Thursday, 19 September 2024
Email
Make My Homepage
RSS
Register
Bayani Kan Aure (1) Print E-mail
Written by administrator   
Tuesday, 05 May 2020 15:59

A darasin da ya gabata a wannan fili na fiqhu an kammala bayanine kan ibadodi. Alhamdu lillah an tabo babobi dabam dabam a wannan sashe misali babin tsarki, Alwala, Taimama, wankan janaba, jinin al’ada na mata kamar-jinin Haila, nifasi, da istihadha. A babin Sallah an kawo bayani dangane shakka a cikin sallah, sujudar sahawi, sallar matafiyi, sallar mamaci, sallar idi, sallal Jumma’a, sallar khusufin wata da kuma rana, Sallar jama’a-jam’i-da kuma bayani kan ayyukan salla. A babin Azumi shima an kawo darussa dabam dabam a cikinsa, haka ma a cikin babi Zakka da Hajji suma an kawo darussa dabam dabam a cikinsu, ga mai buqatar ganin wadannan Darussa baki dayansu yana iya komawa ga shafin wannan fili a internet wato www.tambihi.net wanda a cikinsa zai ga baya ga wannan darasi na fiqhu akwai darasi na Aklaq, Tarihi da dai sauransu.’Yan uwa lokaci bayan lokaci sukan bugo su ce mi zai hana a maida wadannan rubuce rubuce da ake gabatarwa a wannan fili na tambihi zuwa littafi ko littafai misali Fiqhu ayi mashi littafi , Aklaq shima ayi nashi dabam, Munasabobi suma nasu dabam, Tarin Manzon Allah [SAAW] da kuma Aimma na Ahlul bayt [AS] suma nasu dabam da dai sauran darussa da aka gabatar a wannan fili a tsawon shekarun da suka gabata, tabbas Malam Turi shima ya taba yin Magana akan haka na cewa zai yi kyau in tattara wadannan rubuce rubuce a maida su littafi to kasantuwar yadda lokaci ya tsawaita kuma wasu darussan mun jima da kammala su alal misali darussan munasabobi mun kammala shi da jimawa wato an kawo muna sabobi tun daga watan Muharram har ya zuwa watanZul-hijja, haka nan a fagen Tarihi an kawo Tarihi da kuma Darussa daga Rayuwar Man zon Allah da kuma Imamai 12 daya bayan daya tun daga Imam Ali [AS] har ya zuwa Imam Mahdi [AF] dai dai gwargwadon iko, haka nan wannan darasi na Fiqhu gashi an kammala sashen ibadodi daidai gawgwadon iko wanda shima za a iya buga shi a matsayin littafi akan asasin haka ni ta bangarena nike ganin idan akwai wani dan uwa ko wasu ‘yanuwa da zasu iya daukar dawainiyar buga wadannan littafai ko wani daga cikinsu to ana maraba da haka sai a bugo domin fara aikin. ko a fannin Tarihi baya ga na Maasumai da aka ambata,akwai rubutu da nayi na Tarihin 1-Shehu Usman dan Fodiyo. 2-Imam Khumaini. 3-Sayyid Ibrahim Zakzaky .shi wannan Alhamdullahi an samu an buga shi wanda a cikinsa an kawo tarim Malam da kuma wannan Harka daidai gwargwadon iko, suma na Shehu Usman da Imam Khumaini in an samu wadanda zasu dauki dawainiya bugawa saboda yin musharaka ga ladar aikin shima ana maraba da yin haka. Dawowa ga wannan darasi da muke ciki to yanzu insha-Allah zamu shiga sashen Muamalat ne a wannan darasi na fiqhu wanda kuma babin da zamu fara a cikinsa shine babin Aure yana da fasaloli masu yawa, ga wasu daga cikin fasalolin da za a gabatar a cikinsa:

1-Ma’ana da Falalar Aure.

2-Siffofin maaurata.

3-Aqadin Aure.

4-Walimar Aure.

5-Dhukulin Aure.

6-Zamantakewa ta Aure.

7-Haqqoqin ma’aurata.

8-Dalaq-saki

9-Khul’i: Wani nau’i na saki idan ya kasance mata ce bata son mijinta kuma tana so ya sake ta to anan Shari’a taba da damar ayi abinda ake ce ma khul’i wato zata fanshi kanta ta hanyar biyan wasu kudade ga mijin domin yayi wani Auren, bayani sanka-sanka zai zo akansa in mun kawo wajen.

10-Idda.

11-Kome a Aure.

12-Ila’i: Shine mutum ya rantse ba zai taki matarsa ba har abada ko wani mudda mai tsawo fiye da wata hudu, hukunce-hukunce-hukunce sanka sanka zai zo nan gaba insha Allah.

13-Nafaqa.

14-Haihuwa.

15-Asbabu -Tahrim. Babi ne da zai yi bayanin wadanda ya haramta mutum ya Aura.

16-Rabe-aben Aure.

17-Li’an: Shi ana yin sane idan mutum wal’iyazu billahi yana tuhumar matarsa da zina ko kuma kore abinda aka haifa masa misali ya ce ba dansa bane ko ba ‘yar bane shima bayanisa sanka-sanka zai zo idan an zo wajen..

18-Raban gado na maurata wato idan dayansu ya rasu miji ko mata yadda rabon gadonsu yake, shima sai an zo wajen insha Allah .

19-Rabon kwana ga wa]anda suke da mace fiye da daya to hukunce hukencen rabon kwanansu..

20-lokutan kusantar iyali. Da yake akwai wasu darare makruhine mutum ya sadu da iyalinsa a ciki misali daren da aka yi khusufin wata ko daren farko da daren 15 da kuma daren qarshe na kowane watan Musulunci, makruhine saduwa da iyali a wadannan darare daka ambata, bayani sanka sanka zai zo akai idan mun zo wajen. A taqaice wadannan wasu kenan daga cikin fasaloloi da za a yi bayani kenan gwargwadon iko kafin muje ga wani babi na Muamala qila na ciniki insha Allah.Yanzu zamu fara binsu daya bayan daya.

          1-Maana da kuma muhimmancin Aure: Kalmar Aure a larabci tana da maana guda biyu,maana a lugacce da kuma maana a isdilahance wato a fanni na fiqhu. Maana Nikah a lugacce yana nufin hada abu ko tara abu amma a isdilahin fiqhu yana nufin qullin auratayya tsakanin namiji da mace akan asasin sharuddan da addinin Musulunci ya shinfida. Idan muka juya ga daya bangaren wato Falalar Aure shima zamu ga cewa akwai hadisai masu yawa da aka ruwaito daga Manzon Allah [SAAW] da kuma Aimma na Ahlul bayt [AS] da ke nuna muhimmancinsa da kuma falalarsa, ga wasu daga cikin Hadisai: 1-Manzon Allah [SAAW] Ya ce, “Babu wani gini da aka yi a cikin Musulunci mafi soyuwa zuwa ga Allah kamar Aure.”2-Imam Sadik[AS] ya ce, “Raka’a biyu da mai Aure zai yi tafi raka’a saba’in da marar Aure zai yi.”3-Manzon Allah [SAAW] ya ce, “Wanda yayi Aure haqiqa ya cika rabin Addininsa saboda haka yaji tsoron Allah a sauran rabin.”4-Manzon Allah [SAAW] ya ce, “ Kuyi Aure domin Aure yana daga cikin sunna ta.5-Manzon Allah (SAAW) ya ce ma wani saurayi. “Ya kai saurayi kayi Aure kashedinka da yin Zina domin yinta zai cire imani daga cikin zuciyarka.”6- Imam Ali[AS] Ya ce, “Yin Aure sunna ce daga cikin sunnonin Manzon Allah wanda ya bar shi to ya rabar sunnar Manzon Allah.”7-A wani Hadisi Manzon Allah [SAAW] ya ce, “Yaku taron samari duk wanda ya samu ikon yin Aure daga cikinku to ya yi Aure domin shine mafi kiyayewa ga ganinku da kuma Al-aurarku.” Da dai sauran Hadisai masu yawa akan haka, akwai ma wani Hadisi da aka ruwaito daga Manzon Allah [SAAW] Ya ce, “Duk wanda ya bar yin Aure saboda gudun talauci to haqiqa ya munana zato ga Allah Ta’ala.”A wani Hadisi Manzon Allah [SAAW] Ya ce, “Mafi yawan ‘yan wuta gwarayene.” Wato wa]anda basu da Aure,a wani Hadisin kuma Manzon Allah [SAAW] Ya ce, “qasqantun matattunku sune gwaraye.” In mutum ya duba cikin littafin Tariril wasila na Imam Khumaini zai ga ya kawo wasu daga cikin wadannan Hadisai da aka kawo har da wannan mai cewa mafi yawan ‘yan wuta……

2-Siffofin Maaurata: Wato siffar wadda ya kamata namiji ya Aura ko mace ta Aura,idan mutum yayi bincike zai ga akwai Hadisai masu yawa da aka ruwaito akan siffofin matar da mutu ya kamata ya Aura, misali ga wasu daga cikin wa]annan Hadisai:1-Manzon Allah [SAAW] Ya ce, “Ana Auren mace saboda abu hudu saboda dukiyarta ko matsayinta ko kyawunta ko saboda riqo da Addininta, cikon Hadisin sai Manzon Allah ya ce, ka fifita maabuciyar addini wato a cikin wadannnan siffofi ka zabi wadda take riqo da Addini. 2-Manzon Allah[SAAW] Ya ce, “Duk wanda ya auri mace saboda dukiyarta ko kyawunta to ba zai samu dukiyarta ba ko kyawun nata amma wanda ya Aure ta saboda Addininta to Allah zai Azurta masa dukiyarta da kuma kyawunta.”Daga cikin siffofin da ake so mutum ya lura dasu shine ta kasance mai kamun kai ,mai kyakkyawan hali da dai sauransu, to haka nan ita ma mace ta zama ta muhimmantar da maabucin Addini,mai kamun kai,mai kyakkyawan dabi’a da dai sauransu,kiyaye wannan asasi ko rashin kiyayewa to yana iya tasiri ga ‘ya’yan da za a haifa bayan Auren.

3-Aqadin Aure: Wato daura Aure zai iya kasancewa ta fuskoki ko hanyoyi guda hudu: 1-Ta hanyar waliyyai misali mahaifin Ango da mahaifin Amarya. 2-Ta hanyar wakilai wato wakilin Ango da wakilin Amarya. 3-Ta hanyar waliyyi da wakili ko waliyyi da Ango misali mahaifin Amarya da wakilin Ango. 4-Ta hanyar maauratan kai tsaye tsakaninisu wato Ango da Amarya su daura ma kansu Aure,ta yiyu wani abin ya bashi mamaki ko ya kawo ish-kal cewa to ina shaidu,idan mutum ya duba littafin Fiqhu ala- mazahibil-khamsa zai ga cewa dangane da kafa shaidu na daurin Aure ga abinda ya ce, Mazhabar Shafi-iyya, Hanafiyya da Hanbaliyya sun tafi akan cewa daurin Aure bai qulluwa sai da shaidu amma a Malikiyya ba wajibi bane.A Imamiyya mustahabbi ne kafa shaidu ba wajibi ba wato lokacin daura Aure amma a saki kafa shaidu wajibi ne bayaninsa zai zo nan gaba insha Allah fasali na saki idan anzo.Saboda haka A mazhabar Malikiyya da Imamiyya kafa shaidu a lokacin daurin Aure ba wajibi bane mustahabbi ne akan wannan asasi da maaurata zasu daura ma kansu Aure yayi sai dai sun rasa ladar mustahabbi na rashin kafa shaidu amma a sauran mazhabobi kamar Hambaliyya da Shafi’iyya bai yi ba. A wannan fasali na Aqadi ababe 5 za a dan yi bayani akansu yadda ya sawwaqa saboda gudun tsawaitawa sune: A-Siga. B-Sadaki. C-Sharuddan masu daurin Aure. D-Hukuncin sharadin da aka yi lokacin Aure. E-Lokacin da ya dace a daura Aure. Insha Allah a darasi na gaba za a yi bayani kan wadannan ababe da aka ambata.

         

         

 
Home Darusan Fiqh Bayani Kan Aure (1)
Copyright © 2024. www.tambihin.net. Designed by KH