Saturday, 02 December 2023
Email
Make My Homepage
RSS
Register
Dabi’oin Imam Zainul Abidin (AS) Print E-mail
Written by Administrator   
Tuesday, 26 March 2019 17:44

Kasantuwar wannan wata da muke ciki na Muharram wanda daga cikin munasabobin dake cikinsa akwai wafatin ko shahadar Imam Zainul Abidin[AS] ya zo akan cewa yayi shahada ne sakamakon guba da khalifan Umayyawa na lokacin mai suna Walid dan Abdul Malik yasa masa a ranar 25 ga watan Muharram shekara ta 95 bayan hijira.Nan kuma wasu daga cikin Aklak ne na Imam Zainul Abidin domin su kasance darasi garemu da zamu darastu dasu :

            IBADARSA (AS): Imam Zainul Abidin ya kasance mai yawan Ibada. Wannan la}abin nasa na Zainul Abidin ya samo asali ne saboda yawan Ibadarsa da kuma ruhin da ke cikin Ibadar. Ga wasu misalai daga cikin Ibadodinsa:

a.Sujudarsa: Imam Zainul Abidin (AS) ya kasance mai yawan Sujuda saboda ma yawan Sujudarsa wannan la}abi nasa na ‘SAJJAD’ ya samo asali, kamar yadda hakan ya zo daga Imam Ba}ir (AS), ya ce: “Babana Ali bai tuna wata ni’ima da Allah (T) ya yi masa ba face ya yi sujuda ta godiya a kai, bai karanta wata Aya daga cikin Al}ur’ani ba alhali Ayar ta sujuda ce face ya yi sujuda, Allah (T) bai tun}u]e masa wani mummuna da yake gudu ko wani kaidin mai kaidi ba face ya yi sujuda a kai, bai gama wata Salla ta Farilla ba face bayanta ya yi sujuda ta godiya. Haka nan bai samu gyara tsakanin mutum biyu da matsala ke tsakaninsu ba face ya yi sujuda”. Saboda haka ake ce masa la}abi da Sajjad, wato wannan ya nuna sujuda ta godiya ba ta ta}aita da sujudar bayan Salla ba, a’a duk wata ni’ima da Allah (T) ya yi wa mutum ko kuma ya tunku]e masa wata musiba, to ya yi sujuda ta godiya ga Allah (T). Misali, ko da tafiya mutum ya yi ya dawo, to ya yi sujuda ta godiya ga Allah (T) da ya kai shi lafiya ya dawo da shi lafiya. Kuma kamar yadda aka sani godiya ga Allah (T) hanya ce ta samun da]i daga gurinsa (T), kamar yadda yake cewa cikin littafinsa: “Idan kuka gode, zan }ara maku.” Saboda haka, duk lokacin da mutum ya gode wa Allah (T) kan wata ni’ima da ya yi masa ta addini ko duniya, to kamar ya bu]e wa kansa }ofar samun }ari ne.

A ta}aice dai, rashin godiya ga ni’imar da Allah (T) ya yi wa mutum ko kuma sa~a wa Allah(T) a ni’imar, yakan sabbaba }wace ni’imar. Shi ya sa in mutum ya duba tarihin bayin Allah zai ga suna gode wa Allah (T) ga ni’imomin da ya yi masu ta hanyar ayyukan Ibadodi daban-daban. Misali, kamar yadda ya zo daga Manzon Allah (S) cewa, yakan tsaya wajen yin Sallar Tahajjud har dugadugansa su tsattsage. Da aka tambaye shi, me ya sa yake yin haka alhali Allah (T) ya gafarta masa? Ya ce: “Ba zan zamo bawa mai godiya ba.” Wato, wannan ya nuna mana lokacin da mutum ke yin Tahajjud ya zamanto yana shu’urin godiya ga Allah (T) da ni’imomin da ya yi masa.

b. Sallolinsa: Imam Zainul Abidin (AS) ya kasance mai yawan Salla. Ya zo a tarihinsa cewa a kowacce rana yakan yi Salla ta nafila raka’a dubu ]aya, kuma ya kasance a wa]annan Sallolin nasa mai gayar khushu’i. Kamar yadda aka sani, khushu’i a cikin Salla ya kasu kashi biyu: Akwai khushu’i na ‘}alb’, wato zuciya; akwai kuma khushu’i na ‘badan’, wato jiki. Ga misalan wa]annan khushu’ai guda biyu a cikin Sallolinsa:

An samo daga Imam Ba}ir (AS) yana cewa: “Imam Zainul Abidin (AS) ya kasance idan ya tsaya a Salla yakan tsayu kamar ka ce itaciya ce a tsaye, wato saboda rashin motsi.” Haka nan Abu Hamzatus Sumaliy yana cewa: “Na ga Imam Zainul Abidin yana Salla sai Alkyabbarsa ta goce a ]ayan kafa]arsa, bai sa hannu ya gyara ba har sai da ya gama Salla, sai aka tambaye shi a kan haka, wato me ya sa bai gyara ba? Sai ya ce masa: “Kaiconka! Ka san ko gaban wanda nake tsaye? Ai ba a amsar Sallar bawa face a kan asasin yadda ya halartar da zuciya a cikinta.” To, mu duba Sallolinmu mu gani ya muke wajen tsayuwa da wannan khushu’i na zuciya da kuma na jiki. Ya ma zo a tarihinsa cewa, saboda gayar khushu’insa a cikin Salla, in ya soma Salla bai jin duk wani abin da yake faruwa sai bayan ya gama Salla, sai ya ga ashe kaza da kaza sun faru yana Salla.

Ta }issar wani bawan Allah (T) yana Salla shi da almajiransa, sai wasu suka zo wajen wannan bawan Allah, da suka samu suna Salla sai suka ce, bari su je su dawo. Bayan Salla sai almajiransa suka ce ai ko sun ji zuwan su wane, sun ce za su je su dawo.sai bawan Allan yace “Ana Salla har kuka ji wasu sun zo sun ce kaza”. Ya ce masu; “To ku tashi ku sake Salla”. Wata }issa ta wani bawan Allah (T) shi ma ya yi Salla, bayan wani Limami, sai aka ga ya yanke Sallar ba a gama da shi ba. Shi ne bayan da aka gama aka tambaye shi, me ya sa haka? Ya ce, yaya zan bi Liman yana Salla alhali zuciyarsa na kasuwa. Aka je aka samu Liman aka ce ka ji abin da wane ya ce, ya ce tabbas haka ne, da nake ba da Salla ina tunanin in na gama zan je kasuwa in sayo kaza da kaza. Amma tambihi a nan shi ne, irin wannan Salla da ba khushu’i da ruhi a cikinta a Fi}ihance Sallar mutum ta yi, a Irfanance ne Sallar take da matsala. Insha Allah a darasin Akhla} in aka zo bayani dangane da ‘tazkiyya’ ]in Nafs, za a yi bayani dangane da ruhin Salla.

Haka nan Imam Zainul Abdin (AS) ya kasance idan Nafilfilin da ya saba yi suka ku~uce masa, a cikin yini yakan rama su da daddare, har ma an ta~a tambayar sa a kan haka, ya ce ba wajibi ba ne, amma yana da kyau in mutum ya saba aikata wani aiki na alheri ya dawwama a kansa. Kuma ya zo a kan cewa, aikin da Allah (T) ya fi so shi ne wanda aka dawwama a kansa komai }an}antarsa. Shi ya sa ya zo a kan cewa, mustahabbi ne mutum ya rama Salloli na Nafila da suka ku~uce wa mutum. Misali, a ce mutum bai samu yin Sallolin Nafila na Azahar da La’asar ba, to yana iya ranka su da daddare ko kuma Nafilar Magrib da Isha’i, ko kuma Sallarsa ta Tahajjud, bai samu yin su ba, saboda wani uzuri to zai iya rama wa]annan Nafilolin a cikin yini,

c. Addu’o’insa: Imam Zainul Abidin ya kasance mai yawan Addu’o’i kuma idan mutum ya bibbiyi tarihin Imamai ]aya bayan ]aya, zai ga cewa babu wani Imami daga cikin Imamai da aka tattara Addu’o’insa kamar yadda aka tattara na Imam Sajjad (AS). Mutum ya duba Sahifah ta Imam Ali (AS) da Imam Hasan (AS), Husaini (AS) har ya zuwa Sahifah ta Imam Mahdi (AS), ya kwatanta da Sahifah Sajjadiyya, wanda kuma har yau har gobe ana kan tattara wa]annan Addu’o’in nasa. Shi ya sa in muka duba za mu ga akwai Sahifah Kamilah, akwai Jami’ah, wato mai }arin wasu Addu’o’i na Imam Zainul Abidin (AS), wanda mai Sahifah Kamilah bai kawo ba. Kuma littafin Sahifah Sajjadiyyah ya kawo Addu’o’i na Yaumiyya, Usbu’iyya, Shahariyya da kuma Sanawiyya da kuma Addu’o’i na bu}atoci na duniya da kuma lahira, ga kuma Munajatoti daban-daban wanda za su taimakawa mutum wajen ]amfaruwarsa da Allah (T). A ta}aice dai, littafi ne wanda ya kamata a ce kowanenmu ya kasance, akwai wata Addu’a ko Addo’o’i da zai lizimci karanta wa kowace rana ko dare a cikinsa.

d. Karatun Al}ur’anin Imam Zainul Abidin (AS): Ya kasance mai yawan Karatun Al}ur’ani. Akwai lokacin da yake cewa, da mutanen Gabas da Yamma za su mutu (wato mutanen duniya gaba ]aya) da ba zan yi kewa ba, matu}ar akwai Al}ur’ani tare da ni. Domin tabbas, duk wanda yake karatun Al}ur’ani (karatu wanda yake akwai halartar da zuciya a ciki), ba ya kasance mutum na karatun da harshe amma zuciyarsa na wani waje, wato yana tunanin wani abu ba abin da yake karantawa ba. To irin wannan karatu mai ruhi, yakan sa mutum tunaninsa ya fita daga wannan duniya zuwa wata duniya, wato daga duniyar ‘Mulk’ zuwa duniyar ‘Malakut’, kamar dai yadda ‘Urafa’u’ suka yi bayani. A ta}aice dai, Imam Zainul Abidin (AS) saboda yawan Ibadarsa da kuma yadda }afafuwansa suke tsattsagewa wajen Salla, Imam Ba}ir (AS) har kuka yake yi in ya gan shi wani lokaci, saboda tausayi. Ga mai bu}atar ganin wasu Ibadodinsa, yana iya duba littafin ‘MUNTAHAL AMAL’, juz’i na 2.

            2. SHAJA’ARSA: Imam Zainul Abidin (AS) ya kasance mai gayar jaruntaka, wanda ya bibbiyi tarihin rayuwarsa zai ga haka. Ya ma zo a kan cewa, a zamaninsa babu wanda ya kai shi a wannan fage na Shaja’a. Misali, daga irin wannan jarunkata tasa, shi ne lokacin da aka kai shi wajen Ibn Ziyad (LA) ya fa]a, ya fa]i, ya fa]a, ya fa]i, ya fa]a, ya fa]i, daga }arshe Ibn Ziyad ya fusata ya ce a je a kashe shi. Imam Zainul Abdin (AS) ya ce: “Ahaf! Ai mu ba ka san cewa kisa al’ada ne a wajenmu (wato abin da aka saba) ba? Kuma karamarmu a wajen Allah (T) ita ce shahada”. Domin shi Ibn Ziyad yana ganin waye zai fa]a masa irin wa]annan maganganu da Imam Sajjad (AS) ya fa]a masa.

Makamancin haka ma ya kasance a fadar Yazid (LA), shi ma ya fusata ya ce a je a kashe Imam Sajjad(AS). Daga cikin abin da Yazid ya fa]i, Imam Sajjad(AS) ya mayar masa akwai cewa da ya yi,”Godiya ta tabbata ga Allah wanda ya kashe Babanka, ya zubar da jininsa”. Imam Sajjad (AS) ya mayar masa da cewa: “Allah ya tsinewa wanda ya kashe Babana.” Maganganu masu tsawo sun gudana tsakaninsa da Yazid da kuma wani Malamin fada na Yazid wanda shi ma Imam Sajjad ya fa]a masa maganganu, majalisin nasu ya tsawaita, har lokacin kiran Salla ya yi. Da mai kiran Salla ya zo wajen cewa na shaida Muhammad Manzon Allah ne, sai Imam Zainul Abidin (AS) ya dubi Yazid ya ce: “Wannan Manzon mai daraja Kakanka ne ko Kakana? In ka ce kakanka ne, duk wanda suke wannan majalisi da ma mutane baki ]aya sun san }arya kake yi. In kuma ka ce Kakana ne, to me ya sa ka kashe Babana, saboda zalunci da }iyayya kuma ka ribace matayensa? Azaba ta tabbata gare ka ranar }iyama, idan Kakana ne zai yi husuma da kai.” Yazid ya sake fusata. Ladan ya gama kiran Salla, ya ce ya ta da I}ama saboda yadda Imam Sajjad (AS) ya kunyata shi ya kuma wawaitar da shi a majalisin.

Ya ma zo a kan cewa tun asali, shi Yazid bai so ya bar Imam Sajjad (AS) ya yi magana ba, ]ansa Mu’awiyya shi ya matsa masa a kan ya bar shi ya yi magana, shi ne Yazidu yake cewa ]an nasa; “Ba ka san wa]annan sun gaji ilimi da fasaha ba, kuma sun ]an]ani ilimi ]an]ana? ]an nasa ya ce duk da haka dai ka bar shi, sa’annan ya }yale shi ya yi magana.

            3. AKHLA{ [INSA: Shi ma a wannan fage na Akhla} a zamaninsa ba wanda ya kai shi ballantana ya wuce shi. Ga misalan wasu daga cikin Akhla} ]insa:

a. Afuwarsa da kuma kau-da-kai daga wautar masu wauta. Akwai wani da ya ta~a zuwa ya samu Imam Sajjad (AS) ya ce, wane ya fa]i maganganu marasa kyau game da kai. Sai Imam Sajjad (AS) ya ce tashi mu tafi wajensa, suka tashi suka tafi. Shi wannan mutumin ya ]auka zai je ne ya fa]a masa shi ma maganganu. Lokacin da suka isa, sai ya ji Imam Sajjad (AS) na ce wa mutumin, “In abin da ka fa]i ba gaskiya ba ne, to Allah ya gafarta maka”. Akwai kuma wani lokaci da wani ya zo yana ta fa]in maganganun da ba su dace ba ga Imam Sajjad (AS), sai ya yi kamar bai ji shi ba. Ya yi ta yi, ya yi ta yi, sai can mutumin ya ce; “Da kai fa nake”. Sai Imam Sajjad (AS) ya ce, da kai nake kau da kai (wato ina ji na }yale ne). Mu dubi irin wannan jarabawa ta tsokanar fa]a.

Haka nan akwai wata rana ya fita sai wani mutum ya ha]u da shi, ya zage shi. Bayin Imam Sajjad (AS) da kuma mabiyansa da ke tare da shi a lokacin suka zabura za su ]auki mataki kan mutumin, sai Imam Sajjad (AS) ya ce masu, a’a. Sai ya samu mutumin ya ce masa, al’amarinmu ya ~oyu gare ka, kana da wata bu}ata mu taimaka maka? Mutumin sai kunya ta kama shi. Sai Imam Sajjad (AS) ya ba shi mayafin da ke tare da shi, ya kuma ce a ba shi Dirhami dubu. Bayan haka shi wannan mutum duk inda ya ga Imam Sajjad (AS), ya kan ce masa: “Lallai na shaida kai ]an Manzon Allah (S) ne.”

Ya zo a kan cewa, akwai wani ]an uwan Imam Zainul Abidin (AS) na jini da ya ta~a samun sa yana Masallaci shi da Sahabbansa, ya fa]a masa maganganu da ba su dace ba. Imam Zainul Abidin (AS) ya yi shiru bai ce masa uffan ba. Ya gama maganganun da zai yi ya tafi. Sai da dare ya yi Imam Zainul Abidin (AS) ya tafi ya same shi ya ce masa; “Ya ]an uwana in abin da ka ce dangane da ni gaskiya ne, to Allah ya gafarta maka”. Ya yi mai sallama ya juyo. Sai ]an uwan nasa ya yi nadama kan abin da ya yi, har ya biyo shi yana kuka. Har yake ce masa wallahi ba zan sake yi maka abin da bai dace ba, sai Imam Zainul Abdin (AS) ya ce masa; “Na yafe maka duk abin da ka ce”.

Mu dubi yadda A’imma (AS) suka fuskanci jarabawowi ba wai kawai daga masu tafi da iko ba, a’a, daga mutanen gari da ma ’yan uwansu na jini.

            Daga }arshe ga wasu sassa na rayuwarsa mai albarka:

1-Haihuwarsa:An haifi Imam Zainul Abidin a madina ranar jumma’a 5 ga watan shaaban shekara ta 38 bayan hijira.

2-Nasabarsa:Sunan mahaifiyarsa Maryam a wata ruwaya Fa]ima,asalinta ba farisa ce wato mutuniyar Iran,kuma ita ]iya ce ga sarkin Iran na lokacin mai suna Yazdajir,.kafin zuwansu Madina ta yi mafarki da Manzon Allah[S] da kuma Sayyida Zahra[AS].

3-Nash’a]insa:Imam Zainul Abidin ya tashi a madina,bayan haihuwarsa Allah ta’ala ya yi ma mahaifiyarsa rasuwa kuma shi ka]ai ne a wajen mahaifiyarsa.ya rayu tare da kakansa Imam Ali shekara biyu,tare kuma da Amminsa Imam Hasan shekaru 12,tare kuma da mahaifinsa Imam Husain shekaru 23.Ya kuma rayu bayan shahadar mahaifinsa shekaru 34 ne.

4-Shekarunsa:Imam Zainul Abidin[AS]ya rayu a duniya shekaru 57 ne.

5-La}ubbansa:Imam Zainul Abidin yana da la}ubba masu yawa,amma la}ubbansa da suka fi fice sune Sajjad wato saboda yawan sujudarsa.Zainul Abidin wato saboda yawan ibadarsa.kuma ana yi masa kinaya da Abu Muhammad.

6-Muddan Imamancinsa:Shekaru 34 ne.

7-‘Ya’yansa:Imam Zainul Abidin ya kasance yana da ‘ya’ya 15 maza 11,mata hu]u.

8-Wafatinsa:Ya rasu ranar 25 ga watan muharram shekara ta 95 bayan hijira.

9-{abarinsa:Yana a Madina ne wato a ma}abartar Ba}i’a.

 
Home Darusan Akhlaq Dabi’oin Imam Zainul Abidin (AS)
Copyright © 2023. www.tambihin.net. Designed by KH