Tuesday, 09 August 2022
Email
Make My Homepage
RSS
Register
Kusantowar bayyanar Imam Mahdi (AS) Print E-mail
Written by administrator   
Tuesday, 05 May 2020 16:00

Kasantuwar wannan wata da muke ciki na Sha’aban aka haifi hujjar Allah a doron qasa kuma shugaban wannan zamani wato Imam Mahdi [AS]. Kuma rubutu ya gabata a shekarun baya dangane Alamomin bayyanarsa da kuma ladubban zamanin gaiba. Haka kuma Darussa 12 daga rayuwarsa.To a wannan shekara Insha Allah rubutun zai kasance kan kusantowar bayyanarsa musamman idan muka yi la’akari da hali da yanayi da duniya take ciki yanzu wato na wannan Annonaba ta corona virus,idan mutum yayi bincike cikin littaffan Hadisai zai ga ruwayoyi masu yawa da aka ruwaito daga Manzon Allah [SAAW] da kuma Aimma na Ahlul bayt [AS] da suke bayani dangane da Alamomin bayyannarsa wanda mutum zai iya kasa su gida ukku. Na farko akwai Alamomin da zasu kasance gabanin bayyanarsa. Na biyu akwai Alamomin da zasu kasance gab da bayyannarsa. Na ukku akwai Alamomin da zasu kasance idan ya bayyana. Idan mutum ya dubi na farko wato Alamomin da zasu kasance gabanin bayyanarsa mutum zai ga cewa da yawansu sun bayyana misali yawan fasadi a bayan qasa, yawaita zalunci a doron qasa da dai sauransu, yanzu abinda ya rage shine Alamomin da zasu kasance gab da bayyannarsa wanda kusan shi muke ciki yanzu, alal misali yazo a Hadisai cewa gabanin bayyanarsa zaa yi Annoba wadda za a samu mace-mace da yawa a cikinta. gabanin bayyannarsa za a samu qaura ce ma masallatai wato ya zamanto an barsu,gabanin bayyannarsa za a samu karyewar tattalin Arziki na duniya da samun tsadar kayayyaki kamar yadda yake gudana a yanzu na cewa tattalin arzikin duniya ya karye, gabanin bayyanarsa za a samu tsoro da yunwa ya mamaye duniya,gabanin bayyanarsa za a hana aikin Hajji da dai sauransu,wadannan ababe da aka ambata duk akwai Hadisai akai da aka ruwaito daga Manzon Allah da Aimma na Ahlul bayt, gabanini zuwan wannan hali da muke ciki ire-iren wadannan Hadisai in mutu ya karanta ba zai fahimce sosai ba saboda bai ga abun a aikace ba misali na qauracewa masallatai yanzu gashi a aikace musammam ma mu nan Kaduna kaga lokacin Sallah yayi a kira sallah ma domin fadakar da wadansu cewa lokacin sallah yayi bazaka jiba wato kamar yadda ake a wasu qasashe ko garuuwa,wani lokaci idan lokacin sallah yayi saboda sabo da jin kiran sallah a masallatai yanzu ko shiru sai in ce wannan uguwa tamu kamar ta maguzawa.Amma idan muka dubi qasar Saudiyya da Kuwait da sauran qasashen larabawa duk da ba a zuwa masallatan amma aqalla ladan yakan zo ya kira sallar a masallaci har daga qarshe a cikin kiran sallar sai ya qare da cewa “SALLU FI BUYUTIKUM” Wato kuyi salla cikin gadajenku,shine nike cewa to ita wannan jumla da suka qara a cikin qiran sallah ina suka samo ta har da suka maida ita yanzu juz’i na kiran salla,alhali hayyi ala kharan Amal da suke kace nace akai akwai ta a Hadisai.

Ga wasu daga cikin Hadisai da aka ruwaito na Alamomin gab da bayyanarsa,An ruwaito daga Imam Ali [AS] ya ce, gab da bayyanar Mahdi za a samu abinda ake ce ma Mautul Ahmar da kuma Mautul Abyad, Mautul Ahmar shine yaqe-yaqe da kashe-kashe, Mautul Abyad shine Annoba da za a samu mace-mace a ciki,wannan Hadisi hatta Malaman Sunna sun ruwaito shi,wannan ma dana kawo a cikin ruwayar Ahlus sunna na ciranto shi daga Suyudi. A kuma wani Hadisi da aka ruwaito daga Imam Sadiq ya ce, “Ba makawa gabanin bayyanar Imam Mahdi za a samu Annoba wanda mace-mace zasu auku a cikinta. game da kuma qaura ce ma masallatai an ruwaito daga Imam Ali ya ce, “Idan aka wofintar da masallatai to ku saurari babban al’amari.” Amma su a ruwayar Ahlus sunna sun kawo shi a cikin alamomini tashin qiyama ne, wani abunda na lura dashi a littafan Hadisai na Ahlus sunna in dai abu ya shafi alamomin bayyanar Imam Mahdi galibi akan jirkita shi da cewa alamomi na tashin qiyama ba mamaki a lokacin Bani Umayya aka samu wannan canje-canje din da yake a lokacin akwai Hadisai masu yawa da suka qago akwai masu yawa da suka jirkita su musamman ma idan sun shafi Ahlul bayt.. Na shi kuma hana Hajji, ita ma ruwayar daga Imam Ali aka ruwaito ta yana cewa, kuyi dakon yenkewar aikin Hajji, idan duka alamomin suka cika to Mahdi zai bayyana, su kuma a ruwayar Ahlus sunna kamar yadda yazo a cikin Littafin Hadisi na Buhari, Manzon Allah ya ce, “Ba za a yi tashin qiyama ba har sai an kai lokacin da ba za ayi aikin Hajji ba.” Kwanakin baya da suka wuce Ministan aikin Hajji na Saudiyya ya fito qarara ya fada ma qasashen musulmi cewa su dakatar da amsar kudin zuwa Hajji saboda qila baza a samu yin aikin Hajjin ba. dai sauran Hadaisai da suka zo kan wadannan Alamomi na gab da bayyanarsa kamar na karyewan tattalin arzikin duniya wanda ba za a iya kawo suba saboda gudun tsawatawa. A taqaice dai yanzu duniya ta shiga wani Hali wanda bata taba shiga ba misali Annoba an yi da dama a tarihi amma in mutum ya bincika zai ga irin wadannan Annoba basu game mafi yawan qasashen duniya ba kamar wannnan wato zaka samu cewa annobar ta shafi wani yenki na duniya misali kamar Annobar lasa fever da ta auku a wannan qasa. Haka nan kuma Ire-ire Annabar da suka auku a tarihi basu tsaida harkokin mutane na Duniya ba amma in muka duba yanzu kusan fiye da rabin mutanen Duniya harkokin na yau da kullum sun tsaya cak suna zaune a gidajensu.

Kuma abin mamaki ga cuta ta bayyana amma kuma wai ba maganinita sai komawa ga Allah Ta’ala hatta shugabannini qasashen yamma misali shugaban qasar Italiya an nuno shi yana jawabi yana kuka cewa duk matakan da zasu dauka domin magance wannan Annoba sun dauka yanzu mafita kawai sai ga Ubangiji,haka nan shugaban America sai da ta kai yasa aka gayyato masa limaman kirista da na musulmi dana yahudawa ya ce kowa yayi Addu’a yana zauna yana jinsu,da naga abun sai da naji mamaki cewa ashe Donel yasan a koma ga Allah. To tambaya yanzu minene abin yi musamman gamu mabiya Ahlul bayt? Amsa babban abin yi shine kowannemu yaga cewa ya kyatata alaqarsa da Imam Mahdi,in mun ci sa a qila ya bayyana wannan qarni da muke ciki insha Allah domin ko a cikin wasiyyar Shehu Usman dan Fodiyo ya yi hasashen cewa qila ya bayyana a qarni na sha biyar,a lura da kyau wannan hasashe yayi ba wai ya ayyana lokaci bane saboda akwai Hidaisai da suka zo kan hani na Ayyana lokacin da zai bayyana amma gini kan hasashe da tsammani da kuma fata wannan ba matsala,in da matsalar take mutum ya ayyana ya ce zai bayyana lokaci kaza. Dawowa ga bayani dangane da kyatata alaqa da Imam Mahdi.Wannan maudu’i,maudu’ine wanda wasu daga cikin Malamai na Imamiyya sunyi bayanai da kuma rubuce-rubuce akai,alal misali idan mutum ya duba littafin ‘Uswatul- Arifin’littafine da ya yi bayanin Tarihin Ayatullahi Bahjati da kuma wasu bangarori na rayuwarsa,to a cikin littafin Fasali na 12 zai ga an kawo irin wadannan hanyoyi na kyautata alaqa da Imam Mahdi. Haka kuma a wani littafi mai suna ‘Fi madrasati Ayatullah Shaikh Bahjati’ Shi kuma littafine da aka kawo Darussa dabam-dabam na koyarwa Ayatullahi Bahjati,to a cikin littafin a fasali na 7 shi ma bayanai dabam dabam sun zo akai.Saboda haka a nan za a kawo wasu sassa na bayanan Ayatullahi Bahjati dake cikin littafan biyu da suke da alaqa da wannan maudu’in.Kuma kamar yadda wasunmu suka sani Ayatullahi Bahjati yana daya daga cikin manya-manya Urafa’u na wannan zamanin,mu duba matsayin Imam Khumaini a fagen Irfan,amma duk da haka wasu ababe da suka shafi Irfan yakan mai da su ga Ayatullahi Bahjati,akwai ma lokacin da wasu suka tambayi Imam Khumaini ya fada masu wani malami da zasu dunga komawa gareshi dangane da abubuwan da suka shafi Irfani,sai yace ga Ayatullahi Bahjati.Kuma maraji’ai da dama a lokacin yana raye musamman wadanda suke cikin birnin qum suna qwadaitar da mabiyansu da yin sallah a bayansa,domin yin sallah a bayansa kamar yadda da yawa suke cewa yana gusar da bushewar zuciya.Shi yasa ga wadanda suka san masallacinsa,masallacine wanda in kazo awa daya ko biyu gabanin lokacin sallah to ba zaka samu waje ba a ciki,saboda da yawa kafin lokacin sallar wani zai zo ya zauna,wani kuma ya aje wata alama misali littafi ko jaka a sahun ya tafi harkokinsa sai lokacin sallah yayi yazo.A taqaice dai a wannan zamani namu bayin Allah Arifai wa]anda Allah Ta’ala ya bayyanar ba wadanda suke boye ba, to ba kamar Ayatullahi Bahjati,mutum na iya duba wancan littafi na Tarihinsa da aka ambata a sama mai suna Uswatul-Arifin zai ga haka.Saboda haka bayanan da za a kawo nan na hanyoyin kyautata Alaqa da Imam Mahdi[AS],bayanai ne wadanda suke fito daga wanda yake da Alaqa da Imam Mahdi (AS) Alaqa ta zahiri da badini.Ayatullahi Bahjati ya ce, “Ya hau kan kowane mutum shi qashin kansa yayi tunanin hanyar da zai kyautata alaqa da kuma dangantaka da Imam Mahdi [AS],ko da ko bayyanar Imam Mahdi[AS] tana kusa ne ko nesa. Domin alaqantuwa da Imam Mahdi [AS] wani abune da yake qarqashin zabinmu da kuma ikonmu sabanin bayyanarsa shi a hannun Allah yake.Saboda haka mi yasa bamu damuwa muga cewa mun haqqaqar da wannan alaqa da kuma dangantaka da Imam Mahdi[AS]? Mi yasa muke gafalallu ga wannan maudu’i,kawai abinda ya dame mu bayyanar Imam Mahdi[AS] ko kuma ha]uwa da shi? Tare da sanin cewa idan bamu himmatu ba wajen gyara kawukanmu ba domin mu alaqantu da Imam Mahdi ba,to akwai abun tsoro akan hakan,domin muna iya guje masa in ya bayyana.”Anan Ayatullahi Bahjati yana nuna mana muhimmancin kowannenmu namiji ne ko mace yayi tunanin hanyar kyatata alaqa da Imam Mahdi[AS],domin shi wannan abune wanda in mutum yasa kansa zai iya yiyuwa sabanin bayyanar Imam Mahdi[AS] shi yana hannun Allah Ta’ala ne,saboda haka mufi damuwa da kyautata alaqa da shi fiye da bayyanarsa,domin idan ba haka ba,ko da ya bayyana muna iya barinsa saboda kafin bayyanarsa bamu da kyakkyawar alaqa da shi.

Tabbas akwai Hadisai da suka zo daga Aimma na Ahlul bayt[AS] cewa akwai ‘yan shi’ar da idan Imam Mahdi[AS] ya bayyana zasu yi inkarinsa.wannan abu ko akwai ban tsoro a ciki.A wani waje kuma Ayatullahi Bahjati yana cewa, “Ina bayin Allah wadanda suke da alaqa da Imam Mahdi suka tafi? Mu gashi bamu da irin wannan alaqa,idan kuka ce mu ba zamu iya isa ga Imam Mahdi ba? Amsarku itace to mi yasa ba zaku lizimci ayyukan da’a ba kuma ku nisanci ayyukan zunubi,domin barin ayyukan da’a da kuma aikata ayyukan zunubi sune shamaki da suka shamakance mu daga haduwa da Imam Mahdi.” A wani waje kuma yana cewa, “Kasantuwar bayyanar Imam Mahdi[AS] yana kusa,saboda haka ya wajaba ga kowane mutum ya gyara kansa domin waccan ranar,daga cikin abubuwan da mutum zai soma yi,shine ya tuba daga zunubai.Muna roqon Allah Ta’ala kada mu kasance cikin wadanda suke addu’ar Allah ya gaggauta bayyanar Imam Mahdi da Harsunansu,amma kuma da ayyukansu suna jinkirtar da bayyanarsa.”A wani waje kuma yana cewa, “Duk da cewa Imam Mahdi ya faku daga garemu,saboda haka mun rasa falalar kasancewa da shi,amma ai mun san ayyuka da suka yi muwafaqa da tafarkinsa da kuma ayyuka da suka saba ma tafarkinsa.To shin mun aikata ayyukan da suka yi muwafaqa da tafarkinsa domin mu sa farin ciki a zuciyarsa,ko kuma mun aikata ayyuka da suka saba ma tafarkinsa wadanda zasu sa baqin ciki a zuciyarsa?Allah Ta’ala kadai yasan yadda muke wajen Imam Mahdi.Shine fa wanda ake kai ayyukanmu a wajensa so biyu a mako litinin da Alhamis.Saboda haka mun tabe kuma munyi hasara idan ya zamanto ga qin mutane garemu,kuma Imam Mahdi bai karbe mu ba.”wato nan Ayatullahi Bahjati yana nuna mana muhimmancin mutum yabi koyarwar Aimma na Ahlul bayt[AS] da kuma rayuwarsu sau da qafa,domin ta yin haka ne zamu samu karbuwa a wajensu,in ko ba haka zai kasance mun yi hasara,wato anan duniya mun rayu mutane suna qiyayya da gaba da mu saboda kasantuwarmu ‘yan shi’a.Saboda haka yana da muhimmanci alaqarmu da Aimma na Ahlul bayt ,kada ta taqaita ga iitiqadinmu da matsayinsu da kuma cewa sune khalifofi a bayan Manzon Allah[S] tare da haka kuma ya zamanto muna koyi dasu da kuma bin karantarwarsu dai dai gwargwadon ikonmu.Saboda kamar yadda yazo a wasu ruwayoyi na hadisai cewa dukkan ayyukanmu kyawawa da munana duk ana kai masu,wasu su faranta masu rai wasu kuma su bata masu rai.Akwai lokacin da Imam Sadiq [AS] yake cema mabiyansa,ku dai na munana ma Manzon Allah jin haka duk sai hankalinsu ya ta shi,sai suka tambayi Imam Sadiq yaya zamu munana ma Manzon Allah? sai ya ce masu baku san cewa ayyukan ku ba ana kai ma Manzon Allah wasu ayyukan su faranta masa rai wasu kuma su bata masa rai.Saboda haka yana da muhimmanci mutum shi qashin kansa ya dunga tunani lokaci bayan lokaci ya yake wajen Manzon Allah da kuma Aimma na Ahlul bayt[AS]? Ya kuma Manzon Allah da Aimma na Ahlul bayt[AS] suke a wajensa? Tunani kan ya mutum yake wajen Manzon Allah da Ahlul bayt,mutum zai yi la’akarine da ayyukansa da ake kai masu,idan ayyuka kyawawa ne zasu dunga faranta masu rai,wanda wannan zai zama sanadiyyar su so shi.In kuma ayyukansa da ake kai masu munana ne to zasu dunga bata masu rai,wanda wannan zai zama sanadiyyar su qi shi.Wato dai kamar yadda yazo a wani Hadisi daga Manzon Allah[S] yace; “Wanda na fi so daga cikinku,wanda kuma ya fi kowa kusa da ni gobe qiyama shine wanda ya fiku kyawawan dabi’u.” kowannenmu yana so ya kasance kusa da Manzon Allah da kuma Aimma[AS] ranar qiyama da kuma a cikin gidan Aljanna.To wannan duk ya ta’allaqa ne ga yadda mutum yake wajen Manzon Allah da Aimma[AS] a wannan gida na duniya.Saboda haka idan mutum yana raye a wannan gida na duniya to dama ce babba gareshi na kyautata Alaqarsa da Manzon Allah[S] da kuma imamin zamaninsa wato Imam Mahdi[AS],in ko ba haka ba to mutum na mutuwa shi kenan dama ta kubuce masa.Sai kuma ta fuskacin yaya Manzon Allah[S] da kuma Aimma[AS] suke a wajen mutum? To a nan mutum zai dubi abun ta fuskoki dabam dabam,alal misali yaya saninsa ga Manzon Allah[S] da kuma Aimma[AS],yaya sonsa da shauqinsa ga Manzon Allah[S] da kuma Aimma[AS]? Yaya girmamawarsa da kuma damuwarsa da cutarwar da aka yi ma Manzon Allah da kuma Ahlul baitinsa? Da dai sauran Alaqoqiqalbiyya wato na zuciya,to irin waannan alaqoi na badini wato kamar sonsu girmamasu,shauqinsu……. Da kuma alaqoqi na zahiri kamar koyi da su da kuma dabi’antuwa da dabi’oinsu.To su ake so mutum ya gina kansa akai domin samun alaqantuwa da Imam Mahdi[AS] da kuma sauran Ma’asumin[AS].

                Haka nan daga cikin hanyoyin kyautata alaqa da Imam Mahdi[AS] akwai yin ziyara gareshi.Shaikh Kaf’ami ya ce a cikin littafinsa mai suna Baladul Amin,mustahabbi ne ziyartar Imam Mahdi[AF] a kowane waje a kuma kowane lokaci.Ziyarorin Imam Mahdi [AS] idan mutum ya bibiyi ruwayoyin da suka zo akai,za a iya kasasu gida ukku.Akwai ziyara yaumiyya wato ta kullum,akwai ziyara usbu’iyya wato ta mako,akwai ziyara sanawiyya wato ta shekara.Ziyarar yaumiyya wato ta kullum itace wadda ake yi ga Imam Mahdi[AS] ko wace rana bayan sallar Asuba,idan mutum yana so yaga sigar ziyarar to ya duba littafin Mafatihul jinan fasali na goma,bayan Du’aun Nudba zai ga ziyarar.           

  Ziyara usbu’iyya kuma wato ta kowane mako itace ziyarar da ake yima Imam Mahdi[AS] ko wace ranar Jumma’a,ita ma idan mutum yana so yaga sigar ziyarar ya duba mafatihul jinan fasali na biyar.Ziyara sanawiyya wato ta shekara itace wadda ake yi ga Imam Mahdi[AS] ranar haihuwartsa wato 15 ga watan shaaban.ita ma idan mutum yana so yaga sigogin ziyarar da yake suna da yawa to yana iya duba mafatihul jinan fasali na goma,a fasalin zai ga yasa maqamul Awwal can gaba kuma an sa maqamus sani to a maqamus sani zai ga ziyarorin,ziyara ta farko zai ga ta soma da Salamun Ala ali yasin…..idan mutum ya bibiyi ziyarorin zai ga sun dangana da du’aun nudba.Saboda haka ana so ranar haihuwarsa mutum ya biya wadannan ziyarori na sanawiyya.Sai dai wani tambihi anan shine yana da muhimmanci lokacin da mutum yake bi ya wadannan ziyarori na Imam Mahdi[AS] idan har yana so ya samu tasirin ziyarar a ruhinsa to ya kasance lokacin da yake biyawa zuciyarsa tana halarce ga abun da yake biyawa,wato kada ya kasance yana biya ziyarar amma zuciyarsa tana can wani waje a tunani,domin yin haka zai haifar da zuciya ta gafala ga abun da yake karantwa.

                Daga cikin hanyoyin kyautata alaqa da Imam Mahdi[AS] akwai yi masa addu’a,Akwai ma umarni da yazo daga Imam Ridha[AS] na yi ma Imam Mahdi[AF] addu’a,kai hatta ma sigar addu’ar Imam Ridha[AS]ya bayyana,saboda haka ga mai buqatar ganin addu’ar yana iya duba littafin mafatihul jinan,zai ganta a gaban du’aun nud ba,wato addu’a ta hudu,addu’ar ta soma da Allahumma idfa’a an waliyyika…..in son samu ne duk ranar jumma’a mutum ya dun ga biya wannan addu’a ga Imam Mahdi[AF].Bayan haka kuma ana so mutum ya yawaita addu’ar Allah Ta’ala ya gaggauta bayyanarsa,wato addu’ar Allahumma Ajjil faraja maulana sahibuz zaman.Domin Ayatullahi Bahjati yana cewa da yawa bayin Allah da suka ga Imam Mahdi[AF] a mafarki ko a falke,daga cikin abunda ya kance shine; “Ku yawaita addu’ar Allah Ta’ala ya gaggautar da bayyanata.”Akwai kuma wata addu’a ga Imam Mahdi[AF] wadda ake son biyata bayan ko wace sallah ta wajibi.Addu’ar tana farawa da “Allahumma kun li waliyyikal Hujjatu Bn Hassan…….”

                Daga cikin hanyoyin kyautata alaqa da Imam Mahdi[AS]Akwai Hadiyya gare shi wato mutum yayi wani aiki na Ibada ko alhairi da niyyar Allah Ta’ala ya kai ladar gareshi.misali mutum yayi wata kyauta da niyyar ladar taje ga Imam Mahdi[AS]ko kuma kamar loncin da ake yi wani lokaci,to sai mutum yayi loncin din da niyyar yinsa gare shi.Akwai ma wata sallah ta nafila da ake ce ma Salatul-Hadiyya,ana yinta ga Manzon Allah ne[S] da kuma Ahlul bayt[AS]yana da kyau da kuma muhimman ci mutum ya dun ga yin sallar ko wace rana gare su.Sallar da kuma bayanin yadda ake yinta mutum na iya duba mafatihul jinan sashen Baqiyatus-salihat babi na biyu.Domin aikata ire-ire wadannan ayyuka na ibada da kuma da’a da niyyar Allah Ta’ala ya kai ladar gare shi zai faranta masa rai,tun da duk ayyukan da muke aikatawa ana kai su gare shi.

            Daga cikin hanyoyin kyautata alaqa da Imam Mahdi[AS] Akwai Tawassuli da kuma Istigasa da shi ga dukkan matsaloli da kuma al’amuran mutum na yau da kullum.Yana da kyau mutum ya sa ba ma kansa da haka.Domin yin haka zai taimaka ma mutum wajen samun alaqa qalbiyya wato ta zuciya da shi.

            Daga cikin hanyoyin kyautata alaqa da Imam Mahdi akwai yin Bai’a gare shi,yama zo akan cewa mustahabbi ne yin haka ko wace rana,ko mako musamman ma ko wace ranar jumma’a idan mutum ba zai iya yi ko wace rana ba,domin yin haka yana da falala babba.Sigar Bai’a din itace wadda tazo a wata addu’a da ake ce ma Du’aul-Ahad, tana nan cikin mafatihul jinan gaban Du’aun Nudba,Akwai ruwaya ma da tazo daga Imam Sadiq [AS] cewa ; “Duk wanda ya bi ya wannan addu’a ta Ahad,kwana 40 bayan asuba,to zai kasance cikin mataimakan Imam Mahdi,in ko ya mutu gabanin bayyanarsa to Allah zai fito da shi daga cikin kabarinsa[wato Raja’a] Haka nan ko wace kalma daya karanta ta a addu’ar za a ba shi lada dubu a kuma goge masa zunubi dubu.”Saboda haka yana da muhimmanci ga kowannen mu ya samu kwanaki 40 yana biya wannan addu’a ta bai’a ga Imam Mahdi[Af] domin samun wannan falala da kuma samun kasancewa cikin mataimakan Imam Mahdi[AS]mataimakan Imam Mahdi[AS] sun kasu ka shi biyu,Akwai mataimaka na khassa wato sune 313 nan.Akwai kuma mataimaka na Amma wato sune sauran bayin Allah da yayi masu muwafakar kasancewa tare da Imam Mahdi[AS] da kuma taimaka masa idan ya bayyana.

                Daga cikin hanyoyin kyautata alaka da Imam Mahdi[AS] akwai kiyaye munasabar haihuwarsa da kuma sauran munasabobi na wilada da wafatin Ma’asumin[AS] wato Manzon Allah[S] da kuma Ahlul bayt[as]Domin yin haka A matsayi na dai-daiku ko jama’a yana daga cikin raya al-amarin Ahlul bait,yama zo daga Imam Sadiq yace; “Allah Ta’ala yayi rahama ga wanda ya rayar da al’amarinmu.” A wani hadisi kuma yace; “Allah Ta’ala yayi rahama ga bawan da ya sanya soyayyarmu a zukatan mutane.”Saboda haka yana da gayar muhimmanci duk lokacin da wilada[Haihuwa] ko wafati[rasuwa] na wani daga cikin Ma’asumin[AS] ya zaga yo a kowane wata misali wiladar Imam Ali[AS] ko kuma shahadarsa,to a ranar misali bayan sallar Asuba sai mutum yayi sallama ga Imam Mahdi[Af] kamar yace; Assalamu Alaika ya sayyidi ya maulaya-ya sahibuz zaman,Ya shugabana ina taya ka murnar zagayowar wannan rana ta haihuwar Imam Ali[AS] in kuma wafatinsa ne sai yace bayan wannan sallama da zagayowar wannan rana ta shahadar Imam Ali[AS]mutum sai ya kammala yin wannan sallama da mika ta’aziyya ko murna ga Imam Mahdi[AS] da neman yayi maka addu’a,kan wata bukata taka ko kan neman tsari da wani abu.wato dai mutum ya mi}a bu}atar wannan addu’a daga wajensa da shu’urin kamar kana ganinsa kuma yana jinka.In mutum ya lizimci yin haka ga duk wata munasaba ta wilada ko wafatin wani daga cikin Ma’asumai to tabbas zai dun ga jin tasirin hakan a Ruhinsa.

            Daga qarshe akwai wata Addu’a wadda ake ce ma Du’aul Ahad wadda aka ruwaito daga Imam Sadiq ana son karanta aqalla na kwanaki 40 wato kowace rana in san samu ne mutum ya karanta ta bayan Saalar Asuba.in kuma haka bai samu to a cikin yinin dai ya karanta sau daya,Imam Sadiq yace duk wanda ya karanta tan a tsawon kwana Arba’in to zai kasance cikin wadanda zasu tai maka ma Imam Mahdi kuma Allah zai bashi ladar kowace kalma lada dubu kuma za a kankare masa zunubi dubu.Ga mai son ganin Addu’ar yana duba cikin littafin mafatihul-jinan tana nan gaban Du’aun Nudba bayan wata ziyara to sai ita,itace ta ukku.Imam Khumaini ya kasance yana yawan kwadaitar da mabiyansa kan biya wannan Addu’a,saboda in mutum bai taba yin taba to ya dage yayi ta a wannan lokaci na tsawon kwanaki 40 din in kuma ya taba to zai iya sake maimaitawa domin haka Imam Khumaini yake yi in ya kai kwanaki 40 sai kuma ya sake maimatawa har ya koma ga Allah Ta’ala aka haka yake saboda bayan rasuwarsa da aka dauki mafatihunsa aka bude sai aka ga har yasa alama ranar da ya faro biyawar 8 ga watan Shawwal shi kuma ya rasu 28 ga watan Shawwal. Muna roqon Allah Ta’ala ya dada tsare mu daga wannan Annoba da dukkan ‘yan uwanmu muminai da suke doron qasa ya kuma yaye ma wannan Alumma ta Manzon Allah wannan Annoba ya jefa ta ga maqiyansa da kuma maqiyan Musulunci da Musulmi.

 
Home Maudu'oi daban-daban Kusantowar bayyanar Imam Mahdi (AS)
Copyright © 2022. www.tambihin.net. Designed by KH