Tuesday, 09 August 2022
Email
Make My Homepage
RSS
Register
Annoba A Mahangar Ahlul-Bayt (AS) Print E-mail
Written by administrator   
Saturday, 09 May 2020 19:24

Kasantuwar wannan Annoba da Duniya baki daya take ciki wanda in mutum ya bibiyi tarihin Annoba zai ga cewa galibi ta kan faru ne a wani sashe na duniya amma saura sassa na duniya sai dai suji labari amma in muka dubi wannan Annoba mutum zai iya cewa kusan babu sashe na duniya da bata shiga ba,ba kawai ta shiga ba kusan ta tsaida komi na harkokin yau da kullum,akan asasin haka ne wasu daga cikin malaman madrasa din Ahlul bayt suka tafi akan cewa lalle wannan na daga cikin alamomin kusatowar bayyanar Imam Mahdi [AF] Idan mutum ya dubi ababen da suke faruwa cikin Annobar zai ga wasunsu sun zo a Hadisai na alamomin bayyanarsa misali

1-yawan mace-mace.

2-Rugujewar tattalin arziki na duniya.

3-Qauracewa wa Masallatai.

4-Dakatar da aikin Hajji.

5-Zama cikin firgici da yunwa da dai sauransu, to wadannan ababe da aka ambata dama wadanda ba a ambata kowannensu akwai Hadisi da aka ruwaito daga Manzon Allah [SAAW] da kuma Aimma na Ahlul bayt [AS] akan haka na cewa wasu ababe ne da zasu gudana gabanin bayyanar Imam Mahdi [AS] kuma wannan Annoba da ta faru ta girgiza duniya to somin tabi ne na abubuwan da zasu faru nan gaba misali na jin Magana daga sama wanda duk wani dan Adam da yake doron qasa sai yaji maganar koda ko barci yake yi kuma koda da wane yare yake Magana, ga kuma kusufin rana da za a yi a tsakiyar wata da kuma kusufin wata a qarshen wata wanda haka bai taba faruwa ba a tsawon tarihin duniya sai a lokacin gab da bayyanarsa, wanda abun da aka saba dashi shine kusufin rana yakan kasance a qarshen wata ne na wata kuma yana kasancewa a tsakiyar wata a taqaice dai mutum zai iya cewa babbar jarabawa ce ke fuskantar duniya.

Dawowa ga shi maudu’in, da farko wannan maudu’i na Annoba a mahangar Ahlul bayt mutum zai iya bincike akansa ta fuskoki dabam dabam na fannonin ilimi alal misali mutum zai iya bincike akansa ta fuskacin Tarihi, Fiqhu, Usulul Fiqhu, Hadisi, Aklaq. Insha Allah yanzu za a dauke su daya bayan daya domin yin bayani akan su a taqaice.

  1. Idan mutum yayi bincike a bangaren Tarihi zai ga cewa Annoba ta farko da ta faru bayan wafatin Manzon Allah itace wadda ta auku a garin Sham shekara ta 18 bayan hijira,wannan Annoba ana yi mata laqabi da AMWAS mutane da yawa sun rasu a cikinta, wata ruwaya ta nuna wadanda suka mutu a cikinta sun kai dubu Ashirin da biyar, a cikin wannan adadi akwai Sahabbai da yawa da suka rasu a ciki misali a cikin wannan Annoba ne Bilal ya rasu lokacin yana zaune a Sham, kasantuwar zaman Madina ya wuyata masa a lokacin saboda wasu ababen da suka faru na qin yin Bai’a ga Abubakar a matsayin Khalifa Umar a lokaci yake ce masa yanzu Bilal wannan shine sakamakon da zaka yi ma Abubakar na ‘yanta ka da yayi wato lokacin yana bawa, shine sai Bilal ya ce ma Umar in dai Abubakar ya ‘yanta ni ne saboda Allah to ya barni ga Allah in kuma ba saboda Allah ya ‘yanta ni ba to gani yayi abinda ya ga dama dani, kan maganar bai’a kuma Bilal ya ce masa ni ban kasance zan yi bai’a ga wanda na san cewa ba shine Manzon Allah ya khalifantar ba wanda ya khalifantar bai’ar sa tana wuyan mu har zuwa ranar qiyama, to shine Umar da yaji haka sai ya ce lalle ba zaka zauna tare damu ba. Wannan annoba da aka sa ma suna Amwas ta auku ne a lokacin Imamancin Imam Ali, a mahanga ta Ahlus sunna a lokacin khalifancin Umar.

          2-Fiqhu: A bangaren Fiqhu in mutum yayi bincike zai ga cewa sashen wasu daga cikin Maraji’ai sun ba da fatawowi dangane yin Azumi a wannan yanayi na wannan Annoba ga misali guda daga ciki da aka tambayi Ayatullahi Khamna’i: Tambaya-Mine ne hukuncin yin Azumin watan Ramadan a irin wannan yanayi da ake ciki na yaduwar cutar corona virus? Amsa: Azumi a matsayinsa na wani nauyi-takalifi-na ubangiji, wata ni’ima ce ta musamman ta ubangiji ga bayinsa, kana kuma daya daga cikin tushe na daukaka da kamalar dan Adam, kamar yadda kuma an wajabta shi ga al’ummomin da suka gabata. Daya daga cikin tasirorin azumi shine samar da yanayi na kyautatuwar ruhi da tsarkaka ta zuci, samar da tsoron Allah da ruhin gwagwarmaya tunkarar wahalhalu, kamar yadda yake taka rawa wajen tabbatar da lafiyar jiki. Allah Ta’ala ya tanadi lada mai yawan gaske ga masu Azumi. Azumi daya ne daga cikin wajibai na Addinin Musulunci, kana kuma jigo na shari’ar Musulunci, don haka barin yin azumin watan Ramadan baya halatta, sai dai idan mutum ya samu wata madogara ta hankali da ke tabbatar masa da cewa, daukar azumin zai haifar masa da 1-Rashin lafiya. 2-Ko zai qara masa tsananin ciwo. 3-Ko kuma zai jinkirta warkewar ciwon da yake fama dashi. A irin wannan yanayi azumi ya fadi akansa amma zai biya daga baya. A fili yake cewa, idan mutum ya samu wannan tabbaci daga wajen likita qwararre kana kuma ma’abucin addini, to hakan ya wadatar. A saboda haka idan har mutum yaji tsoron faruwar wadannan abubuwa da aka ambata a sama, sa’annan kuma wannan tsoro nasa ya samo asali ne daga tushe na hankali, azumi ya fadi akansa, to amma wajibi ne ya rama azumin daga baya.

          3-Usulul fiqhu: Bayani akan wannan kamata ya yi a ce a ajin karatu ne, da yake yana daga cikin fannoni ilimi da se wadanda suka yi zurfi a neman ilimi suke yinshi amma ga dan bayani a taqaice kuma a dunqule. Wani lokaci hukunce-hukunce na shari’a suna canzawa daga asalin hukuncin zuwa akasin haka sakamakon bijirowar wasu larurori misali yin musafaha ko yin sallar jam’i, in muka dube su zamu ga cewa suna da asali a shari’a amma yanzu sakamakon wani yanayi na lalura da ake ciki sai hukuncin su ya canza na nisantar yin su har ya zuwa lokacin da lalurar zata gushe to ire-ire wadannan ababe da sukan bijiro sun canza asalin hukunci a babin lalura su ake ce ma hukuma a wannan fanni, kuma yin haka ya halatta, ba wai mutum zai yi jumudi wato ya doge akan dole-dole shi yana nan akan hukunci na asali wato ba zai canza ba saboda wata lalura.

          4-Hadisi: Akwai wasu daga cikin Hadisai da suka shafi annoba idan ta auku ko take faruwa to hallaccin barin wajen domin komawa in da ba annobar,Hadisan da aka ruwaito a mahanga ta Ahlus sunnan yin haka bai halatta, ko a wannan hali da muke ciki na ji Malamai da yawa na Ahlus sunna suna kawo su cewa ya zo a hadisi idan annoba tana faruwa to mutumin dake wajen ko garin kar ya bar wajen wanda kuma bai wajen kada yaje wajen. To amma idan mutum ya dubi Hadisan a mahanga ta Ahlul bayt zai ga akasin haka na cewa idan annoba tana faruwa a waje mutum na da damar ya canza waje in yana ganin shine maslaha gareshi,in da kawai bai halatta ya canza waje ba idan annobar tana gudana sai idan a fagen jihadi ne ko ribadi wato in da ake tsammanin shigowar maqiya sai akasa wasu mayaqa domin gadin wajen to a wannan yanayi mutum ba zai bar wajen ba. Ga misalin wani Hadisi akan haka. An tambayi Imam Sadiq dangane da Annoba da ta kasance a wani gari sai mutum ya bar gari zuwa wani garin, sai Imam Sadiq ya ce ba komi akan haka, Manzon Allah ya yi hani akan haka ne ga mutanen da suke dakon zuwa abokan gaba sai annoba ta faru inda suke sai su bar wajen wato suna ribad. Amma in ba a ribadi bane ko a fagen jihadi babu komai idan mutum ya bar wajen.

          5-Aklaq: Amahanga na Aklaq duk lokacin da Annoba ta faru a waje to abu na farko shine tuba zuwa ga Allah Ta’ala a matsayi na daidaiku da kuma jama’a wato kowa ya koma ga Allah. Abu na biyu shine yawaita addu’oi da niyyar Allah ya yaye, har wala yau da kuma yin tawassili da Aimma na Ahlul bayt da kuma biya ziyar ashura shima yana maganin Annoba. Akwai wato Annoba da aka taba yi a karbala kusan ba gidan da ba a rasu ba sai gida guda daya gidan wani malami, da aka tambaye shi gashi wannan annoba ta shiga kowane gida ban da gidansa miye sirrin haka sai ya ce to shi dai ya kasance ko wace rana sai ya karanta ziyarar ashura a gidansa haka nan kuma ko wace rana yana yakan karanta du’au Tawassul a gidansa. Haka nan kuma komin yadda abubuwa suka kai da tsanani mutum kada ya cire tsammani ya kyautata zato ga Allah cewa zai tseratar dashi daga halin da ake ciki. Haka nan kuma duk lokacin da ake cikin yanayi na Annoba ana son mutum ya yawaita sadaka domin yazo a ruwayoyi na Hadisai cewa tana maganin musiba da kuma bala’oi.Wani tambihi muhimmmi anan shine ita annoba in ta auku tana iya kama kowa hatta da salihan bayi na Allah Ta’ala ko a wannan rubutu ga misalin Bilal da aka kawo,Bilal yana daya daga cikin manyan sahabban Manzon Allah kuma yana daga cikin shi’atu Ahlul bayt,haka nan idan muka dubu wannan annoba da muke ciki akwai wasu bayin Allah da ta kama daga ciki akwai wani malami da na sani yana ma matsayin Ayatullahi ne amma Alhamdu lillahi Allah Ta’ala ya bashi lafiya, a taqaice abinda nike so in fitar anan shine cewa annoba kamar yadda take kama fajiran bayi to haka nan tana iya kama bayin Allah domin ita nau’i ne na jarabawa da kuma uquba daga wajen Allah Ta’ala. Akwai ababe guda ukku da suka shafi mutuwa a hannun Allah suke ba ga mutum ba sune:1-Lokacin da mutum zai mutu. 2-In da mutum zai mutu. 3-Abinda zai zama sanadiyyar mutuwar mutum.Wadannan ababe da aka ambata mutum bai da iko akai duk suna qarqashin ikon Allah ne saboda haka sai dai mutum ya bisu da addu’a.

          Daga qarshe muna roqon Allah Ta’ala wannan Annoba ya dada tsaremu da kuma kiyayemu daga gareta ya kuma yaye ta ga wannan alumma ta Manzon Allah ya jefata ga maqiyansa da kuma maqiyan musulunci da musulmi.

 
Home Maudu'oi daban-daban Annoba A Mahangar Ahlul-Bayt (AS)
Copyright © 2022. www.tambihin.net. Designed by KH