Tuesday, 09 August 2022
Email
Make My Homepage
RSS
Register
Nizamin Ibadodi Print E-mail
Written by Administrator   
Tuesday, 26 March 2019 17:51

Wannan maudu’i na tsarin ibadodi maudu’i ne mai gayar muhimmanci domin zai taimaka mana insha-Allah wajen tsara ibadodin mu da kuma fahimtar littafai na ibadodi.Malaman Irfan sun yi bayani akan cewa ayyuka na Ibadodi a nizamin su sun kasu kashi biyar:1-Ayyuka Yaumiyya[wato wadanda ake son aikatawa kullum] 2-Ayyuka Usbu’iyya[wato wadanda ake son aikatawa ko wane mako] 3-Ayyuka Shahariyya[wato wandanda ake son aikatawa ko wane wata] 4-Ayyuka Sanawiyya[wato wandanda ake son aikatawa ko wace shekara] 5-Ayyuka Umriyya[wato wadanda ake son aikatawa ko da so guda a rayuwar mutum].To irin wannan nizami na ibadodi ake so kowannen mu ya tsara ma kansa kuma ya tsayu da aikata su.Kuma ayyuka na ibadodi kamar Salloli,Addu’oi,Karatun Al}ur’ani,Azkar,Azumi,Ziyarori na Ma’asumin[AS],to ko wannen su idan mutum yayi bincike a littafai na addu’oi zai ga cewa suna cikin wannan tsari guda biyar da aka ambata.Littafai na Addu’oi ko ayyuka suna da yawa,amma wa]anda suka fi shahara sune:

1-Misbahul-mutahajjid na Shaikh [usiy.

2-Misbahu na Shaikh Khaf’ami.

3-Misbahu na Sayyid ibn Ba}iy.

4-Baladul Amin na Shaikh Khaf’ami.

5-Zadul-Ma’ad na Allama Majlisiy.

6-I}bal.

7-Falahus-sa’il.

8-Jamalul Usbu’i.

9-Duru’il-Wa}iya.dukkan su na sayyid ibn [awus.

10-Iddatu-da’i.

11- Dhiya’us-salihin.

12- Mafatihul jinan na Shaikh Abbas Al-}ummiy,cikin wa]annan littafai akwai wa]anda suke baki ]ayan abin da ke ciki ayyuka ne sanawiyya misali littafin I}bal da kuma Zadul Ma’ad.Saboda haka wannan rubutu insha-Allah zai gudana ne akan wa]annan tsari guda biyar, a kuma cikin wa]annan littafai da aka ambata.

            1-Ibadodi Yaumiyya:Ibadodi yaumiyya sune ayyukan ibadodi da mutum ke maimaita aikata su ko wace rana.Ga misalan wasu daga cikin ayyukan ibadodi na yaumiyya.

A-Salloli:Yin salloli raka’a 51 ko wace rana.Wannan raka’a 51 ya ha]a da sallolin wajibai da nafilfilinsu da kuma sallar tahajjud tare da sallar shafa’i da witiri.A warware ga lissafin adadin raka’o’in na salloli wajibai,wato daga sallar Asuba zuwa sallar Isha’i in mutum ya lissafa zai ga 17 ne.Sai nafilfilin ko waccensu:Raka’a 2 gabanin sallar Asuba.Raka’a 8 gabanin sallar Zuhur.Raka’a 8 gabanin sallar Asar.Raka’a 4 bayan sallar Magriba.Raka’a 2 a zaune bayan sallar Isha’i,amma 2 nan ya na makwafin 1 ne.Sallar Tahajjud Raka’a 8, Sallar Shaf’i Raka’a 2,Sallar Witri Raka’a 1.in mutum ya lissafa zai ga adadin ya kama 34,wato na raka’o’in nafilfin,in mutum ya lissafa da wa]ancan raka’o’i na wajibai 17 zai ga ya ta shi akan 51.

B-Addu’o’i:Addu’o’in yaumiyya suna da yawa,misali addu’o’i na safe da yamma,idan mutum ya duba littafin mafatihul jinan sashen Ba}iyatus-salihat babi na farko fasali na biyar zai ga irin wa]annan addu’o’i na safe da yamma,haka nan in mutum ya duba cikin littafin Dhiya’us-salihin shafi 275 zai gani.Daga cikin addu’o’i na yaumiyya akwai addu’o’i na ta’a}ibat ]in salloli,wato addu’o’in da ake bayan salloli na wajibai,kuma wa]annan addu’o’i na ta’a}ibat sun kasu kashi biyu.Akwai ta’a}ibat na amma,akwai kuma ta’a}ibat na khassa.Ta’a}ibat na amma sune wa]anda ake son karanta su bayan ko wace sallah ta wajibi.Ta’a}ibat na khassa kuma sune wa]anda suka ke~anta ga ko wace sallah ta wajibi,wato ko wace sallah daga cikin wa]annan salloli wajibai biyar ta na da na ta.To littafin da ya kawo wa]annan ta’a}ibat na Amma da khassa shine Misbahul mutahajjid,idan mutum ya bincika zai ga cewa kusan dukkan sauran littafan addu’o’ da suka kawo ta’a}ibat na salloli zai ga cewa daga misbahul mutahajjid suka ciranto shi,misali mutum na iya duba littafin baladul Amin ko misbahu dukkansu na sheikh Khaf’ami.ko kuma mutum ya duba littafin mafatihul jinan a ta’a}ibat na salloli da ya kawo a babi na farko fasali na farko zai ga cewa shima daga cikin Misbahul mutahajjid ne ya ciranto.

C-Karatun Al}ur’ani:Akwai wasu surori ko ayoyi da ake son karanta su ko wace rana,misali yazo a hadisi cewa ana son mutum ya karanta suratul mulk,suratu sajada,suratu Dhukan,suratu Yasin,suratul Wa}i’a kafin mutum yayi barci da daddare da dai sauransu kamar suratul }adri,suratul Iklas,suratu Takasur.Haka nan ana son karanta suratu Yasin da safe.Haka nan akwai wasu surori da ayoyi da ake son karantawa bayan salloli na wajibai kamar suratul iklas da ayatul kursiyyi.Haka nan akwai wasu surori da ake son karanta su a salloli na wajibai da kuma na nafilfili,misali a sallar tahajjud raka’a ta farko ana so bayan fatiha mutum ya karanta }ulhuwallahu 30,haka nan ma a raka’a ta biyu.A raka’a ta 3 bayan fatiha mutum ya karanta suratul muzammil,raka’a ta 4 bayan fatiha suratun naba’i.A raka’a ta 5 bayan fatiha suratu yasin da dhukan,raka’a ta 6 bayan fatiha suratul wa}i’a da suratul mudassir.A raka’a ta 7 bayan fatiha suratul mulk,raka,a ta 8 bayan fatiha suratul Insan.Wani tambihi anan shine bayan mutum ya karanta wa]annan surori na ko wace raka’a to zai iya karanta wani sashe na Al}ur’ani wato ya ]ora akai.Wannan kuma shine misalan karatun Al}ur’ani na yaumiyya,wato wannan baya ga hizfi na karatun Al}ur’ani da mutum yake yi ko wace rana,misali idan izu biyu yake kullum ko 10 ko 20,kuma mutum na iya sa karatun hizifofin da ya sa ba yi a cikin sallar tahajjud ]in sa..

D-Azkar:Akwai azkar na yaumiyya masu yawa da suka zu,misali azkar na safe da yamma ko Azkar na bayan sallah da dai sauransu.

E-Ziyarori:wato na Ma’asumin,alal misali akwai ziyara ga Imam Mahdi[AS] da ake son mutum ya dun ga yi ko wace rana bayan sallar Asuba,ga mai son ganin zirayar yana iya duba mafatihul jinan gaban Du’a’u Nudba zai ga ziyar.Haka ana son ziyartar Imam Husain safe da yamma,}arancin abin da mutum zai ce a wannan ziyarar shine:Assalamu Alaika ya Aba Abdullah,Assalamu alaika warahmatullahi wabarakatuh.Idan mutum na son ganin ayyuka na yaumiyya,to akwai littafi da aka yi musammam akan haka sunan littafin shine Falahus-sa’il na Sayyid ibn [awus.

            2- IBADODI USBU,IYYA:Ibadodi na usbu’iyya sune ibadodin da mutum ke maimaita aikata su a cikin ranakun mako,ga misalan wasu daga ciki.A-Salloli:

1.Daren jumma’a raka’a 2,ko wace raka’a bayan fatiha }ulhuwallahu 70.sai kuma ranar jumma’a raka’a 8 ko wace raka’a }ulhullah

2.Daren Asabar raka’a 4,ko wace raka’a bayan fatiha }ulhullah 7.Sai kuma ranar Asabar raka’a 4,ko wace raka’a bayan fatiha }ul ya ayyuhah kafirun 3,bayan mutum yayi sallama a raka’a ta 4,sai ya karanta ayatul kursiyyu

3.Daren lahadi raka’a 6,ko wace raka’a bayan fatiha }ulhullahu 7.Ranar lahadi raka’a 2,raka’a ta farko bayan fatiha Inna A’a]aina 3,raka’a ta biyu bayan fatiha }ulwullah

4.Daren litinin raka’a 2,ko wace raka’a bayan fatiha,Ayatul kursiyyu,}ulhuwallah,sai suratul fala}i da nasi dukkansu sau 1.Bayan sallama sai yace Astagfirullah 10.Ranar litinin raka’a 4,raka’a ta farko bayan fatiha Ayatul kursiyyu 1.Raka’a ta biyu bayan fatiha }ulhuwallah 1.Raka’a ta ukku bayan fatiha }ul-azu-birabbil-fala} 1.Raka’a ta hu]u bayan fatiha }ul-azu-birabbin nas

5.Daren talata raka’a biyu,raka’a ta farko bayan fatiha Inna Anzalnahu 1.Raka’a ta biyu bayan fatiha }ulhuwallahu 7.Ranar talata raka’a biyu,ko wace raka’a bayan fatiha,Wattini,{ulhuwallah,fala}I da Nasik o wane sau

6.Daren laraba raka’a biyu,ko wace raka’a bayan fatiha Ayatul kursiyyu,Inna anzalnahu,Iza ja’a ko wane sau 1.sai kuma }ulhullahu sau 3.Ranar laraba raka’a 2,ko wace raka’a bayan fatiha Iza-zul sau 1,sai kuma }ulhuwallah sau

7.Daren Alhamis raka’a 6 ko wace raka’a bayan fatiha }ulya-ayyuhal kafirun sau 1,sai }ulhuwallah sau 3.Ranar Alhamis raka’a biyu,bayan fatiha ko wace raka’a Iza-ja’a da kuma Inna-A’a]aina kowace so 5.Wa]annan salloli sune salloli na ranakun mako,in mutum ya duba cikin littafin Dhiya’us-Salihin zai ga ya kawo su.Kuma yana da muhimmanci ko wannen mu ya tsayu da wa]annan salloli wato baya ga wa]ancan raka’o’i 51 na yaumiyya.

B- Addu’o’i:Idan mutum ya duba cikin mafatihul jinan babi na ]aya,fasali na ukku zai ga ya kawo addu’ar ko wace rana na cikin mako.Haka nan idan mutum ya duba littafin Dhiyaus-salihin,zai ga ya kawo addu’ar ko wane dare da kuma rana na mako.irin wa]anan addu’oi sune ake ce ma addu’o’i na mako,saboda in ka yi na ko wace rana to sai makamanciyar ranar ta zagayo zaka sake yi.Idan mutum na son tsawaitawa a addu’o’i na usbu’iyya yana iya duba misbahul mutahajjid ko Baladul Amin.Haka nan Du’au kumail da Du’au Nudba duk suna cikin addu’o’i na usbu’iyya.

C-Karatun Al}ur’ani:Akwai surorin da ake son karantawa a wasu daga cikin ranakun mako misali daren jumma’a ana son karanta wa]annan surorin:Suratul Isra’i,suratul khahafi,suratu shu’ara’i,suratu Namli’suratul {isas,suratu Sajda,suratu Yasin,Suratu Sad, Suratu Fussilat,Suratu Dhukan,Suratul Ah}af,Suratu [ur,Suratul {amar,Suratul Wa}i’a da kuma suratul jummu’a.Haka nan kuma ranar ko wace jumma’a ana son karanta wa]annan surori:Suratu Ali-Imran,Suratu Nisa’i,Suratu Hud,Suratu Saffat da kuma Suratur-Rahman.Haka nan kuma ana son karanta Suratul Ma’ida ko wace ranar Alhamis.Haka nan kuma akwai wasu surori da ake son karantawa a cikin salloli na wajibai a cikin mako,misali a sallar magriba ta daren jumma’a ana son karanta suratul Jumma’a a raka’a ta farko wato bayan fatiha,a raka’a ta biyu kuma }ulhuwallah.A sallar Isha’i kuma raka’a ta farko suratul jumma’a,raka’a ta biyu kuma Sabbihis-ma rabbikal-a’ala.A sallar Asuba ta ranar jumma’a raka’a ta farko bayan fatiha suratul jumma’a,raka’a ta biyu }ulhuwallah.A sallar jumma’a ko Azahar,raka’a ta farko bayan fatiha suratul jumma’a,raka’a ta biyu suratul munafi}un.A sallar la’asar ranar jumma’a,Raka’a ta farko suratul jumma’a,raka’a ta biyu }ulhuwallah.Haka nan a ranar Litinin da Alhamis a sallar Asubar su,raka’a ta farko suratul Insan,raka’a ta biyu Suratul Gashiya.Haka nan a sallar Tahajjud ta daren jumma’a ana son karanta wa]annan surori a cikin su.Raka’a ta farko a sallar tahajjud ]in ana son mutum ya karanta }ulhullah sau ]aya,raka’a ta biyu }ulya ayyuhal kafirun sau ]aya.Raka’a ta ukku suratu Sajada,raka’a ta hu]u suratul Mudassir.Raka’a ta biyar suratu Fussilat,raka’a ta shidda suratul Mulk.Raka’a ta bakwai suratu Yasin,raka’a ta takwas suratul Wa}i’a.

D-Azumi:Azumin mako shine na ranar litinin da Alhamis.

E-Ziyara:Idan mutum ya duba cikin mafatihul jinan babi na farko fasali na biyar zai ga ya kawo ziyarorin da ake yi ga Manzon Allah[S] da kuma Ahlul bayt[AS],wato ko wace rana da ma’asuman da ake ziyarta.Haka nan kuma ana son duk daren jumma’a ko ranar jumma’a mutum ya karanta ziyarar Ashura.Saboda haka ana son mutum ya kasance yana da wannan nizami na ibadodi Usbu’iyya.Ga mai bu}atar ganin littafi da aka yi musamman kan ayyukan ibadodi na mako yana iya neman littafi mai suna Jamalul-Usbu’i na Sayyid ibn [awus.In sha-Allah a darasi na ga ba za a kammala bayani akan wannan maudu’i na nizamin ibadodi.

 
Home Maudu'oi daban-daban Nizamin Ibadodi
Copyright © 2022. www.tambihin.net. Designed by KH