Wednesday, 24 April 2024
Email
Make My Homepage
RSS
Register
Ibadodin Daren Jumma’a da Ranar Jumma’a Print E-mail
Written by administrator   
Tuesday, 09 March 2021 11:14

Kasantuwar ranar Jumma’a tana matsayin shugaba a ranakun mako kamar yadda ya zo a ruwaya kuma idan mutum ya yi bincike a littafan Addu’oi kamar su littafin Mafatihul jinan, Misbahul Mutahajjid, Jamalul Usbu’i na Sayyid ibn Dawus da dai sauransu zai ga ayyuka na ibadodi masu yawa a daren Jumma’a da kuma ranar Jumma’a, saboda haka yana da gayar muhimmanci kowanenmu dan’uwa ko ‘yar’uwa mu ribaci wadannan muhimman lokuta masu albarka na dararen Jumma’a da kuma Ranakun Jumma’a domin fur sace babba garemu kuma ko bajima ko badade zata kubuce mana, mu yi tunanin wadanda suka rasu yau wannan dama ta kubuce masu. Insha Allah bayanai dai dai gwargwadon iko zasu gudana kan wadannan ababe:

1-Falalar daren Jumma’a.

2-Ibadodin daren Jumma’a.

3-Ibadodin ranar Jumma’a.

4-Ababen da suke Mustahabbai a ranar Jumma’a.

5-Ababen da suke Makuruhai a ranar Jumma’a.

1-FALALAR DARE DA KUMA RANAR JUMMA’A: Akwai Hadisai masu yawa da aka ruwaito daga Manzon Allah [SAAW] da kuma Aimma [AS] Dangane da falaloli na daren Jumma’a da kuma ranar Jumma’a ga wasu daga cikin Hadisai:

1-Manzon Allah [SAAW] Ya ce, “Daren Jumma’a da kuma Ranar Jumma’a sa’oi 24 ne, Allah Ta’ala a cikin kowace sa’a yana ‘yanta bayinsa dubu dari shidda daga Wuta.”

2-Imam Sadiq [AS] Ya ce, “Duk wanda ya rasu tsakanin zawal na ranar Alhamis zuwa zawal na ranar Jumma’a to Allah zai tsare shi daga azabar qabari.”

3-Har wala yau daga Imam Sadiq [AS] Ya ce, “Lalle Jumma’a tana da wani Haqqi, kashedinka ka tozarta wannan haqqi ko kuma ka taqaita ga wani abu na ibadar Allah Ta’ala da kuma kusanci gareshi da ayyuka kyawawa da kuma barin dukkan abubuwan da aka haramta domin Allah yana nunnuka lada a ciki yana kuma goge zunubai da kuma daukaka darajoji a cikinsu, ranar Jumma’a kamar darensa ne-wato a daraja da daren da ranar duk daya suke- Saboda haka in kana da ikon raya daren da Salloli da kuma Addu’oi to ka yi. Allah madaukaki yana aiko da Mala’iku zuwa saman Duniya domin su nunnuka kyawawan ayyuka a ciki su goge munanan ayyuka, Allah Ta’ala mai yelwatawa ne kuma mai karimci.” A cikin wannan Hadisi akwai darussa masu yawa a ciki daga ciki akwai cewa mutum ya kasance a duk daren Jumma’a da kuma ranar Jumma’a mutum ya dunga shu’uri a cikin ran sa na alfarma da daraja da wadannan lokuta suke dashi, bayan haka kuma in mutum zai iya a duk daren Jumma’a ya raya shi da ibadodi, in ba zai iya ba ya raya rabin daren ko kuma aqalla daya bisa ukku na daren, a taqaice ya kasance Tahajjud da mutum ya saba yi kowane dare to ta daren Jumma’a ta zamo ta musamman wajen qarin lokaci misali mutum ya saba tashi qarfe biyu na dare to a daren Jumma’a sai ya tashi qarfe daya ko sha biyu. Daga cikin darussan da ke cikin wannan Hadisi akwai nuna muhimmancin nisantar saba ma Allah Ta’ala a daren Jumma’a ko ranar Jumma’a saboda in mutum ya aikata wani sabo misali ya yi qarya ko ya yi giba da sauransu to za a nunnuka masa zunubi ne saboda darajar dake cikinsu. Imam Baqir [AS] Ya ce, “Allah Ta’ala yana umartar Mala’ika da ya yi kira a kowane daren Jumma’a tun daga farkon daren har ya zuwa qarshen sa da cewa: Shin akwai wani bawa da zai  roqeni kan wani abu na lahira ko na Duniya gabanin ketowar alfijir in karba masa? Shin akwai wani bawa da zai tuba zuwa gareni gabanin ketowar alfijir in amshi tubarsa? Shin akwai wani bawa da yake cikin qunci na rayuwa ya roqeni gabanin ketowar alfijir in yelwata masa? Shin akwai wani bawa Mumini da bai da lafiya ya roqeni in bashi lafiya gabanin ketowar alfijir in bashi lafiyar? Shin akwai wani bawa Mumini da yake cikin damuwa ko aka tsare shi ya roqeni in sake shi daga tsarin da aka yi masa gabanin ketowar alfijir in sake shi? Shin akwai wani bawa Mumini wanda aka zalunta da zai roqe ni in saka masa kan zaluntarsa da aka yi gabanin ketowar alfijir in taimake shi? Mala’ikan ba zai gushe ba yana kira kan buqatu dabam dabam har sai alfijir ya keto.” Wannan kadai ya isa ya nuna muhimmancin daren Jumma’a saboda haka bai kamata a ce mutum ya gafala ba, maimakon haka ya yi mujahada wajen ribatar daren ta fuskoki dabam dabam. Imam Ali [AS] Ya ce, “Allah ya zabi ranar Jumma’a babu wani da zai roqe shi da wata buqata fa ce ya biya masa. A wani Hadisi Manzon Allah [SAAW] Ya ce, “Ranar Jumma’a ita ce shugaban ranaku.” Imam Sadiq [AS] Ya ce, “Ku nisanci sabo a daren Jumma’a saboda zunubin ana nunnuka shi, duk wanda ya bar sabon Allah a daren Jumma’a to Allah zai gafarta masa dukkan zunubansa da ya aikata a baya. Duk wanda ya saba ma Allah a daren Jumma’a to Allah zai kama shi da duk zunuban da ya aikata a rayuwarsa kuma Allah zai nunka masa azaba saboda wannan sabo da ya yi a daren Jumma’a.” Wannan Hadisi yana da ban tsoro saboda haka yana da gayar muhimmaci ga wane dan uwa ko ‘yar’uwa a duk daren Jumma’a ko ranar Jumma’a mu yi iyakar iyawar mu ba wai Haramun ba a’a makruhi ma muga cewa ba mu aikata ba insha Allah. Hanya guda da za mubi kan haka shine kiyaye gabobinmu misali harshenmu, idanuwanmu, kunnuwanmu da dai sauran gabobi na Zahiri guda bakwai, haka nan kuma a badinance mu kiyaye zuciyarmu misali daga Riya, Ujub, Hassada ko kuma munana zato ga junanmu da dai sauran cututtuka na zuciya. Wadannan bayansu ya gudana a darussan Aklaq da aka yi a baya. Wannan kenan a taqaice dangane falalar dare da kuma ranar Jumma'a.

2-IBADODIN DAREN JUMMA’A: Akwai ibadodi masu yawa da aka ruwaito wadanda ake son aikatawa a daren Jumma’a ta fuskoki dabam dabam ga wasu daga ciki:

A-Salloli.

B-Karatun Alqur’ani.

C-Azkar.

D-Addu’oi.

E-Ziyara da dai sauransu.

A.Salloli: Akwai Salloli na Nafiloli masu yawa da aka ruwaito na daren Jumma’a, idan mutum ya duba cikin littafin Misbahul Mutahajjid na Shaikh Addusy a cikin fasalin da yake bayani kan ayyukan ibadodi na Mako, in mutum ya duba zai ga cewa a daren Jumma’a ya kawo Salloli na nafiloli dabam dabam in zai iya yin su duka Alhamdu lillah in ba zai iya ba to sai ya yi wasu daga ciki, in kuma haka bai samu ba to aqalla ko da guda daya daga cikin Sallolin mutum ya lizimta amfanin haka shine ko da a ce wani daren Jumma’a mutum bai da lafiya ko ya yi tafiya ko dai wani uzuri ya bijiro masa to za a rubuta masa ladar kamar yadda ya saba yi, amma idan ya kasance jefi-jefi yak e yi to duk ran da wani makamancin abun da aka ambata ya same shi misali rashin lafiya to fa bai da tabbacin samun ladar saboda ko da yana da lafiyar ba lalle ba ne ya yi. Ga nau’i ukku na wadannan Salloli:

1-Manzon Allah [SAAW] Ya ce, “Duk wanda ya yi Sallah a Daren Jumma’a Raka’a biyu kowace Raka’a bayan Fatiha ya karanta Iza zul 15 to Allah zai amintar da shi azabar qabari da kuma firgicin ranar qiyama.”

2-Manzon Allah [SAAW] Ya ce, “Duk wanda ya yi Sallah a daren Jumma’a Raka’a biyu bayan Fatiha kowace Raka’a ya karanta qulhuwallah 50 To Allah zai gafarta masa zunubansa da suka gabata da kuma na nan gaba. A qarshen Sallar ana son mutum ya ce, Allahumma Salli ala nnabiyyi al’arabiy.

3-Manzon Allah [SAAW] Ya ce, “Duk wanda ya yi Sallah Raka’a biyu kowace Raka’a bayan Fatiha ya karanta qulhuwallah 70 bayan ya yi sallama ya ce Astagfurullah 70 ita wannan Sallah tana da falala mai yawa. Wadannan misalan wasu daga cikin Sallolin kenan, kasantuwar za su fi sauqin aikatawa shi yasa na kawo su amma akwai masu qulhullah qafa 1000.

B-Karatun Alqur’ani: Da farko Sallolin na wajibi na daren Jumma’a da kuma Ranar Jumma’a akwai Surorin da ya zo a ruwaya ana son karanta su, A Sallar Magarib na daren kowace Jumma’a ana son a Raka’ar farko bayan fatiha ya karanta Suratu Jumma’a, a raka’a ta biyu bayan Fatiha ya karanta qulhuwallah. A Sallar Isha’i a Raka’ar farko bayan Fatiha Suratu Jumma’a, a raka’a ta biyu bayan Fatiha ya katanta suratul A’ala wato Sabbi. A ranar Jumma’a a sallar Asuba Raka’a ta farko bayan Fatiha Suratu Jumma’a, a raka’a ta biyu kuma bayan Fatiha qulhuwallahu. A Sallar Jumma’a ko Zuhur a raka’ar farko bayan fatiha suratu Jumma’a, a Raka’a ta biyu bayan Fatiha Suratul Munafiqun. A Sallar Asar bayan Fatiha suratu Jumma’a, a raka’a ta biyu kuma qulhuwallahu, idan mun lura za mu ga cewa a kwace Raka’a ta farko na wadannan salloi na farilla na daren Jumma’a da ranar Jumma ana karanranta Usabbihu ne, saboda haka yana da kyau mu kiyaye saboda mu samu ladar dabbaqa wannan Mustahabbi. Akwai wasu Surori na Alqur’ani da ake son karanta a duk daren Jumma’a, ga Surorin: Suratul Jumma’a. Suratul qamar. Suratu Dur, Suratu Ahqaf, Suratu Dhukan. Suratu Fussilat. Suratu Sad. Suratu Yasin. Suratu Sajada. Suratu qasas. Suratu Namli. Suratu Shu’ara’i. Suratu Isra’i. Suratu Khaha’fi. To in san samu dukkan wadannan Surori da aka ambata mutum ya karanta su kowane dare na Jumma’a, in kuma haka bai samu ba to wasu sashe da ga cikinsu saboda kowace tana da falala na musamman na karantata a daren saboda gudun tsawaitawa shi yasa ba a kawo wadannan falaloli ba.

C-Azkar: A daren Jumma’a ana son yawaita zikiri amma babban zikirin da aka son yawaitawa shine Salati ga Manzo da Alayensa in son samu ne kowane daren Jumma’a mutum ya yi aqalla guda dubu. An ruwaito daga Abi Abdullahi Ya ce, “Tun daga yammacin ranar Alhamis ya zuwa daren Jumma’a Mala’iku suna saukowa daga sama, suna tare da Alqaluma na Zinare da kuma takardu na Azurfa, basu rubuta komi tun daga lokacin har ya zuwa ranar Jumma’a da yamma face ladar masu Salati ga Manzon Allah.

D-Addu’oi: Akwai Addu’oi masu yawa da aka ruwaito daga Manzon Allah [SAAW] da kuma Aimma [AS] da ake son karantawa a daren Jumma’a, kasantuwar Addu’oin suna a sassa dabam dabam na littafan Addu’oi saboda haka sai da a ambaci sunayen littafan a duba a ciki ga wasu daga ciki: Misbahul Mutahajjid, Misbah na Shaikh Kaf’ami, Sahifatu Nabawiyya, Jamalul Usbu’i, Mafatihul Jinan da dai sauransu. In mutum ya duba su zai ga Addu’in dabam dabam in zai iya yin su duka haka ake so in kuma haka bai samu ba to sai ya yi abun da ya sauqaqa, in kuma duka basu samu ba to aqalla ka da mutum ya bar Du’au Khumail ko wane daren Jumma’a.

E-Ziyara: Akwai falala mai yawa na ziyaran Imam Husain [AS] Ko wane daren Jumma’a, in san samu ne mutum ya lizimci karanta Ziyarar Ashura a kowane dare na Jumma’a ko kuma wata Ziyara da ta sauqaqa ta Imam Husain [AS].

3- IBADODIN RANAR JUMMA’A: Ranar Jumma’a ita ma tana da ibadodi masu yawa kamar daren Jumma’a ga wasu daga ciki:

A-Salloli.

B-Karatun Alqur’ani.

C-Azkar.

D-Addu’oi.

E-Ziyara.

A-Salloli: Akwai Salloli masu yawa da aka ruwaito yawansu ma ya fi na daren Jumma’a, in mutum ya koma ga littafan da aka ambata zai ga wadannan Salloli. Amma akwai wata Sallah Raka’oi 20 wanda Imam Sajjad [AS] Yakan yi su gabanin Sallar Jumma’a, ana iya duba su cikin littafin Sahifatu Sajjadiyya akwai ma Addu’oin da ake karantawa bayan kowace Raka’a biyu har mutum ya kammala.

B-Karatun Alqur’ani: Akwai wasu Surori na Alqur’ani da ake son karantawa duk ranar Jumma’a sune: Suratu Ali-Imran. Suratun Nisa’i. Suratu Hud. Suratu Saffat. Suratur Rahman. In mutum zai iya yin su duka yana da falaloli masu yawa, ko kuma wasu daga ciki,in kuma duka ba zai iya ba to aqalla ya lizimci Suratur Rahman duk Jumma’a bayan Sallar Asuba.

C-Azkar: Ana so mutum ya yawaita Azkar a ranar Jumma’a musamman Salatin Manzo Allah da Alayensa shi ma aqalla sau dubu a duk ranar Jumma’a.

D-Addu’oi: Suma suna da yawa amma akwai wasu Addu’oin da bai kamata mutum ya bar suba daga ciki akwai Du’aun Nudba akwai Addu’ar zamanil gaiba akwai ta cikin littafin Mafatihu, Akwai kuma Du’au Simat ko Du’au Shabur wadannan addu’oi da aka ambata ana son yin sune da yamma wato gab da faduwar Rana, ya zo a ruwaya cewa Addu’a a lokacin karbabbiya ce, ya zo a tarihin Sayyida Zahra [AS] cewa ta kan lizimci Addu’oi a dai dai lokacin faduwar rana a duk Ranar Jumma’a. Da dai sauran Addu’oi ma’asurai da suka zo a littafai.

E-Ziyara: Babbar Ziyara a ranar Jumma’a ita ce ta Imam Mahdi [AF] Akwai ta cikin littafin Mafatihu yana da kyau mutum ya karanta ta a duk ranar Jumma’a, in kuma mutum zai iya sai ya biya dukkan Ziyarori da littafin Mafatihu ya kawo da suka shafi Sahibuz zaman wato daga ziyarar Ali Yasin har ya zuwa qarshe suna kusa da Du’au Nudba ne.

4-ABABEN DA SUKE MUSTAHABBI RANAR JUMMA’A: Akwai wasu ayyuka da suke yin su Mustahabbi ne a duk ranar Jumma’a. Ga wasu daga ciki:

1-Wankan Jumma’a.

2-Yenke farce-qunba- Yazo a Ruwaya cewa yenke farce duk ranar Jumma’a yana qara Arziki yana kuma goge zunubi.

3-Sa Turare wato idan mutum na sakaci da sa turare to duk ranar Jumma’a ya ga cewa ya sa, mustahabbi ne sa turare a duk sallar da mutum zai yi ta wajibi.

4-Da da kyautata ma iyali a duk ranar Jumma’a wato a ranar ya sawo masu abun da bai saba sawo masu ba misali na ‘ya’yan itace da dai sauransu ta yadda za su dun ga farin ciki da ranar Jumma’a.

5-Cin Ruman: Imam Kazim [AS] ya ce, “Duk wanda ya ci Ruman ranar Jumma’a to zuciyarsa za ta haskaka.

6-Ziyarar maqabarta: Sayyida Zahra [AS] Ta kasance a duk ranar Jumma’a ta kan ziyarci qabarin Sayyiduna Hamza da sauran shuhada’u na Uhud.

7-Yin Addu’oi ga ‘yan uwa Muminai wato mutum ya kasance daga cikin ayyukan ibadodi da zai lizimta ma kansa shine yi ma ‘yan uwansa na Addini da kuma na jini aqalla mutum 40 addu’a a duk daren Jumma’a ko ranar Jummar.

5-ABABEN DA SUKE MAKRUHI A RANAR JUMMA’A: Daga cikin su akwai sauraren waqe wadanda bana addini ba, akwai ma bayin Allah hatta waqoqi na adddini suna nisantar su a daren Jumma’a da kuma ranar Jumma’a saboda Hadisai da suka zo akan haka. Haka nan Makruhi ne yin tafiya ranar Jumma’a gabanin Sallar Jumma’a amma bayan Sallah ba matsala.

 
Home Darusan Akhlaq Ibadodin Daren Jumma’a da Ranar Jumma’a
Copyright © 2024. www.tambihin.net. Designed by KH