Tuesday, 09 August 2022
Email
Make My Homepage
RSS
Register
Falalar Kukan Juyayin Imam Hussain (AS) Print E-mail
Written by administrator   
Thursday, 17 September 2020 16:45

Watan Muharran da kuma watan safar watanni ne na juyayi da kuma kuka ga Ahlul bayt[AS] da kuma mabiyansu saboda abubuwa da yawa da suka auku a cikin watannin na juyayi alal misali a cikin watan Muharram kamar yadda aka sani 10 gare shi ne shahadar Imam Husain.A 12 ga Muharram ]in a wata ruwaya wafatin Imam Zainul-Abidin amma a ruwayar da tafi shahara shine cewa yayi shahada ne a 25 ga watan Muharram.A cikin watan Safar kuma 7 gare shi a wata ruwaya shahadar Imam Hassan amma a ruwayar da tafi shahara shine cewa yayi shahada ne a 28 ga watan safar.A 28 ne wafatin fiyayyen halitta wato Manzon Allah[SAAW] A wata ruwayar a }arshen safar ne shahadar Imam Rida[AS] amma ruwayar da tafi shahara itace 23 ga watan Zul-}ida.To kasantuwar wa]annan ranaku na juyayi a cikin wa]annan watanni suka mai dasu watannin juyayi da kuka ga mabiya Ahlul bayt,akwai ma Malaman da na sani a duniyar Shia a tsawon wa]annan watanni biyu kullum cikin ba}a}en kaya suke,wato watan muharram da Safar basu sa wasu kalan kaya in ba ba}a}e ba.

          Dawowa ga shi wannan maudu’i na Falalar kukan juyayin Imam Husain,insha Allah bayanai zasu gudana kan wa]annan ababe:

1-Matsayin kuka a addinin Musulunci.

2-Nau’oin kuka.

3-Falalar kukan Imam Husain[AS].

4-Kukan Manzon Allah [SAAW] da kuma Aimma [AS] ga Imam Husain.

5-Kukan halittu ga Imam Husain [AS].

6-Ababen da suke haifar da rashin kuka.

7-Ababen da suke sa kuka.

            1-MATSAYIN KUKA A ADDININ MUSULUNCI:Wani tambihi anan shine kukan da ake maganan anan shine kuka da yake da ala}a da addini misali kuka saboda tsoron Allah ko kukan juyayin Imam Husain amma ba kuka da yake da ala}a da duniya ba,to irin wannan kuka da yake da ala}a da addini yana da matsayi babba a cikin addinin Musulunci,alal misali ga wasu Hadisai akan haka:1-Manzon Allah ya ce, “Wanda yayi kuka saboda Allah-misali saboda tsoron Allah ko shau}in son saduwa da shi-to za a gina masa gida a cikin aljanna daga kowane ]igon hawaye da ya zubar.” 2-Manzon Allah[SAAW] ya ce, “Wanda idanuwansa suka zubar da hawaye saboda tsoron Allah to zai kasance ranar }iyama a ma’auninsa,kowane ]igon hawaye yana da lada kamar dutsen Uhud.” 3-Imam Ali[AS] ya ce, “Kuka saboda tsoron Allah mabu]i ne zuwa ga rahamar Allah kuma yana haskaka zuciya kuma yana tsare mutum daga dawwama akan zunubi.” 4-Imam Husain[AS] ya ce, “Babu ]igo da suka fi soyuwa ga Allah kamar ]igon hawaye da aka zubar saboda tsoron Allah da kuma ]igon jini da aka zubar a tafarkin Allah Ta’ala.” 5-Imam Ba}ir[AS] ya ce, “Ko wane ido zai zo ranar }iyama yana kuka sai idanuwa guda ukku idon da yayi kuka saboda tsoron Allah a gidan duniya,idon da ya raya dare saboda Allah-misali da ibadodi- da idanuwar da aka tsare su daga kallon haramun.” Da dai sauran Hadisai masu yawa da ke magana kan haka.

            2-NAU’OIN KUKA:Kuka a fagen addini yana da fuskoki dabam dabam ga wasu daga ciki:1-Kuka saboda tsoron Allah.2-Kuka saboda shau}in Allah ko shau}in Manzon Allah da kuma Aimma na Ahlul bayt.3-Kuka saboda wani zunubi da mutum ya aikata.4-Kuka na }as}anta da kai gaban Allah Ta’ala.5-Kuka na juyayi da kuma ba}in cikin abubuwan na cutarwa da aka yi ma Manzon Allah da kuma Ahlul bayt[AS].Wannan maudu’i na falalar kukan juyayin Imam Husain ya shiga cikin wannan babin ne.6-Kukan tausayi wato kukan da wani lokaci ya kan bijiro ma bayin Allah saboda tausayin su ga mutane a fagen addinin su ko duniyar su musamman ma a fagen addinin su misali anan shine yazo akan cewa Imam Husain a ranar Ashura bayan da yayi jawabai dabam-dabam ga ma}iya ko zasu samu canjin tunani daga wannan mummunan aiki da suke su aiwatar amma haka bai yi yu ba,sai aka ga hawaye na gangaro ma Imam Husain sai aka tambaye shi mi yasa yake kuka sai ya ce yana tausaya ma wa]annan mutane ne saboda wannan abu da zasu yi wuta zai kai su.Haka nan yazo a tarihin Imam Khumaini cewa wani lokaci in yana kallon labarum duniya a TV in yaga an nuno wasu mutane da suka cikin mawiyacin hali a duniyan ce sai a ga yana kuka saboda tausayawa garesu.7-KUKAN MUNAJATI:Wani kuka ne da ya kan bijiro ma bayin Allah Ta’ala lokacin da suke munajati da Allah Ta’ala misali ta hanyar adduo’i da makamantansu.Ga wasu Hadisai da suka zo kan wa]annan nau’oin kuka da aka ambata.An ruwaito daga Imam Husain yana cewa, “Wanda yayi kuka saboda wani zunubi da ya aikata to Allah zai gafarta masa zunubin.Wanda yayi kuka saboda tsoron wuta to Allah zai tsare shi daga shiga wutar.Wanda yayi kuka saboda Shau}i zuwa ga Aljanna to Allah zai shigar dashi Aljannar.Wanda ya yi kuka saboda tsoron Allah to Allah zai tada shi ranar }iyama tare da Annabawa da siddi}ai da Shuhada da kuma Salihai.Saboda haka yana da gayar muhimmanci ga kowannen mu yaga cewa wa]annan nau’oi na kuka dabam dabam da aka ambata yana yinsu a rayuwarsa domin samun falalarsu a ranar }iyama.

          3-FALALAR KUKAN IMAM HUSAIN:Akwai Hadisai masu yawa da aka ruwaito daga Aimma na Ahlul bayt[AS] dangane muhimmanci da kuma falala na juyayin kukan Imam Husain ga wasu daga ciki:1-Wani daga cikin sahabban Imam Sadi} ya ce, “Na kasance tare da Imam Sadi} sai muka ambaci Husain sai muka ga Imam Sadi} yana kuka, muma sai muka yi kuka,sai Imam Sadi} ya ce, Imam Husain ya ce, “Mumini ba zai ambace ni ba ko ya tuna dani face yayi kuka.” Ya zo a tarihin Imam Khumaini cewa duk lokacin da aka ambaci Imam Husain a gabansa sai an ga ya zubar da hawaye.Wato gasgatawa ga Hadisin da aka ruwaito daga Imam Husain cewa, Mumini ba zai ambace ni ba ko ambace ni a gabansa face yayi kuka.A wata ruwaya ya zo akan cewa, duk lokacin da aka ambaci Imam Husain gaban Imam Sadi} to a yinin baki ]ayansa ba za a ga murmushinsa ba.2-Imam Sadi} ya ce, “Duk wanda yayi kuka saboda juyayi Imam Husain to zai shiga Aljanna.”3-Imam Sadi} ya ce ma wani mawa}in Ahlul bayt da ake ce masa Aba Ammara, “Ya Aba Ammara duk wanda yayi wa}e na juyayin Imam Husain har aka samu mutum 50 suka yi kuka a majalisin to yana da Aljanna,wanda yayi wa}e na juyayin Imam Husain har aka samu mutum 30 suka yi kuka to yana da Aljanna,wanda yayi wa}e na juyayin Imam Husain har aka samu mutum 20 suka yi kuka to yana da Aljanna,wanda yayi wa}e na juyayin Imam Husain har aka samu mutum 10 suka yi kuka to yana da Aljanna,wanda yayi wa}e na juyayin Imam Husain har aka samu mutum 1 yayi kuka to yana da Aljanna.” Mu dubi yadda adadin ya dunga raguwa har ya zuwa 1 wanda ke nuna gayar falalar da kukan juyayin Imam Husain yake dashi.A wata ruwaya Imam Sadi} ya ce, “Babu wani mai wa}e da zai yi dangane da juyayin Imam Husain har yayi kuka kuma a samu wani majalisin shima yayi kuka face an gafarta masu kuma Aljanna ta tabbata a garesu.4-Imam Rida ya ce, “Duk wanda ya ambaci ko ya tuna da cutarwar da aka yi mana har ta kai da yayi kuka saboda haka to zai kasance tare damu a ranar }iyama.” A wata ruwaya kuma Imam Rida ya ce, “Duk wanda yayi kuka saboda juyayi da ba}in cikin cutarwa da gallazawa da ma}iya suka yi mana to Allah zai tada shi tare damu Ahlul bayt. 5-Imam Ba}ir ya ce, “Babu wani bawa da aka ambaci Ahlul bayt a gabansa har ta kai ga yayi kuka kan cutarwar da aka yi masu to sai Allah ya gafarta masa dukkan zunuban da ya aikata.” Da dai sauran Hadisai masu yawa wa]anda ba za a iya kawo su duka ba saboda gudun tsawaitawa.

          4-KUKAN MANZON ALLAH DA AIMMA NA AHLUL BAYT GA IMAM HUSAIN[AS]:Idan mutum ya bibiyi tarihi da kuma wasu Hadisai da aka ruwaito zai ga cewa tun ranar da aka haifi Imam Husain Manzon Allah ya fara kuka na juyayin kisan da za a yi mashi alal misali lokacin da aka haifi Imam Husain Manzon Allah yazo gidan Sayyida Fa]ima[AS] sai ya ce ma Asma’u bintu Umais ta mi}o mashi abinda aka haifa,sai ta mi}a masa yana lullu~e da wani mayafi fari sai Manzon Allah yayi kiran sallah a kunnensa na dama bayan haka kuma yayi i}ama a kunnensa na hagu bayan haka sai ya aza shi a cinyoyinsa masu albarka sai aka ga yayi kuka,sai Asma’u tace Baba na da Mama na su zamo fansa gareka mi yasa kake kuka?Manzon Allah ya ce,ina kuka ne saboda shi,sai tace to ai yanzu aka haife shi,sai Manzon Allah ya ce mata ya Asma’u za a samu wasu azzalumai ‘yan tawaye daga cikin bani umayya za su kashe shi a bayana,ba zasu ta~a samun ceto na ba,sai Manzon Allah ya ce mata amma kada ki shaida ma Fa]ima wannan Magana kasantuwar bata jima da haihuwarsa ba.To tun daga wannan ranar idan mutum ya bibiyi tarin Manzon Allah zai ga cewa lokuta dabam dabam a kuma wajaje dabam dabam har ya zuwa }arshen rayuwarsa Manzon Allah yayi kukan juyayi na kisan Imam Husain,kai hatta a ranar sunan Imam Husain wato rana ta bakwai da haihuwarsa sai da Manzon Allah yayi kuka,in mutum ya duba a dai wannan ruwaya da aka ruwaito daga Asma’u take cewa a ranar ta bakwai Manzon Allah yazo gidan Sayyida Fa]ima ya ce in mi}o masa Husain aka yi masa A}i}a-Dabbar da ake yenka ma abinda aka haifa a ranar ta bakwai-aka kuma yi masa aski bayan haka kuma ya ]ora shi akan }afafuwansa sai aka ga Manzon Allah yana kuka,sai Asmau tace ranar farko kayi wannan kukan sai ya ce,ina kuka ne saboda kisan da laanannun mutane zasu masa,sai ya yi addu’a ya ce, “Ya Allah ina ro}a ma Hassan da Hussain abinda Ibrahim ya ro}a ma zuriyyarsa,ya Allah ka sosu ka so duk wanda yake son su ka tsine ma duk mai }insu.” Wani tambihi anan dangane da ita wannan baiwar Allah wato Asma’u ‘yar Umais shine cewa tana daga cikin matayen farko da suka Musulunta a Makka wanda in ana lissafin matayen farko da suka Musulunta to ba ta kai ta goma ba,kuma ita matar Ja’afar ]an Abi [alib ce saboda haka hijirar farko da aka yi zuwa Habasha da ita aka yi kasantuwar mijinta Ja’afar shi ya jagoranci hijirar,wani babban abu wanda tarihi ma zai manta da ita akai ba shine ita ce farkon wadda ta assasa anfani da makara wadda ake sa gawa akai a tsakankanin al’ummar musulmi,abinda ya faru shine kasantuwar tana da gayar kusanci da Sayyida Fa]ima to lokacin da take jinyar rashin lafiyar da ta yi wafati a cikinsa,sai Sayyida Fa]ima ta ce mata ita ko bata son yadda in mutum ya rasu ake ]auko gawarsa zuwa ma}abarta babu wani shamaki,sai Asma’u ta ce mata zaman da suka yi na Hijira a Habasha ta ga yadda suke yi ma gawa,sai ko ta yi shigen yadda ta ga suke yi wato dai ita makara ]in,lokacin da ta kammala makarar sai Sayyida Fa]ima ta yi murmushi ta yaba ma abun,ta bar wasiyyar cewa in ta rasu a saka ta a cikinsa.Wato gabanin haka in mutum ya rasu namiji ne ko mace bayan an kintsa shi sai dai a lullu~e shi a tabarma ko wani zuwa ma}abarta,amma tun da Asma’u ta yi wannan makara ya zamanto har yau al’ummar musulmi ke amfani dashi.A ta}aice ita Asma’u ita ce wadda ta }ir}iro yin anfani da makara a tsakankanin musulmi kuma Sayyida Fa]ima itace farkon wadda aka saka a ciki.Haka nan kuma ita Asma’u tana cikin shi’atu Ahlul bayt,akwai bayanai masu yawa dangane da ita wannan baiwar Allah ga mai bu}atar dubawa yana daba wani littafi mai suna, “A’alamu Nisa’il Mu’uminati” Dawawo ga shi wannan babi da ake bayani wato na kukan Manzon Allah ga Imam Husain,baya ga ita wannan ruwaya da tazo na kukan da Manzon Allah yayi a ranar da aka haifi Imam Husain da kuma ranar sunansa to haka nan akwai ruwayoyi masu yawa da aka ruwaito cewa Manzon Allah ya kan yi makamancin wannan kuka ga Imam Husain idan yazo wajen sa wato lokacin da ya tasa yana yaro ga wasu misalai shima daga ciki:Wata rana Manzon Allah ya kasance a gidan Ummu Salma wato ]aya daga cikin matayensa, sai Husain yazo lokacin yana }arami,bayan wani lokaci sai na shiga wajensu sai na ga Husaini akan }irjin Manzon Allah kuma Manzon Allah na kuka a hannunsa akwai tur~aya yana sun bartar ta,sai Manzon Allah ya ce, ya Ummi Salma Mala’ika Jibrilu ne yake shaida man cewa wannan ]a za a kashe shi ga }asar da za a kashe shi a kanta saboda haka ki aje ta a wajen ki duk ran da kika ta zama jini to tabbas an kashe shi.Ummi Salma ta aje wannan }asa,shi yasa lokacin da Imam Husain ya fita Madina zuwa Kufa an ce kowace rana sai ta ]auko wannan }asa ta duba,wata rana da ta ]auko ta,taga ta zama jini tun lokacin ta samu ya}inin cewa lalle an kashe Husain lokacin ita tana Madina ne haka wannan rana ta wuni tana kukan juyayi na Imam Husain.Haka nan makamancin haka ya kasance a gidan Aisha ta ce,wata rana Manzon Allah ya zaunar da Husain akan }afafuwansa sai yana sun bar tar Husainin,sai Mala’ika jibrilu ya ce masa al’ummarka zasu kashe shi a bayanka sai Manzon Allah yayi kuka.Bayan haka kuma akwai wata rana Manzon Allah yayi tafiya shi da sahabbansa akan hanya da suka zo wani waje sai aka ga ya tsaya yana ta Inna-lillahi-wa-inna-ilaihi-raji’un yana kuma kuka sai aka tambaye shi lafiya? Sai ya ce Mala’ika Jibril ne ya shaida man cewa za a kashe Husaini a wani waje da ake ce masa Karbala,kamar ina ganin irin abubuwan da za a yi masa da kuma su Zainab da kuma yadda za a kai kan Husain gaban Yazidu[LA] An ce Manzon Allah da ya dawo wannan tafiya tasa cikin damuwa da ba}in ciki,yaje masallaci ya hau mumbari ya hawo mumbarin tare da Hassan da Husain,yayi khu]uba yayi wa’azi,lokacin da ya gama khu]ubar sai yasa hannunsa na dama akan Hassan,hannunsa na hagu kuma kan Husain sai ya ce,Ya Ubangiji lalle Muhammadu bawanka ne kuma Manzon kane,ga wa]annan mafificin zuriyyata Jibril ya fa]a man wannan za a kashe shi da guba,wannan kuma za a kashe shi da takobi ka sanya shi ya zama shugaban Shahidai.Sahabban dake cikin masallacin suka ~arke da kuka,sai Manzon Allah ya ce,yaku mutane kuna kuka amma kuma ba zaku taimaka masa ba a lokacin da za a kashe shi.Akwai darussa masu yawa a cikin wannan al’amari na kukan Manzon Allah ga Imam Husain musamman kan wata tambaya da Malaman Ahluls sunna suke yawan yi cewa mi yasa ‘yan shi’a wai kukan juyayin Imam Husain kawai suke yi bamu ga suna yin haka ga sauran Imamansu ba ko ga Manzon Allah ba? Amsa ta}aitacciya a nan itace sune dai ba su sani ba amma kamar yadda ake gudanar da munasabar shahadar Imam Husain to haka ake gudanar da munasabar shahadar ko wane imami da kuma munasabar wafatin Manzon Allah.Kuma ana kuka da juyayi a irin wa]annan munasabobi har ma da sa ba}a}en kaya,ta ya yi wani ya sake tambayar cewa amma baku muhimmatar dasu kamar yadda kuke yi gana Imam Husain,to shima sai muce yadda muka ga Manzon Allah ya muhimmatar da abun tun gabanin ya faru to ina ga bayan ya faru.Saboda haka kuka kan juyayi Imam Husain Sunna ne daga cikin sunnonin Manzon Allah.domin ma’anar sunna shine abinda Manzon Allah ya ce ko ya aikata ko kuma ya gani ana yi bai hana ba.To wannan kuka na juyayin kisan Imam Husain Manzon Allah yayi shi ba ]aya ba ba biyu ba ba ukku ba.Allah ka]ai ya san adadin haka kai hatta a rashin lafiyar }arshe da Manzon Allah yayi ta wafatinsa sai da yayi wannan kuka na kisan Imam Husain,ga ruwayar Abdullah ]an Abbas ya ce, lokacin da rashin lafiyar Manzon Allah wadda ya rasu a cikinta tayi tsanani ya rungume Husain zuwa ga }irjinsa yana kuka yana cewa Allah ya tsine ma Yazidu.To haka nan idan muka juya zuwa ga Tarihin Imamai 12 ]aya bayan zamu ga cewa Tun daga kan Imam Ali har ya zuwa kan Imam Mahdi zamu ga cewa babu wani Imam wanda bai yi kukan juyayin kisan da aka yi ma Imam Husain ba amma saboda gudun tsawaitawa da ambada misali daga kowane Imami,in mutum na son ganin wa]annan misalai yana iya duba littafi mai suna, “{atilul-abrati-fi-fadhilatil-buka’i-ala-shahidil-itra.”

          5-KUKAN HALITTU GA IMAM HUSAIN:Shima wannan in mutum yayi bincike a littafan shia da sunna zai ga haka cewa halittu baki ]aya duk sun yi kukan kisan Imam Husain misali Mala’iku sun yi,salihan Aljannu sun yi,salihan mutane sun yi,dabbobi sun yi,sama da }asa sun yi,duwatsu sun yi da dai sauransu.Bacin gudun tsawaitawa da an kawo misalai na irin kowane halitta da aka ambata irin kukan da suka yi,amma ga mai bu}ata gani yana komawa ga littafai musamman ma wanda aka ambata a sama na {atilul abra.

          6-ABABEN DA SUKE HAIFAR DA RASHIN YIN KUKA:Wato abubuwan da suka sabbaba ma mutum rashin kuka,ya kasance yana son yayi saboda tsoron Allah ko shau}insa amma kuma bai iya yi to me yake janyo haka? Ababen da suke haifar da bushewar idanuwa suna da yawa amma ga wasu daga ciki:1-Imam Ali ya ce, “{e}ashewar zuciya yana haifar da rashin kuka a idanuwa kuma abinda yake haifar da }e}ashewar zuciya shine yawan zunubi.” Daga wannan Hadisi da aka ruwaito daga Imam Ali zamu fahimci cewa duk lokacin da mutum ya wayi gari idanuwansa basa iya yin kuka na wa]annan nau’oin kuka da aka ambata a sama to abunda haka yake nunawa shine cewa zuciya ta bushe wanda ya haifar masa da bushewar idanuwa,yawan zunubi kuma shi ke haifar da bushewar zuciya.A ta}aice abinda ake so a bayyana anan shine duk lokacin da mutum ya ga cewa bai cikin ajin masu kuka to zuciyarsa bata da lafiya.2-Son Duniya:Daga cikin abubuwan da suke haifar da bushewar zuciya akwai son duniya,a munajatin da Allah Ta’ala yayi da Annabi Musa yake ce masa, “Ya Musa kada ka tsawaita burinka a Duniya domin haka zai }e}asar maka da zuciya kuma duk mai }e}asasar zuciya to yana nesa ne dani.” Wato yawan shagaltuwa da duniya yana shagaltar da zuciya da tunaninta wanda in ya yawaita yana sabbaba bushewar zuciya.3-Yawaita Magana ba tare da ambaton Allah ba wato yawan surutu ba tare da zikiri ba shima yana kawo bushewar zuciya.4-Yawan Dariya,wato yawaita dariya shima yana jawowar bushewar zuciya,shi yasa yazo a darasin Akla} cewa mutum yayi ma kansa tarbiyya Murmushi ya zamanto shine dariyarsa wato saboda gudun bushewar zuciya.

          7-ABUBUWAN DA SUKE SA KUKA:Wato ababen da suke lausasa zuciya har ya zamanto mutum ya samu shiga cikin ajin bayin Allah masu kuka.Akwai ababe da yawa da Malaman Akla} suka yi bayani da in mutum ya lazimce su to zuciyarsa zata lausasa ga wasu daga ciki:1-Yawan tunanin mutuwa da kuma tunanin wa]anda suka mutu misali na ‘yan uwansa na jini ko na addini,wato mutumya tarbiyyantar da kansa da cewa in ya safiyantu yaji cewa ba zai kai yamma ba zai koma ga Allah,in kuma ya yammatu yaji cewa ba zai kai safe ba zai koma ga Allah, mutum ya ]an gwada haka ko da na sati ]aya ne lalle zai ga canji a rayuwarsa musamman a addinance domin zai taimaka masa wajen zama cikin hayyacinsa da kuma ]a’ar Allah Ta’ala,misali idan mutum ya wari gari yana ganin kafin yamma ajalinsa zai sauka to ina zai yi tunanin yayi aiki na sa~on Allah misali }arya ko giba ballatana cin amana da dai sauransu.2-Yawaita karatun Al}ur’ani ko kuma sauraren karatun Al}uranin.Karatun Al}ur’an hanya ce na gane lafiyar zuciya ko rashin lafiyarta wato duk lokacin da mutum yake karatun Al}ur’ani ko yake sauraron karatunsa bai yi kuka ba ko bai ji tasirin haka ba a zuciyarsa to lalle zuciyar bata da lafiya,saboda mutum ya dubi ayoyi masu yawa da suke bayanin ranar }iyama da abubuwan da zasu faru a cikinta wato abun kwai tada hankali sosai.3-Kusantar bayin Allah da suke da irin wannan baiwar ta kuka,mu anan sun }aranta sosai amma a wasu nahiyoyi musamman a duniyar shia ga su nan da yawa,zan iya tunawa lokacin ina ]ialibta a birnin Qum na san malamai da yawa suna shajja’a ]alibai yin salla bayan Ayatullahi Bahajati saboda yin hakan yana taimakawa wajen samun laushin zuciya saboda baki ]aya in ya fara salla har ya gama cikin kuka yake,wato yana tsaye a sallah kuka yake,cikin ruku’u kuka yake yi,cikin sujuda kuka yake yi haka nan idan yana tashahhud wato tahiya kamar yadda ake cewa shima kuka yake yi,abin sai dai wanda ya gani,domin alhamdu-lillahi na yi sallah a bayansa a lokuta da yawa kuma na ga hakan kuma na tasirantu sosai da hakan duk da lokacin ya tsawaita sosai saboda ya faru ne tun 1994.Haka nan Majalis na zaman makoki suma duka suna taimakwa wajen samun laushin zuciya musamman ma idan ana kawo irin wahalhalu da kuma gallazawa da Ahlul bayt da mabiyansu saka fuskanta daga hannun azzalumai.

          Daga }arshe yana da gayar muhimmanci kowannenmu ]an uwa ne ko ‘yar uwa ya yi mujahada wajen ganin cewa ya shiga cikin ajin bayin Allah masu Kuka saboda falaloli masu yawa da yake da shi kamar yadda muka gani,wato dai ya kasance ko wace rana ko kuma ko wane dare musamman lokacin sallar tahajjud mutum ya yi kuka saboda tsoronsa ga Allah ko kuma tafiyar dake gabansa ta zuwa lahira misali ga al’amarin mutuwa,kayi tunanin yadda zaka ha]u da mala’ikan mutuwa,tunanin fitar rai,zamam {abari,tambayoyin }abari,tashin {iyama hisabi da dai sauransu,in mutum ya yawaita tunani haka idan yana sallar tahajjud to wannan insha Allah yau da gobe zai sa ya dun ga kuka na wa]annan ababen dake gabansa kuma suke jiransa kuma babu makawa akai,Allah Ta’ala ya tausaya mana ya kuma sa mu dace,ya kuma sa wannan sabuwar shekarar da muka shiga ta kasance shekara ta faraj ga su Malam da dukkan ‘yan uwanmu da suke hannun azzalumai.

 
Home Maudu'oi daban-daban Falalar Kukan Juyayin Imam Hussain (AS)
Copyright © 2022. www.tambihin.net. Designed by KH