Friday, 24 May 2024
Email
Make My Homepage
RSS
Register
Dabio’in Imam Musa Al- Kazim [AS] Print E-mail
Written by administrator   
Tuesday, 05 May 2020 15:14

Kasantuwar wannan watan da muke ciki mai alfarma, wato watan Rajab 25 gare shi ne Shahadar Imam Musa Alkazim (AS). Kamar yadda aka sani, shi ne Imam na bakwai a jerin kidaya na Imamai 12 (AS).

Imam Kazim (AS) an haife shi ne ranar Lahadi 7 ga watan Safar shekara ta 128 bayan hijira, a wani gari da ake ce wa Abwa, yana tsakanin Makka da Madina ne. Wannan gari na Abwa Imam Sadiq (AS) ya yada zango ne a cikinsa, shi da iyalinsa da kuma wasu daga cikin mabiyansa a kan hanyarsu ta dawowa daga aikin Hajji. Lokacin da Mahaifiyar Imam Kazim (AS) ta ji alamun naquda, sai ta aika wa Imam Sadiq (AS), an ce lokacin yana cin abinci tare da wadannan mabiya nasa, sai ya taso da gaggawa, lokacin da ya zo wajenta ba a jima ba sai ta haihu. Imam Sadiq (AS) ya amshi wannan da mai albarka duniya da lahira, ya yi Azan a kunnensa na dama, ya kuma yi Iqama a kunnensa na hagu.

Bayan haka ya koma wajen Sahabbansa ya shaida masu wannan abin farin ciki, ya ce masu Allah (T) ya azurta ni da da mai albarka mai daraja, shi ne kuma Sahibinku (Wato Imami bayansa), saboda gayar farin ciki na wannan abin haihuwar mai albarka, Imam Sadiq (AS) walima ya yi har kwana uku a jere. Kuma ya zo a tarihin Imam Sadiq (AS) cewa yana gayar son Imam Kazim (AS), an taba tambayarsa dangane da wannan son da yake yi wa Imam Kazim (AS), sai ya ba da amsa da cewa; “Ya yi fata da kuma burin bai da wani da face shi, saboda kada wani ya yi tarayya da shi a son.

Sunan Mahaifiyar Imam Musa Kazim (AS) Hamida. Kuma kamar yadda ya zo a tarihinta, a fagen ilimi ta kai mustawa aaliya, har ta kai Imam Sadiq (AS) yakan umurci mataye da su koma wajenta dangane da abubuwa na hukunce-hukunce. Akwai wani lokacin da yake cewa Hamida tsarkakakkiya ce daga dukkan aibobi.

Imam Kazim (AS) yana da laqubba da yawa, amma wadanda suka fi shahara su ne Kazim da kuma Babul Hawa’ij. Ana kuma yi masa kinaya da Abu Ibrahim da kuma Abul-Hassan, da dai sauransu, da yake wadannan su suka fi shahara a kinayarsa.

Ya rayu a Madina tare da Mahaifinsa, wato Imam Sadiq (AS) shekaru 20 wato yana da shekara 20 Imamanci ya dawo gare shi. Muddan Imamancinsa shekaru 35 ne. Imam Kazim (AS) yana da ’ya’ya 36, 17 maza 19 mata. Ga sunayen mazan, Imam Aliy Arridah (AS), Ibrahim, Abbas, Kasim, Isma’il, Harun, Hassan, Ahmad, Muhammad, Abdullahi, Ishak, Ubaidullah, Zaid, Fadhal da kuma Sulaiman. Matan kuwa su ne Fadimatul-Kubra, Fadimatul-Sugra Ruqayya, Hakima, Ummi Abiha, Ruqayyatu-Sugra, Kulsum Ummi Ja’afar, Lubaba, Zainab, Khadija Aliyya, Aminatu, Hasana, Buraiba, Ummu Salma, Maimunatu, Ummi Khulsum.

Imam Kazim (AS) ya rayu a duniya shekaru 55, ya yi shahada a ranar Juma’a 25 ga watan Rajab, shekara ta 183 bayan hijira, sakamakon guba da aka sa masa. Ya yi zamani da Khalifofin Abbasawa guda hudu, su ne Mansur, Muhammad Mahdi, Musal-Hadi, Harunar-Rashid. Mu duba mu gani sunaye da laqubba na bayin Allah (T), amma su masu sunayen ba su yi aiki na qwarai ba. Qabarin Imam Musa Kazim (AS) yanzu haka yana Kazimiyyah, wato Iraqi.

Sai kuma abin da ya shafi wasu bangarori na rayuwarsa, domin su kasance darussa gare mu da kuma madubi da za mu dubi kawukanmu da su, domin kullum abin da ake so ga mutum, ya yi ma kansa hisabi ya duba ya ga tsakanin abin da yake aikatawa da kuma abin da zai iya yi, akwai gibi, idan akwai sai ya yi qoqari ta hanyar mujahada da nafs dinsa, domin ya cike gibin, wato ya kasance dai kullum yana samun ci gaba a fagen addini, ba ya zamanto yana waje daya, ko kuma yana ci baya ko kuma ya yi gaba ya yi baya ba.

1. IBADARSA: Imam Kazim (AS) ya kasance mai yawan ibada. A zamaninsa a wannan fage na ibada, ba wanda ya kai shi. Masoya da maqiyansa duk sun tabbatar da haka. Saboda yawan ibadarsa da kuma mujahadarsa, cikin laqubbansa akwai Zainul-muj-Tahidin, da kuma Abdus-Salih. Ga wasu misalai na bangarori na ibadarsa.

A. Sallolinsa: Imam Kazim (AS) ya kasance mai yawan Salla da kuma sujuda, ya zo a tarihinsa cewa akwai lokacin da ya shiga Masallacin Manzon Allah (S) ya yi sujuda guda daya tun daga farkon dare har ya zuwa qarshensa. A cikin sujudar, wannan Addu’ar ya dinga maimaitawa “Zunubi ya girmama gare ni, ina meman afuwa daga wajenka domin kai ne ma’abocin gafara.” Mu duba mu gani a i’itiqadinmu Imami kuma Ma’asumi, amma yana irin wannan shu’uri da kuma i’itirafi gaban Allah (T), to ina ga mu. Kuma dama wannan ita ce dabi’a ta bayin Allah (T) suna da kusanci ga Allah (T), amma kuma lokaci guda kuma suna jin cewa sun fi kowa lalacewa da kuma yawan zunubi, in mutum ya bibiyi addu’o’in A’imma (AS) jefi-jefi a cikin addu’o’in zai ci karo da irin wadannan sigogi na i’itirafi da zunubi. Amma dai Malaman Irfan sun yi bayanin irin wadannan sigogi na ambaton zunubai daga Ma’asumai (AS) mai yake nufi? Bayanin hakan na a muhallinsa. Wato littafan Irfan. Hakan nan ya zo a kan cewa wata rana Abu-Hanifa ya shiga wajen Imam Sadiq (AS) sai ya ce masa na ga danka Musa yana Salla, amma mutane na gittawa gaba gare shi. Sai Imam Sadiq (AS) ya ce a kira masa shi, da Imam Musa Kazim (AS) ya zo, sai Imam Sadiq (AS) ya yi masa magana dangane da haka, sai Imam Kazim (AS) ya ce, na’am haka ne ya babana. Amma wanda nake Salla saboda shi ya fi kusa gare ni da su. Wannan kuma yana nuna mana gayar fana’insa a cikin Salla.

Haka nan ya zo a tarihin Imam Kazim (AS) cewa ya kasance yana raya dararensa da Salla ne, idan kuma ya yi Sallar Asuba yakan zauna ya yi ta’aqibat har ya zuwa fitowar rana. Idan rana ta fito yakan yi sujuda, ba zai dago daga sujudar ba har sai zawal ya yi, kuma kamar yadda ya zo a ruwayar, ya kasance ya lizimci yin haka sama da shekara 10, wato kullum zai yi wannan sujudar tun daga ketowar rana zuwa zawwal na rana. In mutum ya dubi tsakanin wadannan lokuta na ketowar rana zuwa zawal, ba wai mintuna ba ne, a’a awoyi ne, amma shekaru ya yi a haka. Saboda haka yana da kyau mutum ya sunnanta wa kansa yin sujuda bayan ya gama ta’aqibat dinsa na Sallar Asuba idan rana ta fito, ya yi wannan sujudar. Ya yi ko da mintuna ne, ko awa daya daidai ikonsa. Wato saboda yin koyi da Imam Kazim (AS).

Tambihi a nan, ita wannan sujuda ba ta shuk-ra ba ce da ake yi bayan Salla, a’a ita daban take. In ma son samu ne zikir din da ake so mutum ya yi a sujudar shi ne ‘La’illaha Illa anta-subhanaka inni kuntu minazalimin. Wato ya yi ta nanata haka a sujudar yadda ya sauqaqa masa. Akwai Malaman Irfan da suka yi bayanin cewa lizimtar wannan sujuda da kuma wannan zikiri a cikin kowace rana, yana da gayar tasiri a zuciya.

Ya zo a kan cewa Khalifan Abbasawa da ake ce wa wai Rashid, lokacin da ya sa Imam Kazim (AS) a kurkuku. To kullum yakan hangi wani daga benensa, ya dauka tufafi ne. Sai wata rana ya tambaya wai wancan tufafin da nake gani kowace rana a wancan wajen fa? Sai aka ce masa ba tufafi ba ne. Musa dan Ja’afar ne, kullum sai ya yi sujuda daga fitowar rana zuwa zawwal. Sai Rashid ya kada baki ya ce, lallai wannan shi ne Abidin (mai ibadar) Bani Hashim, sai mai kula da kurkukun ya ce masa, to ka sake shi mana. Sai Rashid ya ce ai ba makawa. Mu duba irin wannan zalunci haka nan.

Ya zo a tarihin Imam Kazim (AS) cewa a kurkukun da ya zauna na qarshe, a hannun wani la’ananne mai suna Sindiy dan Shahik. To ’yar uwarsa take ba da labarin zaman Imam Kazim (AS) a kurkuku. Take cewa yana addu’o’i har ya zuwa tsakiyar dare, bayan haka kuma sai ya tashi ya kama Salla har ya zuwa Asuba. An ce wani lokaci in ta dubi Imam Kazim (AS) ta kan ce; “Mutanen da suka cutar da wannan mutum sun tabe. Wannan bawa ne Salihi”. Wannan ke nan a taqaice dangane da Sallarsa.

B. Karatun Alqur’ani: Ya kasance mai yawan karatun Alqur’ani. Kuma ya zo a kan cewa in yana karatun Alqur’ani yana kasancewa cikin gayar tadabbur da kuma tafakkur a kan abin da yake karantawa, haka nan ya kasance yakan kyautata sauti. Wajen karanta shi, har takan kai ma masu sauraro in suna jin karatunsa, sukan yi kuka.

Akwai wani na kusa da Imam Kazim (AS) da ya siffanta qira’arsa, da cewa in yana yi ya kan kasance cikin huzun (baqin ciki). Kamar yadda aka sani akwai ladubba na zahiri da kuma ladubba na badini a lokacin karantun Alqur’ani. To daga cikin ladubba na badini lokacin karatun Alqur’ani akwai wannan, wato Huzun, misali a ce lokacin da mutum yake karatun sai ya biyo ayoyin da suke bayani dangane da wahalhalun da Annabawa suka sha, ko jingina masu abin da bai dace ba. Misali jingina masu hauka, bokanci, ko kuma kamar yadda Fir’auna ya ce wa Annabi Musa (AS), wulaqantacce da dai sauransu. Ko kuma ayoyin da ke bayanin jingina wa Allah (T) abin da bai dace ba. Misali da. To duk ire-iren wadannan ayoyi idan mutum ya biyo ta wajen ana so mutum ya kasance cikin huzun, haka nan baya ga huzun, ana so kuma mutum ya kasance a lokacin tilawar Alqur’ani cikin hali na ‘Khauf’ (tsoro), shi ma yana cikin ladubba badiniyya na karatun Alqur’ani, wato mutum ya kasance cikin tsoro, idan ya biyo ga ayoyin da suke magana kan wuta da kuma azabobin da ke ciki da dai sauransu. Haka nan kuma daga cikin ladubba badiniyya na karatun Alqur’ani akwai shauqi. Wato lokacin da mutum ya biya ayoyin da suke magana dangane da Aljanna da kuma ni’imomin da ke ciki mutum ya kasance mai shauqi, wato bege ga haka.

A taqaice dai wadannan ladubba guda uku na badini wato huzun, kauf, da kuma shauqi, yana da gayar muhimmanci lokacin da mutum yake karanta Alqur’ani ya zamanto yana jin tasirinsu a zuciyarsa. Ga mai buqatar ganin ladubba na zahiri da kuma badini na karatun Alqur’ani ya duba littafi mai suna Mahajjatul Baida’a na Faidul Kaslaniy ko kuma littafin Ihya’ul-ulumuddin na Gazzali.

C. Azkar dinsa: Imam Kazim (AS) ya kasance mai yawan zikiri. Ya zo a tarihinsa cewa, akwai lokacin da yake fada wa wani daga cikin mabiyansa cewa, kowace rana yana yin Istigfari dubu biyar. Saboda haka ke nan yana da muhimmanci ko wanenmu, a kowace rana bai yi da yawa ba ya yi dubu daya, domin idan wanda bai yin zunubi zai yi istigfari kowace rana dubu biyar, to ina ga mai yin zunubin? Baya ga wannan kuma ya kasance mai yawan Tasbihi, Hailala, Tahmidi da kuma salati ga Manzon Allah (S).

D. Azuminsa: Imam Kazim (AS) ya kasance mai yawan Azumi. Ya zo a tarihinsa cewa lokacin da yake a kurkuku, kullum Azumi yake yi. Kuma Azumi kamar yadda Malaman Irfan suka yi bayani akwai na yaumiyyah, wato yin Azumi kowace rana in ban da ranakun da aka haramta yin Azumi a ciki, kamar ranakun Idi. Irin wannan Azumin na yaumiyyah in mutum ya bibiyi tarihin wadansu bayin Allah (T) zai ga sun sunnata wa kansu wannan Azumin. Akwai kuma Azumi na Usbu’iyyah, wato na mako. Misalinsa, Azumin Litinin da Alhamis. A wata ruwayar Alhamis da Juma’a. Akwai kuma Azumi na Shahariya, wato wata-wata, misalinsa Azumin 13,14,15 na kowane wata, ko kuma Azumin Alhamis din farkon na goman farko na wata da kuma Azumin Larabar farko na goman tsakiya na wata. Da kuma Azumin Alhamis din qarshe na goman qarshe na wata. Sai kuma Azumi na Sanawiyyah wato na shekara-shekara misalinsa Azumin watan Rajab ko Sha’aban, ko kuma wasu muhimman ranaku a cikin shekara da ya zo ana son yi Azumi a ciki, kamar ranar Ghadir, Mubahala, Mab’as da wasu ranaku na munasabar wilada na Ma’asumi (AS). Saboda haka a nan ana so mutum ya sunnanta wa kansa wannan nizami na Azumi, musamman ma na Usbu’iyya, Shahariyya da kuma na Sanawiyya.

E. Hajjinsa: Imam Kazim (AS) ya zo a tarihinsa cewa ya yi Hajji shi da dan uwansa, Aliy dan Ja’afar da kuma iyalinsa baki daya sau hudu. A qafa suka taka, tun daga Madina zuwa Makka. Ba wai don ba dabbar da za su hau ba ne. Shi ne ma har dan uwansa,, wato Aliy dan Ja’afar yake cewa tafiyarsa ta farko sun yi kwana 26 a hanya, ta biyu kwana 25, ta uku kwana 24, ta hudu 21. A taqaice dai Imam Kazim (AS) ya kasance mai yawan Ibada ta kowace fuska. Ya zo a tarihinsa cewa lokacin da yake kurkuku, har godiya yake ga Allah (T) da ya ba shi faraga domin Ibada gare shi.

2. KUKANSA: Imam Kazim (AS) ya kasance mai yawan kuka ne saboda tsoron Allah (T). Ya zo a tarihinsa cewa yakan yi kuka har takan kai gemunsa ya jiqe da hawaye. Kuka saboda tsoron Allah (T) yana da falala mai yawa.kamar Yadda ya zo a Hadisai daban-daban. Ga wasu daga ciki. An samo daga Imam Husain (AS) ya ce; “Babu wani ido face ya yi kuka gobe qiyama, sai idan dai ya yi kuka saboda tsoron Allah (T), (wato a wannan gida na duniya).” An samu daga Imam Baqir (AS) ya ce; “Babu wani digo wanda ya fi soyuwa ga Allah (T) kamar digon hawaye wanda aka zubar da shi a cikin duhun dare saboda tsoron Allah (T) wanda wani bai gani ba.” Wato misali, lokacin Tahajjud da dai makamantansu. An samu daga Imam Sadiq (AS) ya ce Manzon Allah (S) ya ce; “Duk wanda idanunsa suka zubar da hawaye saboda tsoron Allah (T), to zai kasance yana da gida a Aljannah a kowane digo na hawayensa”. Haka nan Manzon Allah (S) ya ce; “Kuka saboda tsaron Allah (T) mabudin rahma ne. Kuma alamar karbar aiki ne, kuma qofar ijaba ce.” Wato ana karbar addu’a lokacin kuka saboda tsoron Allah (T). An samo daga Imam Ali (AS) ya ce; “Kuka saboda tsoron Allah (T) yana haskaka zuciya, yana kuma kange mutum daga aikata zunubi”. Manzon Allah (S) ya ce; “Idanuwa biyu wuta ba ta shafarsu, idon da ya yi kuka saboda tsoron Allah (T), da kuma idon da ya kwana yana gadi saboda Allah (T). A kuma wani Hadisi, Manzon Allah (S) ya ce; “Babu wani abu mafi soyuwa ga Allah (T) kamar digo biyu. digon hawaye saboda tsoron Allah (T) da kuma digon jini da aka zubar saboda Allah (T), da dai Hadisai masu yawa wanda ba za a iya kawo su ba, saboda gudun tsawaitawa.

Haka nan, ya zo a tarihin Imam Kazim (AS) cewa idan yana Sallah, ko karatun Alqur’ani ko Addu’o’i, ya kan yi su yana kuka. Saboda haka yana da muhimmanci ya zamo mun siffantu da wannan siffa ta kuka a lokacin da muke aikata wadannan ayyuka na Ibadodi. Watau a Sallolinmu, karatun Alqur’ani, da sauran Azkar dinmu da Addu’o’inmu, ziyarorinmu na Ma’asumain (AS) da dai sauransu, musamman na tahajjud dinmu. Domin bushewar ido. Sabab dinsa shi ne bushewar zuciya. Bushewar zuciya kuma sabab din shi ne yawan zunubi.

3. JARABAWOWIN SA: Imam Kazim (AS) ya fuskanci jarabawowi masu ywan gaske a rayuwar sa, akwai jarabawowin da ya fuskanta daga masu tafiyar da iko, akwai kuma wadanda ya fuskanta daga mutanen gari, akwai kuma wadanda ya fuskanta daga mabiya. Misali jarabawar da ya fuskanta daga masu tafiyar da iko, su ne sa ido a kan sa, fitar da shi daga Madina, kama shi da kuma daure shi a kurkuku, daga qarshe kuma aka kashe shi. Kamar yadda ya zo a tarihi Imamai hudu ne suka yi zaman kurkuku, su ne Imam Bakir (AS), Imam Kazim (AS), Imam Hadi (AS) da Kuma Imam Askari (AS). To a cikin wadannan Imamai hudu, wanda ya fi su tsawon zama a Kurkuku ya kuma zauna a kurkuku daban-daban, shi ne Imam Kazim (AS), domin ya zo a wata ruwaya cewa, ya zauna a kurkuku na tsawon shekara 17, kuma wadannan Khalifofi na Abbasawa 4 da ya yi zamani da su uku daga cikinsu babu wanda bai kama shi ba, ya daure kuma cikinsu wanda ya fi gallaza masa da kuma cutar da shi, shi ne wanda ake cewa wai Harunar Rashid. Kuma da umarninsa ne aka sa ma Imamu Kazim (AS) guba wadda ta zama sanadiyyar Wafatinsa. Gabanin haka ma ya sha yunqurin kashe Imam Kazim (AS), amma Allah (T) ya kare shi. Domin gabanin Shahadar Imam Kazim (AS) yana cewa, “An sa masa guba dai-dai har sau tara a lokuta daban-daban, Allah yana kare shi.”A taqaice dai Imam Kazim (AS) ya fuskanci jarabawowi masu yawa a hannun masu tafi da iko.

Misalin jarabawar da ya fuskanta daga mutanen gari, akwai wani mutum a Madina, a lokacin yana cutar da Imam Kazim (AS), ta kai ga duk inda ya ga Imam Kazim (AS) sai ya zage shi ya kuma zagi Imam Aliy (AS), sai mabiyan Imam Kazim (AS) suka ce masa ya ba su dama su kashe shi. Imam Kazim (AS) ya hana su, hani mai tsanani.

Wata rana sai Imam Kazim (AS) ya tambayi mutumin, aka ce masa ya tafi gona. Sai Imam Kazim (AS) ya bi shi can, yana ganin Imam Kazim (AS) sai ya kama cewa kada ka taka man shuka. Imam Kazim (AS) dai ya yi taka tsantsan kada ya taka mai shuka, har ya isa wajensa. Yana yi masa magana yana murmushi ya tambaye shi nawa ka kashe a wannana shukar taka? Sai mutumin ya ce masa dinari 100, sai ya ce masa nawa kake tsammanin za ka samu idan ka girbe shukar? Sai mutum ya ce ai ni ban san gaibu ba. Sai Imam Kazim (AS) ya ce masa, ai na ce nawa kake tsammani ne? Sai mutum ya ce dinari 200, sai Imam Kazim (AS) ya ba shi dinari 300, ya kuma ce masa wannan shuka Allah ya sa mata albarka. Abin kuma da ke tsammanin samu a shukar, Allah ya azurta ka da shi. Nan take sai mutum ya sumbanci Imam Kazim (AS), ya kuma nemi ya yi masa afuwa kan abubuwan da ya yi masa a baya. To ire-iren wadannan jarabawowi daga mutanen gari, Imam Kazim (AS) ya fuskance su.

Sai kuma jarabawowi da ya fuskanta daga mabiyansa. Imam Kazim (AS) ya fuskanci jarabawowi a wasu daga cikin mabiyansa. Kasantuwar mafi yawan lokutan Imamancinsa a Kurkuku yake ba a waje ba. Ita wannan jarabawa ko matsala da ya fuskanta daga wasu, a cikin mabiyansa. Ta soma ruruwa ce tun yana raye, amma ba ta bayyana balo-balo ba, sai bayan Shahadarsa (AS), wadda wannan matsalar ta haifar da wani gungu da ake ce masu WAQIFIYYA. Kuma su wadanda suka haifar da wannan fitina ta waqifiyya. Asasin abin shi ne son duniya da kuma abin duniya. Ga mai buqatar ganin wannan matsala ta waqifiyya, ya duba littafin SIRATU-RASULILLAH WA-AHLI BAITIHI- juzi na biyu.

 
Home Darusan Akhlaq Dabio’in Imam Musa Al- Kazim [AS]
Copyright © 2024. www.tambihin.net. Designed by KH