Dabi’oin Imam Ridha (AS) |
![]() |
![]() |
Written by administrator | |||
Tuesday, 05 May 2020 15:15 | |||
Kasantuwar wannan wata da muke ciki na Zul –Qada a cikinsa ne wilada da kuma wafatin Imam Ali ibn Musa Ar-Ridah [AS] suka kasance, domin yazo a tarihi cewa an haife shi ranar Alhamis 11 ga watan zulqada a shekara ta 148 bayan hijira. Ya rasu 23 ga watan zulqada shekara ta 203 bayan hijira. Amma a wata ruwaya,yazo a kan cewa rasuwarsa ta kasance a watan safar ne. Shaikh Abbas Al-qummiy ya tafi akan 23 ga watan zulqada, kamar yadda ya kawo a littafinsa na mafatihul Jinan. Har ya ci gaba da cewa sunna ne ziyarar Imam Ridha [AS] a ranar daga kusa ko kuma nesa. In mutum ya duba littafin mafatihul jinan zai ga ya kawo ziyarori dabam-dabam na Imam Ridha. In mutum zai iya biya suduka a ranar yana da kyau, ko kuma ya karanta abinda ya sauqaqa masa na ziyarar. Haka nan in aka duba za a ga cewa tsakanin haihuwar Imam Ridha [AS] da rasuwar Imam Sadiq [AS] Kusan kwanaki 15 ne. Domin wafatin Imam Sadiq [AS] a watan shawwal ne 25 gare shi, shekara ta 148, shi kuma wiladarsa 11 ga watan zulqada shekara ta 148. Ya mazo a kan cewa Imam Sadiq [AS] yayi fata da shauqinhaduwa da Imam Ridha [AS] domin ya gan shi, har ambatonsa yayi da kalmar MALAM, tun gabanin a haife shi, kamar yadda zamu ga haka in sha Allah dangane da bayani na ilminsa. Imam Ridha [AS] kamar yaddaaka sani shine Imam na takwas a jerin Imamai 12, an haife shine a Madina, sunan mahaifiyarsa,Dahira, sunanmahaifinsa kamar yaddaaka sani Imam Kazim [AS] kuma yana da laqubba da yawa, amma wanda yafi shahara shine wannan laqabin nasa na Arri-dha. An tambayi Imam Jawad [AS] cewa mi yasaake cewa babanka Arri-dha, ya ba da amsa da cewa; Saboda maqiyansa sun yarda da shi, kamar yadda masoyansa suka yarda dashi. Ya ce haka bai kasance ga Imamai da suka gaba ce shi ba.Shekarunsa a duniya 55, muddan shekarun Imamancinsa 20, wato ya na da shekaru 35 a duniya Imamanci ya dawo gare shi. kabarinsa yana a khurasan ne,wato a qasar Iran. Kuma yaro daya yake da shi shine, Imam Jawad [AS] idan mutum ya bincika zai ga cewa Imam Ridha [AS] shine mafi qarancin’ya’ya, idan an kwatanta da Imaman da suka gabace shi da kuma wadanda suka biyo bayansa, in ka cire Imam Hasan Al-askari [AS] da yake yazo akan cewa shima yaro daya yake dashi, shine Imam Mahdi [AF]. Bayan haka insha Allah za’a kawo wasu darussa daga rayuwar Imam Ridah[AS] da nufin ya zama madubin da zamu dubi kawukanmu dashi da kuma yin sa’ayi da kuma mujahada wajen ganin mun aikata su, domin su amfane mu duniyarmu da kuma lahirarmu. 1.IBADARSA: Imam Ridah[AS] ya kasance mai yawan ibadah,domin a zamaninsa babu wanda ya kai shi yawan ibadah,ga misalan wasu daga cikin ibadodinsa. A.SALLOLINSA: Imam Ridah ya kasance mai yawan sallah,yazo a tarihinsa cewa ko wane dare ya kan yi salla ta nafila raka’a dubu,wato yana daya daga cikin Imamai guda hudu wanda a tarihin rayuwarsu yazo akan cewa kowane rana suna salla raka’a dubu ta nafila.Wadannan Imaman kuwa sune, Imam Ali[AS],Imam Husain[AS],Imam Zainul Abidin[AS],da kuma Imam Ridah[AS].Ya ma taba ba wani daga cikin mabiyansa rigar sa,Imam Ridah yace masa, “ka kiyaye wannan rigar domin na yi sallah dare dubu da ita,ko wane dare raka’a dubu,kuma na sauke Alkur’ani sauka dubu da ita”.Mu duba wannan yawan ibada, mu kuma kwatanta da kawukanmu mu ga gibin dake tsakani.Haka nan yazo a tarihinsa cewa da daddare kadan yake bacci,mafi yawan darensa yakan raya da ibadodine,wasu dararen ma, baki dayansu yakan raya sune.An tambayi daya daga cikin matayensa dangane da ibadarsa,tace ya kasance idan yayi sallar Asuba,yakan sallace ta a farkon lokacinta,ya kan yi ta’aqibat na Azkar bayan sallah, bayan haka yayi sujuda ba zai dago kai ba har sai rana ta keto.Akwai ma wani da ya taba ganinsa bayan ya gama sallah,sai yaga yayi sujuda,sai yaji yana tasbihi,sai shi wannan mutumi ya shiga lissafa tasbihin, sai da ya lissafa guda 500,saannan yaga ya dago daga sujudar. B-KARATUN –ALKUR’ANI-Imam Ridha ya kasance mai yawan karatun qur’ani,domin yazo a tarihinsa cewa ya kan sauke shi a duk kwana ukku.Harma ya kance;Da ina so in sauke qasa da kwana ukku da na sauke,amma ina karatunsa ne,duk ayar da na biya na kan yi tunani a kan me ta sauka?kuma yaushe ta sauka?Saboda haka nake sauke shi kwana ukku.’’Kuma yazo a tarinsa cewa,zantukansa baki daya da kuma amsoshin tambayoyi da aka yi masa,ya kan bada su, da Ayoyin Alkur’ani ne.Wato shigen qissar wata bai war Allah, mai suna FIDDHA,ta kasance tana yiwa Sayyida Fadimahidima ne,To yazo a tarihinta ta shekara 30 bata yi magana da wani abu ba face ayoyin Ayoyin Alkur’ani.Misali ko abu take so sai ta fade shi da wata aya da tayi kama dashi domin a fahinta.A taqaice dai Imam Ridhaya kasance mai yawan karatun Alkur’ani.Mu duba abinda aka ambata a sama na rigar daya ba, daya daga cikin sahabbansa,yace masa ya sauke Alkur’ani da ita sauka dubu. C.AZUMINSA: Imam Ridah ya kasance mai yawan azumi,kuma azumi na kowane wata basu kubuce masa,wato ya kasance yana lizimtarsu, a zumin shahariyya wato wata-wata Sune Alhamis din farko na ko wane wata da kuma Alhamis din qarshe da kuma larabar farko ta goman tsakiya,ya kance duk wanda ya lizimci wannan azumin,to kamar yana azumin kullum ne.Kuma yazo a tarihinsa cewa in yayi azumi baya bude baki sai yayi sallah. D.ADDU’O’IN SA:Imam Ridah ya kasance mai yawan addu’oi,akwaiadduoi da yawa wanda aka ruwaito daga wajensa.Mai buqatar wadannan addu’oi yana iya samun littafin addu’a mai suna SAHIFATUR -RIDHA,wanda wani malami mai suna shaikh Jawadqayyumiy, ya rubuta.Ana samun sahifa din. Sai dai wani tambihi muhimmi anan shineakwai wata addu’a da aka samo daga Imam Rida wanda yayi umarni da a din ga biyawa, ga Sahibul-AmrwatoImam mahdi[AF], Saboda haka ya na da muhimmanci ga kowannenmu ya lizimci biya addu’ar aqalla ko wace juma’a,addu’ar akwai ta cikin littafin littafin Mafatihul jinan,mutum ya duba ta gaban Dua’ul Nudba,to addu’a ta qarshen fasalin,to itace,zai ga ta soma da “Allahumma idfa’a, an waliyyika wa khalifatuka…….. E.AZKAR DIN SA:Imam Ridah ya kasance mai yawan Azkar,ya mazo a tarihinsa cewa idan yayi sallar Asuba yakan zauna yayi azkar,wato tasbihi da tahmidi da takbiri da tahlili(Subhanallah -walhamdulillah wala ilaha illallah -wallahu akbar) da kuma salati ga Manzon Allah da Alayensa,ya kan yi haka har rana ta keto.Wani tambihi anan shine idan mutum yayi sallar Asuba yana da gayar muhimmanci ya kasance bai koma bacci ba har sai rana ta keto,domin sunna ce ta Manzon Allah da kuma Ahlulbayt .Kuma akwai hadisai masu yawa da suka zo da bayani dangane da falalar da ke tsakanin ketowar Alfijir zuwa ketowar rana,da kuma kashedi dayin barci tsakaninsu.Alal misali ga wasu daga cikin hadisan.An samo daga Imam Baqir yace, “Allah Ta’ala yana raba arziki tsakanin ketowar Alfijir zuwa ketowar rana,saboda haka kashedinku da yin barci tsakaninsu”.Haka nan an samo daga Imam Rida dangane da tafsirin wannan ayar “Fal muqassimati Amra”.yace, “Mala’iku suna raba arzikin ‘yan Adam tsakanin ketowar Alfijir zuwa ketowar rana,duk wanda yayi barci tsakaninsu,to yayi barci daga arzikin sa”.Wato ba zai zamo daga cikin wadanda za’a raba wa arziki na ranar ba..Har ila yau an samo Hadisi daga wajen Imam Baqir yace, “Iblis la’antar Allah ta tabbata gareshi yakan watsa rundunarsa lokacin ketowar rana da kuma lokacin faduwarta.Saboda haka ku yawaita Azkar da ambaton Allah a wadannan lokuta guda biyu,kuma ku nemi tsarewar Allah daga iblis da rundunarsa,kuma ku nemi tsari ga yaranku a wadannan lokuta guda biyuwatau safe da kuma yamma daga sharrori na zahiri da kuma badini.Imam Baqir ya qarasa hadisin da cewa domin wadannan lokuta guda biyu lokaci ne na gafala. Haka nan yazo akan cewa Manzon Allah idan yayi sallar Asuba yakan zauna inda yayi sallar yana Azkar har rana ta fito,Akwai ma hadisin da Manzon Allah yake cewa “In zauna a In da nayi sallar Asuba, ina Azkar har zuwa hudowar rana,yafi soyuwa gare ni akan in ‘yanta bayi guda hudu”. An samo dag Imam Hasan yace, “Naji Babana,Ali dan Abi dalib yana cewa,Manzon Allahyace, “Duk mutumin daya zauna,a in da yayi sallar Asuba yana Azkar har rana ta fito,to yana da lada kamar wanda yayi aikin hajji,kuma Allah zai gafarta masa zunuban daya gabatar”. Haka nan daga Imam Ali yace, “ wanda yayi sallar Asuba ya zauna in da yayi sallar, har rana ta keto,to wannan zai kasance hijabi tsakaninsa da wuta”.A taqaice dai akwai hadisai masu yawa da suka zo akan haka,shi yasa fuqaha suka tafi akan cewa makaruhi ne yin barci tsakanin ketowar Alfijir zuwa ketowar rana,ana so mutum ya raya tsakaninsu da ibadodikamar Azkar,karatun Alkur’ani,adduo’i, da dai makamantansu,haka nan idan rana ta fito mustahabbi ne kafin ya tashi daga wajen yayi nafila raka’a biyu,wato salatul Ishraq wato sallar fitowar rana,itama akwai hadisi akan haka wanda aka ruwaito daga Imam Hasan.Da fatan za’a kiyaye wannan tambihi domin samun falalar dake cikin lokacin. 2-AKHLAQ DINSA:Imam Ridha a wannan fage na Aklaq, a zamaninsa ba wanda ya kai shi ballantana ya wuce shi,ga misalan wasu daga cikin Aklaq dinsa. A.TAWALIU’NSA: ImamRidhaya kasance mai gayar tawali’u,saboda ma yawan tawaliu’nsa,yazo a tarihinsa cewa mafi yawan lokuta shi yake yima kan sa hidima.Haka nan idan yayi baqi da kansa ya ke yi masu hidima.Akwai lokacin da yayi baqo,sun zauna suna tattaunawa,fitilar dake wajen sai ta dan canza,wato haskenta ya ragu,da yake da daddare ne,to sai shi wannan baqo yayi nufin ya gyara fitilar,sai Imam Ridha ya tashi da kansa ya gyara fitilar.Sai yake cewa ba}on ; “Mu mutane ne wadanda ba musa baqinmu hidima.’’ Daga cikin tawali’unsa,yazo akan cewa wani lokaci ko abinci zai ci yakan kira bayinsa domin suci tare.Shine wani daga cikin sahabbansa da ya ga haka,sai yace wa Imam Ridah “in zamo fansa gare ka,wadannan ai da an zuba masu nasu daban su koma gefe suci.” Da yake yawancin bayin nasa launin jikinsu baqi ne,wato baqar fata, kamar yadda yazo a ruwayar,sai Imam Rida ya bashi amsa da cewa, “Ai asasi ubangiji daya ne,uwa daya,uba daya.sakamako akan asasin aiki ne” wato ba’a launi ba.Haka nan daga cikin tawali’unsa,yazo a tarihinsa cewa wani lokaci ko da, daya daga cikin bayinsa ya kira domin yasa shi wani aiki,to idan bawan na cin abinci ne,yakan ce yaje ya gama sannan yazo. B.KYAUTARSA:Imam Ridahya kasance mai yawan kyauta da kuma sadaka.Saboda ma gayar kyautarsa,da kuma sadakarsa,akwai wani da yayi zamani dashi,yake cewa “Duk wani wanda ku kaji yana riya cewa yaga wanda ya kai Imam Ridah kyauta da kuma sadaka,to kada ku gaskata shi.yazo a tarihinsa cewa a lokacin yana khurasan, yaba da baki ]ayan abinda ya mallaka ga matalauta.Haka nan ya kasance idan aka kai masa abinci,to kafin ya fara ci, yakan ce a kawo masa kwano,sai ya debi abincin yasa a kwanon,sai yace akai ma miskinai.Haka nan daga cikin kyautarsa yazo akan cewa yakan sai, bayi ba don kome ba,sai don kawai ya ‘yanta su daga bauta.A kan asasin haka yazo akan cewa sai da ya’yanta bayi dubu. Akwai qissar wani da yazo aikin Hajji,sai kudinsa suka qare,ya zamanto abin da zai mai da shi Madina ba shi dasu,sai ya samu Imam Ridah ya shaida masa halin da yake ciki.Don haka yana roqonsa ya taimaka masa da abinda zai koma garinsu,alabashi in ya koma yayi sadaka da abinda ya taimaka masa din.Sai Imam Ridah yace ya zauna,ya shiga gida ya dauko kudi dirhami dari biyu ya bashi,yace masa gashi yayi guzuri da shi da kuma biyan buqatunsa.In ya koma garinsu ba sai yayi sadakar ba, da abinda yaba shi,da ma lokacin da wannan mutumin yazo, Imam Ridah yana tare da wani sahabinsa mai suna Sulaimanil ja’afari,shine sai yace ma Imam Ridah “In zamo fansa gareka,haqiqa ka kyautata ma wannan mutumin, amma naga da zaka bashi ka suturta fuskarka,me yasa haka?” Da yake kamar yadda yazo a qissar, da Imam Ridah ya shiga gida da ya dauko kudin da zai miqa masa,sai ya miqo hannunsa ta qofa ya bashi,shine wannan sahabin sa yake tambaya akai.Sai Imam Ridah yace “Nayi haka ne saboda gudun kada in ga qasqancin tambaya a fuskarsa,domin na biya masa buqata.Ba kaji hadisin Manzon Allah da yake cewa ba,mai boye kyawawan aiki ya nada lada kamar wanda yayi Hajji saba’in”.Da dai misalai da yawa na irin kyautar Imam Ridah saboda gudun tsawaitawa ba za’a iya kawo suba. C.AFUWARSA:Imam Ridah ya kasance mai yawan afuwa ga wadanda suka zalunce shi ko kuma suka yi masa abin da bai dace ba,akwai wanda yayi masa abinda bai dace ba,shi da iyalansa,amma da Imam Ridah ya samu sulda wato iko akansa sai yayi masa afuwa.A taqaice dai kyawawan dabi’u, a zamaninsa babu wanda yakai shi,kamar yadda wani wanda yayi zamani dashi mai suna Ibrahim dan Abbas ya tabbatar.Yake cewa ni ban taba gani ko jin wanda yakai Imam Ridahkyawawan dabi’u ba, ban taba ganin wani mutum ya kawo masa wata buqata, a wajensa bai biya masa ba.Kuma ban taba ganin yana qyal-qyatar dariya ba,dariyarsa itace murmushi,da dai sauran Akhlaq na Imam Ridah da ya jero. 3.ILIMINSA:A wannan fage na ilimi, shima a zamaninsa baki daya ba wanda ya kai shi,kamar yadda wani da yayi zamani da shi yake cewa, “Ban taba ganin wanda ya kai Ali bn Musa Ridah ilimi ba,kuma duk malamin da ya gan shi sai yayi masa wannnan shaida,irin shaidar da na yi mashi”.Akwai ma lokacin da khalifan Abbasawa a lokacin mai suna Ma’amun, ya tara malamai na fannoni ilimi daban daban da malaman yahudawa da kuma nasara, akan suyi muqabala da Imam Ridah ,baki dayansu daga qarshe kowannensu sai da ya tabbatar da fifikon ilimin Imam Rida akansa.kuma irin wannan majlisi,shi Ma’amun din ya sha shirya yin hakawatau ita muqabalar a lokuta daban daban. Akwai ma lokacin da Imam Ridah yake cewa, “Na kasance na kan zauna a rauda a cikin massallacin Manzon Allah, Malaman Madina masu yawa(da suke karantarwa amassallancin)idan dayansu wata matsala ta shige masu duhu ko kuma bai sani ba,sai suyi ishara zuwa gareni da a zo a tambayeni,ni kuma sai in basu amsa.’’Haka nan Imam Kazim ya kance ma ‘ya’yansa “Wannan dan uwan naku Ali, Malami ne na Ahlul baitiku tambaye shi dangane da mas’alolin addininku,Abinda ya fada maku to ku kiyaye,domin na ji babana, Ja’afar dan Muhammadba sau daya ba, ba sau biyu ba,yana ce mani lalle Malami na gidan Manzon Allahyana tsatson ka,ina ma dai na riske shi.Sunan sa yayi muwafaqa da na Amiru muminin.’’Mu duba shaidar kakan sa Imam Sadiqgare shi tun gabanin a haife shi.Ya ambace shi da kalmar MALAM.Ikon Allah tsakanin rasuwar Imam Sadiqda kuma haihuwar Imam Ridha kusan kwanaki goma sha biyar ne.Haka nan yazo akan cewa tafiyar da suka yi daga madina zuwa khurasan,Birni da qauye da suka yada zango jama’a kan zo suyi tambayoyi na mas’aloli na Addini,ya kan basu amsa,da kuma fada masu Hadisai na Manzon Allahda kuma Ahlul-Bait, Saboda haka nema Ma’amun khalifan Abbasawa,abubuwan da yaji kuma ya gani daga Imam Ridha na ibada da kuma ilmi,sai Ma’amun din,yace wannan shine mafi ilimi a bayan qasa.mu duba shaidar maqiyinsa,watau wannan khalifa na Abbasawa,shaidar da yayi masa na fifikon iliminsa a doron qasa a lokacin. Akwai ma wani da yake cewa bai taba ganin an tambayi Imam Ridha akan wani abu ba,face ya san abun,da dai misalai da yawa na ilimin Imam Ridha wanda baza a iya kawo suba, saboda gudun tsawaitawa. 4.ZUHUDUNSA:Watau gudun duniyarsa,Imam Ridah a wannan fage ya kai mustawa aliya,wanda a zamaninsa babu wanda ya kai shi a wannan fage na gudun duniya,akwai qissar wata kuyanga baiwa ta khalifan abbasawa Ma’amun, tana zaune a gidan Ma’amun din ne,sai ya bada ita ga Imam Ridah.Sai ta koma gidansa,shine take cewa lokacin da take gidan ma’amun tana cikin wal-wala da jin dadi na abinci da abin sha,da kudade,amma da ta koma gidan Imam Ridah duk sai ta rasa wadannan abubuwa na jin dadi.Tacekuma baya ga haka a gidan akwai wata mata, aikinta shine ta dinga tada su sallar tahajjud -sallar dare-tace to wannan shi yafi tsanani gare ni watau tashi sallar.Tace, “Ina ta fata da burin in bar gidan,daga qarshe Imam Ridah ya bada ni ga wani.Da na koma gidansa sai na kasance kamar an sani a Aljannah.” Daga qissar wannan mata zamu iya fahimtar rayuwa ta zuhudu na Imam Ridah.Akwai misalai da yawa,amma gudun tsawaitawa za’a taqaita da wannan. 5.ALAQARSA DA SHI’ARSA:Wato mabiyansa Akwai wani da ake cema Musa dan sayyar yace, “Na kasance tare da Imam Ridah,mun kusan isa dus wato garin Mash-had a yanzu sai muka ga janaza.Sai Imam Ridah ya nufaci wajen janazar,sai yace min, “ya Musa dan sayyar duk wanda ya raka janaza ta dan shi’a daga cikin shi’armu,to zai fita daga zunubansa kamar ranar da mahaifiyar sa ta haife shi.” watau zai dawo bai da zunubi ko guda. Lokacin da aka zo za’asa Mamacin a kabari,kafin sa shi sai Imam Ridah ya tabaqirjinsa yace, “ya wane dan wane albishirin ka da aljannah,babu tsoro gare ka bayan wannan lokacin.” Sai shi wannan da ke tare da Imam Ridah ya ce in zama fansa gare ka,kasan wannan mutumin ne? Domin wallahi baka taba tako wannan qasa ba gabanin yau. Sai Imam Ridah ya ce masa, “ya Musa dan sayyar,shin baka san cewa, mu A’imma ana bijirowa da ayyukan shi’armu gare mu safe da yamma ba? Abinda suka taqaita na ayyukansu,mu roqa masu Allah ya yafe masu,abin da suka aikata mai kyau,mu roqa masu Allah ya qara masu.” A wannan al’amari zamu ga akwai darussa masu yawa a ciki ,amma ga guda uku daga ciki: 1.Alaqar Imam na kowane Zamani da shi’arsa,domin shi wannan mutum da yake tare da Imam Ridah yana mamakin ina yasan wannan mutumin, alhali bai taba zuwa wannan waje ba,wannan kuma yana nuna wilaya Tak-winiyya da kuma Wilaya Tashri’iyya da A’imma suke dashi.Insha Allah wani lokaci za’a yi bayani dangane da wadannan wilaya guda biyu na A’imma a muhallinsu. 2.Tausayin Imamin kowane zamani akan mabiyansa na zamaninsa,su duba in an kai, aikin da bai dace ba ko kuma aka taqaita,su roqi Allah ya yafe wa mutum. 3.Wanda yake yana da gayar muhimmanci, shine mutum ya san da cewa,duk aikin da yake aikatawa mai kyau da kuma mara kyau,to akan kai shi ga Imamin zamaninsa.mu a wannan zamanin namu akan kai shi ga Imam Mahdi ne,saboda haka kowannen mu yayi tunanin ayyukan da yake aikatawa,ayyuka ne da in an kai ma Imam Mahdi zai yi farin ciki dasu ko kuma zai yi baqin ciki dasu? Domin tabbas kai ayyukan bayi ga Ma’asumai wani abu ne wanda yazo a ruwayo yin hadisai masu yawa.Wanda shima wannan wani lokaci a muhallinsa za’a kawo wadannan hadisai,saboda haka yana da muhimmanci kowannen mu ya lizimci ayyukan da zasu kyautata alaqarsa da Imaminsa,ba wadanda zasu raunana alaqarsa da shi ba.kamar fadin wata magana ta Ayatullah Bahjati yana cewa, “kada mu dinga fadi da harsunan mu,Allah ya gaggauta bayyanar Imam Mahdi,amma kuma da ayyukan mu muna jinkintar da zuwansa.” 6.JARABAWOWINSA:Imam Ridah ya fuskanci jarabawowi masu yawa a rayuwarsa,kamar sauran A’imma na Ahlulbayt da suka gabace shi da kuma wadanda suka biyo bayansa. Domin idan mutum ya bibiyi tarihin Imamai daya bayan daya, zai ga kowannensu ya fuskanci jarabawa iri biyu.ta farko jarabawa ta amma,ta biyu jarabawa ta khassa.Jarabawa ta amma itace jarabawar da dukkan Imamai sha biyu sun yi musharaka a ciki.Misali A- jarabawar qwacen tafi da iko daga gare su wanda haqqinsu ne,wanda Allah Ta’ala ya basu. B-Zaluntar su da kuma mabiyansu da kuma sauran jama’a suna ganin haka,amma babu yadda za su yi. C- Tasarrufi a cikin shi Addinin. Watau masu iko su qago abu ko su jirkita yadda yake,su sa shi a cikin addini,kuma su gina mutane akan haka, har saboda ginuwa akai mutane su dauka Addini ne. Da yake nan ba muhallinsa ba ne da an kawo misalai akai.To,idan mutum ya duba wadannan misalai guda ukun da aka kawo zai ga duk A’imma sun yi tarayya wajen wannan matsaloli da aka haifar. Jarabawa ta khassa itace wadda kowa ne Imami ya fuskanta shi qashin kansa daga masu tafi da iko na zamaninsa,.Wannan jarabawa tasa itace ta “ Waliyyul-Ahd” watau nada shi a matsayin khalifa mai jiran gado wanda khalifan Abbasawa Ma’amun yayi,wanda in mutum ya dubi abin a zahiran ce,zai dauka ko abu mai kyau Ma’amun yayi,alhali abin ba haka nan yake ba,a badininsa makirci ne da kuma yaudara.Asasin wannan abu ya taso ne daga shi wannan khalifa na Abbasawa Ma’amun,lokacin daya hau khalifanci yaga matsaloli sun yi masa yawa,ga matsalar dan uwansa mai suna Amin,wanda yana yaqar sa domin ya tunkude shi shi ya hau kan mulkin.Ga kuma ta wa]anda suka yi masa tawaye daga sassa daban daban a lokacin,musamman ma daga bangaren mabiya Ahlulbait,Saboda abin da baban shi Ma’amun watau Harunar-Rashid, yayi na kashe Imam Kazim a kurkuku,ta hanyar sa masa guba.To,wadannan matsaloli daya ga sun yi masa yawa,kuma matsalar da yafi jin tsoro daga cikin wadannan matsaloli,ita ce ta bangaren mabiya Ahlulbait,sai yayi tunani shi a qashin kansa ba tare da yayi shawara da kowa ba,na bari ya dauko Imam Ridah daga madina ya kawo shi khurasan,lokacin itace cibiyar tafi da ikonsa.Domin ya bashi muqami na khalifa mai jiran gado.Manufarsa boyayya itace domin ya kwantar da wancan tawaye da mabiya Ahlulbait suka yi a sassa daban daban, wanda daga qarshe idan abubuwa suka lafa,komai ya koma dai dai na ikonsa sai ya kashe Imam Ridah ta hanyar sa masa guba.Wannan ‘plan’ din shi a qashin kansa ya kitsa.Imam Ridah ne ya tona asirin haka lokacin daya hadu dashi ya ce masa,nasan manufarka.Sai Ma’amun yace masa mece ce manufata? Imam Ridah ya fada masa,nan take ya daburce ya fusata,saboda ya san wannan abin bai fada wa kowa ba,amma gashi Imam Ridah ya fadi,don hatta ‘yan uwansa na jini,lokacin da ya ba Imam Ridah wannan matsayi,sun yi ta maganganu me yasa zai yi haka? Don bai bayyana wa kowa manufarsa ba. Bayan Ma’amun ya kitsa wannan tunani a zuciyarsa,sai ya fara daukar mataki na aiwatar dashi.Saboda haka sai ya aika aje madina a zo masa da Imam Ridah,da ‘yan saqo suka isa madina,suka samu Imam Ridah suka shaida masa saqon Ma’amu,jin haka sai Imam Ridah ya tafi masallacin Manzon Allah domin ya yi ban kwana dashi,saboda yasan qarshe yazo,kuma zamansa a birnin Manzo ya qare.Saboda haka yaje kabarin Manzon Allah yayi bankwana dashi,yana kuka sai ya fito masallacin,sai ya sake komawa domin sake bankwana,yana bankwana da Manzon Allah yana kuka.Har wani daga cikin mabiyansa,ya gan shi yayi masa sallama Imam Ridah ya amsa masa sallamar,ya kuma ce masa ka ziyarce ni domin ni za’a raba ni da birnin Manzon Allah. Zan rasu a can ina baqo.Bayan haka ya koma gida ya tara iyalansa baki daya yayi masu jawabi. Acikin jawabin nasa ya ce masu “TO zan tafi bazan dawo ba har abada,saboda haka mai juyayi yayi juyayi,mai kuka yayi kuka a gare ni.” Bayan haka ya raba masu kudi,Dirhami dubu goma sha biyu.Lokacin da zai fita ya dubi dansa,guda daya da yake dashi watau Imam Jawad lokacin ya nada shekaru bakwai a duniya,ya kama hannunsa ya shiga dashi masallacin Manzon Allah, ya isa kabarinsa,ya kama hannun wannan da nasa ya aza a kabarin Manzon Allah ya ce “To ya Manzon Allah gashi nan ajiya gare ka.” Haka ya bar madina birnin Manzon Allah, suka kama hanya dashi zuwa khurasan.Don ma makirci da dasisa irin na Ma’amun,cikin umurnin daya ba wadanda ya aika su zo da Imam Ridah har da ce masu,kada ku biyo dashi ta gari kaza da kaza,ya ambaci wasu garuruwa,watau duk garin da ya san akwai ‘yan shi’a da yawa,ya ce kada a biyo dashi ta nan,daga ciki har da birnin- qum. Mu duba irin wannan dasisa da makirci,haka suka yi watanni har suka isa khurasan. Kuma duk wanda Allah Ta’ala yasa yaga wannan waje,ko ya san yanda wannan yanki yake da Hamada da kuma tsanuka da zafin yana yi,wani wajen kuma sanyin yana yi, zai fahimci matsanancin wahalar da Imam Ridah ya sha a tafiyar. Domin zan iya tunawa zuwana Iran na farko a 1994, lokacin da Malam ya tura mu karatu a birnin qum mu goma sha biyu, Allah yasa mun tafi daga qum zuwa mashhad a mota, tafiyar kimanin awa goma sha daya ce. To,a lokacin da ake tafiyar yadda naga tsaunuka daban daban, ga Hamada wani wajen, ga tsananin sanyi, akwai garin da muka biyo, dole tasa aka tsaya muka sa kayayyakin sanyi, sa’annan aka ci gaba da tafiya. To,lokacin abinda nake tunani a raina shine,yanzu a wannan yana yi na Hamada da tsaunuka da sanyi da zafi tun daga madina har ya zuwa mashhad,watau khurasan aka biyo da Imam Ridah. A irin wannan yanayi ne ‘yan uwansa na jini bayan shekara daya da tafiyarsa, suka kamo hanya daga madina da nufin su same shi a khurasan. Wa sunsu akan hanya Allah Ta’ala yayi masu rasuwa aka binne su anan, har yanzu kabur-buransu na nan,in mutum yabi ta hanyoyi zai gani,wanda wannan tafiya har yau har gobe,idan na tuna da ita,sai naji tasirinta a zuciyata. Sayyida Ma’asuma akan hanyar su,ta zuwa khurasan,domin zuwa wajen Imam Ridha rashin lafiya ya kamata,wani waje da ake ce ma Sawa.Ta tambaya,tsakanin nan da qum, far-sakhi nawa ne? Aka ce mata goma,tace to a qarasa da ita qum.Kuma wani abin baqinciki da ban takaici da ya faru gare su,da suka iso wannan gari na Sawa.Shine Hujumin da akayi a kansu,wanda ya kai ga an kashe wasu daga ciki,wasu kuma aka ji masu rauni.Wasu malaman Tarihi sun tafi akan cewa,wannan rashin lafiya nata,yana da alaqa da wannan mummunan abin da aka yi masu,mu duba mu gani zuriyar Manzon Allah sun taso daga madina su kimanin 30 kamar yadda yazo a ruwaya aka tare su a hanya aka yi masu wannan mummunan abu.Malaman tarihi sun yi tambaya kan wannan abu cewa,Ma’amun ne ya kitsa ayi wannan abu,ko ko su mutanen Sawa ne suka yi? Domin yazo a tarihi cewa su mutanen Sawa a lokacin, sun kasance suna gayar gaba da qiyayya da Ahlulbait.Ko ma dai mene ne,musabbabin wannan aika-aika da akayi ma su Sayyida Ma’asuma. To yau ina Ma’amun din? ina mulkin nasa? ina kuma wadanda ya mulka? Bayan isar su Imam Ridah khurasan, Ma’amun ya gana dashi,ya shaida masa abinda yake buqata,na ya kasance khalifa mai jiran gado.Imam Ridah ya ce masa a’a, sai Ma’amun ya ce masa ko dai ya amshi wannan matsayi na Waliyyul-Ahd, ko kuma ya kashe shi.Imam Ridah ya amsa,amma da sharadin cewa ba zai zartar da komai ba.Wannan ya kasance babbar jarabawa ga Imam Ridah saboda yasan meye manufar Ma’amun kan wannan abu. Haka Imam Ridah ya zauna a cikin wannan jarabawa,wadda sai da ta kai koda wane lokaci in ya dawo daga masallacin juma’a, yakan daga hannu sama ya ce “Ya Ubangiji idan faraj dina yana ga rasuwata,to ka gaggauta wafatina.” An ce ko da wane lokaci yana cikin damuwa da kuma baqin ciki har ya koma ga Allah Ta’ala. Daga qarshe Ma’amun Yasa masa guba a inabi,a wata ruwaya a rumman,wanda hakan yayi sanadiyar shahadarsa. Ya rasu yana da shekara 55 a duniya.
|