Saturday, 14 December 2024
Email
Make My Homepage
RSS
Register
Waki'oin da suka biyo bayan Karbala Print E-mail
Written by administrator   
Thursday, 17 September 2020 16:54

Bayan wa}i’ar Karbala a kwai wasu wa}i’oi da suka biyo bayanta a}allala guda ukku ta fuskcin mutanen gari,a lokacin wa}i’ar Karbala zaka iya kasa mutane gida ukku,na farko akwai Imam Husaini[AS] da wa]anda suka bishi,na biyu akwai Yazidu [LA] da magoya bayansa.na ukku akwai Jama’ar gari wanda za a iya siffatu su a matsayin ‘yan kallo.To tambaya anan itace minene mutanen gari suka yi bayan wa}i’ar Karbala? Domin matsayin Imam Husain ba ~oyayye bane a wajensu a }alla babu wanda yake musun ko shakka cewa Imam Husain ]an Sayyida Fa]ima ne ita kuma ‘yar Manzon Allah[SAAW]Saboda haka duk wani Musulmi a lokacin in dai har yana da imani to kashe Imam Husain zai tayar masa da hankali,akan asasin haka akwai wa}i’oi da suka auku bayan Karbala,ga guda ukku da suka fi shahara:

1-Wa}i’ar Harra.

2-Wa}i’ar Tawwabun.

3-Wa}i’ar Muktarus-sa}afiy.

1-WA{I’AR HARRA

          Wa}i’ar Harra wata wa}i’a ce da ta auku a birnin Madina bayan wa}i’ar Karbala,abinda ya faru shine bayan labari ya bayyana kuma ya watsu a birnin Madina cewa an kashe Imam Husain kasantuwar su Sayyidana Zainab lokacin da suka taso daga Sham to zuwa birnin Madina suka dawo kai tsaye duk da cewa bayan an kashe Imam Husain Yazidu ya aiko da umarni ta hannun gwamnan sa dake Madina cewa ya rushe gidan Imam Husain dake Madina da duk gidan wani da ya bishi zuwa Karbala,shi yasa ko lokacin da Sayyida Zainab suka iso Madina sun samu gidajensu mai rusau ya rushe su.To su mutanen Madina bayan jin cewa an kashe Imam Husain sai Ansarawa suka zauna suka tattauna kan abina da zasu yi sai suka yenke shawar cewa su aika wata tawaga zuwa Sham su binciko masu abubuwan da ake fa]i kan Yazidi gaskiya ne na cewa shi Mashayin giya ne fasi}i, baya salla da dai sauransu,bayan wa]annan tawaga sun tafi Sham domin wannan bincike su ka dawo da bayanin cewa lalle abubuwan da ake fa]i game dashi gaskiyane har ma suka zo da bayanan wasu abubuwan da yake yi na Shai]ananci wa]anda basu sani ba to shine mutanen Madina suka yenke shawar cewa su sun sauke Yazidu wato sun yi tawaye ma shugabancinsa yanzu sun na]a wani da ake ce ma Abdullahi ]an Hanzala a lokaci guda kuma suka kori gwamnan Yazidu dake Madina haka nan kuma suka kori duk bani umayya dake cikin Madina,bayan haka kuma suka shirya ma ya}i.Lokacin da labari ya isa ga Yazidu cewa mutanen Madina sun yi masa tawaye kuma sun kori gwamnansa dake Madinar nan take ya shirya rundunoni na ya}i da nufin zuwa Madina }ar}ashin jagorancin wani mujrimi da ake ce ma Muslim ]an U}uba saboda munanan ayyukansa da kashe mutane Malaman tarihi na Ahlus sunna basu ce masa Muslim suna ce masa Musrif ]an U}uba ma’ana ma~arnaci.Lokacin da zasu kama hanya zuwa Madina daga cikin abubuwan da Yazidu ya fa]a ma wa]annan maya}a har da cewa in sun samu galaba kan mutanen Madina to ya halatta masu madina tsawon kwana ukku ma’ana tsawon wa]annan kwanaki su yi abun da suka dama a cikin Madinar,kuma haka suka yi mutum ya binciki littafan Tarihi na Ahlus sunna zai ga sun kawo wannan wa}i’a ta Harra sanka-sanka fiye da yadda suka kawo wa}i’ar Karbala a littafansu.

Daga cikin munanan abubuwan da suka yi a garin Madina akwai kashe-kashe na Sahabbai da tabi’ai masu yawa yazo a tarihi cewa sun kashe a}alla mahaddata Al}ur’ani kusan 700 sun yi ‘yan mata a}alla 1000 fye]e,sai da takai mutanen Madina basu da wata mafaka face zuwa ga Massallacin Manzon Allah[S] amma haka wa]annan laanannun mutane suka bisu har Massalcin suna yi masu wannan ta’asa,suka she}ar da jini a ciki suka yi fasadi sai da ta kai a cikin wa]annan kwanaki ukku da suka halatta Madina ba a samu yin sallar Jam’i ba a wannan Masallaci mai al-barka.Bayan wa]annan kwanaki ukku sai wanda ya jagoranci wannan ya}i wato Musrif ]an U}uba ya bu}aci wa]anda suka rage wato ba a kashe ba da su zo su yi bai’a ga Yazidu,kuma sigar bai’ar ma ta wala}anshi domin mutum zai ce ne , “Ya mi}a bai’a ga Yazidu a matsayin bawansa kuma yana da ikon yayi abinda ya ga dama dashi da kuma dukiyarsa.” In mutum ya}i yin bai’ar da wannan sigar sai a kashe shi haka suka bi gida-gida cikin Madina suna am sar bai’ar,abin mamaki gidan da suka fara zuwa shine gidan Ummu-Salama matar Manzon Allah suka same ta tare da wani jikanta suka bu}aci da yayi bai’a da wannan siga ya ce masu shi dai zai yi ba’a ga Allah da Manzonsa ba wai ga Yazidu ba, nan take Musrif ya ce a kashe shi.Daga cikin munanan ababen da suka yi lokacin da suke bi gida-gida shine duk gidan da suka shiga duk abunda suka gani in dai suna da bu}atarsa to suna ]auka ne kawai alal misali akwai gidan wani sahabin Manzon Allah mai suna Aba Sa’idil Khidriy da suka shiga suka kwashe kayan gidanshi baki ]aya hatta abinda yake shan ruwa basu bar mashi ba bayan sun bar gidan wasu maya}a goma suka sake shiga gidan da suka ga basu samu komai ba.sun samu shi sahabin yana salla ne amma saboda bushewar zuciya na wa]annan maya}a buzun da yake Sallah akai suka fizge shi akai.Ta yiyu wani yai tambaya lokacin da wa]annan maya}a suka shigo birnin Madina ina Imam Zainul Abidin yake? Akwai ruwayoyi guda biyu,akwai ruwayar da ta nuna cewa a lokacin Imam Zainul Abidin baya cikin Madina,a wata ruwayar kuma an ce yana cikin Madina amma tsawon wa]annan kwanaki su wa]annan maya}a basu ganshi ba wato shi yana ganinsu amma su basa ganinsa sakamakon wata addu’a da yayi,akwai kuma wata ruwayar da ta nuna cewa su wa]annan maya}a tun gabanin su fito daga Sham Yazidu ya umarci jagoran maya}an cewa in sun shiga Madina ka da ya ta~a Zainul Abidin kada kuma ya bu}aci bai’a daga wajensa.A ta}aice haka wa]annan maya}a na Yazidu suka kwashe kwanaki suna ta’asa a birnin Manzon Allah,bayan da suka bar Madina suka nausa suka yi Makka da nufin abinda suka yi a Madina zasu yi a can to akan hanyarsu ta zuwa Makka sai Jagoran maya}an wato Musrif ]an U}uba ya mutu suka binne shi anan suka ci gaba da tafiya,lokacin da shi Musrif yaga mutuwa zai yi sai ayyana wani daga cikin maya}an da nufin ya jagorance su, ya kuma ce masa duk abunda ya ga ya yi a Madina to yayi hak a Makka,ile ko haka suka aiwatar har ma da }ona Ka’aba.Mu dubi irin wannan cin zarafi na Musulunci da Musulmi da Yazidu ya aikata,wannan na da daga cikin ababen da Imam Husaini ya hango yasa ya ]auki matakin da ya ]auka domin ya zama sanadiyyar farkawar alumma,saboda su bani Umayya addini suka so su kawar,tun lokacin da sa}on Musulunci yazo suke fa]a dashi har zuwa lokacin, misali Abu Sufyan ya ya}i Manzon Allah, Mu’awiya ya ya}i Imam Ali da Imam Hassan,Yazidu ya ya}i Imam Husain.

Wannan wa}i’ar ta Karbala da Yazidu ya aukar ita tayi sanadiyyar gushewar daular bani Umayya domin tun bayan Karbala daularsu bata samu zaman lafiya ba,matsaloli suka dunga bijiro mata har daga }arshe daular ta ruguje,wannan yana daga cikin illolin zalunci ga Azzalumai tun a gidan duniya wato }wace abinda suke tin}awo dashi na iko,shi yasa in mutum ya dubi tsawon zamanin da daular bani umayya da kuma daular Abbasawa suka yi zai ga akwai banbanci na tsawon zamani misali Daular bani Umayya sunyi shekaru 100 da wani abune akan mulki su kuma banil Abbas sun yi shekaru sama da 500 ne kan mulki duk da suma sun yi zalunci ta fuskoki dabam dabam.Wannan kenan a ta}aice kan wannan wa}i’a ta Harra.Kamar yadda nace mai bu}atar }arin bayani yana iya duba lttafin Tarihi na ibn Kasir ko tarihin [abari ko Tarikul khulafa na Suyu]i.

2-WA{I’AR TAWWABIN

Wannan wasu gungun jama’a ne da suka ha]u }ar}ashin wani mutumi da ake ce masa Sulaiman ]an Surad Alkuza’iy da nufin sun tuba zuwa ga Allah Ta’ala kan rashin taimaka ma Imam Husain da basu yi ba,wasun suma suna daga cikin wa]anda suka rubuta ma Imam Husain wasi}a da cewa ya zo Kufa,su wa]annan Tawwabin ]in suka zauna tsakaninsu suka tattauna kan wannan tuba tasu,wasu suka kawo shawar cewa duk su kashe kawukansu kamar yadda Bani Isra’ila suka yi,wasu suka ce to ai in sun yi haka sun yi kuskure abinda ya kama su yi shine suje su ya}i wa]anda suka ya}i Imam Husain ko da ko zai kai ga dukkansu a kashe su, saboda haka suka shirya ya}i suka nufi sham,daga }arshe kusan dukkansu sun yi shahada.Wa}i’ar Tawwabin ta auku ne bayan mutuwar Yazidu,lokacin Abdul Malik ]an Marwan ne yake shugabanci.Adadin wa]annan Tawwabin a wata ruwaya sun kai kusan dubu ukku.

3-WA{IAR MUKTARU-SA{AFIY

          Wa}I’ar Muktaru-Sa}afiy ta faru ne a cikin garin Kufa,wannan bawan Allah tun gabanin bayyanarsa Imam Ali yayi albishir da bayyanarsa da kuma abinda zai yi haka nan Imam Husain a ranar Ashura bayan da yi hu]ubobi har guda ukku ga su ma}iya amma basu canza tunaninsu ba to shine daga }arshe yayi Addu’a akansu wanda yake ishara da salla]ar Muktaru Sa}afi akansu.Wannan wa}i’a ta ]oru ne akan ]aukar fansa ga wa]anda suka yi musharaka ta gefen ma}iya a wa}i’ar Karbala,kuma Alhamdu-lillah duk wa]anda suka yi musharaka ta gefen ma}iya musamman ma jagororinsu to Muktar sai da ya kashe su ]aya bayan ]aya alal misali Muktaru Sa}afi shi ya kashe Ibn Ziyad,Umar ]an Sa’ad,Shimru,Harmala da dai sauran na fitattun ma}iya, abinda yayi ya faranta ran Ahlul bayt da masoyansu,lokacin da Muktar ya kashe Ibn Ziyad da Umar Ibn Saad sai ya yenke kawukansu ya aika ma Imam Zainul Abidin,a lokacin da Imam Zainul Abidin yaga wa]annan kawuka a gabansa yai farin ciki, yai godiya ga Allah, yace daman ya ro}i Allah kada ya kar~e shi sai yaga mutuwar wa]annan mutane.{abarin Muktar yanzu haka yana garin Kufa ne kusa dana Muslim dan A}il.Ga bayanin a ta}aice yadda Muktar ya kashe wa]annan ma}iya da aka ambata

          1-Ibn Ziyad[LA] Shima idan mutum ya dubi }arshen rayuwarsa zai ga cewa kashe shi aka yi aka kuma sare kansa kamar yadda yasa a sare kan Imam Husain[AS] da sahabbansa bayan an sare kansa aka kaima Muktar assa}afi a lokacin yana cin abinci shine yake cewa ina godiya ga Allah Ta’ala cewa an kai kan Imam Husain gaban ibn Ziyad yana cin abinci ni kuma gashi an kawo mani kan ibn Ziyad ina cin abinci,a lokacin da aka kawo kan shi ibn Ziyad to akwai wasu kawuka na wasu daga cikin makusantansa wa]anda suma aka kashe su aka kuma sare kawukansu,to wa]annan kawuka suna zube gaban Muktar kawai sai ga maciji ya bayyana ya hawo kan wa]annan kawuka sai aka ga ya shiga cikin hancin ibn Ziyad ya fita ta cikin kunnensa saaannan kuma ya sake shiga ta kunnensa ya fita ta cikin hancinsa,lokacin da Muktar ya gama cin abinci sai ya tashi ya tattaka fuskar ibn Ziyad da takalminsa,bayan haka sai ya tu~e takalminsa yaba wani bawansa akan yaje ya wanke masa shi ya ce saboda wannan najasar da ya taka dashi.Bayan haka kuma ya aika da wannan kai na ibn Ziyad da sauran kawuka ga Imam Zainul Abidin lokacin yana Makka,Ikon Allah lokacin da aka kai wannan kai na ibn Ziyad gaban Imam to yana cin abinci ne,shine Imam Zainul Abidin yake cewa, “An kaini da kuma kan mahaifina gaban ibn Ziyad yana cin abinci shine na ro}i Allah kada ya kar~i rai na har sai na ga kan ibn Ziyad ina cin abinci saboda haka ina godiya ga Allah Ta’ala da ya amsa mani wannan addu’a.” To wannan shine }arshen ibn Ziyad a wannan gida na duniya.

          2-Umar ]an Saad:Shima idan mutum ya bibiyi tarihinsa zai ga cewa yayi mummunan }arshe ne daman Imam Husain ya fa]a masa cewa duk al}awurar da aka yi masa misali na zama gwamna a garin Rayyi da sauransu to ba wanda zai samu kuma daga }arshe za a kashe shine a kuma sare kansa,yara kuma a kufa zasu yi ta }ollo da kan nasa,tabbas kuma haka abun ya auku wato na babu wani abu da ya samu na al}awuran da aka yi masa kuma daga }arshe kashe shi aka yi aka sare kan bayan an gama tangaliliya da kansa a garin Kufa aka aika ma Imam Zainul Abidin,lokacin da aka kai kan ibn Saad gaban sai ya yi sujuda ta godiya ga Allah Ta’ala ya ce, “Godiya ta tabbata ga Allah da ya ]aukan man fansa daga ma}iyanmu, Allah kuma ya saka ma Muktar da alhairi.”

          3-Shimru[LA]Shine ainihin wanda ya kashe Imam Husain shima in mutum ya bibiyi tarihin }arshen rayuwar sa zai ga cewa bacin matsaloli da yai ta fuskanta bayan wannan wa}i’a daga }arshe Muktar yasa a farauto masa shi,lokacin da Shimru yaji cewa ana nemansa sai ya gudu ya tafi wani }auye aka jin labarin in da yake nan ma aka bishi,sai ya sake gudu shi da wasu da suka yi musharaka a wannan wa}i’a ta Karbala suka je daji suka zauna,haka sojojin Muktar suka same su in da suka ~oye,da yake dare yayi lokacin har sun yi barci sai kawai suka ga an zagaye su a ta}aice dai anan take aka kashe Shimru aka sare kansa tare da wa]anda aka kashe tare dashi aka kawo kan ga Muktar shi kuma ya aika kawukan ga Imam Zainul Abidin.Mu dubi yadda }arshen wannan laanannan ya kasance zama cikin garin Kufa ya gagare shi ya gudu yaje }auye can ma ya gagare shi daga }arshe ya }arata a daji.

          4-Harmala:Shi Harmala shine wanda ya kashe ]an Imam Husain mai suna Abdullah jariri ]an wata shidda wato wanda Imam Husain ya ]aga gaban su ma}iya ya ce masu idan kuna ganin ni na yi maku wani abu to shi wannan jaririn fa bakwa bashi ruwa ya sha ba kawai sai Harmala ya harbo kibau sai ga wuyan wannan jariri! Akwai wani mutumin Kufa da yazo wajen Imam Zainul Abidin a Madina sai Imam Zainul Abidin yake tambayarsa dangane da Harmala sai ya ce na barshi a Kufa a raye,sai Imam Zainul Abidin ya ]aga hannunsa masu albarka sama ya yi addu’a ya ce, “Ya Allah ka ]an]ana masa zafin wu}a ka ]an]ana masa zafin wuta.” Wannan mutumi ya ce da na koma Kufa na samu Muktar ya soma ]aukar fansa na duk wa]anda suka ya}i Imam Husain,da muka ha]u dashi yake ce man kwana biyu bamu ha]u ba sai ya ce masa ai na yi tafiya ne ban jima da dawowa ba,sai wannan mutumin ya ce muna cikin magana da Muktar sai ga wani yazo wajensa yake ce masa sun gano in da Harmala yake sai Muktar ya aika wasu maya}a akan suje su kamo shi,ba a jima ba sai gashi an kamo Harmala aka kawo shi gaban Muktar.Muktar ya dubi Harmala ya ce masa na gode ma Allah da ya bani iko akanka,shine Muktar ya ce a nema masa mahauci kuma yazo da wu}a,da mahaucin yazo sai ya ce masa yenke min hannuwansa ya yenke,sai ya sake ce masa yenke min }afafuwansa aka yenke,sai Muktar ya ce a hura huta aka hura sai ya ce ku jefa shi a ciki,sai abokin shi Muktar ya ce Subhanallah,sai Muktar ya ce masa tasbihi abu ne mai kyau amma mi yasa kayi,sai ya ce masa wannan tafiyar da na yi zuwa Makka naje wajen Imam Zainul Abidin sai yake tambaya ta dangane da Harmala na ce masa aiko na barshi a Kufa yana raye nan take sai ya ]aga hannu yai addu’a Allah ya ]an]ana masa zafin wu}a da kuma wuta,sai Muktar ya ce masa tabbas kaji Imam Zainul Abidin yana wannan addu’a,sai mutumin ya ce masa wallahi na jishi yana fa]in haka nan take sai Muktar ya yi sallah raka’a biyu ta godiya ga Allah Ta’ala kuma ya tsawaita sujuda, kafin ya gama sallar Harmala ya }one }urmus cikin wutar,bayan haka sai shi wannan mutumi ya bu}aci Muktar da suje gidansa su ci abinci,sai Muktar ya ce masa haba wane ka fa]a min ga addu’ar da Imam Zainul Abidin ya yi kuma Allah ya amsa masa wannan Addu’a da yayi ta hannuna saannan kace in ci abinci? Ai yau azumi zan yi saboda godiya ga Allah kan wannan ni’ima da yayi mani.To mu duba mu gani wannan shine }arshen Harmala a gidan Duniya ballantana kuma a ranar Lahira,Harmala yayi munanan abubuwa da yawa a wannan wa}i’a ta Karbala bilhasali ma shine ya ]auki kan Imam Husain daga Karbala zuwa Kufa.

 
Copyright © 2024. www.tambihin.net. Designed by KH