Tarihin Sayyida Aminatu, Mahaifiyar Manzon Allah (SAAW) |
Written by administrator | |||
Thursday, 02 February 2023 18:49 | |||
Kamar yadda wannan fili na Tambihi ya saba a irin wannan munasaba ta maulidin Manzon Allah [SAAW] akan dauki wani janibi da yake da alaqa da Manzon Allah domin tunasar da juna akai, insha Allah a wannan munasabar ta maulidin Manzon Allah da kuma Imam Ja’afaru Sadiq [AS] za a tunasar da juna ne dangane da Tarihin Mahaifiyar Manzon Allah wato Sayyida Aminatu da kuma Mahaifiyar Imam Ja’afaru Sadiq wato Sayyida Fadimatu bintul Qasim. Ma’anar Aminatu a lugga yana nufin amintacciya. SAYYIDA AMINATU BINTU WAHAB Da farko Nasabarta idan mutum ya bibiyi nasabarta zai ga cewa ita Ba Quraisha ce ta wajen Uwa da Uba alal misali nasabarta ta wajen mahaifi. Sunan mahaifinta Wahab shi kuma dan Abdu Munaf shi kuma dan Zahrata shi kuma dan Kilab shi kuma dan Murra shi kuma dan Ka’ab shi kuma dan Lu’ayyi shi kuma dan Galib. Nasabarta ta wajen Uwa. Sunan mahaifiyarta Barratu ‘yar Abdul Uzza dan Usman dan Abdu Dar ‘dan qusayyi dan Kilab dan Murra dan Ka’ab dan Lu’ayyi dan Galib. Idan muka juya nasabar Mahaifin Manzon Allah zamu ga cewa shine Abdullahi dan Abdul Mudallib dan Hashim dan Abdu manaf dan Qusayyi dan Kilab dan Murra dan Ka’ab dan Lu’ayyi dan Galib dan Fihir dan Malik dan Nadar dan Kinana dan Khuzaimah dan Mudrikah dan Iliyas dan Mudar dan Nizar dan Ma’ad dan Adnan. Idan aka lura da nasabar mahaifin Manzon Allah da kuma nasabar mahaifiyarsa zamu ga cewa a kakanni akwai inda suka hadu. Anasabar ta wajen mahaifinsa za a ga cewa an tsaya ne a kakansa Adnan saboda akwai Hadisi da aka ruwaito daga Manzon Allah ya ce, “Idan nasaba ta ta kai ga Adnan to ku kame.” Wato daga cigaba da ambaton nasabar, zan iya tunawa Daurar karatu da muka je watannin baya a birnin Najaf a bangaren Tarihi, Malamin da ya karantar damu wato Ayatullah Sayyid Sami Albadriy a wani littafin Sira da ya rubuta mai suna “Siratu Nabawiyya” to da muka zo wajen da ya shafi nasabar Manzon Allah ga Adnan sai ya kawo mana wannan Hadisi da aka ruwaito daga Manzon Allah shine har yake yi mana bayani cewa wannan nasaba ta kakannin Manzon Allah tun daga Abdul mudallib zuwa Adnan Malaman Tarihi sun yi ittifaqi wato ba a samu wani sabani akai ba sunna da shi’a, ya ce amma inda mutum zai bibiyi nasabar Manzon Allah daga Adnan zuwa Annabi Ibrahim ko Annabi Adam zai ga cewa ba wai kawai Malaman Tarihi ba hatta Malaman Nasaba zai ga sun sassaba ma juna a kai, ga mai buqatar qarin bayani yana iya komawa ga wannan littafi da ya rubuta wanda aka ambata ko wasu littafansa na Tarihi da ya rubuta da yake ya ruba littafai masu yawa musamman a fannin Tarihi da kuma Tafsir kuma ana samun littafansa a net in mutum ya bincika, idan mutum ya lissafa zai ga cewa kakannin Manzon Allah tsakanin Abdul Mudallib zuwa Adnan kakanni 20 ne. Mahaifin Manzon Allah ya auri Sayyida Aminatu yana da shekara 25 a wata ruwaya yana da shekara 30, kuma a shekarar da suka yi aure bayan wasu watanni Allah Ta’ala yayi masa rasuwa wato ko shekara basu yi da auren ba ya rasu, bayan rasuwarsa da wasu watanni aka haifi Manzon Allah. Akwai ruwayoyi dabam dabam kan rasuwarsa wata ruwayar ta zo akan cewa lokacin da Sayyida Amina tana gab da haihuwa sai suka tafi Madina shi da mahaifinsa wato Abdul Mudallib domin sawo ababen da za a yi walima dashi idan ta haihu, wata ruwayar kuma tazo akan cewa ya tafi sham ne kan abinda ya shafi kasuwanci wato tijara to akan hanyarsu ta dawowa da suka iso Madina sai rashin lafiya ya kama shi yayi jinya a Madina ya rasu, an ce Abdul mudallib shi yai masa wanka yasa masa likkafani ya kuma binne shi. Yazo akan cewa yayi kuka sosai na rasuwar wannan daa nasa mai al barka saboda duk cikin ‘ya’yansa maza babu wanda yake so kamarsa da yake yana da ‘ya’ya maza guda goma daga cikinsu akwai Abbas, Hamza, Abu dalib, Abdullahi, Haris, Abu Lahab da dai sauransu. Haka nan ita ma Sayyida Aminatu tayi kuka mai yawa kan wannan babban rashi, yazo a tarihinta cewa tun bayan rasuwarsa kowace shekara ta kan ziyarci qabarinsa a Madina, a irin wannan ziyara da takai wata rana sai ta kamu da rashin lafiya ta rasu a Abwa wani gari ne tsakanin Makka da Madina, lokacin da ta rasu Manzon Allah yana da shekaru shidda a wata ruwaya yana da shekaru hudu. Yunqurin kashe Sayyida Aminatu Akwai wata mata mai suna Zarqa’a, asalinta daga Sham take tazo Makka to sakamakon wani haske da ake gani a Fuskar Sayyida Aminatu kuma labari ya bazu tsakankanin mutane cewa lalle wannan haske na Annabin qarske ne wanda zai rushe gumaka da duk wani abun bauta ba Allah Ta’ala ba to shine hassada da gaba ya kwashe ta akan ya za ta yi ta kashe wannan mata wato Sayyida Aminatu a lokaci guda kuma bata son a gano ita ta yi kisan, sai ta yi tunanin ta yi amfani da wadda take yima Sayyida Aminatu kitso, ta je tasameta, sai mai kitson ta ce mata yana ganki cikin damuwa da baqin ciki, ta ce mata damuwa ta da kuma baqin ciki na shine na wannan ciki da za a Haifa wanda zai zama sanadiyyar rushewar gumaka da kuma kauda bokanci da kuma sihiri to ita kuma wannan mata Zarqa’a daga cikin ayyukan da take yi akwai bokanci da kuma sihiri, sai tace mai kitson idan tazo kitso wajenki ga wannan qarfen nasa masa guba ki caccaka mata shi, in kin aiwatar zan baki dukiya mai yawa, wata rana Sayyida Aminatu taje kitso wajenta kamar yadda ta saba, ta zauna domin yin kitson ashe ita wannan mata ta boye wannan qarfe mai guba wanda zata yi wannan mummunan aiki dashi, da ta fara kitson sai ta nemi ta dauko qarfen domin ta aiwatar da mummunan shirin sai taji hannunta bai motsi to a lokacin Sayyida Aminatu ta fahimci makircin da aka qulla wasu matan ma suka fahimci haka shine aka tambayi mai kitson ke ko mi ya kaiki ga aikata wannan mummunan aiki? Ta ce son Duniya da kuma rudu to shine ta basu labarin wadda ta sata wato ta tona mata asiri. Saboda haka haihuwar Manzon Allah bata zo ma mutanen Makka da bazata ba wato tun gabanin a haife shi mutane suna jira domin akwai bayanai akai da ya yadu tsakankanin mutane saannan kuma ga ayoyi daban da suka auku a lokacin haihuwars alal misali lokacin da aka haife shi Sayyida Aminatu ta ce taji wani sauti na cewa kin haifi shugaban halittu kisa masa suna Muhammad ga kuma haske da ya haskaka garin Makka a daren haihuwarsa, sa’annan duk wani abinda ake bauta ba Allah Ta’ala ba sai da aka ga wata alama a gareshi misali masu bautar gumaka sai da aka ga gumakan sun sunkuya, masu bautar wuta kuma sai da aka ga wutar ta bice, bayan haka kuma Fadojin masu mulki sai da aka ga katangunsu sun tsatsage a taqaice dai babu wani dan Adam da aka Haifa wadanda ayoyi dabam dabam suka bayyana a lokacin haihuwarsa kamar Mnzon Allah. Haka nan idan mutum ya karanci Tarihin Manzon Allah tun tasowarsa har ya zuwa yo masa wahayi wato cikarsa shekaru 40 shi ma mutum zai ga cewa cike suke da ayoyi da kuma mu’ujizozi alal misali ko tafiya yake duwatsu da itatuwa suna yi masa sallama wata suna cewa Assalamu alaika ya nabiyyullah da dai sauransu. Rayuwar Manzon Allah a wata mahanga za a iya kasa ta zuwa marhaloli hudu; Marhala ta farko gabanin haihuwarsa wato bayanai da suka zo akan haka ta hanyar Annabawa ko littafan da aka saukar kama Attaura da Injila. Marhala ta biyu bayan haihuwarsa zuwa gabanin Annabta wato aiko masa da wahayi. Marhala ta ukku zamansa a Makka bayan Annabta wato kafin Hijira. Marhala ta hudu zamansa a Madina kafin wafatinsa. SAYYIDA FADIMATU BINTUL QASIM Itace mahaifiyar Imam Sadiq [AS] Idan mutum ya bibiyi nasabarta zai ga cewa tana tuqewa ne ga Abubakar alal misali Fadima ‘yar qasim shi kuma dan Muhammad dan Abubakar, idan mutum ya karanci tarihinsu zai ga cewa Muhammad da qasim dukkansu ‘yan Shi’a ne, Muhammad yana daga cikin manyan sahabban Imam Ali shine ma wakilinsa a Misra wato a lokacin, sunan mahaifiyarsa Asma’u bintu umais asalinta matar Ja’afar dan abu dalib ce wato yayan Imam Ali bayan Shahadar Ja’afar sai Abubakar ya aure ta ta Haifa masa wannan da Muhammad a shekara da aka yi hajjin bankwana, bayan rasuwar Abubaka Imam Ali ya auri ita Asmau bintu umais saboda haka shi Muhammad a hannun Imam Ali ya tashi, kuma duka yaqoqin da Imam Ali ya yi na Jamal da Siffin duk yana tare da Imam Ali ne misali a yaqin Jamal bai kasance tare da Aisha ba wadda take matsayin yaya gareshi tun da mahaifinsu daya. Lokacin yana gomna na Misra Mu’awiya ya aika da runduna ta mayaqa qarqashin jagorancin Amru dan As akan suje su yaqe shi a cikin wannan yaqi yayi shahada bayan haka kuma suka qona gawarsa. shi kuma qasim yana daga cikin sahabban Imam Zainul Abidin haka nan Sayyida Fadimatu bintul qasim tana daga cikin mabiyan Imam Zainul Abidin, akwai ma fadin Imam Sadiq da yake cewa, “Mahaifiyata ta kasance Mumina, mai taqawa mai kyautatawa Allah yana son masu kyautatawa.” Lokacin da Imam Muhammad Baqir ya tafi neman aurenta wajen mahaifinta sai ya ce masa babu matsala yaje ya samu mahaifinsa ya daura masu aure da wannan ‘ya tasa, wadda haka yana nuna gayar sallamawarsa ga imamin zamaninsa. Sayyida Fadimatu bintul qasim ta kasance mai yawan ilimi, a bangaren mataye tana daga cikin wadanda suka ruwaito Hadisai masu yawa daga Aimma na Ahlul bait, akwai ma wani Hadisi da ta ruwaito daga Imam Zainul Abidin yana cewa, “A kowace rana yana roqon Allah Ta’ala har sau dubu ya gafarta ma Shi’arsa zunubansu.” Akwai ma wani abun da ya taba faruwa tana dawafi a Ka’aba sai wani yaga ta yi wani abu sai wani mutum da yake dawafi ya ce mata baiwar Allah kin kuskure sunna sai ta bashi amsa da cewa mu wadatattu daga iliminka wato shine ya yi kuskure ba wai ita ba amma shi bai san haka ba saboda a lokacin da yawan mutane suna kan sunnonin masu mulki ne amma ba sunnonin Manzon Allah [SAAW] ba.
|