Tuesday, 09 August 2022
Email
Make My Homepage
RSS
Register
Tarihin Sayyida Khadija (AS) Print E-mail
Written by administrator   
Tuesday, 09 March 2021 11:56

Kasantuwar wannan wata da mu ke ciki na Rajab a wata ruwaya da ta fi shahara a cikinsa ne rasuwar Sayyida Khajidatul Kubra (AS) Saboda ya zo a tarihi cewa tsakanin rasuwar ta da Abu dalib kwana ukku ne, shi kuma ya rasu a 26 ga watan Rajab shekara ukku gabanin Hijira wato shekaru 10 da aiko saqo ga Manzon Allah (SAAW). To zai zama ke nan ta yi wafati ranar 29 ga watan Rajab, ta yi yu mutum ya ga ruwayoyin da suka saba ma haka amma dai wannan shine wanda Malaman tarihi suka tabbatar. Rubutu ko bayani dangane Sayyida Khadija fage ne mai fadin gaske, akwai malamai ma da suka rubuta littafi dangane da Tarihinta da kuma rayuwarta alal misali akwai littafi da wani Malami ya rubuta dangane da Tarihinta mai su na, ‘Assayyidatu khadijatul Kubraa Ummil Mu’uminin.’ Akwai kuma wanda shima wani Malami ya rubuta mai suna, ‘Khadijatul Kubraa’ Da dai wasu daga cikin Malamai da suka yi rubutu dangane da ita, a nan insha Allah za’a kawo wasu bangarori na rayuwar ta ne da aka rairayo daga cikin littafai:

1-Haihuwarta.

2-Darajojinta.

3-Aurenta.

4-Dabi’ointa.

5-Wafatinta.

1-HAIHUWARTA: An haifi Sayyida Khadija a Makka, Shekara 15 gabanin shekarar giwa. Rayuwar ta baki daya a Makka ta yi su wato a nan aka haife ta a nan ta rayu, a nan ta rasu, yanzu haka qabarinta yana Makka ne.

2-DARAJOJINTA: Ko da ma a ce babu wasu Hadisai da suka zo da bayani kan darajojinta to kasantuwar ta matar farko ga fiyayyen halitta kuma mahaifiya ga shugabar mata baki daya to wannan ya isa ya zama daraja babba gare ta, ga ta kuma ita ce farkon wadda ta amshi saqon da Manzon Allah ya zo da shi wato farkon wadda ta musulunta a cikin mataye baki daya. Ga wasu Hadisai dangane darajojinta.

1-Ya zo a cikin Sahih Muslim daga Abi Huraira yana cewa Manzon Allah (SAAW) ya ce, “Mala’ika Jibril (AS) ya zo man, ya ce: ‘Ya Manzon Allah, ga Khadija nan ta zo maka, tare da ita akwai kwano wanda a cikinsa akwai abinci. To idan ta zo maka ka karanta gare ta daga wajen Ubangijinta kuma har da ni ma ina yi mata sallama, sa’annan ka yi mata albishir da gida a Aljanna na zinariya. To mu dubi irin wadannan darajoji a ce mutum ya kai matsayin da Allah Ta’ala ne ya aiko cewa yana gaida shi, haka nan ma Mala’ika Jibril yana gai da shi bayan haka kuma aka mata albishir da Aljanna. Wani tambihi a nan shine mutum ya binciki Hadisin da aka ruwaito cewa Sahabbai 10 da aka yi masu albishir da Aljanna ya ga ko tana ciki, kai bama ita ba, ya ga ko zai ga shugabannin samarin Aljanna cikin sunayen wato Imam Hassan (AS) da Imam Husain (AS). Da kuma na mahaifiyarsu, al-hali kuma a Hadisai kasantuwar cewa su ‘yan Aljanna ne yana cikin littafan Ahlus sunna, wannan ya nuna lalle wasu abubuwa sun auku a tarihin wannan al’umma. Akwai Hadisai da yawa da aka ruwaito kan darajojinta amma saboda gudun tsawaitawa za mu wadatu da wannan.

3-AURENTA: Akwai tambayoyi masu yawa da kuma muhimmanci dangane da auren Sayyida Khadija ga wasu daga ciki:

1-Me yasa Sayyida Khadija ta Auri Manzon Allah (SAAW)

2-Shekarunta nawa a duniya lokacin da ta auri Manzon Allah?

3-Sayyida Khadija ta taba auren wani gabanin Manzon Allah?

4-‘Ya’yan ta na wa tare da Manzon Allah?

5-Shin Manzon Allah ya ha]a ta da wata wato ya yi mata kishiya?

1-Me yasa Sayyida Khadija ta Auri Manzon Allah? Dalilin yin wannan tambaya shine akwai masu kudi da Mulki da suka so su aure ta amma taqi daga qarshe ta auri Annabin Allah, tarihi ya nuna hatta Abu Jahal da Abu Sufyan sun so su aure ta amma ba ta yarda ba, amsa a nan ita ce wannan yana nuna gayar kamala na Sayyida Khadija kuma abin duniya bai tsone mata ido ba, ta wata fuska kuma mutum zai iya cewa Sayyida Khadija ajiya ce ko tanadi da Allah Ta’ala ya yi ma Manzon Allah, mu dubi lokacin da saqo ya zo ga Manzon Allah nan take ta yi Imani da saqon da ya zo dashi kuma dukiyar ta baki daya ta sadaukar domin tafi da wannan saqo, haka nan duk wahalhalun da aka fuskanta a Makka tare da ita aka fuskanta, wannan ka dai ya isa ya nuna maka wace ce Khadija da kuma matsayinta. Akwai ma wani mutum attajiri, mai suna Afif al-Kindi wata rana ya zo Makka sai ya ga wani mutum ya tsaya ta wajen Ka’aba yana sallah. Sa’annan sai wata mata ta fito tana sallah tare da shi. Sa’annan sai wani yaro ya fito ya tsaya kusa da shi yana sallar. Sai wannan baqon ya tambayi Abbas su waye wadannan kuma wane addini ne haka? Sai Abbas ya ce, “Wannan Muhammad dan Abdullahi ne. Ya riya cewa Allah ya aiko shi. Wannan kuma matarsa ce Khadija ta yi Imani da shi. Wannan yaron kuma Ali dan Abi dalib ne ya yi Imani da shi. Na rantse da Allah ban san wani ba a doron qasa akan wannan addini ban da wadannan ukkun.” Wani dalin kuma da yasa ta auri Manzon Allah shine tasirantuwar da ta yi na labarurruka dabam dabam da ta ji na Manzon Allah musamman ma tafiyar da mai kula mata da dukiya wato Maisara su ka yi da Manzon Allah na irin kyawawan dabi’u da ya gani na gaskiya da riqon amana da ma wasu Mu’ujizozi da ya gani a tafiyar da Manzon Allah alal misali yadda in suna tafiya giragizai suna yi masa inuwa to da ya dawo duk ya ba Sayyida Khadija labari, sai ta ji kawai tana son Manzon Allah da dai sauran dalilai.

2-Shekarunta nawa a duniya lokacin da ta auri Manzon Allah? Akwai sabani mai yawa akan haka tsakanin Sunna da Shi’a. Wadansu sun ce tana da shekaru 25, wasu kuma 28, wasu kuma 40 shi yafi shahara a Ahlus sunna.

3-Shin Sayyida Khadija ta taba auren wani gabanin Manzon Allah? Ita ma wannan mas’ala ce da aka samu sabani akai tsakanin Sunna da Shi’a. Shi’a sun tafi akan cewa ba ta taba auren wani ba gabanin Manzon Allah. Sunna sun tafi akan cewa ta yi aure gabanin Manzon Allah, ga mai buqatar bincike a kai yana iya komawa ga littafan da aka ambata zai ga hujjojin kowa.

4-‘Ya yan ta nawa tare da Manzon Allah? Shima wannan akwai sabani akai wanda yafi shahara shine ‘ya’ya bakwai maza ukku mata hudu, shima in mutum yayi bahasi akai mutum zai ga akasin haka musamman ma na ‘ya’ya matan wato Zainab, Ummu khulsum,, Ruqayya, wasu Malamai sun tafi akan cewa su ‘ya’yan ‘yar uwar Khadija ne mai suna Hala. A taqaice ‘ya’yan Manzon Allah dukkansu daga Khadija ne in ban da Ibrahim shi dan Mariya ne, shi kuma a Madina aka haife shi sauran ‘ya’yan duka a Makka aka haife su.

5-Shin Manzon Allah ya hada ta da wata? Amsa, tarihi ya tabbattar da cewa Manzon Allah bai hada ta da kowa ba wato duk sauran matayen Manzon Allah ya Aure sune bayan Rasuwar Khadija, shi wannan kusan babu wani sabani a kai, wato dai kamar shigen yadda Imam Ali bai haba wata mata da Sayyida Zahra ba sai bayan rasuwarta ya auri mataye har hudu.

4-DABI’OINTA: Sayyida Khadija ta kasance saboda tsarkakuwa daga munanan dabi’u da kuma siffatuwar ta da kyawawan dabi’u ko a lokacin Jahiliyya mutane DAHIRA suke ce ma ta. Idan mutum ya bibiyi tarihin Sayyida Khadija zai ga cewa ta kasance mai kyawawan dabi’u ta kowace fuska musamman ta fuskacin Tawadi’u, kyauta da kuma sadaukar da dukiya a tafarkin Allah Ta’ala, Manzon Allah ya yi ma ta shaida akan haka, alal misali Aisha ta ce: “ Manzon Allah ya kasance kusan baya fita daga gida sai ya ambaci Khadija kuma ya yi yabo gare ta. To sai ya ambace ta wata rana daga cikin ranaku sai kishi ya kama ni, sai na ce: Ta kasance wani abu ne face tsohuwa kuma Allah ya canza maka wadda ta fi ta? Sai yai fushi sosai. Manzon Allah ya ce, “A’a wallahi Allah bai canza man ba wadda ta fita. Ta yi Imani da ni lokacin da mutane suka kafirce, kuma ta gasgata ni alhali mutane sun qaryata ni, kuma ta bani dukiyar ta lokacin da mutane suka hana ni, kuma Allah ya azurta ni da ‘ya’ya daga gare ta lokacin da ya hana ni daga wasu! Aisha ta ce: Sai na ce a raina: Ba zan sake ambatonta da mummuna ba har abada”. Wannan Hadisi Buhari da Muslim duk sun ruwaito shi. Kuma Hadisin ya nuna cewa a dukkan matayen Manzon Allah Sayyida Khadija ta fisu kamala ta kowace fuska saboda fadin Manzon Allah, Allah bai canza man ba wadda ta fita.

Haka nan Sayyida Khadija ta kasance mai haquri da dauriya alal misali lokacin da ta Auri Manzon Allah Matan quraishawa da yawansu sun ba ta baya wato sun de na mu’amala da ita amma haka ta yi haquri ta daure har ta koma ga Allah Ta’ala, kuma dukkan wahalhalun da Manzon Allah ya sha a Makka lokacin da ya fara Da’awa da ita aka sha, alal misali tsare su Manzon Allah da aka yi tare da wadanda suka yi Imani da shi na tsawon shekaru ukku, aka hana sayar masu da komai da kuma mu’amala da su har sai da ta kai abinci ya yenke masu, suka dawo suna cin ciyayi to duk da Sayyida Khadija aka fuskanci wadannan matsalloiln. Da dai sauran wasu dabi’ointa masu girma.

5-WAFATINTA: Sayyida Khadija ta rasu ne qarshen watan Rajab shekaru ukku gabanin Hijira. Da za ta rasu ta bar ma Manzon Allah wasiyyoyi guda ukku su ne:

1-Ta roqi Manzon Allah da ya yi mata Afuwa saboda ta na ganin ta taqaita wajen yi masa hidima da kuma tsayuwa da Haqqinsa, nan take Manzon Allah ya ya ba mata na ayyukan alhairi da ta yi da kuma gudunmawa da ta baiwa wannan Addini da kuma Addu’ar Allah ya saka mata da alhairi.

2-Wasiyya ta biyu shine ta nu na ‘yarta Sayyida Fadima cewa ka da wani ko wasu su cutar da ita a bayanta.

3-Wasiyya ta ukku ta ce ma Manzon Allah tana jin kunyar fadi amma za ta fada ma Fadima za ta fada masa, shine Manzon Allah ya tashi ya fita daga cikin dakin shine Sayyida Khadija ta ce ma’yarta Sayyida Fadima, ‘Ki fada ma mahaifinki cewa ina jin tsoron qabari saboda haka in na rasu ina so ya ba ni tufafinsa da ya ke sawa idan za a yi masa wahayi, ya kasance likkafani na, Sayyida Fadima ta zo ta fada ma Manzon Allah saqon, nan take ya dauki tufafin ya ba ta ta kai mata, Sayyida Khadija tai farin ciki sosai. Bayan da Khadija ta rasu sai Manzon Allah yai mata wanka na gawa to lokacin da ya zo zai sa mata likkafanin sai ga Mala’ika Jibril ya sauko ya ce masa, “Allah Ta’ala ya ce in fada maka cewa likkafanin Khadija a wajen mu ya ke saboda ta ba da dukiyarta baki daya a tafarkinmu sai ya bashi likkafani da ya zo da shi daga Aljanna.” Saboda haka Sayyida Khadija likkafani biyu a ka yi mata daya na Manzon Allah, daya kuma daga wajen Allah Ta’ala. Amincin Allah ya tabbata a gareki a ranar da aka haife ki da kuma ranar da kika rasu da kuma ranar da za’a tada ke.

 
Home Maudu'oi daban-daban Tarihin Sayyida Khadija (AS)
Copyright © 2022. www.tambihin.net. Designed by KH