Thursday, 19 September 2024
Email
Make My Homepage
RSS
Register
Addu’a a mahangar Ahlulbayt (AS) Print E-mail
Written by administrator   
Sunday, 02 May 2021 11:10

 

Kasantuwar wannan wata da muke ciki na amsar addu’oin bayi domin babu wani wata daga cikin watannin Musulunci 12 wanda Allah Ta’ala yake amsar Addu’oin bayinsa kamar wannan wata na Ramadan, a watan Ramadan din ma musamman a  kwanaki goma na qarshensa saboda daren Lailatul qadri da yake cikinsa. Idan mutum ya yi bincike akan asasin mahangar Sunna da Shi’a dangane da Addu’a zai ga cewa gudunmuwar da Shi’a suka bayar a wannan fage yafi yawa kan na Sunna alal misali mutum ya dubi dinbin littaffan Addu’oi da shi’a suke dashi, nasan a shekarun baya wato a farko-farkon bayyanar fahimtar Ahlul-bait a tsakankanin ‘yan’uwa akwai wani fitaccen Malamin Tijjaniyya da wasu sashen ‘yan uwa suka ziyarta to a lokacin sun tafi da littafin Mafatihul Jinan da nufin su nuna masa, da yake lokacin Littafin Mafatihun yana farko-farkon shigowa cikin ‘yan uwa to da Shaihin ya amshi littafin sai ya buqaci zai duba shi zuwa wani lokaci, da lokacin ya yi aka zo za’a amsa ya sake buqatar da a qara masa lokaci daga qarshe dai ya buqaci a bar masa littafin, wannan al’amari ya faru ne sama da shekaru 30 da suka wuce kuma Alhamdu lillahi Shaihin yana raye har yanzu. A taqaice abinda nike son fitarwa a nan shine lalle littafan Addu’oi masu yawa da Shi’a suke dashi to Sunna basu dashi alal misali mu dauki Addo’oi na watan Ramadan. Wane littafi na Sunna mutum zai iya ambata mai dauke da addu’oi kamar haka, daya daga cikin fitattun littafan Addu’oi da sunna suke dashi akwai littafin Azkar na Nawawi to idan mutum yana dashi ya dauko shi ya duba addu’oin watan Ramadan da ya kawo musamman ma na daren lailatul qadri zai ga cewa Addu’a daya ya kawo wanda aka ruwaito daga Aisha da ta tambayi Manzon Allah Addu’ar da za ta yi a daren lailatul qadri yace ta ce, “Allahumma innaka afuwwun tuhibbul afwa fa’afu anni.” to mutum ya kwatanta da littafin Mafatihul Jinan a ayyukan watan Ramadan da ya kawo zai ga cewa ko daya bisa goma bai kai ba. Haka nan idan mutum ya bibiyi tarihin Imaman Ahlul bayt 12 zai ga cewa babu wani Imami wanda ba a ruwaito dinbin addu’oi daga gareshi ba, alhamdu lillahi a wannan zamani namu akwai wani Malami da ya tattara addu’oi dabam dabam da aka ruwaito daga kowane Imami ya mai da shi littafi. Ta yi yu wani ya yi tambaya to miyasa Shi’a suka fi Sunna yawan littafan  Addu’oi? Amsa sassauqa a nan itace yanayi da ‘yan shi’a suka kasance ko suka samu kansu a tsawon tarihin wannan al’umma na cutarwa da gallazawa a hannun masu tafi da iko da mutanen gari ya banbanta da na Sunna, in ma mutum bai san tarihi ba to ya dubi wannan zamani a kuma wannan qasa da yake ciki yaga irin cutarwa da kuma gallazawa da mabiya tafarkin Ahlul bait suke ciki musamman Almajiran Malam [H]. Bayan wannan ‘yar shinfida bayani kan wannan maudu’i zai gudana insha Allah kan wadannan ababe.

1-Falalar Addu’a.

2-Ladubban Addu’a.

3-Sabubban da suke sa a amshi addu’a.

4-Sabubban da suke hana amsar Addu’a.

5-Wasu daga cikin littafan Addu’oi.

6-Qissoshin bayin Allah masu Addu’a.

1-Falalar Addu’a: Akwai ayoyi da Hadisai masu yawa da aka ruwaito daga Manzon Allah [SAAW] da kuma Aimma [AS] da suke nuni dangane da falalar Addu’a ga wasu daga ciki:

 1-Manzon Allah [SAAW] ya ce, “Shin in nuna maku wani makami wanda zai tseratar daku daga maqiyanku sa’annan kuma ya bubbugar maku da arziki? Suka ce Naam, sai ya ce Ku roqi Ubangijinku dare da rana, domin makamin Mu’umini shine Addu’a.” A lokacin waqi’ar Abaca lokacin da jami’an tsaro suka zo gidan Malam da nufin wai su yi binciken makamai, to haka suka buqaci shiga daki-daki a gidan Malam to da suka zo dakin Malam da yake Malam yana tare dasu a lokacin su duba nan, su duba can kai har cikin sili to a cikin dakin akwai in da dardumar Malam take akanta akwai littafin addu’oinsa to shine Malam ya ce masu ga makamai nan sai jami’an tsaron duk hankalinsu ya dawo wajen, sai Malam ya nuna masu littafan addu’oi ya ce masu wadannan sune makamanmu da muke harbin ku dasu sai suka yi garau basu gane komi ba. Haka nan akwai lokacin da wani dan uwa a farkon al’amari wato marigayi Malam Hassan Khalifa Allah ya jikansa  ya tambayi Malam Sahifa Sajjadiyya sai Malam ya ce masa yanzu baka da ita a gidanka sai ya ce bai da ita, sai Malam cikin murmushi ya ce Assha kace baka da makami a gidanka, wato mu dubi yadda Malam yake ganin wadannan littafan Addu’oi a matsayin makamai da ake harbin Azzalumai da su, wato makaman da basu sansu ba kuma basu da irinsu. kuma addu’ar wanda aka zalunta karbabbiya ce.

 2-Imam Zainul Abidin [AS] ya ce, “Addu’a tana tunkude bala’i wanda ya sauka da wanda bai sauka ba.”

 3- Imam Ali [AS] ya ce, “Addu’a garkuwa ce ga Mumini.”

4- Imam Kazim [AS] ya ce, “Addu’a tana tunkude abinda aka qaddara ma mutum da kuma wanda ba a qaddara masa ba.”

5-Amiril muuminin [AS] ya ce, “Mafi soyuwar aiki zuwa ga Allah a bayan qasa shine Addu’a.” Idan mutum yayi tunani zai ga cewa babu wani abu da ya shafi rayuwar dan Adam face akwai addu’a a ciki misali in zai ci abinci to akwai addu’ar cin abinci, haka in zai yi barci ko zai zauna ko zai fita daga gida ko zai zaga bayi ko zai yi wanka kai hatta idan mutum zai duba fuskarsa a madubi  ko zai taje kansa to akwai addu’arsu, ko zai hau abin hawa misali mota ko mashin shima akwai addu’arsa, a taqaice dai duk wani abunda mutum zai aikata to akwai addu’arsa sai dai in mutum bai sani ba ko kuma ya sani amma bai aikata ba, ta nan mutum zai ga dimbin lada da muke hasara idan bamu yi wadannan addu’oin ba a rayuwarmu ta yau da kullum.

2-Ladubban Addu’a: Akwai ladubba na Zahiri da badini da ake son aikatawa a lokacin addu’a, idan mutum ya duba cikin littafin Ihya ulumiddin na Gazaliy a fasalin addu’a zai ga ya kawo wadannan ladubba har guda goma saboda haka anan wasu daga ciki ne, daga cikin ladubba na Zahiri akwai kasancewa cikn alwala wato lokacin da mutum zai yi Addu’a mustahabbi ya zamanto da alwala. Haka nan mustabbi ne lokacin addu’ar ya fuskanci alqibla ya kuma daga hannayensa lokacin Addu’ar, Manzon Allah [SAAW] Ya ce, “Ubangijinku mai karamci ne kuma mai kunya, yana jin kunyar bawansa idan ya daukaka hannayensa lokacin addu’a ya dawo dasu ba komai.” Haka nan in ya kammala addu’ar sai ya shafi fuskarsa da hannayensa  kamar yadda aka ruwaito haka daga Imam Sadiq [AS] Haka nan daga cikin ladubba na Zahiri akwai yin kuka lokacin Addu’a, idan mutum ya bibiyi tarihin bayin Allah zai ga cewa sun kasance suna kuka  a lokacin Addu’oinsu musamman ma Addu’oi da aka ruwaito daga Ma’asumai misali Du’au Khumail da sauransu zaka ga cewa suna karanta ta suna kuka. Idan muka juya ga ladubba na badini suma daga ciki akwai cewa mutum ya halartar da zuciyarsa lokacin addu’a wato addu’oin da mutum yake karantawa ya kasance tunaninsa yana biye da abunda yake karantawa ba wai mutum ya kasance yana biya addu’a amma zuciyarsa tana wani waje, halartar da zuciya a lokacin addu’a shine ruhin addu’a saboda haka in bai samu ba to ya zama kamar jiki ba ruhi ne, kuma addu’ar zai zamo bata da tasiri a cikin zuciyarsa. Daga cikin ladubba na badini a lokacin addu’a shine mutum ya kyautata zato ga Allah dama yaqini cewa Allah ya amsa masa. Haka nan daga cikin ladubban badini na Addu’a ko da mutum yaga jinkirin biyan buqata wato abunda mutum ya roqa bai ga biyan buqata ba to kada ya debe tsammani wato ka sa ran cewa Allah  zai biya maka buqata saboda ita addu’a idan mutum ya yi to dayan ukku ko dai ya ga biyan buqata a lokacin ko kuma a jinkirta masa biyan buqata zuwa wani lokaci ko kuma baki daya bai ga biyan buqata ba wato Allah ta’ala ya tunkude masa wani bala’i da ya tunkaro shi maimakon a biya masa buqatar to sai Allah ya tunkude masa bala’in, ya zo a ruwaya cewa ranar qiyama idan bawa ya ga wasu sakamako da Allah Ta’ala ya bashi da nufin na wasu addu’oi da ya yi a gidan duniya amma ba a biya masa buqata ba sai a yanzu to shine mutum saboda girman sakamakon da ya gani ya ce ina ma dai duk Addu’oin da ya yi a gidan Duniya ba a amsa ba.

3-Sabubban da suke sa a amshi addu’a: Ababen da suke sa a amshi addu’ar mutum suna da yawa kamar yadda yazo a ruwayoyi na Hadisai ga wasu daga ciki:

1-Lokacin da aka yi addu’ar wato akwai wasu lokuta masu daraja da falala da idan mutum yayi addu’a a cikinsu Allah Ta’ala yana amsar Addu’ar misali a cikin watanni akwai watan Ramadan, a Mako akwai daren Jumma’a da kuma Ranar Jumma’a, a cikin yini lokacin Zawal da kuma qarshen dare da dai sauransu.

2-In da aka yi addu’ar wato akwai wasu wajaje masu tsarki da in mutum ya  yi addu’a a wajen to karbabbiya ce misali filin Arfa, kusa da Ka’aba ko Haramomi na A’imma da sauransu.

3-Bayan aikata wasu ayyuka na ibada, wani lokaci ruwaya ta Hadisi zata ce wanda ya aikata kaza bayansa ya gabatar da addu’a to Allah zai amsa misali bayan salloli na wajibi ko bayan karanta ziyarar Ashura da sauransu.

4-Sakamakon wani yanayi, wani lokaci mutum kan iya kasancewa a wani yanayi da in yayi addu’a Allah Ta’ala ya kan amsa misali Addu’a a lokacin ruwan sama, ko Addu’ar wanda aka zalunta da dai sauransu.

5-Gabatar da Salati ga Manzon Allah da Alayensa gabanin addu’a ko tsakiyar addua ko qarshen Addu’a shima yana sabbaba amsar Addu’a, idan ma ba a yi salati ba to to yana iya zama hijabi daga rashin amsar Addu’a kamar yadda aka ruwaito daga Imam Sadiq ya ce, “Addu’a bata gushewa da shamaki har sai an yi salati ga Manzo da alayensa.

6-Sa Zoben Aqiq lokacin Addu’a shima yana sabbaba amsar Addu’a, an ruwaito daga Imam Sadiq ya ce, “Babu wani tafi da aka daga mafi soyuwa ga Allah kamar tafin da akwai Zoben Aqiq jikinsa. Zoben Aqiq yana da falaloli masu yawa.

7-Yi ma wani ko wasu Addu’a shima yana daga cikin hanya babba ta samun abunda ka roqa masa wato idan mutum ya yi ma dan uwansa Mumini addu’a misali Allah ya bashi kaza ko ya kiyaye shi daga kaza to abinda ya  roqa masa shima sai a bashi irinsa, shi yasa wasu bayin Allah addu’oinsu suna roqa ma wasu ne, alal misali an ruwaito daga Imam Hassan ya ce  akwai wani daren Jumma’a da ya ga mahaifiyarsa Sayyida Fadima tun daga farkon daren har qarshensa tana addu’ar alhairi ga wasu sai ya ce mata na ji wasu ki ke yi ma Addu’a amma banji kin yi ma kanki ba, sai ta ce masa ya kai dana Maqwabci sa’annan gida.

4-Sabubban da suke hana amsar Addu’a: Akwai dalilai da yawa da suke janyo ma mutum idan yayi addu’a ya zamanto Allah Ta’ala bai karbe ta ba, daga ciki akwai

1-Cin Haramun ko Shubha saboda haka idan mutum na son addu’arsa ta zamo karbabbiya to dole ya kasance Halal ne yake ci.

2-Nisantar sabon Allah saboda mutum zai iya aikata wani zunubi misali zalunci ya janyo masa aqi amsar addu’arsa.

3-Gabatar da Addu’a a cikin gafala wato lokacin da yake addu’ar zuciyarsa ko tunaninsa yana wani waje ba ga addu’ar ba to haka yana sabbaba Allah Ta’ala ba zai amsa addu’ar ba.

5-Qissoshin bayin Allah masu Addu’a: Akwai wasu bayin Allah da suka yi fice ko shahara da yawan Addu’a wato zaka ga Addu’oi masu tsawo amma sun hardace su akwai lokacin da Ayatullahi Bahjati yake cewa ya ga wasu bayin Allah masu yawa da Addu’ar Abu Hamzata Sumaliy suke qunitin witri da ita wato da ka suke yinta, akwai ma wani bawan Allah ya hardace Du’au Khumail saboda haka shi a sujuda yake biyata baki daya, ya zo a tarihin Imam Khumaini cewa kusan babu wata Addu’a dake cikin mafatihul jinan wadda bai biyata ba, haka nan akwai wani bawan Allah da Addu’oin watan Ramadan baki daya kullum yana karanta su baki dayansu kuma ba tare da fashi ba misali Addu’oin watan Ramadan na yini da kuma na dare, a taqaice dai mutum ya kasance mai yawan karanta Addu’oi da aka ruwaito daga Ai’mma na Ahlul bait.

6-Rabe-rabe Addu’oi: Addu’oi kamar yadda Malaman Aklaq suka yi bayani sun kasa su zuwa gida biyar akwai;

1-Addu’oi yaumiyya wato wadanda kullum ana karanta su misali Addu’oin safe da yamma ko kuma  Ta’aqibat na bayan Salloli na wajibi dadai sauransu.

2-Addu’oi Usbu’iyya wato na mako, ko wace rana na mako tana da addu’ar ta misali ranar Jumma’a tana da nata, haka nan Asabar, lahadi, litinin……kowanne nada nashi wa]annan Addu’oi akwai wadanda aka ruwaito daga Imam Zainul Abidin da kuma wasu Imamai.

3-Addu’a Shahariyya wato ta wata-wata, tana farawa ne tun daga 1 ga wata har ya zuwa 30 ga wata na watannin Musulunci in mutum ya duba cikin littafin Dhiya’us salihin zai ga ya kawo Addu’oin.

4-Addu’oi Sanawiyya wato na shekara-shekara misali Addu’oi na watan Ramadan da muke ciki suna cikin wannan aji ne wato na sanawiyya saboda bayan watan Ramadan sai kuma wani watan Ramadan.

5-Umuriyya wato akwai wasu addu’oin da basu da wani ayyanan nan lokaci to irinsu ana son mutum ko da sau daya ya biya su a rayuwarsa. To haka ake so kowane dan uwa ko ‘yar’uwa ya yi ma kansa wannan nizami na Addu’oi kuma ya lizimce su har ya zuwa saukar ajalinsa.

Daga qarshe ina roqon Allah Ta’ala ya karba mana ibadodinmu da kuma Addu’oinmu ya kuma sa kada wannan wata na Ramadan ya zamanto shine na qarshe a rayuwar mu, muna roqo Allah  ya rayamu ya nuna mana wani watan Ramadan mai zuwa dama wasu shekaru insha Allah cikin qoshin lafiya da kuma yelwar Arziki.    

 
Home Maudu'oi daban-daban Addu’a a mahangar Ahlulbayt (AS)
Copyright © 2024. www.tambihin.net. Designed by KH