Saturday, 02 December 2023
Email
Make My Homepage
RSS
Register
Dabio'in Imam Sadiq {AS} Print E-mail
Written by Administrator   
Tuesday, 26 March 2019 18:08

1-AKLA{-[INSA:

A-AFUWARSA,Imam sadi}[AS] ya kasance mai yawan afuwa,ba wai kawai ya kan yi afuwa ga wanda yayi masa laifi bane,a’a yakan ma nema masa afuwa a wajen Allah[T]misaliakwai wani mutum da yaje wajen sa sai yace ma Imam Sadi}[AS]waneko yace kaza da kaza gare ka,wato marasa kyau,ciki har da zakikamar yadda yazo a ruwayar,sai Imam Sadi}[AS] yace ma kuyangar sa[baiwarsa] kawo min abin al-wala,data kawo sai yayi alwala,bayan haka yai sallah raka’a biyu bayan haka kuma yai addu’a yace, “Ya ubangiji wannan mutumin ya ta~a ha}}ina,to,na yafe masa,kai ne mafificin yafewa,ka yafe masa kada ka kama shi,ko kayi masa hisabi saboda ni.”Shi wanda ya kawo wannan maganarsai yai tsammani,Imam Sadi}[AS] zai ma mutumin mummunar addu’a ne,amma sai yaga akasin hakawannan babban darasi negare mu.Haka nan an ruwaito cewa wani mutum cikin mahajjata sai jakar ku]insa ta fa]i,ya dudduba bai gani ba,sai ya ga Imam Sadi} [AS] yana sallah a masallacin Manzon Allah [S].To da yake bai san ko waye ba,kawai wal’iyazubillah sai yace shi ya ]aukar masa jaka.Sai Imam Sadi} [AS] yace masa cikin lausasawa,mene ne cikin jakar? Yace dirhami dubu ke ciki.Sai Imam Sadi} [AS] ya bashi dirhami dubun.Mutumin ya wuce kenan beyi nisa ba,sai ya ga jakar ku]in nasa,sai ya dawo wajen Imam Sadi} [AS] yana cewa ya yafe masa ,ya mi}a masa dirhami dubun,sai Imam Sadi} [AS] yace ba zai amsa ba,ya tafi ya bashi yace masa, “Duk abinda ya fita hannuna ,to ba zai dawo ba”.Shine wannan mutum abin ya bashi mamaki ,sai yaje ya tambaya,wai waye wannan? Sai aka ce masa Ja’afarus- Sadi} ne.Shine ya tafi yana cewa haba,shi ya san wannan aiki sai shi! Shine Imam Sadi} [AS] ya ke cewa, “Mu Ahlul Baitin Manzon Allah,]abi’unmu shine yin afuwa ga wanda ya zalunce mu”.Mu duba wannan }issa mu gani,zamu ga cewa A’imma [AS] ba wai kawai sun fuskanci jarabawowi wajen masu tafi da iko na zamunansu bane,a’a har da jarabawowi daga mutanen gari,in ba haka ba don ba kaga kayanka ba,mutum na sallah sai kace shi ya ]aukar maka.

 B:KYAUTAR SA [AS]:Imam Sadi} [AS] ya kasance mai yawan kyauta,wani daga cikin sahabbansa,ya shiga wajensa yace masa yana cikin matsalolina rayuwasaboda haka yana son Imam Sadi} ya taimaka masa da addu’a,sai Imam Sadi} [AS] ya aika akawo masa wata jaka da aka kawo ya mi}a masayace wannan jaka akwai dirhami ]ari hu]u,kaje ka biya bu}atarka da shi kuma zan yi maka addu’ar.                                                                                                                                                        Haka nan wani fa}iri ya ta~a zuwa neman taimako wajensa,sai ya bashi dirhami 400,sai fa}irin ya amsa ya tafi yana godiya.Sai Imam Sadi} [AS] yace wa khadiminsa je kace wa mutumin ya dawo .Sai wannan khadimin yace masa baya tambaye ka ba,ka kuma bashi? Sai Imam Sadi} [AS] ya amsa masa da cewa ; “Manzon Allah [S] yace mafificiyar sadaka itace wadda ta wanzar da wadata,sai Imam Sadi} [AS] ya mi}a masa zobe mai tsada,kamar yadda yazo a ruwayar,yace masa duk lokacin da aka shiga cikin matsala ka sayar da zoben.                                                                                                                                             Kuma Imam Sadi} [AS] ya kasance yakan aika da kyauta ga wani ko ga wasu ba da sanin cewa daga wajensa bane,misaliakwai wani ]an uwansa na jini lokaci bayan lokaci yakan aika da kyautar ku]i mutumin ya tambayi ]an sakon wannan da yake aiko wa da wannan sa}on lokaci bayan lokaci wa nene? Sai ]an sa}on yace masa bai son a bayyana ko wanene,kawai sai wannan mutumin ya kada baki yace kai wannan mutumi na taimaka mana,amma ga Ja’afar ]an uwana ne,ga shi da ku]i amma ko dirhami ]aya bai taimake ni da shi ba.Mu duba kuma irin wannan jarabawa daga ‘yan uwa na jini,shi yana }ule da Imam Sadi} [AS]alhali shi yake aika masa da wannan taimako.   

Haka nan kuma yazo akan cewa Imam Sadi} [AS]idan dare yayi, lokacin da duhu yayi duhu yakan ]auki kayayyaki na abinci da kumaku]i, ya ]auka da kansa yana bin gidajen matalauta yana raba musu,basu san ko waye ba,sai bayan rasuwar Imam Sadi} [AS] suka ga abubuwan da aka saba basu na agaji ya yanke,suka fahimci ashe Imam Sadi}[AS] ne ke kai masu wa]annan kayayyakin.

                C:TAUSAYINSA:Imam Sadi} [AS] ya kasance mai yawan tausayi.Akwai wani daya shiga wajen Imam Sadi} [AS] sai ya gan shi launinsa ya canza,kuma cikin damuwa,sai mutumin yace masa lafiya? Sai Imam Sadi} [AS] yace masa; “Na hana hawa saman daki ,sai na shiga cikin gida na ga ]aya daga cikin kuyangina ta hau ]auke da ]aya daga cikin yara na da take reno,ganina sai ta firgita ta ]imauta har wannan yaron ya fa]o ya kuma rasu to wannan damuwa da kaganni a ciki ba wai saboda rasuwar wannan yaron nawa bane, a’a yadda na ga ta firgita hankalinta ya tashi shine tausayinta ya kama ni”.Daga }arshe Imam Sadi} [AS] yace mata ba komai har sau biyu.Yace kuma ta tafi ya ‘yanta ta saboda Allah [T].

                2.GIRMAMAWARSA GA MANZON ALLAH [S]:An ruwaito cewa akwai wani daga cikin sahabban Imam sadi} [AS] ya kasance ya kan je majalisin Imam Sadi} [AS],sai aka kwana biyu bai je ba,ran da yaje sai Imam Sadik [AS] yace masa,kayi kwana ki bangan ka ba.Sai yace masa haihuwa aka yimin,an sami da namiji,sai Imam Sadi} [AS] yace Allah yayi masa albarka,ya tambaye shi wane suna kasa mishi? Sai yace nasa masa Muhammad,jin haka sai Imam Sadi} [AS] ya sunkuyar da kansa }asa yana cewa har sau uku, Muhammad! Muhammad! Muhammad!!! Sa’annan yace kaina da na iyali na da wa]anda suke a doron kasa baki ]aya,su kasance fansa gareka ya Manzon Allah [S]”.Daga }arshe yace masa. “Tunda kasa masa suna Muhammad,to kada ka zage shi,kada ka dake shi,kada ka munana masa”.Yace kuma ka sani babu wani gida a doron }asa wanda akwai mai suna Muhammad a ciki face mala’iku zasu dinga tasbihi kowace rana a gidan.Akwai ma Hadisi da yazo cewa talauci baya shiga gidan da akwai mai suna Muhammad.Mu duba ta’azimin sa ga Manzon Allah [S] na sun kuyar da kai,da yaji sunan Manzon Allah [S],da kuma abinda ya fa]a ma wannan mutum daya sa ma ]ansa sunan Manzon Allah [S],yace kada kayi masa kaza da kaza,wato wannan yana alamta gayar girmamawar sa ga Manzon Allah [S].

                3.IBADARSA:Imam Sadi} [AS] ya kasance mai yawan ibada,yazo akan cewa a zamaninsa baki ]aya babu wanda ya kai shi yawan ibada,akwai ma fa]in Malik ]an Anas,wato shugaban mazhabar malikiyyah yace; “Na jajje wajen Ja’afar ]an Muhammad lokuta da yawa,amma duk lokacin da naje sai in samu yana ]ayan uku; ko yana sallah,ko karatun Al}ur’ani,ko kuma yana Azumi”.Akwai kuma wani da ya ga Imam Sadi} [AS] ya yi sujuda a masallacin Manzon Allah [S],mutumin yana zaune yana jin Imam Sadi} [AS] ya na tasbihi a cikin sujudar,sai wannan mutumin ya ]aukar wa kansa cewa,ko zai dinga }idaya wannan tasbihi da yake yi,yana ta }idayawa,sai da Imam Sadi} [AS] ya yi tasbihi 360 sannan ya ]ago daga sujudar.Akwai kuma wata rana Imam Sadi} [AS] yana karanta Al}ur’ani a cikin sallah sai aka ga yanayinsa ya canza,bayan da ya gama sallar sai aka tambaye shi akan haka sai yace, “Ban gushe ba ina karanta wa]annan ayoyi na Al}ur’ani ba, har na kai matsayin da kamar ina jinsu mubasharatan daga wanda ya saukar dasu”.Haka ma Imam Sadi} [AS] ya ta~a kasancewa a wani wata na Ramadan ba shi da lafiya,amma duk da haka a daren 23 na watan yace akai shi masallacin Manzon Allah [S],haka ya dunga ibada duk da halin da yake ciki na rashin lafiya har wayewar gari.                                                    

      Akwai wata rana suna tafiya da wani mutum akan dabba kawai sai yaga Imam Sadi}[AS] ya sauko yayi sujuda,kuma ya tsawaita a sujudar,shine da ya ]aga kai daga sujudar sai shi wannan mutumin ya tambayi Imam Sadi} [AS] dalilin haka.Sai Imam Sadi} [AS] yace masa yayi ne saboda godiya ga Allah [T] kan wata ni’ima da yayi masa,watau sujudu shukru.Kuma ita wannan sujuda ta godiya ana son mutum ya saba da yin ta a duk lokacin da Allah [T] yayi masa wata ni’ima,ko kuma ya tun ku]e masa wata musiba saboda yin haka hanya ce ta da]a samun abinda Allah ya ba ka ko kuma da]a tsare ka daga abin da ya tsare kawato kamar yadda Allah Ta’ala yake cewa idan kuka gode zan }ara maku.                         

   Haka nan yazo akan cewa duk lokacin daya tsaya zai yi sallah akan ga launin sa ya canza,kuma jikinsa na makyarkyata ba don komai ba sai saboda tsoron Allah [T] da kuma ta’azimin wanda zai tsaya gaba gare shiwato Allah [T].                                                                                                                  

Haka nan kuma ya kasance mai yawan addu’oi,an samo addu’oi da yawa daga wajensa,akwai ma wani malami daya tattaro addu’oin da aka ruwaito daga wajen Imam Sadi} [AS] ya mai she shi littafi,yasa masa suna Sahifatu-Sadi}iyya ana samun littafin.Haka nan kuma Imam Sadi} [AS] ya kasance mai yawan azumi,kuma ya kasance ya kan kwa]aitar da mai azumi cewa idan mutum na azumi to ya kiyaye ruhin azumin alal misali ya kan ce; “Idan kana azumi to jinka da ganinka da harshenka suyi azumi [wato su kame] daga munanan abubuwa,yace kada ranar da kake azumi ta zama kamar ranar da baka azumi.Wato ranar da mutum yake azumi ya da]a kame ga~o~insa daga sa~a wa Allah [T] fiye da ranar da bai azumi.Yazo akan cewa wata rana Imam Sadi} [AS] yana fa]in cewa “Na kasance lokacin ina saurayi,wato matashi,na kasance ina yawan ibada,har Babana yace min in sassauta saboda idan Allah [T] yana son bawa,to yakan yarda da ka]an daga wajensa”.A ta}aice dai Imam Sadi} [AS] ya kasance mai yawan ibada ta kowace fuska,wato a salloli,karatun Al}ur’ani,Azkar,Azumi,Addu’oi da dai sauransu.

                4.ILIMINSA:Mutum zai iya cewa duk janibobin rayuwar Imam Sadi} [AS] babu wani janibi daya fi fice akai,kamar wannan janibi na iliminsa saboda ya samu yana yi na ba da ilimi da kuma ya]a shi fiye da sauran A’imma na Ahlulbayt [AS]har ma yana yawan fa]in cewa; “Ku tambaye ni gabanin ku rasa nidomin babu wanda zai baku Hadisai a bayana kamar yadda nake baku Hadisan”.Akwai kuma in da yake cewa; “Na san littafin Allah [Al}ur’ani] ciki da bai kamar tafin hannuna”.Akwai kuma in da yake cewa na san abinda yake cikin sama da abinda ke cikin }asa da abinda ke cikin Aljanna da kuma wuta da abinda ya kasance da kuma abinda zai kasance daga nan har zuwa sa’ar }iyamah”.                                                              Shugabannin mazhabobi guda biyu na madrasa ]in Ahlus Sunnah duk a wajen sa suka yi karatu,wato Abu Hanifashugaban mazhaban Hanafiyya ,akwai ma wata Magana tasa da yake cewa;ba domin shekaru biyu da yayi yana karatu gun Imam Sadi} [AS] ba,to daya halaka.Haka nan Malik ]an Anas wato shugaban mazhaban Malikiyya,shima yayi karatu a wajensa,ba wai kawai yayi karatu a wajensa bane,a’a ya tasirantu sosai da wasu abubuwa daya gani daga rayuwar Imam Sadi} [AS]misaliyadda yaga Imam Sadi} [AS] yana ta’azimin Manzon Allah [S] in zai ambaci sunansa a wajen bada hadisi ko kuma idan yaji sunansa ko kuma ba zai fa]i wani hadisi na Manzon Allah [S] ba sai yana da alwala,ire-iren wa]annan abubuwan sun yi tasiri ga Malik sosai,domin takai ma shima ya kwaikwayi haka daga Imam Sadi} [AS].Akwai ma lokacin da Imam Sadi} [AS] yace masa “Yana son sa”.Yazo akan cewa duk lokacin da Malik ya tuna wannan magana ya kanyi farin ciki,kuma ya gode wa Allah [T].                             

     Kuma Imam Sadi} [AS] koyarwar da yayi,yayi ne a dukkan fannoni na ilimi kamar Tafsir,Tauhid,Fi}hu,Hadisi da dai sauransu.A ta}aice dai babu wani fanni wanda Imam Sadi} [AS] bai karantar ba,kai hatta fannin ilimin kimiyya wato ilimin ‘science’ kamar Chemistry,Biology, da kuma Physics duk asalin su daga wajensa ne.Hatta malaman kimiyya magabatansu sun tabbatar da haka.Kuma a cikin almajiran Imam Sadi} [AS]wanda ya yi fice a wannan ilimi na kimiyya shine Jabir ]an Hayyan.Mutum in yana son }arin bayani sosai kan wannan ilimin kimiyya da Imam Sadi} [AS] ya koyar, ya samu littafi mai suna A’IMMATUNA juz’I na ]aya ya duba.

10- Zantukan Malamai dangane da shi:- 1-Abu Hanifa ya ce; “Ja’afar ]an Muhammad shi ne mafificin Fa}ihu da na gani.” Wani wajen kuma yana cewa; “Ban ta~a ganin mafi sani ba, kamar Ja’afar ]an Muhammad.” Haka nan akwai wani da ya tambayi Abu-Hanifan cewa, mene ne za ka ce dangane da wanda ya yi wa}afin dukiyarsa ga Imam, to wane Imam ne ya cancanta a yaba? Ya ce wanda ya cancanta, shi ne Ja’afar ]an Muhammad, domin shi ne Imam ]in gaskiya.

2-Imam Malik ya ce; “Idonsa bai ta~a gani ba, kunnensa bai ta~a ji ba, wanda ya fi fifiko kan Ja’afar ]an Muhammad”. A ilimi ibada da kuma tsantseni. A wani waje kuma ya ce, Ja’afar ]an Muhammad yana daga cikin masu gayar ibada da zuhudu da kuma tsoron Allah (T).

3-Abdullahi Asshafi’iy ya ce; “Ja’afarus Sadi} yana da darajoji masu yawa.” Limamai masu yawa (wato na mazahib) sun ruwaito Hadisai daga wajen sa, misali, Malik ]an Anas, Abu Hanifa, Sufyanu-Sauri, Ibn Juraih, Shu’uba da dai wasunsu. A ta}aice dai akwai zantukan Malamai masu yawa, a kan fifikonsa a kan Malamai da sauran mutanen zamaninsa.

11- Wasiyyarsa:- Imam Sadi} (AS) ya yi wasiyyoyi masu yawa, wasu ga ]ai-]aikun mutane, mabiyansa da ma wa]anda ba mabiyansa ba, wasu kuma ga Shi’arsa, wasu ga ’ya’yansa da dai sauransu. Saboda gudun tsawaitawa ga wasu daga ciki:

1- Wasiyyarsa da ya yi wa wani da ake cewa Abi Usama. “Ina yi maka wasiyya da jin tsoron Allah da tsantseni da mujahada, da fa]in gaskiya, da ri}on amana da kyakkyawar ]abi’a, da kyakkyawar ma}wabtaka. Ku kasance masu kira da ayyukanku, ku kasance }awa gare mu, kada ku kasance muni gare mu. Ina horonku da tsawaita ruku’u da sujada”.

2- A wata wasiyyarsa da ya yi wa wani daga cikin Sahabbansa ya ce; “Idan ]ayanku yana son ba zai tambayi Allah (T) wani abu ba face ya ba shi, to ya ]ebe tsammani daga wajen mutane baki ]aya. Ya kasance bai da wata fata ko }auna face ga Allah (T). In Allah (T) ya ga haka a zuciyarsa, to ba zai tambaye shi komai ba, face ya ba shi. Haka nan kuma ku yi wa kanku hisabi gabanin a yi maku (wato gobe }iyama), domin }iyama tana da matsayi 50, a kowane matsayi, shekara dubu ne.”

3- Sannan gab da zai rasu, ya sa a tara masa mutanen gidansa duka, da kuma ’yan uwansa na jini. Da suka ha]u baki ]aya, ya dube su, ya ce masu; “Cetonmu, bai samun mai wula}antar da Salla.” Da dai sauran wasiyyoyinsa masu yawa, wa]anda suke cikin littafan tarihin rayuwar A’imma.

12- Wafatinsa:- Imam Sadi} (AS) kamar yadda aka ambata ya rasu 25 ga watan Shawwal, a shekara ta 148 bayan Hijira, sakamakon guba da aka sa masa a inabi. Ya rasu yana da shekara 65. A wata ruwaya 68. Kabarinsa na Ba}i’a ne a Madina. Amma ya zo a tarihinsa cewa, kafin rasuwarsa, ya yi jinya ta rashin lafiya, wadda ta kai ma ya samu rama sosai a jikinsa. Wata rana yana cikin wannan jinya, wani daga cikin Sahabbansa ya shiga wajensa, da ya gan shi, sai ya fashe da kuka. Sai Imam Sadi} (AS) ya ce; “Mene ne kake wa kuka?” Ya ce; “Saboda halin da na gan ka”. Sai Imam Sadi} (AS) ya ce; “Ka daina kuka, ai shi mumini komai nasa alheri ne. Ko da ko za a yanka shi gunduwa-gunduwa, alheri ne a wajensa, in kuma ya yi mulkin Gabas da Yamma na duniya alheri ne a gare shi.”

 
Home Darusan Akhlaq Dabio'in Imam Sadiq {AS}
Copyright © 2023. www.tambihin.net. Designed by KH