Monday, 20 January 2025
Email
Make My Homepage
RSS
Register
Tarihin Matayen Manzon Allah (S) Print E-mail
Written by administrator   
Friday, 21 July 2023 20:37

Wannan maudu’i na Tarihin matayen Manzon Allah maudu’i ne wanda galibi akan kawo shi ne a dunqule wato ba'a warware ba misali kowace daga cikinsu a wace shekara Manzon Allah ya aure ta kuma tana da shekaru nawa a lokacin da kuma shekarar da ta rasu da dai sauransu. Bayan haka kuma kasantuwar yanzu ina sa'ayi wajen tattara rubuce-rubuce da aka gabatar a wannan fili na Tambihi ta fannoni dabam dabam kamar fannin Fiqhu, Aklaq, Hadisi, Tarihin Manzon Allah da kuma Aimma na Ahlul bait da dai sauransu wato da nufin mai dasu zuwa littafi saboda yadda ‘yan uwa a lokuta dabam dabam sun yi magana akan hakan, amsar da nikan basu shine cewa insha Allah akwai tunanin yin haka nan gaba, zan iya tunawa Shahid Shaikh Muhammad Mahmud Turi ya taba yi man magana kan haka da jimawa na cewa zai yi kyau in tattara wadannan rubuce rubuce da ake gabatarwa a filin tambihi a maida su littafi. Insha Allah ina fata kafin watan Ramadan za'a kammala tattara su da kuma buga su a matsayin littafi. To littafin da zai kasance na Tarihin Manzon Allah da kuma Ahlul bait zai kasance yana da muhimmanci wannan maudu’i na Tarihin matayen Manzon Allah ya zamo yana ciki. Ababen da bayanai zasu gudana akan su a wannan maudu’i sune:

1- Adadi da sunayen matayen Manzon Allah.

2- Tarihinsu a taqaice.

3- Dalilai na wannan adadi da kuma Aurensu.


1-Adadi da sunayen Matayen Manzon Allah [S]: Tarihi ya nuna cewa Manzon Allah ya auri mataye 13 a rayuwarsa ya rasu ya bar guda 9 da yake akwai wadanda suka rasu tun yana raye, ga sunayensu:

1-Khadijatu ‘yar Khuwailid.

2- Saudatu ‘yar Zam’a.

3- A’ishatu ‘yar Abubakar.

4- Hafsatu ‘yar Umar.

5- Ummu Salma.

6- Juwairiyya ‘yar Haris.

7- Ummu Habiba.

8- Zainab ‘yar Jahash.

9- Safiyya ‘yar Huyayyi.

10- Zainab ‘yar Huzaima.

11- Maimunatu ‘yar Haris.

12- Mariyatul Qib-diyya.

13- Ummi Shuraik.


2-Tarihin su a taqaice:

1-SAYYIDA KHADIJA, Alhamdu lillah an taba rubutu akan Tarihinta a wannan fili na Tambihi sai dai tabarrukan za a dan kawo wasu darussa daga rayuwarta. Kamar yadda aka sani ita ce mata ta farko ga Manzon Allah kuma tsawon zamansu da Manzon Allah bai hada ta da kowa ba wato bai auri wata mata ba tana raye, duka Aurarrakin da Manzon Allah ya yi bayan rasuwar ta ne, kamar yadda in mutum ya karanci tarihin Imam Ali zai ga cewa tsawon zamansu da Sayyida Zahra bai auri wasu mataye ba sai bayan rasuwarta. Haka nan a duka matayen da Manzon Allah ya aura babu wadda yafi so kuma yake yawan ambatonta kamar Sayyida Khadija alal misali ruwayar da aka ruwaito daga wajen Aisha ta ce, “ Ban yi kishin wata mata ba kamar yadda na yi kishin Khadija alhali bamu zauna tare ba, ba dun komi ba sai saboda yadda Manzon Allah yake yawan ambatonta.” A wata ruwaya kuma ta ce Manzon Allah ya kasance so da yawa kafin ya fita gida sai ya ambaci Khadija ya yi yabo gareta, sai wata rana da ya ambace ta kishi ya kama ni na ce ai tsohuwa ce kuma Allah ya musanya maka da wadda tafi ta, sai Manzon Allah yai fushi ya ce mata wallahi a’a bai musanya man ba da wadda tafita saboda ta yi Imani da ni lokacin da mutane suka kafirce mani, ta gasgatani lokacin da mutane suka kafirce mani, ta taimake ni da dukiyarta lokacin da mutane suka hanani, Allah Ta’ala ya azurta ni da ‘ya’ya ta wajenta bai bani daga wasu mata ba, wato yaran Manzon Allah baki daya ta wajen Khadija ne in banda Ibrahim dan Mariya, batun ‘ya’yan Manzon Allah da kuma cewa wai Sayyida Khadija ta auri wani gabanin Manzon Allah wani bahasi ne dabam ga mai buqatar gani yana iya komawa ga rubutun da aka yi kan Tarihin Sayyida Khadija.
2-SAUDATU BINTU ZAM’A: Bayan rasuwar Sayyida Khadija Manzon Allah ya aure ta a Makka wato gabanin Hijira. Saudatu tana daga cikin wadanda suka Musulunta tare da mijinta tun farkon Daawar Manzon Allah tana kuma daga cikin wadanda suka yi Hijira tare da mijinta zuwa Habasha, suna Habasha ne Allah ya yi ma mijinta rasuwa bayan dawowar ta Makka ne Manzon Allah ya aure ta,har wasu daga cikin mutanen Makka suna mamaki na aurenta da Manzon Allah ya yi saboda launin jikinta baqi ne, a harshen wannan zamani wato baqar fata. Lokacin da Manzon Allah ya Aure ta tana da wajen shekara Hamsin ne shi kuma yana da kusan Hamsin da ukku. Bayan rasuwar Manzon Allah ta rayu wajen shekaru goma.
3- AISHATU BINTU ABUBAKAR: Ita ce ta ukku wato bayan Sauda sai ita, abinda ya faru shine kamar yadda ya zo a Tarihi bayan rasuwar Sayyida Khadija wata Dattijiwa mai suna Khaulatu ‘yar Hakim tana daga cikin wadanda suka yi Imani da Manzon Allah ta ce ya Manzon Allah baza ka yi aure ba? Sai Manzon Allah ya ce mata wa zan aura? Ta ce masa in kana so ka auri Budurwa ko Bazawara, sai ya ce mata wace Budurwa ko Bazawara? Ta ce masa Budurwar ita ce Aisha ‘yar Abubakar, Bazawar ita ce Saudatu, Sai Manzon Allah ya ce tana iya sa ayi akai, to shine sai taje wajen mahaifiyar Aisha mai suna Ummi Ruman ta gabatar mata da maganar, a taqaice dai ga mai buqatar ganin bayanai na sa ayinta yana iya duba littafi mai suna, “Nisa’u Haular Rasul” Na sheikh Abu Abdu Rahman Salah. Akwai sabani tsakankanin Malaman Shi’a da Sunna na tana da shekara nawa ne Manzon Allah ya aure ta wato ita Aisha mafi yawan Malaman sunna sun tafi akan tana da shekara tara ne, akwai ma wadanda suka tafi akan cewa an daura auren tana da shekara shidda ne amma tarewar ta gidan Manzon Allah sai a Madina lokacin tana da shekara tara. Amma wasu daga cikin Malaman Shi’a sun tafi akan cewa lokacin tana da shekaru 13 ne aka yi auren, wasu kuma suka ce 17 mutum na iya duba littafin, Assahih mina Sira na Allama Sayyid Ja’afar Murtadha. Aisha ta rayu bayan rasuwar Manzon Allah wajen shekaru 50.
4- HAFSATU BINTU UMAR: Ita ce ta hudu, mijinta ya yi shahada ne a yaqin Uhud a wata ruwaya kuma ta nuna cewa ya samu raunuka ne a yaqin Uhud bayan yaqin ya yi jinya daga baya ya rasu, lokacin da Manzon Allah ya aure ta tana shekaru 19 ne. Ta rayu bayan Manzon Allah [S] da wasu shekaru.
5-ZAINAB BINTU KHUZAIMA: Manzon Allah ya aura ta shekara ta ukku bayan Hijira lokacin tana da shekara 30, ta kasance ana yi mata laqabi da Uwar Miskinai wato saboda yadda take taimaka masu ta fuskoki dabam dabam. Bayan aurenta da Manzon Allah da wasu watanni kimanin wata takwas Allah Ta’ala ya yi mata rasuwa. Ita ce farkon wadda ta rasu a Madina cikin matayen Manzon Allah kuma farkon Matayen Manzon Allah da aka binne a Baqi’a, da yake dukkan matayen Manzon Allah suna Baqi’a ne in ban da Sayyida Khadija ita qabarinta yana Makka ne.
6-UMMU SALAMA: Tana daga cikin farko-farkon wadanda suka yi Imani da Manzon Allah tare da mijinta kuma suna daga cikin wadanda suka yi Hijira zuwa Habasha bayan haka kuma suka yi Hijira zuwa Madina. Lokacin da zasu yi Hijira zuwa Madina tare da mijinta ta samu jarabawa babba, abinda ya faru shine lokacin da zasu tafi sai danginta suka ce basu yarda ta tafi ba sai mijinta ya tafi ya barta da dansu,sai dangin mijin mijin suka zo suka qwace yaron akan sai dai ya koma hannunsu, wannan al’amari ya jefa ta cikin damuwa da baqin ciki har ta kai tana yawan kuka akan haka. Da abin ya tsanani wani daga cikin dnginta ya sa baki cewa abar ta ta riski mijinta saboda haka sai aka ba ta damar cewa za ta iya zuwa Madina, Haka ta kama hanya ita da yaronta zuwa Madina, akan hanya ta hadu da wani bawan Allah ya tambaye ta ina za ta ta ce masa Madina to haka yai masu jagoranci har zuwa Madinar, bayan haka suka cigaba da zama Madina har ya zuwa shahadar Mijinta a yaqin Uhud, bayan haka kuma ta samu albarkar aure da Manzon Allah. A taqaice a cikin matayen Manzon Allah baki daya Ummu Salma ita ce ta qarshe wajen rasuwa tana da shekaru wajen 90 saboda haka ta ga ababe da yawa a rayuwarta. Bayan shahadar Imam Husain ta yi kuka mai yawa kuma tai addu’a ga Allah Ta’ala cewa da ta cigaba da zama cikin maqiya tana son komawa ga Allah Ta’ala,an ce a shekarar Allah Ta’ala yai mata rasuwa. Idan mutum ya bibiyi tarihin rayuwarta zai ga cewa baki daya zai ga cewa a gwagwamarya ne a tafarkin Allah suka qare, musamman ma bayan rasuwar Manzon Allah ta fito qarara ta nuna goyon bayanta ga Ahlul bait ne, misali lokacin da Aisha za ta fita yaqin Jamal tayi-tayi ta gamsar da ita na ta goyi bayanta su fita ta ce mata a’a, ta ce mata ba domin gudun ka da ta saba ma Allah Ta’la ba na cewa su zauna a gidajen su da ita ma ta fita amma za ta goyi bayan Imam Ali ne, shi yasa a lokacin ta aika danta ya kasance cikin rundunar Imam Ali.

Haka nan an ruwaito Hadisai masu yawa daga wajenta wadanda ta ji daga Manzon Allah wadanda suke da alaqa da wilayar Ahlul bait, ayar Tadhir ma a dakinta ta sauka saboda haka abubuwan da Manzon Allah ya yi ga Ashabul kisa’i na lullube su da mayafi duka a gaban idonta ne har ta nemi iznin shiga ciki Manzon Allah ya ce mata a’a amma tana kan alhairi, haka nan kuma lokacin da Manzon Allah zai bar Duniya ya bata qasa a cikin wata kwalba ya ce mata duk lokacin da ta ga launinta ya koma ja to tabbas an kashe Husain, shi yasa lokacin da Imam Husain ya bar Madina zuwa Karbala to kullum sai ta duba qasar, wata rana ko sai ga qasar ta koma ja, nan take ta samu yaqinin cewa lalle an kashe Imam Husain [AS].
7-ZAINAB BINTU JAHASH: Qissar al’amarin aurenta da Zaid dan Haris ya zo a cikin Alqur’ani a cikin Suratu Ahzab ayata 37, ga mai buqatar ganin labarin auren da abubuwan da suka faru sanka-sanka bayan auren yana iya komawa ga littafan Tarihi ko na Tafsirin Ayar a wasu daga cikin littafan Tafsiri. Abinda za a kawo anan shine auren ta da Manzon Allah. Manzon Allah ya aure ta ne a watan Shaaban shekara ta biyar bayan Hijira ne lokacin tana da shekara 35. Bayan rasuwar Manzon Allah to a cikin matayensa ita ce ta fara rasuwa. Ta shekaru kusan goma.
8- UMMU HABIBA BINTU ABU SUFYAN: Asalin sunanta Ramlatu, anai mata kinaya da Ummu Habiba. Sunan mijinta Ubaidullahi dan Jahash ya Musulunta shi da matarsa suna ma cikin wadanda suka yi Hijira zuwa Habasha, amma abin mamaki da kuma baqin ciki lokacin da suke Habasha sai mijinta ya koma kirista amma ita matarsa alhamdu lillah ta zauna cikin Musulunci. Manzon Allah ya aure ta ne bayan Ja’afar dan Abu Dalib sun dawo gudun Hijira daga Habasha wato lokacin sun iso Madina, saboda haka Manzon Allah ya aure ta ne shekara ta 7 bayan Hijira. Mu dubi irin jarabawar da ta kasance a ciki miji ya bar Musulunci ya koma kirista kuma a lokacin Babanta wato Abu sufyan shi yake jagorantar Mushirikan Makka wajen yaqar Manzon Allah saboda haka ba yadda za a yi ta koma gidansu.
9-JUWAIRIYYATU BINTUL HARIS: Sunanta Barratu, Manzon Allah ya canza mata suna zuwa Juwairiiyya, in mutum ya bibiyi tarihi zai ga cewa akwai da yawa daga cikin sahabai maza da mata wadanda Manzon Alla ya canza ma sunaye ga wato daga sunan da basu dace zuwa ga wadanda suka da ce.
10-SAFIYYATU BINTU HUYAYYI: Matayen Manzon Allah akwai wadanda suke asalinsu larabawa ne akwai kuma wadanda asalin ba larabawa ba. To ita Safiyya Asalinta ba cikin larabawa bane a’a cikin Yahudawa ne, tana daga cikin ribatattun yaqi, ‘yanta ta da Manzon Allah ya yi shine ma ya zamo Sadakinta. Manzon Allah ya aure ta ne shekara ta bakwai bayan hijira. Akwai ma wani mafarkin da ta taba yi tun tana wajen tsohon mijinta, ta ce masa ta yi mafarkin wata ya fado cikin dakinta, sai ya ce mata ai wannan mafarki naki yana nufin kina so ki auri Sarkin Hijaz Muhammad ne sai ko ya kwashe ta da mari wanda sai da ya bar tabo a fuskar ta, bayan da Manzon Allah ya aure ta ya tambaye ta dangane da tabon da yake fuskar ta ta, shine ta bashi labarin abinda ya faru.
11- MAIMUNATU BINTUL HARIS: Ita ce qarshen wadda Manzon Allah ya aura cikin matayensa, lokacin da Manzon Allah ya aure ta tana da shekaru 27 ne a lokacin shi kuma Manzon Allah yana da shekaru 61, an yi auren ne a shekara ta bakwai bayan Hijira.
12- MARIYA: Itace mahaifiyar Ibrahim, asalinta daga Misrane, an haifi Ibrahim shekara ta 8 bayan Hijira ne, ya rasu bayan watanni da haihuwarsa wata ruwaya watanni 18 wata ruwayar watanni 16. A mahanga ta mafi yawan Malaman Shi’a qissar Hadisil-Ifki akan Mariya ne ya sauka amma a ruwayar Ahlus Suna kan Aisha ne, koma akan wanene matayen Annabawa ba wai ma na Manzon Allah ba ba zasu taba aikata wannan mummunan aiki ba na alfasha wal iyazu billah saboda yin haka zai taba mutuncin Annabin da kuma da’awarsa.
13-UMMI SHURAIK: Ita ce wadda qissar ta ya zo akan, “ Wahabat nafsaha linnabiyyi” wanda wannan shima khususiyya ce ta Manzon Allah. Wato mace ta aurar da kanta ga Manzon Allah ba tare da sadaki ba, to ita wannan baiwar Allah haka ta yi.
3-DALILAI NA ADADIN MATAYEN MANZON ALLAH (S): Ta yi yu wani ya yi tunani ko kuma ya tambaya miyasa Manzon Allah adadin matansa suka kai haka alhali sauran Musulmi su kuma ka da su wuce hudu? Da farko dai a Musulunci akwai wasu al’amura wadanda suke khususiyyar Manzon Allah ne wato shi ya kebanta dasu, haka nan akwai wasu ababe wadanda suke shi wajibi ne akansa amma a sauran Musulmi ba wajibi ba ne misali Sallar Tahajjud a wajen sa wajibi yinta amma a sauran Musulmi tana matsayin Mustahabbi ne. Bayan haka idan mutum ya bibiyi wadannan aurarraki na Manzon Allah zai ga sun ginu ne kan wasu manufofi na Da’awa da kuma Hikimomi misali saboda kusanto da wasu qabiloli zuwa ga Musulunci ko kuma saboda kashe kaifin qiyayyarsu da gabarsu ga addinin Musulunci misali auren Safiyya ko kuma saboda rusa wata al’ada ta Jahiliyya misali a auren Zainab ‘yar Jahash wadda kafin nan tana auren Zaid ne da dai sauran wasu hikimomi na aurarrakin, amma ba kamar yadda maqiya Musulun ko Munafukai suke nunawa ce wai saboda shaawa ne da makamatansu, wanda ko a hankali mutum ya dubi aurarrakin da Manzon Allah ya yi in ka debe na Sayyida Khadija lokacin yana da shekaru 25, to duka sauran matayen ya aure su ne yana da shekaru sama da 50 ne ko 60 misali Sauda wadda ya aura bayan Khadija, ya aure ta yana da shekaru 53 ko Maimunatu lokacin yana da shekaru 61 saboda haka ya yi ne akan asasin manufofi na cigabar da Addinin Musulunci, in muka dubi tarihi zamu ga haka domin akwai qabilun da suka Musulunta kasantuwa Manzon Allah yana auren ‘yar qabilarsu ko kuma suka rage gaba da qiyyayya da suke da Musulunci.

Last Updated on Friday, 21 July 2023 21:19
 
Copyright © 2025. www.tambihin.net. Designed by KH