Saturday, 02 December 2023
Email
Make My Homepage
RSS
Register
Shahadar Imam Musa Al-Kazim (AS) Print E-mail
Written by administrator   
Tuesday, 09 March 2021 12:15

Kasantuwar wannan wata da muke ciki na Rajab, a cikinsa ne Shahadar Imam Kazim (AS) ya rasu ne ranar Jumma’a 25 ga watan Rajab shekara ta 183 bayan Hijira. Ya yi shahada ne a Kurkuku sakamakon guba da aka sa masa a zamanin Harunar Rashid. Imam Kazim (AS) ya yi zamani da Halifofin Abbasawa guda hudu sune:

1-Mansur.

2-Muhammad Mahdi.

3- Musal Hadi.

4-Harunar Rashid.

Haka yawancin sunayensu wato na Halifofin Abbasawa yake, sunaye da laqubba masu kyau amma ayyukansu marasa kyau, saboda in mutum ya bibiyi tarihi zai ga cewa cikin wadannan Halifofin na su guda hudu daga ciki wato Mahdi, Hadi da Rashid ba wanda bai kama Imam Kazim ba ya sa shi a kurkuku amma wanda yafi gallazawa da cutarwa ga Imam Kazim shi ne Harunar Rashid daga qarshe da ya ga cewa dukkan cutarwa da gallazawa ga Imam Kazim bai haifar da natijar da yake so ba shi ne yaba da umarni da a sa masa guba. Yanzu zamu bi wadannan Halifofi daya bayan daya mu ga irin cutarwa da gallazawa da kowanansu ya yi ga Ahlul bayt da kuma mabiyansu a zamaninsu.

1-Mansur duk da tarihi bai nuna cewa ya kama Imam Kazim ba amma tarihi ya nuna ya sa masa ido sosai ta hanyar ‘yan leqen asiri kuma a lokacin sa ya kama da yawa daga cikin mabiya Ahlul bayt ya kwace masu dukiyoyin su yasa su a kurkuku wasunsu ma cikin Kurkun suka rasu saboda azabtarwa domin ba ci ba sha haka ake barinsu har mutum ya rasu.

2-Muhammad Mahdi shi dan Mansur ne, da yake mulkin na su na gado ne wato wannan ya yi ya gadar ma wannan, wani lokaci ma har wasiyya suke barma junansu cewa in wannan ya hau mulkin in ya mutu sai wane ya hau. Bayan hawan shi Mahadin karagar mulki sai yasa a kama Imam Kazim daga Madina a kawo shi Bagdad a lokacin ita ce cibiyar zartar da Mulki na Abbasawa, da aka kawo shi Bagdad ya sa a wuce dashi zuwa Kurkuku, wata rana sai shi Halifan ya yi mafarki da ya firgitar da shi, a kan a sasin haka yasa a saki Imam Kazim ya koma Madina.

3-Musal Hadi: A zamanin wannan Halifa na Abbasawa abubuwa da yawa na baqin ciki da ta da hankali sun faru ga Ahlul bayt da kuma mabiyansu, daga cikin abubuwan da suka faru akwai wata waqi’a mai suna”WAQI’AR FAKKU” Fakku sunan waje ne kusa da Makka, ya zo a tarihi cewa tun bayan waqi’ar Karbala ba a yi wata waqi’a da aka zubar da jinin zuriyyar Manzon Allah (SAAW) da mabiya Ahlul bayt kamar wannan waqi’a ta Fakku, kuma Manzon Allah kamar yadda ya ba da labarin aukuwar waqi’ar Karbala to haka ya ba da labarin aukuwar wannan waqi’a ta Fakku ga Sahabbansa ga ruwayar, “Wata rana Manzon Allah ya bi yo ta wajen da ake ce ma Fakku sai ya sauka a wajen ya yi Sallah raka’a biyu, lokacin da ya ke raka’a ta biyu sai yai kuka, lokacin da sahabbai suka ka ga Manzon Allah na kuka su ma sai suka yi kuka, lokacin da ya sallema sallah sai ya tambaye su mi ya sa ku kuka? Sai suka ce lokacin da muka ga kana kuka shine mu ma muke kukan. Sai Manzon Allah ya ce masu, Mala’ika Jibrilu ne ya sauka gare ni lokacin da ni ke raka’a ta farko ya ce, Ya Muhammad wani Bawan Allah daga cikin zuriyyar ka za a kashe shi a wannan wajen. Haka nan Imam Sadiq (AS) Shima wata rana tafiya zuwa aikin Hajji ta biyo da shi ta wannan waje, da ya zo wajen sai ya sauka daga kan dabbarsa yai sallah. Wanda su ke tafiyar tare da shi ya tambaya wannan yana daga cikin ayyukan Hajji ne? Ya ce A‘a ba ya daga ciki, sai dai a dai dai wannan waje za a kashe wani daga cikin Zuriyyar Ahlu bayt. Wannan waqi’a ta faru ne sakamakon gallazawa da cutarwa da shi wannan Halifa na Abbasawa yake yi ga Ahlul bayt da kuma mabiyansu to sai wani Bawan Allah daga cikin jikokkin Imam Hassan (AS) ya hada runduna ta mayaqa domin fuskantar wannan zaluncin da a ke yi. Shi kuma Halifa na Abbasawa da ya samu labari sai ya turo da runduna ta mayaqa domin su zo su yaqi wadannan bayin Allah to a wannan waje na Fakku yaqin ya gudana, an samu shahidai da yawa daga cikin mabiya Ahlul bayt a wata ruwaya an samu shuhada’u sama da dari daga cikin shahidai har dashi wanda ya jagoranci wadannan bayin Allah sunan sa shine Husain dan Ali dan Hassan dan Hassan dan Hassan dan Ali ibn Abi dalib, in muka dubi nasabarsa zamu ga akwai kakanni biyu tsakaninsa da Imam Hassan wato dai nasabarsa tana tuqewa ga Imam Hassan ne. Bayan wadannan shahidai akwai kuma wadanda aka kama a matsayin ribatattun yaqi aka kwashe aka wuce dasu Bagdad a gun shi halifan Abbasawa yai masu isgili kala-kala da cin mutunci daga qarshe yasa a je dukkansu a fille masu kai. To lokacin da wannan waqi’a ta faru Imam Kazim yana Madina ne, bayan aukuwar waqi’ar sai shi wannan Halifa na Abbasawa ya dora alhakin abin baki daya ga Imam Kazim cewa shi yasa a yi masa bore saboda haka sai ya ba da umarni da a kama shi a kawo shi Bagdad da nufin sa shi a Kurkuku, a lokacin ne Imam Kazim ya yi Addu’ar Jaushanan Sagir, Asalin Addu’ar dama daga wajen sa aka ruwaito, A taqaice dai bayan da Imam Kazim yai wannan Addu’ar shi wannan Halifa na Abbasawa ko mako guda bai yi ba ya mutu. Ga mai buqatar ganin bayanin wannan waqi’a ta Fakku yana iya duba littafi mai suna, ‘Siratur Rasullullahi wa’ahlu baitihi’ Juz’i na biyu. Bayan mutuwar shi wannan Halifa sai aka saki Imam Kazim ya dawo Madina.

4-Harunar Rashid: Kamar sauran Halifofin Abbasawa da suka gabace shi na cutarwa ga Imam Kazim (AS) Shi ma ya dauki matakan cutarwa gare shi har da ma qarin akan abunda magabatanta suka yi domin shi ya bullo ta hagu da dama saboda ya cimma manufarsa abun bai yi yu ba daga qarshe ya kashe Imam Kazim ta hanyar ba da umarnin a sa masa guba. Da farko wani tambihi anan shine mafi yawan zaman Kurkuku da Imam Kazim ya yi, ya yi shi ne a zamanin shi Harunar Rashid a wata ruwaya ta nuna ya kwashe shekaru 17 a kurkuku a lokacinsa, kuma ya zauna kurkuku dabam dabam har guda hudu a zamanin shi Harunar Rashid, wani abin mamaki duk kurkukun da yasa aka canza masa yana ba da umarnin da a gallaza masa, sai dai yawancin shugabannin kurkukun ba su aiwatar da umarnin na sa saboda yadda suka yi mu’amala da Imam Kazim da kuma karamomin da suka gani gare shi. Akwai ma Kurkun da ya zauna sai ya kasance shugaban Kurkukun ba wai cutarwa ba kyautatawa ma ya dunga yi ma Imam Kazim da labari ya samu Harunar Rashid sai ya sa wani ya je ya duba masa wane hali Imam Kazin yake ciki mummuna ne ko kyakkyawa, aka dawo aka fada masa cewa yana cikin kyakkyawan hali ne, to shine ya sa a kira masa shugaban Kurkukun yasa a yi masa tsirara haihuwar uwarsa kamar yadda Hausawa suke cewa bayan haka ya sa a ka yi masa bulala 100 a wata ruwaya bulala 120 bayan haka a ka canza shi da wani mai suna Sindiy dan Shahik, da shi ya yi amfani wajen sa ma Imam Kazim guba. Da Harunar Rashid ya ga ya dauki matakai dabam dabam na cutarwa bai yi ba sai ya bullo ta dama yai wata wauta, abinda ya yi shi ne ya samu wata budurwa kyakkyawa ya aikata kurkuku wai ta zauna tare da Imam Kazim ta na yi masa hidima, da aka kai ta Imam Kazim ya ce bai da buqata.

Labari ya koma wajen Harunar Rashid cewa ba a buqata to shine ya fusata ya ce a koma a ce masa ai ba da yardar sa muka kama shi ba muka tsare, saboda haka ba mu neman yardar sa ba ne dole ya bar ta, shi ke nan bayan kwana biyu yasa a je a duba ta, ko da dan saqon ya je sai ya samu tana sallah ta yi sujuda, a cikin sujudar ya ji tana cewa ‘Subbuhun {uddusun’ ta na ta maimaitawa, shine aka dawo aka fada masa cewa ai budurwa ta zama Abida kawai, sai Harunar Rashid ya ce ya sihirce ta kawai. To shine Harunar Rashid ya tattauna da makusantansa ya ce masu duk matakan da zai dauka na hagu da dama ba su yi aiki ba yanzu minene abin yi? Sai wani Ya ce shi yana ganin ya aika wani ya cusa mai ra’ayin cewa ya nemi Afuwa, shi kuma sai yai masa afuwa wato dai hukuma ta tafi da izza ba zilla ba. A ka zo aka samu Imam Kazim aka ce masa yanzu da wannan yana yi na qunci da ka ke ciki mi zai hana ka nemi afuwa ga Halifa-alhali shine Khalifa na Haqiqa- domin ya sake ka. Sai Imam Kazim ya ce masa bai da buqatar yin haka. Aka koma aka shaida ma Harunar Rashid sai ya dada fusata to shine ya ba da umarni daga qarshe a sa masa guba ta hannun shi shugaban kurkukun Sindiy, wato ruwayar ta nuna cewa shi Bayahude ne a jini ba wai kawai a aiki ba, saboda ya cutar da Imam Kazim sosai kuma da al’amarin sa gubar ya zo shi ya aiwatar. Ga mai buqatar qarin bayani sosai ya na iya komawa ga littafin da a ka ambata a sama.

Daga qarshe akwai darussa masu yawa da zamu darastu da su na zaman Imam Kazim a Kurkuku wato yadda dan uwa ko ‘yar uwa ya kamata a kasance a cikin kurkuku. Da farko Imaman Ahlul bait da suka yi zaman kurkuku guda hudu ne wato wadanda azzaluman zamaninsu suka kama suka sa a kurkuku sune:

1-Imam Baqir (AS).

2-Imam Kazim (AS).

3-Imam Hadi (AS).

4-Imam Askari (AS)

Amma wanda yafi dadewa a cikin kurkukun shine Imam Kazim kusan ya shafe shekaru ashirin a ciki daga qarshe ma a cikin kurkukun ya yi shahada.Ya zo a tarihin Imam Kazim cewa,lokacin da yake cikin kurkuku dare da rana ya shagaltu da ibadodi ne,har ma yana godiya ga Allah Ta’ala kan wannan ni’ima da yai masa wato ta shagaltuwa ga ibada ga Allah Ta’ala.Akwai kurkukun da ya zauna daya daga cikin maaikatan kurkukun sai ya jishi yana addu’a yana cewa, “Ya Allah ka sani ina roqonka ka bani faraga domin ibada gareka,ga shi ka bani,to ina godiya gareka.” Ya zo a tarihin sa cewa kowace rana ya kasance idan rana ta keto zai yi sujuda mai tsawo ba zai dago kai ba har sai rana ta yi zawal.

Akwai lokacin Harunar rashid ya kan leqo ta benan gidansa sai yake tambayar shugaban kurkukun wai wancan wane tufafi ne nike gani kullum a wajen? Sai ya ce masa ba tufafi ba ne Musa dan Ja’afar kowace rana haka yake wannan sujuda tun daga ketowar rana har ya zuwa zawal. Haka nan ya zo a tarihinsa cewa ko wace rana ya Kasance yana Istigfari dubu biyar. To mu duba mu gani Ma’asumi yana istigfaru 5000 kowace rana to ina ga wanda ba Ma’asumi ba. Istigfari akwai na Awwam, akwai na kusus wato zababbun bayin Allah, akwai na kususul kusus wato zabun zababbun bayin Allah. Na Awwam shine istigfari daga zunubai. Na Kusus shine Istigfari daga gafala. Na Kususul kusus shine Istigfari daga taqaitawa wajen bautar Allah wato su bayin Allah duk yadda suka kai ga ibada ga Allah to suna ganin sun taqaita saboda haka suna neman gafarar Allah kan wannan taqaitawa qila wannan shine istigfari na Imam Kazim amma ba wai na zunubi bane. A taqaice dai ya zo a tarihin Imam Kazim cewa a cikin kurkuku ya kasance kowace rana Azumi yake yi, haka nan kowane dare yana raya shi da ibadodi ne wato Salloli, karatun Alqur’ani, Azkar da dai sauransu. Saboda haka yana gayar muhimmanci duk lokacin da dan uwa ya samu kansa a kurkuku ya yi amfani da fursar da ya samu wajen shagaltuwa da wadannan ayyuka:

1-Ibada.

2-Haddar Alqur’ani, in bai hardace ba in kuma ya hardace to ya dada gyara haddarsa wadda ta zube sai ya dada kokkwafa ta.

3-Tafakkur, lokacin da mutum yake kurkuku yana da lokaci na yin tunani ta fuskoki dabam dabam alal misali tunani dangane rayuwarsa da kuma ni’imomin da Allah Ta’ala yai masa, tunani dangane halittun Allah Ta’ala, tunani dangane da mutuwa da matakan da suke bayan mutuwa kamar qabari, tashin qiyama, hisabi, Wuta, Aljanna da dai sauransu.

4-Karatu: Kurkuku waje ne da mutum zai samu damar yin karatu ko karance-karance na littafai masu yawa fiye da a waje.

5-Rubuta littaffai: Idan mutum ya bibiyi tarihin wasu bayin Allah zai ga da yawa sun yi amfani da zamansu na kurkuku wajen rubuta littafai alal misali littafin Tafsiri mai suna Al’asas fi Tafsi na Sa’idul Hawa wato marubucin Jundullah a cikin kurkuku ya rubuta shi a taqaice in mutum ya bibiyi tarihin bayin Allah da suka bi layin gwagwarmaya zai ga cewa yawancin littafan da suka rubuta sun rubuta sune a kurkuku saboda haka zaman kurkuku idan mutum ya natsu to fursa ce Zahabiyya gareshi saboda wadannan ababen da aka ambata mutum na da damar yinsu a kurkuku fiye da a waje. Muna da kyakkyawa misali daga Malaminmu kuma jagoranmu wato Sayyid Zakzaky (H) duk wadanda suka zauna dashi a kurkuku zasu bada shaidar yawan ibada da yake yi a kurkukun, kai ni wani lokaci ko ‘yar kasala naji wajen ibada da zaran na tuna da Malam cewa ga halin da yake cikin na rashin lafiya amma bai hana shi ibadodi ba, sai in ji kasalar ta gushe. Allah Ta’ala ya qara ba su Malam lafiya ya kuma basu faraj daga wajensa.

 
Home Maudu'oi daban-daban Shahadar Imam Musa Al-Kazim (AS)
Copyright © 2023. www.tambihin.net. Designed by KH