Tarihin Sayyida Fadimatu Bintu Asad (Mahaifiyar Imam Ali (AS)) |
Written by administrator | |||
Thursday, 20 July 2023 22:29 | |||
Kasantuwar wannan wata da muke ciki na Rajab akwai munasabobin maulidin Imam Ali [AS], Imam Baqir [AS], Imam Jawad [AS], Imam Hadi [AS], da kuma shahadar Imam Kazim [AS]. Insha Allah za a gabatar da Tarihin mahaifansu mata sune: 1- Sayyida Fadimatu Bintu Asad- Mahaifiyar Amiril mu'uminin. 2- Sayyida Fadimatu Bintul Hassan- Mahaifiyar Imam Baqir. 3-Sayyida Sabika- Mahaifiyar Imam Jawad. 4- Sayyida Sumanatu- Mahaifiyar Imam Hadi. 5- Sayyida Hamidatu- Mahaifiyar Imam Kazim.
An haifi Imam Ali [AS] a makka ranar Jumma’a 13 ga watan Rajab, shekaru talatin bayan Aamul fil, wato shekarar giwa. Lokacin haihuwar Imam Ali [AS] akwai ayoyi da suka kasance, wanda mutane su ka yi ta mamaki, alal misali akwai wani mutum da ake ce masa ibn Qa’anab ya ce: “Na kasance ina zaune tare da Abbas dan Abdul-Mudallib tare kuma da wasu daga cikin Banu Hashim kusa da Ka’aba, sai ga Fatima ‘yar Asad tana tahowa [wato mahaifiyar Imam Ali a lokacin tana da cikinsa wata tara, naquda ta kamata. Sai suka ji tana cewa: “Ya Ubangijina, ni na na yi imani da kai da kuma abinda ya zo daga wajenka ta hanyar Manzanninka da kuma littafanka, kuma ni ina mai gasgatawa da zantukan kakana Ibrahim [AS]. Ina roqon ka da haqqin wannan daki da wanda ya ginashi da kuma wannan abin da yake cikin cikina, ka sauqaqe min wannan haihuwa. Sai ibn Qa’anab ya ce sai muka ga Ka’aba ta bude, sai Fatima bintu Asad ta shiga ciki, ta faku daga ganinmu. Bayan haka in da ya bude na Ka’abar sai ya rufe da iznin Allah, muka yi muka yi mu bude domin sashen matayenmu su taimaka mata amma qofar Ka’aba ba ta budu ba. Sai muka fahimci cewa to wannan wani al’amari daga wajen Allah Ta’ala. Bayan kwana hudu sai ga shi ta fito dauke da Ali a hannunta.” Ya zo akan cewa lokacin da ta yi nufin fita sai ta ji sautin Magana cewa: “Ya Fatima ki sa masa suna Ali.” Wadannan kwanaki hudu da ta yi cikin Ka’aba ya zo akan cewa ‘ya’yan itace na Aljanna ake kawo mata. Da dai sauran ayoyi da suka bayyana a lokacin haihuwarsa. Mahaifiyar Imam Ali [AS] ta rayu har ya zuwa hijirar Manzon Allah daga Makka zuwa Madina, ta yi hijira ta same shi a Madina, ya zo a tarihi cewa ita ce mace ta farko da ta taka da qafafuwanta ba tare da ta hau dabba ba tun daga Makka zuwa Madina a lokacin hijira. Kuma ta ba da gudunmawa sosai wajen kafuwa da kuma tabbatuwan wannan addini na Musulunci. Haka nan kuma akwai hadisai masu yawa da aka ruwaito daga wajenta wadanda ta ji daga Manzon Allah. Kuma ta kasance lokacin da take riqon Manzon Allah ta kan fifita shi akan ‘ya’yanta baki daya. Lokacin da ta rasu Manzon Allah ya yi kuka mai yawa, kuma shi ya jibinci dukkan al’amuranta na jana’iza, domin hatta likkafaninta Manzon Allah rigarsa ya bayar aka yi dashi. Haka nan a wajen yi mata sallah Manzon Allah kabbarori saba’in yayi, har Umar yake ce ma Manzon Allah ka yi ma wannan matar abun da baka taba yi ma wani ba, Sai Manzon Allah ya ce masa ita Uwa ta ce bayan mahaifiyata. 2- SAYYIDA FADIMATU BINTUL HASSAN: Imam Baqir shine farkon wanda ya hada wannan nasaba mai daraja wato mahaifiyarsa Fadima ‘yar Imam Hassan, mahaifinsa Imam Zainul Abidin dan Imam Husain. Ana yi ma Fadimatu Bintul Imam Hassan kinaya da Ummu Abdullah, Imam Zainul Abidin ya kasance yana ce mata Siddiqa. Imam Sadiq ya ce, “ Lalle ta kasance Siddiqa kuma duk cikin Alil Hassan babu kamar ta.” Sayyida Fatimatu bintul Hassan tana daga cikin matayen da suka halarci waqi’ar Karbala tare da danta Imam Baqir lokacin yana da shekaru 4 a Duniya saboda haka duk ababen da suka faru a Karbala a gaban idonta aka yi misali na shahadar Amminta Imam Husain da kuma dan uwanta Qasim dan Hassan da sauran shahidan Karbala, da kuma abubuwan da aka yi masu bayan waqi’ar Karbala misali ga mijinta Imam Zainul Abidin lokacin yana da shekaru 22 a Duniya. Daga cikin Karamomin Sayyida Fadimatu bintul Hassan kamar yadda aka ruwaito daga Imam Baqir ya ce, “ Wata rana mahaifiyata tana zaune a jikin wata Katanga sai katangar ta tsage tai qara zata fadi, sai tai ishara da hannunta ta ce na gama ka da darajar Manzon Allah kada ka fadi, to haka katangar nan ta tsaya ba ta fadi har ta bar wajen.” 3- SAYYIDA SABIKAT: Ita ce mahaifiyar Imam Jawad, ya zo a ruwaya cewa tana daga cikin zuriyyar Mariya wato mahaifiyar Ibrahim dan Manzon Allah [AS]. Ya isa ya zama daraja babba a wajenta cewa Manzon Allah ya yi ishara da ita. Haka nan Imam Kazim [AS] ya yi bayanita ga wani daga cikin sahabbansa yake ce masa tana daga cikin zuriyyar Mariya Al-qib]iyya kuma ita za ta haifi Imam Jawad daga qarshe ya ce masa idan ya riske ta to ya isar da sallamarsa gareta, wadannan ababe sun faru kamar yadda Imam Kazim ya yi bayani. Sayyida Sabika ana yi mata kinaya da Ummul Hassan. 4- SAYYIDA SUMANATU: Ita ce mahaifiyar Imam Ali Al-hadi, ana yi mata kinaya da Ummul Fadal. Ya zo a tarihinta cewa ta kasance mai yawan Ibadodi musamman Sallar Tahajjuda da kuma karatun Alqur’ani, kuma ta kasance mai Taqawa da kuma tsan-tseni. Idan mutum ya bibiyi Tarihin aurenta da Imam Jawad zai ga cewa wani daga cikin sahabban Imam Jawad mai suna Muhammad dan Ibrahim ya ce, “ Wata rana Imam Jawad ya kirani ya ce wasu ‘yan Kasuwa sun zo Madina daga cikinsu akwai masu sai da Bayi, sai ya bani Dinari saba’in ya ce in sayo masa Baiwa zai ganta da siffa kaza da kaza, ko dayaje sai ya ga shigen wadda Imam Jawad ya siffata masa saboda haka sai ya saye ta. Akwai darussa masu yawa a cikin wannan qissa alal misali kowane Imami yasan matarsa wadda za ta haifi Imamin da zai zo bayansa, wato takan kasance ajiya ce ta Allah, da yake kiyayewa har ya zuwa ga Imamin da za ta aura. Idan mutum ya bibiyi Tarihin iyaye mata na Aimma na Ahlul bait zai ga haka, wato mahaifiyar kowane Imami to a zamaninta tafi kowa kamala a cikin mata. 5- SAYYIDA HAMIDATU: Ita ce mahaifiyar Imam Kazim, Imam Baqir yai mata laqabi da Mahmudati, akwai kuma wadanda suka yi mata laqabi da Lu’ulu’u. Akwai karamomi masu yawa a qissar lokacin Aurenta da Imam Sadiq alal misali wani lokaci wani daga cikin sahabban Imam Baqir ya ziyarce shi a gida a lokacin Imam Sadiq yana tare da mahaifinsa Imam Baqir to lokacin da mai ziyarar ya zo sai Imam Sadiq ya je ya kawo masa Inabi, to a lokacin sai shi wannan baqon ya ce ma Imam Baqir miyasa ba za a yi ma Sadiq aure ba alhali ya isa aure? Sai Imam Baqir ya ce masa, masu sai da bayi zasu zo daga waje kaza, in sun zo nan Madina zasu sauka a gida kaza, ba a jima ba sai gasu sun zo kamar yadda Imam Baqir ya yi bayani sai ya ba da kudi cikin wata jaka da za a sawo baiwa daga cikin bayin da suka zo dashi, da aka je wajen mai sai da bayin ya ce ai ko duk kusan ya sai da bayin sai guda biyu kawai ko suma basu da lafiya, sai ya fito da su, aka sai daya daga cikinsu wadda mutum zai iya siffatawa a matsayin ajiya ta Allah Ta’ala ce, da aka tambayi kudinta sai ya ce Dinare saba’in babu wani ragowa a kai, abin mamaki ko da aka bude wannan jaka ta kudi da Imam Baqir ya bayar sai aka gani Dirhami saba’in ne cif-cif, lokacin da aka kaita wajen Imam Baqir sai ya ba da ita ga Imam Sadiq a matsayin matarsa kuma za ta haifi hujjar Allah, Allahu Akbar ita ta haifi Imam Kazim. Idan muka dubi wannan qissa zamu ga cewa akwai karamomi masu yawa da suka bayyana ga guda uku daga ciki:1- Imam Baqir ya san wadda za ta kasance mata ga Imam Sadiq. 2- Ya bayyana daga in da zasu zo kuma idan sun zo ga in da zasu sauka kuma haka abin ya kasance. 3- Adadin kudin da ya bayar ya dace da abinda mai ita ya fadi da dai sauran karamomi. kuma ya zo a Tarihin cewa ta kasance tana da ilimii mai yawa har ta kai ga cewa Imam Sadiq ya ayyana ta a matsayin duk tambayoyi da ‘Yan uwa mata suke dashi to su je su tambaye kai tsaye. Ta yiyu wani yai tunani ko yai tambaya miyasa wasu daga cikin Aimma suka auri Bayi? Saboda idan mutum ya bibiyi Tarihi zai ga cewa tun daga Imam Sadiq har ya zuwa Imam Al-askari matayensu da suka haifi Imaman da suka biyo bayansu a matsayin Bayi ne. Haka nan idan mutum ya dubi mahaifiyar Imam Zainul Abidin ita ma a matsayin Baiwa aka zo dasu Madina. To amsa a taqaice ita ce da yake ai’amarin yana buqatar dogon bayani shine saboda rusa al’adar larabawa a lokacin musamman yadda suka dauki bayi a lokacin kamar ma ba mutane ba, misali a lokacin Bani Umayya akwai wani Masallaci a wani gari in dai mutum Bawa ne to ba zai shiga Masallacin ba. Haka nan daga cikin Hikimomin dake ciki akwai dada samun hadin kai na Musulmi misali mafi yawan wadannan iyaye mata na Aimma a harshen wannan zamani za a iya cewa daga Africa suke misali wannan Baiwar Allah Sayyida Hamida a laqabinta ana ce mata Almag-rabiyya, Albar-bariyya. Haka nan Sayyida Sumatu ita ma ana ce mata Almag-rabiyya da dai sauransu, kuma idan mutum ya dubi launin jikin wasu daga cikin Aimma na Ahlul bait zai ga cewa Tarihi ya nuna baqin launi ne alal misali Imam Rida, a taqaice dai saboda nuna ma al’ummar Musulmi a lokaci cewa babu wani banbanci tsakanin Balareba da wand aba Balareba face da Taqawa. Haka nan idan mutum ya dubi tarihi a lokacin Manzon Allah [S] Ya yaqi wannan mummunar al’ada ta dubin wulaqanci ga Bayi kuma ta yi rauni amma abun baqin ciki a lokacin Bani Umayya sai suka dawo da wannan mummunar al’ada. Misali a lokacin Manzon Allah Auren da ya auku na Zainab Bintu Jahash da sahabinsa mai suna Zaid dan Harisa wanda asalinsa Bawa ne amma Manzon Allah ya aura masa Baquraisha kuma Bahashima da dai sauran wasu dalilai wanda wani lokaci insha Allah za a kawo su.
|
|||
Last Updated on Friday, 21 July 2023 20:36 |