai kan wannan maudu’i na Isra’i da Mi’iraji, kuma idan mutum ya yi nazari cikin wadannan littafai da aka rubuta zai ga cewa sun qarfafa bayani ne kan ababen da suka faru a wannan tafiya ta Isra’i da Mi’iraji. Haka nan wasu daga cikin Malaman Tafsiri sun kawo bayanai sanka-sanka na ababen da suka faru misali mutum yana iya duba Tafsirin Almizan fi Tafsiril Qur’an na Allama Sayyid Tabataba’i. A dunqule daga cikin ababen da suka faru akwai: 1- wajabta salloli biyar wato wa]anda ake yi yanzu. 2-Haduwar Manzon Allah da Annabawan Allah baki dayansu wato tun daga Annabi Adam har ya zuwa Annabi Isa. 3-Haduwar Manzon Allah da Mala’ikun Allah dabam-dabam da kuma matsyin kowanne alal misali lokacin lokacin da Manzon Allah da Mala’ika Jibril suka kai Sidratul Muntaha sai Mala’ika Jibril ya ce ma Manzon Allah matsayinsa bai kai ya wuce nan saboda haka sai dai Manzon Allah ya cigaba da tafiyar. 5-Sammai Bakwai wato samman nan bakwai babu wadda Manzon Allah bai taka a daren ba tun daga sama ta 1,2,3,4,5,6,7 kuma duk bayin Allah dake ciki sai da Manzon Allah ya gansu suka ganshi. 6-Aljanna da Wuta A wannan tafiya ta Mi’iraji Manzon Allah ya shiga Aljanna ya kuma ga dukkan ni’imomin da Allah Ta’ala yayi ma bayinsa tanadi a cikinta. Haka nan yaga Gidan Wuta da azabobin da Allah yayi tanadi a cikinta kai har dama ganin wadansu wadanda ake azabtar dasu a cikinta sakamakon wasu munanan ayyukansa da dai sauransu. Bayanai wadannan ababe da aka ambata yana iya samun littaffan da aka rubuta kan Isra’i da Ma’iraji musamman wadanda aka rubuta a mahanga na Ahlul bait.
6-Manufa da kuma Hikimar Isra’i da Mi’iraji: Idan mutum ya dubi zahirin aya ta farko da ta zo cikin suratul Isra’i zai ga cewa daga cikin hikima da kuma manufarsa akwai, “Li nuriyahu min ayatina” Wato domin mu nuna masa daga cikin ayoyinmu. A cikin Suratun Najam idan mutum ya dubi ayoyin da suka zo da bayani kan Mi’iraji wato daga aya ta 12 zuwa ta 18 to a aya ta 18 zamu ga fa]in Allah Ta’ala, “Laqad Ra’a min ayati Rabbil Kubra” Wato Tabbas lalle ya ga wadanda suka fi girma daga Ayoyin Ubangijinsa. Wani tanbihi babba anan shine a mahanga ta Ahlul bait Manzon Allah bai ga Allah wato akasin abinda wasu daga cikin Malaman Ahluls Sunna suka tafi akan cewa wai a wannan tafiya ta Mi’iraji yaga Allah Ta’ala, wannan wani bahasi ne dabam wanda yake bu}atar dogon bayani ga mai buqata yana iya komawa ga littafan Aqa’id na Shi’a. Akwai Malamai da suka tafi akan cewa daga cikin manufa ko sabab na Isra’i da Mi’iraji shine saboda yadda Manzon Allah ya kasance a lokacin na rashin masu taimaka masa a lokacin misali Abu-dalib da Sayyida Khadija sun rasu ga kuma abunda ya auku a zuwansa Da’ifa wai akan wannan asasi tafiyar ta kasance wannan dai ra’ayi na wasu Malamai ne amma fadin Allah Ta’ala cewa domin mu nuna masa ayoyinmu ya wadatar wato na kasancewa shine manufar tafiyar.
Daga qarshe kasantuwar wannan wata da muke ciki a cikin sa ne aka haifi Imam Hassan Al-askari kuma shekarun baya an kawo Tarihin Imamai 12 baki daya ga mai buqatar gani yana iya duba site din wannan Shafi a net wato WWW.TAMBIHI.NET amma yanzu kasantuwar munasabobi na wilada ko wafati na Aimma ana kawo Tarihin mahaifansu mata insha Allah yanzu za a kawo Tarihin mahaifiyar Imam Hassan Al-askari amma a taqaice. Sunanta Sumanatu a wata ruwaya Jiddatu wani qaulin Hudaisu, tana daga cikin sahabban Imam Ali al-hadi wato cikin sahabbai mata, akwai ma lokacin da Imam Ali al-hadi yai mata shaida da kyawawan dabi’u da kuma nisantar munanan dabi’u kuma yai mata albishir da cewa zata rayu har sai taga Imam Mahdi [AF] Wanda zai cika Duniya da adalci a lokacin da ta cika da zalunci, wannan baiwar Allah ta rayu har taga jikanta mai Albarka wato Imamul Hujja, yama zo a tarihinta cewa bayan wafatin Imam Hassan Al-askari, shi’atu Ahlul bait wasu tambayoyi na ilimi suna komawa zuwa gareta ne wato suna tambayarta wanda wannan yana nuna kamalarta wajen ilimi. Akwai lokacin da aka tambayi Sayyida Hakima wato ‘yar Imam Muhammad Jawad idan Imam Hassan Al-askari ya yi wafati wajen wa ‘yan Shi’a zasu koma wato kan tambayoyinsu na Addini? Sai ta ba da amsa da cewa zuwa ga Jiddatu mahaifiyar Imam Hassan Al-askari wannan dai yana tabbatar da zurfin ilimintaYazo a tarihinta cewa lokacin da ta auri Imam Ali Al-hadi tana da kimanin shekaru 20 a duniya lokacin da aka haifi Imam Mahdi tana da wajen shekaru 45 ne a Duniya. A taqaice dai wannan baiwar Allah ta rayu har bayan wafatin Imam Hassan Al-askari, akwai ma lokacin da Imam Hassan al-askari ya shaida ma mahaifiyarsa cewa ga lokacin da zai rasu wato kasantuwar qulle-qulle da makirce-makirce da masu tafi da iko na lokacin suke kitsawa akansa. Idan mutum ya bibiyi Tarihin Imaman Ahlul bait 12 zai ga cewa babu Imamin da ya zauna a yanayi na sa ido da takurawa ta fuskoki dabam dabam daga wajen masu tafi da iko kamar Imam Hassan al-askar da mahaifinsa Imam Ali Al-hadi kusan rayuwarsu ma baki daya a barikin soja ne suka yi ta kuma a gari na Ahlus sunna, abin mamaki wannan gari na Samarra har zuwa wannan zamani yana da matsala wato in ka kwatanta da sauran qaburburan Imamai da suke qasar Iraq domin a shekarun baya masu ziyara sai dai su ziyarci Karbala, Najaf da Kazimiyya amma ban da Sammara wato saboda yanayin wajen, ko da ma mutum bai taba zuwa ba amma yana kallo a TV wato na masu ziyara zai ga cewa masu ziyartar Sammara din kadan ne in ka kwatanta da masu kai ziyara a Najaf ko karbala, zan iya tunawa Shekarun baya da muka je Ziyarar Arba’in tare da wasu ‘yan uwa to da muka je garin Sammara da yake mun isa garin da rana ne kuma muna so mu dawo Birnin Najaf a yinin to shine aka bamu shawara mu bar garin kafin faduwar rana saboda yadda ‘yan ta’adda in dare yayi suke ta'addanci a hanyoyi kasantuwar lokacin ‘yan ta'addan Da’ish suna yawan tada bama-bamai a qasar da kuma afka ma masu ziyara. Amma a wannan yanayi na isa ido da takura Imam Hassan Al-askari ya rayu har yai shahada, wannan yana yi da ya kasance a ciki yasa ba a samu ruwaito Hadisai masu yawa daga gare shi ba. Bayan wafatin mahaifiyar Imam Hassan Al-askari an binne ta kusa dashi ne.

Last Updated on Friday, 21 July 2023 21:25
 
Home Maudu'oi daban-daban Bayani kan Isra'i da Mi'iraji
Copyright © 2023. www.tambihin.net. Designed by KH