Sallar Tahajjud |
![]() |
![]() |
Written by administratordr | |||
Sunday, 25 April 2021 21:54 | |||
Kasantuwar wannan wata na ibada da mujahada da muke ciki, daga cikin manyan ibadodi na wannan wata mai albarka akwai Sallar Tahajjud. Sallar Tahajjud yana da gayar muhimmanci ko ba a watan Ramadan ya zamanto mun lizimce ta amma a watan Ramadan sai mu qara qaimi misali in ba a watan Ramadan ba mutum ya saba yana tashi qarfe 2 ko 3 na dare to a watan Ramadan sai mutum ya qara qaimi yam ai dashi qarfe 12 ko 1 na dare saboda falala da kuma darajojin dake cikin watan, kai wasu bayin Allah dararen watan Ramadan baki daya suna raya sune wato basu barci a cikinsu sai a cikin yini saboda haka idan mutum zai iya haka aka fiso in kuma ba zai iya ba to ya zamanto ya raya rabin daren ko sulusinsa, mutum yayi tunani cewa dama ce ta wata guda Allah Ta’ala ya bashi kuma mutum bai sani ba ka shine watan Ramadan na qarshe a rayuwarsa. Idan mutum ya bibiyi tarihin bayin Allah zai ga cewa dukkansu ma’abuta dare ne wato masu Sallar Tahajjud da daddare ne in ma har basu samu yenta ba to sukan kasance cikin damuwa da baqin ciki alal misali ya zo a tarihi Sheikh Abbas Alqummiy wato marubucin littafin Mafatihul Jinan. Dansa yana cewa wata rana sun yi Sallar Asuba tare dashi to bayan sallar Asuba sai yaga yana ta kuka sai ya tambaye shi lafiya? Sai yace masa jiya da daddare bai samu yin Sallar Tahajjud dinsa ba, sai dansa to ai yinta mustahabbi ne ba wajibi ba, sai baban yace masa ban san wane laifi ne na aikata wanda ya hana ni samun muwafaqar yin ta ba. Insha Allah a qarqashin wannan Maudu’i na Sallar Tahajjud bayanai dai-dai gwargwado za su gudana kan wadannan ababe: 1-Falalar Sallar Tahajjud. 2-Lokacin Sallar Tahajjud. 3-Raka’oin Sallar Tahajjud. 4-Surorin da ake karantawa a Sallar Tahajjud. 5-Addu’in da ake karantawa bayan kowace Raka’a biyu na Sallar Tahajjud. 6-Abubuwan da suke hana Sallar Tahajjud. 7-Ramakon Sallar Tahajjud. 8-Qissoshin masu Sallar Tahajjud. 1-Falalar Sallar Tahajjud Sallar Tahajjud ta na da falaloli masu yawa a Addini da Duniya da kuma Lahira Mahaifiyar Annabi Sulaiman ta kan ce masa, “Ya kai dana kashedin ka da yawan barci da daddare saboda yawan barci da daddare ya kan sa mutum ya kasance faqiri ranar qiyama.” Manzon Allah [SAAW] Ya ce, “Sallar dare Fitila ne ga ma’abucinta a cikin duhun qabari.” Wannan Hadisin ya nuna kenan Sallar Tahajjud tana haskaka kabarin mutum idan ya rasu. Allah Ta’ala ya yi wahayi ga Annabi Musa [AS] cewa, “Ka tashi cikin dare domin yin Sallah zan sanya qabarin ka ya zamo dausayi daga cikin dausayoyin Aljanna.” Manzo Allah [SAAW] Ya ce, “Masu daraja a ciki al’umma ta sune: Mahaddata Alqur’ani da kuma ma’abuta dare.” Wato masu yin Sallar dare. Imam Ali [AS] Ya ce, “Sallar Tahajjud tana sa lafiyar jiki, tana sa mutum ya samu yardar Allah da kuma rahamarsa.” Manzon Allah [SAAW] Ya ce, “Duk wanda ya yi Sallar Tahajjud to fuskarsa za ta yi kyau a cikin yini.” Wato za ta kasance cikin annuri. Manzon Allah [SAAW] Ya ce, “Mafi alhairin ku shine wanda ya kyautata Magana, ya ciyar da abinci, ya yi Sallah da daddare mutane suna barci.” Da dai sauran Hadisai masu yawa kan falalar Sallar Tahajjud. 2-Lokacin Sallar Tahajjud Lokacin Sallar Tahajjud yana farawa ne daga tsakiyar dare zuwa ketowar Alfikir. Imam Baqir [AS] Ya ce, “Lokacin Sallar Dare shine tsakanin rabin Dare zuwa qarshen Daren.” Yanzu rabin dare yana somawa ne daga wajen 12:30 Saboda haka yin Sallar Tahajjud gabanin tsakiyar dare sai dai in da wani uzuri misali tafiya misali zai bar Kaduna zuwa Lagos, Motar su za ta tashi qarfe 8 ko 9 na dare to a nan yana iya Sallar Tahajjud din sa tun kafin su tashi, ko kuma bai da lafiya ne kuma magun-gunan da zai sha akwai masu sa barci to gudun barci ya zarce dashi har ya zuwa Alfijir yana iya gabatar da Tahajjud din sa gabanin ya kwanta da dai sauransu. Amma akwai ruwayoyi na Hadisai da suka nuna cewa ko da akwai uzuri da mutum ya yi gabanin lokacin to gwanda ya yi ramakon ta. 3-RAKA’OIN SALLAR TAHAJJUD Sallar Tahajjud Raka’a 8 ne, duk bayan Raka’a biyu zai yi sallama, sai kuma Raka’oi 2 na Shafa’i, sai kuma Raka’a 1 ta witiri. Amma mustahabbi ne gabanin ya soma sallar Tahajjud ya gabatar da Raka’a biyu. A taqaice dai in mutum ya lissafa zai ga Raka’oi 13 To haka ake so kowane Dare mutum ya yi su har ya koma ga Allah Ta’ala. 4-SURORIN DA AKE KARANTAWA A CIKN SALLAR TAHAJJUD Raka’oin biyu na farko da ake son yi gabanin soma Tahajjud din to bayan Fatiha a Raka’ar farko mutum zai karanta qulhuwallahu daya, a Raka’a ta biyu kuma bayan Fatiha ya karanta qulya ayyuhal Kafirun daya. Bayan haka sai ya tashi ya fara Tahajjud to a Raka’ar farko da ta biyu bayan Fatiha ya karanta qulhuwallahu 30-30. A Raka’a ta ukku bayan Fatiha zai karanta Suratul Muzammil, a Raka’a ta hudu bayan Fatiha zai karanta Suratun Naba’i wato Amma. A Raka’a ta biyar bayan Fatiha Zai karanta Suratu Yasin da Suratu Dhukan, a Raka’a ta shidda bayan Fatiha zai karanta Suratu Waqi’a da Suratu Mudassir. A Raka’a ta bakwai bayan Fatiha sai ya karanta Suratul Mulk, a Raka’a ta takwas bayan Fatiha sai ya karanta Suratu Insan wato Hal ata alal insani. A Raka’oin biyu na Shafa’i kuma a Raka’ar farko bayan Fatiha zai karanta Suratu Falaq, a Raka’a ta biyu bayan Fatiha zai karanta Suratun Nas. A Rakar Witiri kuma bayan Fatiha zai karanta qulhuwallahu sau 3 bayan haka sai ya karanta Falaqi da Nasi. Wadannan Surori da ake karantawa a dukkanin Raka’oin ya zo ne a ruwayoyi na Hadisi da aka ruwaito daga A’imma na Ahlul bayt saboda ko da mutum zai karanta wasu Surori to ya ga cewa ya karanta Surar da ake karantawa a Raka’ar gabanin fara surar da yake son karantawa ko bayan Surar da yake son karantawa, wani Tambihi a nan shine ko da a ce bai hardace wadannan Surori ba to zai iya daukar Alqur’ani ya karanta su da yake Sallar Nafila ce wato ba matsala, a Sallar wajibi ne yake da Matsala yin haka. 5-ADDU’OIN DA AKE KARANTAWA BAYAN KOWACE RAKA’A BIYU NA TAHAJJUD Idan mutum ya duba a cikin littafin Misbahul Mutahajjid zai ga ya kawo Addu’oin da ake karantawa bayan ko wace Raka’a biyu ta Tahajjud har ya zuwa sallamewa, yana da kyau mutum ya lizimci yin Addu’oin domin suna da tasiri a zuciya sosai ga kuma ladar da mutum zai samu in ya karanta su. 6-ABUBUWAN DA SUKE HANA SALLAR TAHAJJUD Wasu lokuta mutum kan samu kansa a wani yana yi na cewa ya saba tashi Sallar Tahajjud amma kuma sai yai kwanaki bai samun tashi, to zunubai ke haifar da hakan misali an ruwaito daga Abi Abdullah [AS] Ya ce,” Mutum zai iya yin qarya guda daya amma ta zama sanadiyyar kasa yin Sallar Tahajjud dinsa.” Wani mutum ya zo wajen Imam Ali [AS] Ya ce, “Yanzu ba na iya tashi Sallar Tahajjud kuma ina kwanciya da nufin zan tashi, sai Imam Ali ya ce masa Zunubai ne suka dabaibaye ka”. Imam Sadiq [AS] Ya ce, “Lalle mutum zai iya aikata wani zunubi haka kuma ya yi sanadiyyar kasa tashi domin Sallar Tahajjud dinsa.” Saboda haka abu na farko ga mutum in dai yana son samun Istiqama da sabati akan sallar Tahajjud dinsa to ya nisanci aikata zunubai, mu dubi misalin wancan Hadisin cewa yin qarya guda daya tana iya hana mutum Tahajjud, to ina ga cewa mutum ya kwashe yininsa yana qaryaryaki da kuma giba da kuma kalle-kalle na haramun ko munana zato ga ‘yan uwansa, Akwai wata qissa dana taba karantawa ta wani bawan Allah ya kwashe shekaru yana tashi sallar Tahajjud sai aka wayi gari sai da ya kwashe wata shidda bai samun tashi, kuma kullum ya kan kwanta da nufin zai tashi, to abin ya dame shi so sai, yai ta Addu’oi a kai, daga qarshe sai ya fahimci cewa, akwai wata rana yana tafiya sai ya ga wani mutum na kuka sai a ransa ya ji cewa wannan dai saboda a ce masa bawan Allah yake kukan. To mu dubi wannan al’amari sakamakon munana zato da ya yi ga dan uwansa Musulmi ya jefa shi ga wannan mummunan yana yi, to ina ga ya furta ma wani, shi ka dai a ransa ya yi tunanin saboda haka lalle mu yi hattara. Daga cikin ababen da suke hana sallar dare akwai take ciki da abinci wato duk lokacin da mutum ya cika cikinsa da abinci har ya yi qat to tashi da daddare zai yi masa wahala in ko har ya iya tashi to lalle zai yi tahajjud din ba kushu’i saboda haka yana da muhimmanci mu kiyaye. Malaman suluki da yawa sun ta fi akan cewa yawan barci sanadiyyar yawan cin abinci ne. 7-RAMAKON SALLAR TAHAJJUD Idan mutum sallar Tahajjud ta kubuce masa to mustahabbi ne ya ramata kashe gari wato cikin yini. Yin haka sunna ne saboda ya zo a ruwaya kuma Allah Ta’ala yana son haka wato mutum ya rama wani abun da ya saba aikatawa amma saboda wani dalili bai samu yi ba. 8-QISSOSHIN MASU YIN SALLAR TAHAJJUD Wato yadda wasu bayin Allah suka tsayu da yin sallar Tahajjud tsawon lokaci a rayuwarsu, akwai misalai da yawa na bayin Allah amma za’a bada misalin na Imam Khumaini, Ya zo a tarinsa cewa ya kwashe shekaru saba’in bai taba fashin Sallar Tahajjud ba, hatta a cikin halin tafiya ko rashin lafiya bai bar tahhajjud dinsa ba. To mutum ya tambayi kansa ya taba kwashe wata saba’in ko kwana saba’in ba tare da ya yi fashin Tahajjud dinsa ba? Ga wasu misalai na Sallar Tahajjud din Imam Khumaini: Imam Kumaini ya kasance yana ta shi kowane dare da qarfe biyu, ya lizimci haka hatta lokacin da aka kwantar da shi a asibiti, kuma in ya ta shi qarfe biyu na dare bai komawa barci har sai ya dangana da sallar Asuba. Haka nan a halin tafiya Imam na Tahajjud dinsa in lokacinta ya yi alal misali a cikin jirgin sama ko a mota wadanda su ka yi tafiya da shi duk sun tabbatar da haka cewa lokacin da ya saba yin Tahajjud na yi sai dai a ga yana yi. Haka nan kuma a halin yana yi na gajiya shima Imam bai fashin Tahajjud dinsa, alal misali akwai wani lokaci da aka sako Imam daga Kurkuku wato a lokaci Shah, wanda ke ba da labarin ya ce sun kwashe tsawon yini wajen zagayen tarbar Imam Khumaini ba su iso masauki ba sai 8 na dare, amma duk da haka da lokacin tahajjud din Imam ya yi suka ga ya ta shi da dai misalai masu yawa akan haka. Haka nan imam Khumaini idan yana sallar Tahajjud yakan yi ta cikin kushu’i da kuka, akwai wani abokin Sayyid Mustafa wato babban dan Imam Khumaini ya baqunci Mustafan to da daddare sai yana jin kuka, sai ya tada Mustafa daga barci cewa yana jin kuka daga cikin gida ko zai je ya duba ko wani abune ya faru, Sayyid Mustafa ya dan kasa kunne ya ji sai yace masa babansa ne yake sallar Tahajjud yake kukan, wanda yake nuna cewa ya saba in yana sallar yakan yi kuka., wanda shima wannan wani darasi ne garemu wato idan muna wasu ibadodi misali sallah ko karatun Alqur’ani ko biya Addu’oi mu ga cewa muna kuka ya yin aikata su. Akwai lokacin da na taba jin Sayyid Zakzaky [H] yana bayani cewa zuwansa Iran na farko a 1980, da suka kai ziyara gidan Imam Khumaini sai ya kebance da daya daga cikin wadanda suke yi ma Imam Khumaini Hidima, to daga cikin tambayoyin da ya yi masa akwai dangane da ibadodin Imam Khumaini, sai Hadimin yake ce masa Imam Khumaini ya kasance qarfe biyu na dare yake ta shi sallar Tahajjud dinsa kowane dare, to tun daga lokacin Sayyid Zakzaky ya sunnata ma kansa ta shi wannan lokaci kuma alhamdu lillahi ya tarbiyyatar da ‘yan uwa akan haka, ‘yan uwa da suka kwashe sama da shekaru 30 a wannan Harka za su iya ba da shaida akan haka cewa qarfe biyu na dare ake ta da ‘yan uwa sallar Tahajjud a lokacin Ijtima. A taqaice dai Sallar Tahajjud tana da falaloli da kuma fa’idodi masu yawa a duniyar mutum da kuma lahirarsa kamar yadda Sayyid Tabataba’i wato marubucin Tafsirin Almizan yaka cewa lokacin da ya tafi karatun Hauza a birnin Najaf, bayan da suka haduda babban Malami kuma shugaban Arifai na wannan zamani saboda kusan duk Malaman da suka yi fice a fagen ilimin Irfan da Aklaq to shi ya karantar dasu kamar su Ayatullah Bahjati da sauransu, to abinda shi wannan Malami mai suna Ayatullahi Sayyid Qhadi ya ce ma Sayyid Tabataba’i, “Idan kana neman Duniya to ka lizimci Sallar Dare haka nan in kana neman Lahira to ka lizimci Sallar Dare.” Daga qarshe ina roqon Allah Ta’ala ya amshi ibadodinmu da kuma Addu’oinmu ya kuma sakamu cikin ajin bayinsa wadanda zasu fita cikin wannan wata na Ramadan da certificate na Taqwa.
|