Monday, 02 October 2023
Email
Make My Homepage
RSS
Register
Tarihin Sayyida Dahira mahaifiyar Imam Rida [AS] Print E-mail
Written by administrator   
Friday, 21 July 2023 20:16

Kasantuwar wannan wata da muke ciki na Zul-Qada wanda a cikinsa maulidi da kuma shahadar Imam Rida suka kasance, kuma kamar yadda aka saba munasabobi irin wadannan akan tunasar da juna dangane da Tarihin iyaye mata na Imamin da ake munasabar. Saboda haka a wannan munasabar ta haihuwar Imam Rida da kuma qanwarsa Sayyida Ma’asuma wadda qabarinta yake Birnin Qum Insha Allah bayani zai gudana kan mahaifiyarsu wato Sayyida Dahira, da yake Imam Rida da Sayyida Ma’asuma shaqiqai ne wato Uwa daya Uba daya suke, kuma sun shaqu da juna wato kamar yadda Imam Husain da Sayyida Zainab (AS) suke. Dalilin rasuwar ta ma shine ta baro birnin Madina da nufin tafiya zuwa wajen Imam Rida a Khurasan –birnin mash-had a yanzu – sai rashin lafiya ya kamata a wani gari kusa da birnin Qum, sai ta buqaci da a qarasa da ita birnin Qum domin jinya a can, bayan isar su Qum da wasu kwanaki Allah (T) yai mata rasuwa. Asalin sunan wannan mahaifiya tasu mai albarka shine Najmatu wannan suna Dahira mijinta ta ne wato Imam Kazim (AS) yasa mata shi bayan da ta haifi Imam Rida (AS), kuma ana yi mata laqabi da Ummul Banin, Asalinta ba balarabiya ba ce daga Magrib take amma ta tashi a tsakankanin larabawa, wuce nan ma ta tashi a gidan Imam sadiq (AS) ne.
Aurenta da Imam Kazim: Wata rana Sayyida Hamidatu matar Imam Sadiq kuma mahaifiyar Imam Kazim ta yi mafarkin da Manzon Allah [S] yana ce mata ya Hamidatu ki aurar da Najma ga danki Musa saboda za ta haifa masa mafi alhairi da ke bayan qasa, Alhamdu lillah bayan wannan aure mai albarka shine aka haifi Imam Rida, shine babban da na Imam Kazim. Akwai lokacin da mahaifiyar Imam Rida take cewa bayan da ta samu cikin sa duk wasu matsaloli na ciki ba ta jisu ba, kuma in ta kwanta barci takan ji Tasbihi da Hailala daga cikinta, amma in ta farka sai ta de na ji, haka al’amarin ya kasance har ya zuwa lokacin da ta haifi Imam Rida nan ma wasu ayoyi da ababen banmamaki suka sake bayyana. Tsakanin haihuwarsa da wafatin Imam Sadiq kwanaki 15 ne.
Sayyida Dahira ta kasance mai yawan Ibada, bayan da ta haihu sai tasa a kawo mata mai raino, da aka tambaye ta dalili sai ta ce ibadodin da na saba yi gabanin haihuwa ta, to yanzu sun yi qasa tun bayan haihuwata shine nike so in cike gibin. wannan darasi ne babba ga ‘yan uwanmu ‘yan uwa mata wato hidimar ‘ya’ya ko ta gida kada su shagaltar dasu baki daya dangane da ibadodi ko gwagwarmaya ko kuma neman ilimi. Sayyida Dahira ta kasance tana da gayar kamala a Dabi’ointa, alal misali Sayyida Hamida wato mahaifiyar Imam Kazim akwai lokacin da take ce masa, “ Ya kai Dana ban taba ganin yarinya mai kyawawan dabi’u kamar wannan yarinya ba.” Yazo a Tarihin Sayyida Dahira cewa saboda gayar girmamawarta ga Sayyida Hamida ba ta zama gabanta. Idan mutum ya bibiyi Tarihin iyaye mata na Aimman Ahlul bait zai ga cewa kowace a zamaninta babu wata mace da ta kaita kamala kuma aurensu ba bisa hatsari bane wato zabi ne daga Allah (T) alal misali mafarkin da Sayyida Hamida da ta yi na Manzon Allah yana umartar ta da ta aurar da ita ga Imam Kazim. Haka nan idan mutum ya bibiyi qissar yadda aka yi ta zo gidan Imam Sadiq (AS) zai fahimci cewa lalle wannan wani al’amari ne daga wajen Allah (T).
Kasantuwar wannan wata da muke ciki a cikinsa ne aka haifi Sayyida Ma’asuma, Insha Allah za a kawo Tarihinta da kuma wasu sassa na rayuwarta mai albarka amma a taqaice:
1.WILADARTA: Watau haihuwarta, an haife ta a Madina, 1 ga watan zul qadah, Hijira ta 173.

2.NASABARTA: Mahaifinta shine Imam Kazim (AS). Ya ma zo a tarihinta cewa wato mahaifiyarsu, lokacin da ta haifi Imam Ridah [AS] ta buqaci a nemo mata mai raino, a ka tambaye ta dalili, sai ta ce ibadodin da ta saba yi sun ragu,saboda haka tana buqatar taimakawa wajen reno domin ta cike gibin ibadodinta. Kakanta shine Imam Sadiq [AS]. Ya zo a kan cewa tun gabanin a haife ta ya yi albishir da haihuwarta da kuma fadin falalar ta da kuma ziyarar ta. Daga cikin falalar ta da Imam Sadik [AS] ya fadi, akwai cewa tana da matsayi a wajen Allah [T]. Shi yasa wanda duk Allah [T] yayi wa muwafaqa da ziyarar haramin kabarinta dake birnin Qum, a kofar shiga haramin zai ga an rubuta “Ya Fadima ki ce ce ni a wajen Allah, domin ki na da matsayi a wajensa”. Allah Ta’ala ya saka mu cikin wadanda zata ceta.

3.LAQUBBANTA: Tana da laqubba masu yawa, amma biyun nan su suka fi fice, sune Karimatu- Ahlulbayt da kuma Ma’asuma. Wannan laqabi na Ma’asuma ya zo akan cewa Imam Ridah [AS] ya yi mata laqabi da shi, wanda wannan yana alam ta, gayar kamalar ta da kuma matsayin ta wajen Allah (T).
4.FALALAR ZIYARAR KABARINTA: An samo daga Imam Ridah [AS] cewa duk wanda ya ziyarce ta, Aljanna ta tabbata a gare shi. Haka nan makamancin wannan Hadisin, an samo daga Imam Jawad [AS] cewa duk wanda ya ziyarce ta Aljanna ta tabbata gare shi.

5.KARAMOMINTA: Sayyida Ma’asuma [AS] ta kasance ta na da karamomi masu yawa, tun tana raye da bayan wafatinta, kai har wannan zamanin namu kullum karamominta dada bayyana suke. Za kaga masu ziyararta, zasu yi tawassuli da ita kan buqatocin su, kuma ka ga Allah ya biya musu buqata. marasa lafiya zaka ga an kawo su, ayi tawassuli da ita, ka ga Allah ya basu lafiya. shi yasa wani daga cikin malaman tarihi yake cewa babu wani daga cikin ‘ya’yan ma’asumai [AS] da yake da karamomi masu yawa kamar ta. Haka nan yau a doran qasa babu wata bai war Allah da take samun masu yawan ziyara kabarinta kamar yadda take samu. Domin idan mutum ya je Haramin ta zai ga dare da rana maziyar ta ne, Daga cikin karamominta da ya bayyana a wannan zamanin namu a shekarun baya, shine akwai gyaran ainihin shi kabarin ta da aka yi , aka zabi manyan malamai daga ciki akwai Ayyatullah Najafi A-lmar’ashi, shine yake cewa babu wani abun daya canza na likkafanin ta da kuma jikinta, ya ce kamar ka ce yau a ka sata.
6.JARABAWOYIN TA: Sayyida Ma’asuma [AS] ta fuskanci jarabawoyi masu yawa a rayuwarta, musamman a qarshen rayuwarta, misali bankwana da kuma zafin rabuwa da dan uwanta Imam Ridah [AS] lokacin da zai bar Madina zuwa Khurasan, tafiya wadda ba zai dawo ba, kamar yadda ya shaida masu. Duk da sun yi bankwana, amma ta hau soron dakin na gidansu, tayi ta kallon Imam Ridah [AS] har ta dai na ganinsa, kuma wannan shine qarshen ganinta da Imam Ridha a gidan duniya domin bayan haka basu sake haduwa ba. Alaqa da kuma shaquwa na Imam Ridah [AS] da Sayyida Ma’asuma, kamar alaqa da kuma shaquwa na Imam Husain [AS] da kuma Sayyida Zainab [AS] ne. Bayan haka ga kuma jarabawar mahaifinta, wato Imam kazim [AS] da ta gani na zamansa a kurkuku da kuma shahadarsa a ciki, da dai sauran jarabawowi masu yawa da ta fuskanta, wanda ba za’a iya kawo su ba saboda gudun tsawaitawa.
7.ILIMINTA: Sayyida Ma’asuma [AS] ta kasance mai yawan ilimi, akwai wani abin da ya taba faruwa, wanda ya nuna matsayinta a ilimi wannan abin ko shi ne akwai wani lokacin da wasu daga cikin mabiyan Imam kazim [AS] suka zo daga garinsu zuwa madina, domin su ga Imam kazim [AS] su gai she shi, su kuma gabatar da wasu tambayoyi, da suka zo Madina suka isa gidan Imam kazim [AS] sai suka samu bai nan ya yi tafiya, sai suka rubuta tambayoyi suka ba Sayyida Ma’asuma [AS] cewa in ya dawo ta bashi, kashe gari sai suka dawo suka samu bai dawo ba, alhali su kuma suna son su koma garinsu a ranar, sai Sayyida Ma’asuma [AS] ta rubuta masu amsoshin tambayoyin, suka amsa suna farin ciki. Kan hanyarsu ta komawa sai suka hadu da Imam kazim [AS] yana dawowa sai suka shaida masa maqasudin zuwan su da kuma abinda ya faru sai Imam Kazim [AS] ya ce su kawo amsar takardar ya gani, bayan ya gani ya fadi wannan kalmar sau uku, “ta fanshi babanta”.
8.IBADARTA: Ta kasance mai yawan ibada. Hatta in da take yin ibadar ta,salloli da makamantansu yana nan har yanzu a birnin Qum ana ma kai ziyara wajen.
9.WAFATINTA: Ta rasu tana da shekaru 30 a duniya, sababin rasuwar ta shine; ta bar Madina ita da wasu ‘yan uwanta da nufin su tafi khurasan wajen Imam Ridah [AS], akan hanya a wani waje mai suna SAWA rashin lafiya ya kama ta, ta buqaci a tafi da ita zuwa Qum, da suka isa kwanan ta 17 Allah yayi mata rasuwa. Wannan dai a taqaice kenan dangane da Tarihin Sayyida Ma’asuma [AS]
Har ala yau nan wasu sassa ne na rayuwar Imam Rida (AS)
1. Haihuwarsa: An haifi Imam Rida [AS] ranar 11 ga watan Zul-qada shekara ta 148 bayan hijira.
2-Nasabarsa: Sunan mahaifiyar Imam Rida [AS] Dahira, Sunan Mahaifinsa Imam Musa Alkazim [AS].
3-Tasowarsa: Imam Rida [AS] an haife shi a Madina ne kuma ya taso a Madina, ya kasance a Madinar har ya zuwa kusan karshen rayuwarsa da khalifa na Abbasawa a lokacin ya maida shi Khurasan da zama.
4-Lakubbansa: Imam Rida [AS] yana da lakubba masu yawa amma wanda yafi shahara shine Arrida, an tambayi Imam Jawad [AS] cewa mi yasa ake ce ma mahaifinsa Arrida sai ya ce ana ce masa haka ne saboda makiyansa sun yarda dashi kamar yadda masoyansa suka yarda dashi.
5-Shekarunsa: Imam Rida [AS] ya rayu a duniya ne shekaru hamsin da biyar.
6-Tsawon shekarun imamancinsa: Imam Rida [AS] ya yi Imamanci na tsawon shekaru Ashirin.
7-‘Ya’yansa: Imam Rida [AS] yana da daya ne shine Imam Jawad amma akwai wata ruwaya sabanin haka misali akwai ruwayar da ta zo akan cewa yana da diya mai suna Fadima har ma ta ruwaito Hadisai daga wajensa.
8-Rasuwarsa: Imam Rida [AS] ya yi shahada ranar 23 ga watan Zul-qada a wata ruwaya karshen watan Safar shekara ta 203 bayan hijira.
9-Kabarinsa: Imam Rida [AS] kabarinsa yana a birnin Mash-had ne wato a kasar Iran. Wannan kenan dai a takaice na wasu sassa daga rayuwarsa.

Last Updated on Friday, 21 July 2023 20:35
 
Home Maudu'oi daban-daban Tarihin Sayyida Dahira mahaifiyar Imam Rida [AS]
Copyright © 2023. www.tambihin.net. Designed by KH