Tuesday, 09 August 2022
Email
Make My Homepage
RSS
Register
Nasihohin watan Ramadan Print E-mail
Written by Administrator   
Saturday, 18 May 2019 11:24

Da farko muna godiya ga Allah Ta’ala na wannan babbar ni’ima da ya yi mana na rayamu da yayi ya kawo mu wannan wata na Ramadan mai tarin albarka.Nasihohin watan Ramadan za a iya kasa su gida ukku:1-Akwai nasihohin da ya kamata mutum ya lizimta ko ya aikata gabanin watan Ramadan.2-Akwai kuma wa]anda ake so mutum ya aikata lokacin watan Ramadan.3-Akwai kuma wa]anda ake so mutum ya aikata bayan watan Ramadan.

1-Nasihohin gabanin watan Ramadan:

Kafin shigar ko kamawar watan Ramadan abu na farko da ake son mutum yayi shine Tuba ga Allah Ta’ala daga dukkan zunubai.Tuba kamar yadda Malaman Akla} suka yi bayani ta kasu kasha ukku:A-Akwai tuba ta Awwam itace tuba daga zunubai.B-Akwai tuba ta kusus wato za~a~~un bayin Allah itace tuba daga gafala na tunanin Allah Ta’ala ko kuma tunanin gidan lahira.C-Akwai tuba ta khususul-kusus wato za~a~~un za~a~~un bayin Allah Ta’ala itace tuba dangane ta}aitawa ga bautar Allah,mu dubi }issar da ta zo na Mala’iku cewa akwai Mala’ikan da tun da aka halicce yana sujuda ne ga Allah Ta’ala,wani kuma yana ruku’u,wani kuma yana tasbihi ne da dai sauran nau’oin ibadodi dabam dabam amma duk da haka ranar }iyama zasu ce ma Allah Ta’ala sun ta}aita game da ibada gareshi.Saboda haka wa]annan matakai na tuba guda ukku,ko da ace mutum bai samu shiga cikin mataki na biyu da na ukku ba to a}alla ya kasance a mataki na farko wato ya tuba daga dukkan zunubai misali idan yana aikata wani zunubi kamar yin }arya ko giba ko munana zato ga ‘yan uwansa to sai ya tuba daga aikata su.Abu na biyu da ake son aikatawa gabanin kamawar watan Ramadan shine Tazkiyya na naf’s wato mutum ya tsarkake Ruhinsa saboda tasirin da ruhinsa zai samu na ibadodin da zai yi a watan Ramadan to fa ya danganta ne ga tsarkin da ruhinsa yake dashi saboda haka yana da gayar muhimmanci gabanin shigar watan Ramadan mutum yayi mujahada wajen ganin cewa ya tsarkake ga~o~insa na zahiri misali harshensa,idanuwan,k unnuwansa da dai sauransu daga sa~on Allah,haka nan ya tsarkake zuciyarsa daga }azanta na zuciya misali hassada,riya,ujubu,ananiyya da dai sauransu.Rashin yin wannan tazkiyya ko tuba suna iya haifar ma mutum matsaloli masu yawa a watan Ramadan misali suna iya dabaibaye mutum daga aikata ayyukan ]a’a ko ibadodi ko kuma su hana a amshi addu’oinsa,akwai wani day a ta~a zuwa wajen Imam Ali[AS] y ace masa kullum yana kwanciya da nufin zai tashi ya yi sallar Tahajjud amma kuma bai samun muwafa}ar tashi sai Imam Ali ya bashi amsa da cewa zunubai ne suka yi masa dabaibayi wato zunubai da yake aikatawa su sukayi sanadiyyar rashin tashinsa yin sallar tahajjud.Abu na ukku da ake so mutum ya yi gabanin shiga watan Ramadan shine da]a tunasar da kansa dangane mas’aloli dabam dabam da suke da ala}a da Azumi,haka nan kuma ya da]a horar da kansa ga iba dodi dabam dabam ta yadda in ya shiga watan Ramadan jikinsa ya saba misali yana son raya dararen watan Ramadan ko kuma yana son ya dunga saukar Al}ur’ani duk kwana ukku a watan to sai ya yi ma kansa tarbiyya akan haka tun gabanin kamawar watan ba wai sai an shiga watan ba zai fara.Akwai wani daga cikin mabiyan Imam Rida[AS] da yaje wajensa a na kusan mako guda kafin a fara Azumin watan Ramadan,to shine Imam Rida[AS] yai masa wasu nasihohi da zai aikata kafin shiga watan Ramadan,ga nasihohin: “Ya baban Sult mafi yawan kwanukan Sha’aban sun tafi wannan itace Juma’ar }arshe a cikinsa saboda haka ka ribaci abinda ya rage a cikinsa,ka yawaita karatun Al}ur’ani da Addu’oi da kuma Istigfari,ka tuba zuwa ga Allah daga zunubanka,kada ka bar wata amana dake kanka face ka sauke ta,idan akwai wani abu tsakaninka da wani mumini marar kyau face ka gyara,idan akwai wani zunubi da kake aikatawa to ka tuba ka dena aikatawa,ka siffata da ta}awa,ka dogara ga Allah a dukkan al’amuranka saboda wanda ya dogara ga Allah to ya isar masa,ka yawaita fa]in cewa ya Allah idan baka gafarta man ba a kwanukan da suka shu]e na Sha’ban to ka gafarta min a kwanukan da suke rage daga gareshi”. Ga mai bu}atar ganin wa]annan nasihohi na Imam Rida yana iya duba littafin Mafatihul-Jinan a babin dake bayanin ayyukan watan Sha’aban wato a }arshensa.

2-Nasihohin lokacin watan Ramadan:

          Da farko idan watan Ramadan ya shiga ana so mutum yayi salatu-shukur wato sallah ta godiya ga Allah Ta’ala ga wannan babban ni’ima da yayi masa na kawo shi wannan wata mai albarka saboda mutum yayi tunani akwai wa]anda ya sani misali cikin ‘yan uwansa na jini ko na addini ko kuma ma}wabtansa wanda an yi watan Ramadan dasu na shekarar da ta gabata amma yanzu basa raye wato sun rasu.Saboda haka ko da mutum bai samu yin wannan salatu-shukur ba to a}alla yayi sujudu-shukur.Abu na biyu da mutum ya kamata yayi tunani akai shine cewa watan Ramadan furs ace zahabiyya ga mutum waton golden-opportunity kuma mutum bai sani ko ma shine watan Ramadan na }arshe a rayuwarsa saboda haka mutum yayi amfani da wannan babbar dama da Allah Ta’ala ya bashi ta kasuwar lahira wato idan akwai kasuwar duniya to watan Ramadan wata ne da za a iya siffanta da kasuwar lahira,bayan watan Ramadan zai kasance kenan wanda ya ci riba ya ci riba wanda kuma yayi hasara wa’iyazu billahi yayi hasara.Ibadodin watan Ramadan suna da yawa amma ga wasu daga ciki:1-Salloli:Sallolin watan Ramadan suna da yawa daga ciki akwai sallar kowane dare na Watan Ramadan wato tun daga daren farko har ya zuwa daren talatin,idan mutum ya duba cikin littafin mafatihu ko Dhiya’u zai ga wa]annan salloli saboda haka yana da gayar muhimmanci mutum ya ga cewa kowane daren yayi sallar daren ba tare da yayi fashin gwada dare guda ba.Bayan wa]annan salloli akwai kuma Sallar Asham amma ba kamar yadda tazo a mahanga ta Ahlus sunna ba misali ba a yinta cikin jam’I wato kowa zai yi nashi ne domin haka sahabbai suka yi a lokacin Manzon Allah[S.a.a.w]a lokacin Umar ne yasa a dun ga yinta cikin jam’I,har ma day a gani ana yi, y ace kai madalla da wannan bidi’a.Asham a mahanga ta Ahlul bayt ga yadda take,raka’a ce guda dubu[1000] ga yadda zai yi su,tun daga daren farko har ya zuwa daren ashirin kowane dare zai dunga raka’a 8 bayan sallar magariba,bayan haka sai raka’a 12 bayan sallar Isha’i.A kuma daren goma na }arshe zai dunga yi kowane dare raka’a 8 bayan sallar magariba bayan haka sai raka’a 22 bayan sallar Isha’i.Bayan haka kuma a daren 19,21 da kuma daren 23 }ari a kan wa]ancan kowane dare zai yi raka’a 100,idan mutum yayi total baki ]aya zai ga raka’a dubu kenan saboda haka ba ana nufin mutum yayi raka’a dubu ba a lakaci guda ba.Baya ga wa]annan salloli akwai kuma wasu salloli da aka ruwaito a wasu muhimman darare na watan Ramadan misali daren farko,daren 13,14 da kuma 15 da kuma dararen lailatu }adri suma mutum yayi }o}ari yayi su,a ta}aice dai duk wata sallah da aka ruwaito ana son yinta a watan Ramadan to kada mutum ya yarda ta ku~uce masa.

          2-Karatun Al}ur’ani:Wannan wata na Ramadan ana so mutum ya yawaita karatun Al}ur’ani a cikinsa,in son samu ne a duk kwana ukku mutum ya sauke,wato kullum yayi izu 20,in kuma haka bai samu ba to sai yayi abinda ya sau}a}a,fata dai mutum yayi sauka a cikinsa fiye da sauran watanni,ya zo a tarihin Imam Khumaini cewa a watan Ramadan ya kasance yana sauke Al}ur’ani a duk kwana ukku.Haka nan kuma ana son mutum ya karanta suratul-}adri wato Inna-anzalnahu sau dubu kowane dare.Haka nan ana son mutum ya karanta suratu-Dukan shima kowane dare na watan Ramadan da dai sauransu.A ta}aice dai hasara ce babba ga mutum a ce watan Ramadan ya kama har ya fita mutum bai sauke Al}ur’ani ba wato dai a}alla mutum ya samu ya sauke Al}ur’ani ko da sau ]aya ne.

          3-Azkar:Ana so mutum ya yawaita zikirori a watan Ramadan kamar su hailala,tasbihi,istigfar,salatin Manzon Allah da dai sauransu.Wato dai mutum ya yawaita azkar a cikin watan fiye da sauran watanni,saboda wata ne da ake nunnuka ayyuka na bayi,kuma watan Ramadan fursa ce zahabiyya da bai kamata mutum yayi wasa da ita ba,kuma mutum bai sani ba ko wannan shine watan Ramadan na }arshe a rayuwarsa,mutum yayi tunanin wasu daga cikin ‘yan uwansa na addini ko na jini ko ma}wabtansa wa]anda watan Ramadan na shekarar da ta wuce dasu mukayi amma na bana bamu tare dasu saboda haka yana da gayar muhimmanci mutum ya ribaci wannan lokaci mai tarin albarka da muke ciki.

          4-Addu’oi:Wannan wata na Ramadan yana da addu’oi da aka ruwaito fiye da sauran watanni,kuma wa]annan addu’oi akwai wa]anda ake yin su da daddare,akwai kuma wa]anda ake yi da rana,akwai kuma wa]anda ake son yinsu bayan kowace sallah ta farilla,akwai kuma wa]anda ake yi bayan kowace raka’a biyu ta nafilfili dubu da aka ambata a sama,akwai kuma wa]anda ake yin su lokacin as-har wato kafin ketowar alfijir da dai sauransu.To ana so wa]annan addu’oi baki ]aya mutum ya lizimci yinsu tun daga farkon watan Ramadan har }arshensa,kuma wannan abu mai yiyuwa ne,misali mu ]auki addu’ar da tafi su tsawo duka a watan,wato Addu’ar Abu Hamzatus-sumali wanda ake karanta ta a lokacin Ashar, to akwai bayin Allah da suka haddace ta,kowane dare da ita suke }unutin sallar wutiri.A ta}aice ga mai bu}atar ganin wa]annan addu’oi dabam-dabam da ake yi a watan Ramadan yana iya duba littafin I}bal na Sayyid ibn [awus ko mafatihul jinan ko kuma littafin Minhajul Jinan na Ayatullahi Sayyid Abbas Al-kashani,littafi ne da baki ]ayan sa ya }unshi ibadodin watan Ramadan ne saboda haka yana da gayar muhimmanci mallakarsa domin ana samun littafi,saboda a iya binciken da na yi ban ga wani littafi da ya tattaro ayyukan watan Ramadan ba kamar shi.

          5-Ziyarori:Mustahabbi ne ziyarar Imam Husain[AS] daga kusa ko nesa a daren farko na watan Ramadan,da daren sha-biyar da kuma daren karshe,ko da mutum bai samu biya ziyara kebantacciya ba ta ta wadannan darare to in ya biya ziyarar Ashura a dararen to ya wadatar.Haka nan ziyarar Imam Ali[AS] a daren 21 da dai sauransu.Yin wa]annan ziyarori a irin wa]annan munasabobi yana da falaloli da kuma fa’idodi masu yawa,daga cikin wa]annan fa’idodi shine yana da]a kusanta mutum ga Manzon Allah da kuma Ahlul bayt[AS].

          6-Infa}i:Wannan wata na Ramadan ana so mutum ya yawaita sadaka da kyauta da kuma ciyarwa ta fuskoki dabam dabam kuma ga mutane dabam dabam,yazo akan cewa babu wani wata wanda Manzon Allah yake yawaita infa}i kamar watan Ramadan.Saboda haka ana so mutum ya yawaita sadaka da kyauta ga ‘yan uwansa na jini da na addini da kuma ma}wabta da dai sauransu,muna da kyakkyawan misali daga jagoranmu wato Sayyid Zakzaky[H] yadda yake ciyarwa ta fuskoki dabam dabam musamman ga makwabta a cikin wannan wata na Ramadan.

7-Raya darare:Ana so idan mutum zai iya ya raya dararen watan Ramadan baki ]ayansa,idan kuma ba zai iya ba to sai ya raya wasu daga cikin muhimman darare a cikinsa kamar daren farko,daren 15,19,21,23 da kuma daren }arshe.Raya dare anan ana nufin ya kasance baki ]aya daren mutum bai yi barci ba,wato ya shagaltu da ibadodi dabam dabam.Idan mutum ya bibiyi tarihin wasu bayin Allah zai ga wasu sun kwashe shekaru 40 suna raya dararensu da ibadodi wasu sama da haka,ba mamaki mutum yaga wahalar abun,amma jikin mutum yana da wata ]abi’a shine duk abunda ka ]ora shi akai ko ka saba masa to zai ginu akai,kafin mutum ya saba zai iya shan wahala,amma jikin na sabawa shike nan.Daga cikin siffofin ibadur-Rahman shine cewa suna raya dare da ibada.

          8-Ayyukan dararen lailatul-}adri:Daren lailatul }adri kamar yadda yazo a Al}ur’ani da kuma Hadisi dare ne mai falala da kuma asraru.Sai dai akwai sa~ani tsakanin Ahlus sunna da kuma Ahlul bayt kan wa]anne ne dararen lailatul }adri.Ahlus sunna sun tafi akan cewa daren lailatul }adri imma daren 21,23,25,27 da kuma 29.A mahanga ta Ahlul bayt daren lailatul }adri imma daren 19,21 da kuma 23 ne.Ibadodin wannan dare mai albarka sun kasu gida biyu,akwai na Aam,akwai kuma na khaas,na Aam sune wa]anda ake yi a kowane dare daga cikinsu,na kuma khaas sune wa]anda kowane dare ya ke~anta dasu misali na daren 21 daban yake da na daren 23,ga mai bu}atar ganin wa]annan ibadodi yana iya duba mafatihu ko wasu littafai na Addu’oi.

          9-Wanka:A duk watanni na Musulunci babu watan da yake da wanka na shari’a kamar watan Ramadan,saboda mustahabbi ne a daren 1,3,5,7,9,11,13,15,17,19 mutum yayi wanka,ana so kuma tun daga daren 21 har ya zuwa daren 30 kowane dare mutum yayi wanka.Wanka anan shine shigen yadda mutum yake wankan Jumma’a.Yana da muhimmanci mutum yaga cewa bai rasa ko ]aya daga cikin wa]annan wankan ba,saboda yinsa yana da falaloli masu yawa.

          10-Iitikafi:Daga cikin ibadodin watan Ramadan akwai Iitikafi wato wanda galibi ake yinsa a goman }arshe,kuma yana da hukunce-hukunce da kuma bayanai kamar yadda Fu}aha’u suka yi bayanai a cikin littafan fi}hu,ga mai bu}atar bayani sanka-sanka akansa to sai ya koma zuwa ga Risala ta Mujtahidin da yake Ta}lidi da shi.

          11-Bankwana da watan Ramadan:A duk watanni na Musulunci babu wani wata wanda idan yazo }arshe akwai addu’oi na bankwana dashi sai watan Ramadan,wanda wannan ka]ai ya isa ya nuna falala da fifikon watan Ramadan kan sauran watanni.Wa]annan addu’oi na bankwana akwai wa]anda aka ruwaito daga Manzon Allah[S] da Imam Zainul-Abidin[AS] da kuma Imam Sadik[AS] kuma in son samu ne mutum ya karanta dukkan wadannan addu’oi da aka ruwaito daga wadannan Ma’asumai,idan mutum ya duba cikin littafin Ikbal zai ga ya kawo su duka.

3-Nasihohin bayan watan Ramadan:

Ga biyar daga ciki:- 1- Godiya ga Allah (T) ga wannan babbar ni’ima da ya yi masa, na nuna masa farkon watan Ramadan, kuma ya nuna masa }arshensa. Domin in mutum ya yi tunani zai ga akwai masu mutune da yawa wa]anda ba su samu wannan ni’imar ba. Wato Allah (T) bai raya su, ya nuna masu watan ba. Ko kuma wasu Allah (T) ya nuna masu farkon watan amma ba su ga }arshensa ba. Saboda wannan ni’ima da Allah (T) ya yi wa mutum, sai ya gode masa ta hanyar sujudu-shukur ko salatu-shukur. Wato sujudar godiya ko Sallar ta godiya. Haka nan ya gode ma Allah (T) na muwafa}a da ya yi masa na ayyuka na ibadodi da ya ni’imata shi, kuma ya ba shi ikon aikatawa a cikin watan. Domin in mutum ya yi tunani zai ga wasu, sun kasance a cikin watan, amma ba su da lafiya wanda ya shiga tsakaninsa da aikata wa]annan ayyuka na ibadodi. Ko kuma ga su a cikin watan, amma sune cikin gafala ko kasala na aikata wa]annan ibadodi. Kuma duk lokacin da mutum ya gode wa Allah (T) kan wata ni’ima da ya yi masa, to ya bu]e wa kansa }ofar }ari ne. Wato kamar yadda Allah (T) yake cewa; “ Idan kuka gode zan }ara maku”.

2- Muhasaba:- Wato mutum ya zauna ya yi wa kansa hisabi, ta hanyar tafakkur (tunani) ya tambayi kansa, shin ya samu ci gaba a addininance, in an kwatanta da gabanin kamawar watan Ramadan da kuma yanzu da ya zo }arshe ko ya }are? Misali ala}arsa da Allah (T). Ala}arsa da Manzon Allah (S), ala}arsa da Ahlul Baiti (AS), ala}arsa da gidan lahira. Ala}arsa da aikata addini wajen bin umarnin ko nisantar hani. Duk wa]annan da aka ambata, dama wa]anda ba a ambata ba, ya samu ci gaba ne a cikinsu ko akasin haka? Domin kamar yadda wani Malamin Irfan yake cewa; “Duk wanda watan Ramadan ya kama ya kuma }are, bai samu tasirantuwa da hasken watan Ramadan ba, to ya sani duhun zunubansa sun wuce hasken wannan wata mai haske mai haskakawa.” Kuma ita muhasaba, in son samu ne, mutum ya kasance kowace rana yana yin ta, misali ko da safe ko da yamma, ko kafin ya kwanta da daddare, ko kuma bayan ya tashi Sallar Tahajjud, wato mutum ya yi wa kansa hisabi dangane da kyawawan ayyuka da kuma munanan ayyuka da ya aikata a ranar. Bayan muhasabar, sai ya gode wa Allah (T) na muwafa}a da ya yi masa na aikata kyawawan ayyuka, munanan ayyuka kuma da ya aikata ya nemi Allah (T) ya gafarta masa.

A ta}aice dai yi wa kai hisabi kowace rana, yana daga cikin ayyuka da ke da gayar muhimmanci da mutum ya kamata ya lizimta wa kansa. Domin ya zo daga Imam Kazim (AS) yana cewa; “Baya daga cikin wanda bai yi wa kansa hisabi kowace rana”. Kuma shi hisabi ma kai kamar yadda Malaman Irfan suka yi bayani, ya kasu kashi hu]u:- 1- Akwai hisabi Yaumiyya (na kullum). 2- Akwai hisabi na Usbu’iyya (na mako). 3- Akwai hisabi na Shahariyya (na wata). 4- Akwai hisabi na Sanawiyya (na shekara). Wato in son samu ne mutum ya sunnata wa kansa, yin wa]annan hisabobi guda hu]u na kowace rana shi ne wanda aka yi bayaninsa a sama. Na kowane mako shi ne mutum kowane mako. Misali, kowace ranar Juma’a, mutum ya yi wa kansa hisabi na abin da ya aikata daga waccan Juma’ar zuwa wannan Juma’a na kyawawa ko munanan ayyuka. Na wata kuma shi ne misali }arshen kowane wata ya duba ayyukan da ya aikata a watan? Na shekara kuma shi ne misali na watan Ramadan da aka yi bayani a sama da kuma ya dubi ayyukan da ya aikata, da kuma ci gaba ko rashin ci gaba da ya samu a addinance daga watan Ramadan da ya gabata, zuwa wannan na bana. A ta}aice dai lizimtar yi wa kai hisabi ta wadannan fuskoki da aka ambata, zai taimaka wa mutum sosai wajen mujahadarsa da kuma sulukinsa zuwa ga Allah (T).

3- Afuwa:- Wato kamar yadda ake fata da kuma sa rai ga Allah (T) mutum ya fita watan Ramadan yana yafaffe, wato wanda Allah (T) ya yi wa afuwa daga laifukansa. To shi ma ya yafe wa mutune, musamman ma ’yan uwansa mabiya Ahlul Bait (AS) dangane da laifukan da suka yi masa. Kuma kamar yadda aka yi bayani a shekarar da ta gabata cewa Imam Zainul Abidin (AS) ya kasance yakan yi haka a }arshen watan Ramadan, wato yakan yi afuwa ga duk wa]anda suka yi masa laifi. Domin kamar yadda ya zo Allah (T) mai afuwa ne kuma yana son afuwa. Akwai ma wani bawan Allah da yake cewa zai ji kunyar Manzon Allah (S) gobe }iyama a ce ga shi ya tsaya da wani mabiyin Ahlul Baiti (AS) ]insa, domin neman ha}}insa gare shi. Saboda haka wannan bawan Allah ya kasance kowace rana yakan ce; “Ya Allah! Duk wani mabiyin Ahlul Baiti (AS) da ake rubuta masa laifi saboda ni, na yafe masa”.

A ta}aice dai ]abi’a ta yin afuwa, wata siffa ce da ya kamata mutum ya siffata da ita. Domin idan mutum ya kasance mai yawan afuwa ga ’yan uwansa muminai, haka zai iya kasance masa wata wasila da Allah (T) zai zamanto mai yawan yi masa afuwa

5- Khauf da kuma raja’a:- Wato tsoro da kuma fata, ko }auna ga Allah (T). Ana so ga mutum idan watan Ramadan ya zo }arshe, musamman ma daren }arshe, da ranar }arshe, ya kasance cikin wa]anda shu’uri guda biyu wato na khauf da kuma raja’a. Ya kasance yana tsoron wannan Azumi na watan Ramadan da ya yi da kuma sauran ayyuka na ibadodi da ya aikata a ciki, Allah (T) ya kar~a. Addu’o’in da ya yi Allah (T) ya kar~a, ko bai kar~a ba shi }ashin kansa, Allah (T) ya kar~a shi, a matsayin bawa na gari, ko bai kar~e shi ba. A lokacin guda da yake wannan shu’uri na tsoro ga Allah (T) kan wa]annan abubuwa da aka ambata. To daga }arshe sai ya yi tunanin raja’a, wato }auna da kuma fata na cewa yana ganin Allah (T) ya amshi Azuminsa, ya amshi ayyukan da ya yi na ibadodi ya amshi addu’o’insa, ya kuma kar~e shi a matsayin bawa na gari a wannan watan na Ramadan. Domin kyautata zato ga Allah (T) ga dukkan al’amura yana da muhimmanci mutum ya ginu a kai. Ya ma zo a Hadisi cewa; “Allah (T) yana cewa ina nan inda bawa yake zato na”. Wato in ka kyauta ta wa Allah (T) zato ga al’amura ko mutum ya munana zato a kai, to haka abin zai kasance. Saboda haka ana son mutum ya kasance mai yawan kyautata wa Allah (T) zato ga dukkan al’amuransa, na addini ne, na duniya ne, ko kuma na lahira ne. A ta}aice dai ana son mutum ya tarbiyyantu a kan wa]annan siffofi guda biyu, wato na tsoro ga Allah (T) da kuma }auna da sa rai gare shi, ga dukkan ayyuka na ibadodi da ya aikata da kuma sauran ayyuka na ]a’a da yake yi.

Wannan ke nan baki ]aya a ta}aice dangane da wasu ladubba, da Malaman Irfan suka yi bayani, wa]anda ake so mutum ya aikata idan watan Ramadan ya zo }arshe ko ya }are. Da fatan za a kiyaye, baya haka kuma ana so mutum ya kasance tsarkake, ya kuma ]ore a kan haka har ya zuwa wani wata na Ramadan in Allah (T) ya raya shi. Domin in mutum bai kiyaye wannan tsarkaka ba, to misalinsa zai zama kamar wanda ya wanke tufafinsa ne, ya kuma goge su, bayan haka kuma sai ya jefa su a kwata. Saboda haka tsarkakuwa da mutum ya samu daga zunubansa ta hanyar gafara da kuma afuwa da yake fatan Allah (T) ya yi masa a watan, to sai ya yi iyaka iyawarsa wajen nisantar zunubai na zahiri da ba]ini domin aikata zunubai yana da illoli masu yawan gaske a addinin mutum da duniyarsa da kuma lahiyarsa. A ta}aice dai zunubi guba ce babba mai kisa ga ruhin ]an’adam da kuma }azantar da ruhin. Sannan kuma ana son mutum ya samu isti}ama da sabati ga wa]annan ayyuka na ibadodi daban-daban da ya aikata a watan Ramanda. Wato ya tsayu a kai har ya zuwa wani watan Ramadan ]in insha Allah.

Duk da kasancewa dai da wuya ya yi kamar watan Ramadan a sauran watanni, to ya zamanto dai akwai wani mi}idari na ayyuka ]in da zai lazimta wa kansa, kuma ya tsaya da su, ba tare da yankewa ba, sai da wani uzuri. Domin isti}ama da sabati a kan ibadodin da mutum ya lizimta wa kansa yana da fa’idodi masu yawa, daga ciki akwai; misali idan mutum bai da lafiya, ko ya yi tafiya,ko kuma wasu shigul kamar ‘programms’ na gwagwarmaya. To kasantuwar wa]annan abubuwa da aka ambata, sai ya zama bai samu yin wasu ibadodi da ya saba yi ba, to za a rubutu masa lada na wa]annan ayyuka da ya saba yi kamar ya aikata, sa~anin ko akasin haka. Wato idan ya kasance ayyuka ]in jefi-jefi yake yi, wani lokaci ya yi, wani lokacin kuma ya kasance bai yi ba, wato bai tsayu a kai ba, to irin wannan ko da wa]annan abubuwa sun bijiro masa, kamar rashin lafiya, ko tafiya, ko wani shugul, to ba za a rubuta masa lada na ayyukan ibadodi daban-daban da za su dinga kusanta shi ga Allah (T) ba. Wa]annan ayyuka na ibadodi Malaman Irfan sun kakkasu kashi biyar sune:- 1- Yaumiyya (na kullum). 2- Usbu’iyya (na mako). 3- Shahariyya (na wata). 4- Sanawiyya (na shekara). 5- Umriyya (naso ]aya a rayuwa) kuma dukkan nau’ukan ayyuka na ibadodi kamar; 1- Salla. 2- Karatun Al}ur’ani. 3- Azumi. 4- Addu’o’i. 5- Azkar. 6- Ziyara na Ma’asumin (AS). 7- Muhasaba, ko wanne daga cikin wa]annan yana da wanda ake son yin kullum da mako da wata da shekara, wani kuma daga ciki ko da sau ]aya a rayuwa. Misali a nan shi ne Salla, in za a iya tunawa a Arba’ain ]in Imam Husain (AS) an kawo Salloli da aka samo daga Manzon Allah (S) da kuma Ahlul Baiti (AS) wa]anda ake yi kullum da mako da wata da kuma shekara, wanda ba a kawo ba, ita ce Salla umriyya, wato wadda ake son mutum ya aikata ko da sau ]aya a rayuwarsa. In mutum ya bincika zai ga Imamai 12 na Ahlul Baiti (AS) kowannensu. Akwai Sallarsa, wato tun daga Imam Ali (AS) zuwa Imam Mahdi (AS) in mutum ya duba littafin Mafatihul Jinan ya kawo wa]annan Salla. To irin wa]annan Salloli, ana son mutum ya yi ta kowace Imami, ko da sau ]aya ne a rayuwarsa. To haka kuma ta ~angaren karatun Al}ur’ani in mutum ya duba baya ya sauka da ake son mutum ya yi a}alla sau ]aya wata. To akwai surori na Al}ur’ani da ake son karanta su kullum, misali Suratul Mulk, Suratul Sajada, Suratul Dhukan, Suratul Wa}i’a, Suratul Yasin, Suratul Lu}man, dukkansu in son samu ne ana son mutum ya karanta su kowane mako. Misalin su shi ne a daren Juma’a, akwai Suratul Kahaf, Isra’i, Shu’ara, Namli, {isas, {amar da dai sauran Surori in mutum ya duba littafin Mafatihul a ayyuka na daren Juma’a zai ga surori. Haka nan a ranar Juma’a ana son karanta Suratul Ali-imran, Nisa’i, Hud, Saffat da kuma Suratul Rahman.

Haka nan kuma surorin da ake son karantawa na kowane wata, akwai Suratul A’araf, Anfal, Taubah, Yunus da kuma Suratu Namli. Misali kuma Surori na shekara, shi ne Surar Ankabut da kuma Rum da ake son karantawa a daren 23 na watan Ramadan. To wa]annan Surori na Al}ur’ani na kullum, mako, wata, shekara, suna zaman kansu ne, wato ba su da ala}a da saukar da mutum ya saba yi. To haka nan addu’o’i akwai na safe da yamma da ta’a}ibat na Salloli na mako, kuma shi ne kamar wanda aka samo daga Imam Sajjad (AS) wato kowace rana da addu’arta. Kamar yadda mai Mafatihu ya kawo. Addu’ar wata kuma ita ce wadda mai Dhiyau Salihin ya kawo, in mutum ya duba zai gani tunda ga ]aya ga wata, har ya zuwa 30 ga wata, ita wannan addu’a ta shekara, ita ce kamar shigen na watan Ramadan, wanda wasunsu ana yi cikin yinin Ramadan, wasu kuma a dararen Ramadan.

Addu’a Umriyya kuma ita ce dukkan addu’o’i da aka samo daga Ma’asumai (AS) wato wa]anda suka zo a littafin addu’a. Mutum ya karanta ko wannen su ko da sau ]aya ne a rayuwarsa, wato a nan an nufin addu’o’i da bai lizimta wa kansa karanta su ba. A ta}aice dai irin wa]annan tsari na ibadodi ake son kowannenmu ]an uwa ne ko ’yar uwa ya tsara wa kansa ya kuma tsayu a kai har ya koma ga Allah (T).

 
Home Maudu'oi daban-daban Nasihohin watan Ramadan
Copyright © 2022. www.tambihin.net. Designed by KH