Tuesday, 09 August 2022
Email
Make My Homepage
RSS
Register
Zalunci da illolinsa Print E-mail
Written by Administrator   
Tuesday, 26 March 2019 17:50

Insha Allah a wannan darasi bayani zai gudana kan wannan maudu’i Zalunci da kuma illolinsa wato a Addinin mutum da duniyarsa da kuma lahirarsa.Idan mutum ya bibiyi surori na Al}ur’ani mai girma zai ga cewa ayoyi masu yawa sun yi bayani kan zalunci da kuma azzalumai.Haka nan kuma idan mutum ya bibiyi Hadisai da aka ruwaito daga Manzon Allah[S] da kuma Aimma na Ahlul bayt[AS] kan zalunci da kuma azzalumai zai ga cewa Hadisan suna da yawa.Idan mutum ya dubi rayuwar ]an Adam da kyau a wannan gida na duniya zai samu cewa koda wane lokaci rayuwarsa ]ayan biyu ne ko dai Zalim ko Mazlum wato ko dai azzalumi ko kuma wanda aka zalunta,Imam Ali[AS] a wani Hadisi yana cewa, “Ku je ma Allah ranar lahira kuna wa]anda aka zalunta kada kuje masa kuna Azzalumai”.A wata ruwaya kuma ya ce,“Kada ka kasance azzalumi ka kasance wanda aka zalunta.”Misali mutum ya dubi rayuwar Annabawa da Aimma da kuma sauran bayin Allah Ta’ala ya ga irin zalunci da Azzalumai na zamanoninsu suka yi masu.Daga cikin manufofi na aiko da Annabawa da kuma bayin Allah da suka yi tajdidin addini akwai fada da zalunci da kuma tsaida adalci a bayan }asa,haka nan idan muka dubi babban aikin da Imam Mahdi[AF] zai yi idan ya bayyana shine kauda zalunci da azzalumai a bayan }asa da kuma shinfi]a adalci a duniya baki ]aya,mu kuma dubi wani Hadisil-}udusi wanda Allah Ta’ala yake cewa, “Lalle ni na haramta zalunci akai na kuma na sanya shi haramun a tsakaninku.”Bayan wannan ‘yar shinfi]a bayani zai gudana kan wa]annan ababe:1-Ayoyi na Al}ur’ani kan zalunci da kuma azzalumai.2-Hadisai da suke magana kan zalunci da kuma azzalumai.3-Nau’oin zalunci.4-Taimaka ma azzalumai.5-Taimaka ma wanda aka zalunta.6-Addu’ar wanda aka zalunta.7-Illolin zalunci.

          1-Ayoyin Al}ur’ani kan zalunci da kuma Azzalumai:Akwai ayoyi masu yawa a cikin Al}ur’ani mai girma da suka yi magana kan zalunci da kuma Azzalumai saboda haka ba za a iya kawo su dukkansu ba amma ga wasu daga ciki:Allah Ta’ala yana cewa, “Lalle Azzalumai ba zasu ci nasara ba.”Suratul An’am aya ta 21.A wata aya kuma Allah Ta’ala ya ce, “Lalle Azzalumai suna da azaba mai ra]a]i.”Suratu Ibrahim aya ta 22.A wata aya kuma Allah Ta’ala yana cewa, “Allah baya son Azzalumai.”Suratu Ali Imran aya ta 57.A wata aya kuma Allah Ta’ala yana cewa, “Lalle Allah baya shiryatar da mutane Azzalumai.”Suratul An’am aya ta 144.A wata ayar kuma Allah yana cewa, “Ha}i}a mun halakar da }arnonin dake gabaninku lokacin da suka yi zalunci.”Suratu Yunus aya ta 13.A kuma wata aya Allah Ta’ala yana cewa, “Kada kayi tsammani Allah Ta’ala ya gafala daga abinda Azzalumai suke aikatawa.”Suratu Ibrahim aya ta 42.Da dai sauran ayoyi masu yawa wanda ba za a iya kawo su ba saboda gudun tsawaitawa.

          2-Hadisai da suke magana kan zalunci da Azzalumai:Suma in mutum ya bincika zai ga cewa suna da yawa ga wasu daga ciki:1-Manzon Allah[S] ya ce, “Kuji tsoron yin zalunci domin zalunci duhu ne ranar kiyama.” Wato zai kasance ma mutum musiba ranar lahira.2-Manzon Allah[S] ya ce, “Za a zo da mutum ranar lahira tare da lada mai yawa,sai wani mutum ya zo ya ce,ya ubangiji ya zalunce ni,sai a kwashi ladarsa aba da ita ga wanda ya zalunta,can wani shima ya zo cikin wa]anda ya zalunta a sake ]ibar ladarsa a bashi,haka-haka dai har ta kai ga ba yada wata sauran lada,idan wani wanda ya zalunta ya zo to sai a kwashi zunubinsa a sa masa har ta kai daga }arshe akai wannan azzalumi zuwa ga wuta.”3-Imam Ali[AS] ya ce, “Duk wanda ya ci dukiyar ]an uwansa a bisa zalunci to zai ci wani yenki na wuta ranar }iyama.”4- Imam Sadi} ya ce, “Duk wanda ya yi zalunci to sai Allah ya salla]a masa wani da zai zalunce shi.5-Imam Ali ya ce, “Duk wanda ya yi zalunci to Allah zai gaggatar da halakarsa, a wata ruwaya ya ce, “Duk wanda ya yi zalunci to zai gajarta rayuwarsa.”wato rayuwarsa ba zata yi tsawo ba.6-Imam Ba}ir ya ce, “Kaji tsoron zaluntar wanda bai da wani mai taimako akan ka in ba Allah ba.”7-Imam Ali ya ce, “Ranar hukunci akan azzalumi tafi tsanani akan ranar zalunci kan wanda aka zalunta.” Wato ranar da Allah zai kama azzalumi tafi tsanani gareshi kan ranar da ya zalunci wanda ya zalunta.8-Imam Ba}ir ya ce, “Abinda wanda aka zalunta yake samu daga azzalumi to yafi akan abinda azzalumi yake samu kan wanda ya zalunta.” Wato shi azzalumi ya cutar da wanda ya zalunta a duniyan ce,shi kuma wanda aka zalunta ya yi masa illa a addinan ce kamar misalin wancan Hadisin na sama cewa za a kwashi ladar azzalumi in yana da ita a bama wanda ya zalunta in kuma bai da ita akwashi zunubin wanda aka zalunta a zuba masa,shi yasa a wani Hadisi Manzon Allah yana cewa, “Zalunci nadama ne.” Wato }arshen shi nadama ne ga azzalumi a duniya da lahira,mutum ya dubi yadda }arshen azzalumai yake kasancewa tun a wannan gida na duniya ballantana kuma a lahira.

          3-Nau’oin zalunci:Zalunci kamar yadda Malaman Akla} suka yi bayani ya kasu zuwa nau’oi ko fuskoki dabam dabam wato ba kamar yadda mafi yawan mutane idan an ce zalunci tunani ya kan ta}aita kan zalunci tsakanin mutum da mutane,wato akwai wasu nau’oi na zalunci kamar zaluntar kai shine mutum ya zalunci kansa da kansa misali duk lokacin da mutum ya aikata wani zunubi }arami ne ko babba to ya zalunci kansa, haka nan kuma idan mutum zai iya aikata wani aiki na ibada ko ]a’a ga Allah Ta’ala sai ya zamo bai yi ba to ya zalunci kansa ko kuma ya kasance akwai wani gi~i tsakanin abinda yake yi da kuma wanda zai iya yi na ibadodi amma ya kasance bai cike gi~in ba to shima ya zalunci kansa,ashe kenan yana da gayar muhimmanci mu kasance cikin mujahada domin ganin cewa bamu zalunci kawukan mu ba.Akwai kuma wani nau’i na zalunci wato zalunci ga dabbobi shima zaluntar su yana iya kai mutum ga shiga wuta kamar yadda ya zo a wani Hadisi na wata mata da ta ]aure magenta ba ta bata abinci bata kuma sake ta domin ta je ta nema ba,sakamakon wannan mummunan aiki nata yayi sanadiyyar shigar ta wuta.Akwai kuma zalunci na tsakanin mutum da mutum ]an uwansa,irin wannan zalunci zai iya kasancewa ta fuskoki dabam dabam misali ko ta jiki ko dukiya ko mutunci,ta jiki kamar kashe shi ko raunata shi ko dukansa da dai sauran cutarwa ta jiki,ta dukiya kamar sace dukiyar ko ~arnatata ko wala}antata da dai sauransu,ta mutumci kamar yi masa sharri ko }azafi ko munana zato gareshi da dai sauransu to irin wannan zalunci ta wa]annan fuskoki da aka ambata duk lokacin da mutum yayi su ko wani daga ciki ga ]an uwansa mutum to zai kasance ya haifar ma kansa illa ko illoli masu yawa a rayuwarsa

          4-Taimaka ma Azzalumai:Mutum zai iya fuskantar makoma irin ta azzalumai a ranar }iyama sakamakon taimaka masu da yayi a wannan gida na duniya kan zaluncinsu,shi yasa akwai Hadisai masu yawa da aka ruwaito wa]anda suka yi kashedi da kuma hani ga taimaka ma azzalumai ga wasu daga ciki:1-Manzon Allah ya ce, “Ranar Al}iyama mai kira zai yi kira ina Azzalumai ina kuma wa]anda suka taimaka masu da duk wani nau’i na taimako komi }an}antars,an tattara su tare da su.” 2-Imam Sadi} ya ce, “Mai yin zalunci da wanda yake taimaka masa da kuma wanda yaji da]i ko ya yarda da abunda aka yi to dukkansu sun yi tarayya a zaluncin da aka yi.” Saboda haka lalle mutum yayi hattara na Azzalumi yayi zalunci ya goyi bayan abunda aka yi ko yaji da]i koma ya taimaka akan zalunci,shi azzalumi dama ya sai da lahirarsa domin ya samu duniya wato shi a}alla ya samu duniya kafin ta ku~uce masa lahira kam yayi asararta,to amma ga wanda ya goyi baya ko yaji da]i kan abunda aka yi shi yayi asarar duniya da lahira ne kasantuwar gobe }iyama za a tattara shine da Azzalumai su fuskanci makoma guda,akwai Hadisi da aka ruwaito daga Manzon Allah ya ce, “Mafi sharrin mutane shine wanda ya sai da lahirarsa domin ya samu duniya to mutumin da ya fi wannan sharri shine wanda ya sai da lahirarsa domin duniyar wani.” Wato shi Azzalumi ya samu tarkacen duniya kan zaluncin da yayi.3-Manzon Allah ya ce, “Duk wanda ya taimaka ma Azzalumi kan zaluncinsa to zai zo ranar Al}iyama a goshinsa an rubuta baka ba rahamar Allah.” 4-Imam Sadi} ya ce, “Duk wanda ya ba Azzalumi uzuri kan zaluncin da yayi to ba zai bar duniya ba sai Allah ya salla]o masa wanda zai zalunce shi kuma ba zai samu lada na zaluntar sa da aka yi ba.” 5-Manzon Allah ya ce, “Duk wanda yayi tafiya tare da Azzalumi domin ya taimaka masa kuma ya san cewa zalunci zai yi to ha}i}a ya fita Musulunci.” Wannan Hadisi yana da ban tsoro saboda haka yana da gayar muhimmanci mutum ya nisanci taimaka ma Azzalumai ta kowace irin fuska.Allah Ta’ala yana cewa a cikin Al}ur’ani, “Kada ku karkata ga Azzalumai wuta ta shafe ku.”

          5-Taimaka ma wanda aka zalunta:Akwai Hadisai masu yawa da aka ruwaito daga Manzon Allah da kuma Aimma na Ahlul Bayt kan muhimmancin taimaka ma wanda aka zalunta ga wasu daga ciki:1-Manzon Allah ya ce, “Duk wanda ya taimaka ma wanda aka zalunta daga wani Azzalumi to zai kasance tare da ni ranar {iyama.” 2-Imam Ali ya ce, “In ka ga wanda aka zalunta to ka taimake shi kan wanda ya zalunce shi.” 3-Imam Sadi} ya ce, “Babu wani Mu’umini da zai taimaki wani Mu’umini da aka zalunta face haka ya fi falala gareshi da yayi azumin wata guda.Babu wani Mu’umini da zai taimaki ]an uwansa face Allah ya taimake shi duniya da lahira.Babu wani Mu’umini da zai }i taimakon ]an uwansa alhali zai iya taimaka masa face Allah ya }i taimaka masa a duniya da lahira.

          6-Addu’ar wanda aka zalunta:Shima wannan akwai Hadisai masu yawa akai amma ga wasu daga ciki:1-Manzon Allah ya ce, “Ku ji tsoron Addu’ar wanda aka zalunta domin addu’arsa kar~a~~iya ce.” 2-Manzon Allah ya ce, “Ku ji tsoron addu’ar wanda aka zalunta ko da ko kafiri ne domin addu’ar bata da hijabi.” 3-Manzon Allah ya ce, “Ku ji tsoron addu’ar wanda aka zalunta domin yana ro}on Allah ne ya bi masa ha}}insa,Allah Ta’ala ko ba zai hana ma’abucin ha}}i ha}}insa ba.” Saboda haka duk wanda aka zalunta kuma yai addu’a to koda bai ga ijabar abinda ya ro}a ba, to ba yana nufin Allah bai amshi addu’ar bane a’a lokaci ne bai yi ba na ganin ijabar a aikace,misali mu dubi addu’ar da Annabi Musa yayi ga Fir’auna,Allah Ta’ala ya ce masa ya amshi addu’ar,ya zo akan cewa sai bayan shekaru 40 aka ga kar~uwar addu’ar a aikace,ya zo a wani Hadisil-}udusiy Manzon Allah ya ce, Allah Ta’ala ya ce, “Na rantse da ]aukaka ta da kuma buyata sai na ]auki fansa daga Azzalumi kusa ko nesa.” Wato abin a hannun Allah Ta’ala ya ke.

          7-Illolin zalunci:Duk lokacin da Azzalumi yayi zalunci to ya haifar ma kansa illoli masu yawa ga wasu daga ciki:1-[ebewar albarka:Wato zai kasance komi nesa ba albarka,rayuwarsa zata kasance ba ta da albarka,in mai dukiya ne zata kasance ba ta da albarka,in mai mulki ne zai kasance mulkin bai da albarka da dai sauransu.2-Gajeruwar rayuwa:Mai zalunci bai yawancin kwana a duniya,yama zo a Hadisi daga Imam Ali ya ce, “Duk wanda ya yi zalunci to ya karya rayuwarsa.” Mu dubi Yazidu[LA] koda ya mutu yana da shekaru 37 ne a duniya.3-Gushewar ni’ima ga Azzalumi:Wato zalunci yana sabbaba gushewar ni’ima ga mutum,Imam Ali yana cewa, “Zalunci yana gusar da ni’ima.” Wato in mulki ne Allah Ta’ala ya }wace mulkin misali bayan wa}i’ar Karbala Yazidu ko shekara ukku bai kai ba akan mulki Allah Ta’ala ya halaka shi,in dukiya ce ko lafiya Allah Ta’ala sakamakon zaluncin mutum sai ya }wace su.4-Barin mummunan ambato:Wato Azzalumi idan yayi zalunci to ko bayan mutuwarsa labarin abinda yayi zai wanzu ana fa]a ma wa]anda suka zo daga baya misali }issoshin Azzaluman da suka yi fa]a da Annabawa ko Aimma ko kuma wa]anda suka yi tajdidin Addini.Imam Ali a wani Hadisi yana cewa, “Kashedinka da zalunci saboda zai gushe ga wanda kayi ma amma kai illar zaluncin ya wanzu gareka.5-Zalunci yana kai ga mutum ya zamo muflis ranar }iyama wato ya zamo bai da lada wato ladarsa in ma yana da ita an bada su ga duk wa]anda ya zalunta,in kuma bai da ladar zunuban wa]anda ya zalunta a lafta mashi su.A ta}aice dai zalunci yana da illoli masu yawa ga duk wanda yayi shi a addininsa da duniyarsa da kuma lahirarsa kuma ba na duniya ne abin ji ba domin shi zai iya gushewa a’a na lahira mai dawwama.Imam Ba}ir[AS] ya ce, “Koda an zalunce ka to kai kada ka yi zalunci.”

 
Home Maudu'oi daban-daban Zalunci da illolinsa
Copyright © 2022. www.tambihin.net. Designed by KH