Thursday, 27 January 2022
Email
Make My Homepage
RSS
Register
Darajoji da karamomin Imam Ali (AS) Print E-mail
Written by Administrator   
Tuesday, 26 March 2019 17:37

Rubutu ko bayani dangane da darajoji da kuma karamomin Imam Ali[AS] wani fage ne mai fa]in gaske,saboda idan mutum ya yi bincike zai ga cewa sahabban Manzon Allah[S] baki ]aya,ba a samu wani sahabi wanda malamai na Shi’a da Sunnah suka yi rubuce-rubuce na tarihinsa da kuma darajojinsa kamar yadda suka yi ga Imam Ali.Ahmad ibn Hambal wato shugaban mazhaba ta hanbaliyya ya ce, “Babu wani daga cikin sahabban Manzon Allah wanda darajojinsa suka zo a ruwayoyin hadisai kamar yadda suka zo ga Imam Ali.” Haka nan kuma Abdullahi ]an Abbas yana cewa, “Da a ce itatuwa na duniya baki ]aya za a mai da su al}aluma,koguna kuma su zama tawada,mutane da aljannu su zama marubuta,to ba za su iya }ididdige darajojin Imam Ali ba.” Idan mutum ya yi bincike kan darajojin Imam Ali zai ga cewa akwai darajojin da shi ka]ai ya ke~anta da su a wannan al’umma ta Manzon Allah koma a tarihin ]an Adam baki ]aya.Alal misali daga cikin abin da Imam Ali ya ke~anta da su a tarihin ]an Adam baki ]aya shine haihuwarsa da a ka yi a cikin ka’aba wanda wannan ba wai Malaman shi’a ba,a’a har malaman Ahlus sunna sun tabbatar da haka.Mutum yana iya duba littafin Nurul-Absaar na Shaikh Shablanji wanda yana ]aya daga cikin malaman Ahlus sunnah,a cikin littafin idan mutum ya duba,a in da yake bayani dangane darajojin Imam Ali zai ga ya kawo cewa an haife shi a cikin Ka’aba kuma ba’a ta~a haihuwar wani a cikin ka’aba gabaninsa ba sai shi.Kuma sanin mu ne cewa tarihi bai rubuta an haifi wani a cikin ka’aba ba a bayansa.Ga ma yadda wannan haihuwa tasa mai al-barka ta kasance a cikin Ka’aba:Ya zo daga ibn Ka’anab ya ce, “Na kasance ina zaune tare da Abbas ]an Abdul-Mu]allib tare kuma da wasu Banu Hashim kusa da Ka’aba,sai ga Fa]ima ‘yar Asad ta na zuwa wato mahaifiyar Ali a lokacin tana da cikinsa wata tara,na}uda ta kamata.Sai muka ji tana cewa: “Ya Ubangiji na,ni na yi imani da kai da kuma abinda ya zo daga wajenka ta hanyar manzanninka da kuma littafinka,kuma ni ina mai gasgatawa da zantukan kakana Annabi Ibrahim.Ina ro}onka da ha}}in wannan ]aki da wanda ya ginashi,da kuma wannan abin da ya ke cikin cikina,ka sau}a}e min wannan haihuwa.Sai ibn {a’anab ya ce sai muka ga Ka’aba ta bu}e,sai Fa]ima ‘yar Asad ta shiga ciki ya kasance bamu ganinta,bayan haka kuma in da ya bu]e ]in sai ya rufe,muka yi muka yi mu bu]e saboda sashen matayenmu su taimaka mata,}ofar Ka’aba ba ta bu]u ba,sai muka fahimci cewa to wannan wani al’amari ne daga wajen Allah Ta’ala.Bayan kwana hu]u sai gashi ta fito ]auke da Ali a hannunta.” Ya zo a kan cewa lokacin da ta yi nufin fita daga cikin Ka’aba sai ta ji sautin magana cewa, “Ya Fa]ima ki sa masa suna Ali.” Haka nan kuma Imam Ali shine farkon wanda ya amsa sa}on da Manzon Allah ya zo dashi a wannan al’umma,shine kuma farkon wanda ya yi sallah tare da Manzon Allah.Haka nan kuma a cikin sahabbai shi ya ke~anta da wannan la}abi na ‘Karramallahu wajhahu’ kamar yadda malaman Ahlus sunna suke ce mashi.Kuma ya zo a kan cewa Manzo bai ta~a shugabantar da wani sahabi a kansa ba,in mutum ya yi bincike zai ga haka alal misali ya}o}i da Manzon Allah ya aika wato wa]anda bai je ba to in dai Imam Ali na ciki bai shugabantar da wani a kansa sai dai ya sashi ya zama jagoran ya}in.Haka nan lokacin da Manzon Allah ya koma Madina ya ha]a ‘yan uwantaka tsakanin sahabbai muhajirin da kuma ansaar amma Imam Ali sai ya ke~eshi da ‘yan uwantaka gareshi wato bai ha]a shi da kawo ba sai shi.Haka nan daga cikin fifikon da Allah Ta’ala ya yi masa kan mutane baki ]aya shine aurensa ga Sayyida Fa]ima wato kasantuwar ta shugaban mataye baki ]aya.A ta}aice dai falaloli da kuma darajojin Imam Ali suna da yawan gaske wanda za a iya siffantasu da cewa la tu’addu wala tuhsa.Bayan wannan ‘yar shinfi]a bayani kan wannan maudu’i zai gudana insha Allah kan wa]annan ababe:1-Imam Ali a cikin Al}ur’ani mai girma.2-Imam Ali a cikin Hadisai.3-Imam Ali a cikin zantukan sahabbai.4-Falalar son Imam Ali.5-Karamomin Imam Ali.

          1-Imam Ali a cikin Al}ur’ani mai girma:Wato ayoyi na Al}ur’ani mai girma wa]anda suka sauka masu ala}a da Imam Ali,idan mutum ya yi bincike musammman a littafan tafsirai na Al}ur’ani zai ga cewa suna da yawa,akwai ma in da Abdullahi ]an Abbas ya ke cewa, “Babu wani wanda ayoyi na Al}ur’ani suka sauka dangane da shi kamar yadda suka sauka dangane da Ali,ayoyi ]ai-]ai har ]ari ukku -300- sun sauka gareshi.” Ayoyin Al}ur’ani da suka sauka wa]anda suke da ala}a da Imam Ali sun kasu kashi biyu akwai wa]anda ya yi musharaka da wasu a kai musammam Ashabul-kisa’i, misalin irin wa]annan ayoyi sune kamar ayar mubahala wato ayar, “Faman hajjaka fihi min ba’adi ma ja’aka minal ilmi fa}ul ta’alau nad’u.........”, ko ayar ta]hir wato ayar, “Innama yuridullahu..........” da dai sauransu,akwai kuma ayoyin da suka sauka wa]anda suke da ala}a da shi bai yi musharaka da kowa ba a cikinsu wato sun ke~anta da shine to ire-iren wa]annan ayoyi ne wani daga cikin malaman tafsiri na Ahlus sunna mai suna Mujahid yake cewa, “Ayoyi guda saba’in sun sauka ga Ali bai yi musharaka da kowa ba a cikinsu a wannan al’umma ta Manzon Allah.” Amma abin mamaki idan mutum ya yi bincike zai ga cewa wasu daga cikin ayoyin da Imam Ali ya ke~anta da su na falala an jingina ma wasu sahabbai an ce gare su ta sauka.To kasantuwar ba za a iya kawo dukkan wa]annan ayoyi ba da suka sauka dangane da Imam Ali saboda gudun tsawaitawa,ga mai bu}atar ganin wa]annan ayoyi dabam-dabam yana iya samun wani littafi mai suna ‘Aliyun Fil Kitabi was Sunnah’ juz’i na ]aya in mutum ya duba wannan litaffi zai ga ayoyin a kuma ruwayoyi na Ahlus Sunnah.

          2-Imam Ali a cikin Hadisai:Idan mutum ya bibiyi ruwayoyi na Hadisai zai ga cewa akwai Hadisai masu yawa da aka ruwaito da suke bayani dangane da falaloli da kuma darajoji na Imam Ali ga wasu daga ciki:1-An ruwaito daga Ummu Salma ta ce na ji Manzon Allah yana cewa, “Ali yana tare da Al}ur’ani,Al}ur’ani yana tare da Ali,ba zasu rabu ba har sai sun same ni a tabki.” 2-A wani Hadisi kuma da aka ruwaito daga Abu Zar ya ce,Manzon Allah ya ce, “Ya Ali duk wanda ya rabu da ni ha}i}a ya rabu da Allah,duk wanda ya rabu da kai ha}i}a ya rabu da ni.” 3- A wata ruwaya kuma Manzon Allah ya ce ma Ammar ]an Yasir, “Ya Ammar biyayya ga Ali,biyayya ce gare ni,biyayya gare ni,biyayya ne ga Allah Ta’ala.Ya Ammar idan mutane baki ]aya suka bi wata hanya,Ali shi kuma ya bi wata hanya to kabi hanyar da Ali ya bi ka bar mutanen.”4- Manzon Allah ya ce, “Duk wanda ya cutar da Ali ha}i}a ya cutar da ni,wanda kuma duk ya zagi Ali ha}i}a ya zage ni.” 5-A wani Hadisi Manzon Allah ya ce, “Misalin Ali gareni misalin Haruna ne ga Musa sai dai ba Annabi a bayana.” 6-Manzon Allah ya ce, “Wanda ya fi kowa ilmi a bayana shine Ali ]an Abi [alib,Ali shine taskar ilimi na.” 7-A wata ruwaya Manzon Allah ya ce, “Ali yana tare da gaskiya,gaskiya tana tare da Ali ba za su rabu ba.” Da dai sauran Hadisai masu yawa da aka ruwaito daga Manzon Allah dangane da Imam Ali wa]anda ba za a iya kawo su ba saboda gudun tsawaitawa.

          3-Imam Ali a cikin zantukan sahabbai:Idan mutum ya bibiyi tarihin Sahabbai musamman ma wa]anda suka yi fice daga cikinsu zai ga zantukansu dabam dabam da suke nuna fifikon Imam Ali a kan su,ga misalan wasu daga ciki:1-Maganar Abubakar a kansa:A ranar Ghadir bayan da Manzon Allah ya bayyana cewa Ali shine khalifa a bayansa sai Abubakar yake ce ma Imam Ali, “Ya ]an Abu [alib yanzu ka zama shugaban duk wani mumini da kuma mumina.” Mai son ganin wannan ya duba cikin littafin Futuhatil-Islamiyya juz’i na biyu.2-Maganar Umar a kansa:Akwai in da yake addu’a yake cewa ya Ubangiji ka da ka bar ni cikin matsalar da ba Ali ]an Abu [alib a ciki,akwai kuma lokacin da yake fa]i a cikin masallacin Manzon Allah ga sahabbai cewa ka da wani ya ba da fatawa a cikin wannan masallaci matu}ar Ali na cikinsa.3-Maganar Usman a kansa:Usman ]an Affan yana cewa, “Ba domin Ali ba da Usman ya halaka.”4-Abdullahi ]an Mas’ud yana cewa, “Ali ya fi mu sanin al}alanci.5-Zaidu ]an Ar-}am yana cewa, “Farkon wanda ya yi sallah tare da Manzon Allah shine Ali ]an Abi [alib.6-Jabir ]an Abdullahi al-ansariy yana cewa, “Hanyar da muke gane munafiki a cikinmu shine }iyayya ga Ali.” 7-Abdullahi ]an Abbas yana cewa, “Ali yana da ababe hu]u wa]anda ya ke~anta da su,shine balarabe na farko da ya yi sallah da Manzon Allah,kowane ya}i tutar Manzon Allah a hannunsa take,a ya}o}in da aka gudu aka bar Manzon Allah –wato kamar ya}in uhud da Hunani – to shi ya daure ya tsaya tare da Manzon Allah,shine kuma ya wanke Manzon Allah ya saka shi cikin }abari.8-Aisha:Ta ce, “Ban ga   wani namiji wanda Manzon Allah ya fi so ba kamar Ali ]an Abi [alib.” A wani waje kuma tana cewa, “Ali shi ya fi kowa sanin Sunnar Manzon Allah.” Wannan ka]an kenan daga cikin zantukan wasu da suka yi zamani da Imam Ali,ta yi yu mutum ya yi tunanin ko ya tambaya cewa duk da irin wannan furuci na wa]anda suka yi zamani da Imam Ali to mi yasa abin da ya faru ya faru? Amsa a nan itace akwai abubuwa da yawa da suka janyo haka misali akwai hassada,son mulki,ta’assubbanci na gidaje wato banu wane da banu wane,son duniya,}iyayya da gaba ta jahiliyya da dai sauransu.Akwai lokacin da Manzon Allah da Imam suna tafiya a cikin Madina za su je ma}abartar Ba}i’a sai Imam Ali ya ga Manzon Allah yana zubar da hawaye,ya tambaya ya Manzon Allah lafiya? Sai Manzon Allah ya ce masa na yi tunanine na abin da za a yi maka a bayana na zalunci da kuma musgunuwa,ya cigaba da ce masa akwai }iyayya da gaba da take cikin zukatan wasu daga cikin sahabbai dangane da shi amma ba za su iya bayyanar da wannan gaba da }iyayya ba sai bayan rasuwata.” Tabbas idan mutum ya bibiyi tarihi zai ga haka abin ya faru,Manzon Allah yana wafati ko mako guda ba a yi ba aka samu wasu daga cikin sahabbai suka je suka yi hujumi a gidansa da nufin za su }ona gidan,aka ce masu akwai fa Fa]ima ‘yar Manzon Allah a cikin gidan suka ce koma waye.

          Daga }arshe ga wasu sassa dabam dabam na rayuwar Imam Ali[AS]

1-    Wiladarsa:An haifi Imam Ali[AS] ranar Jumma’a 13 ga watan Rajab.wato bayan haihuwar Manzon Allah[SAAW] da shekaru 30.An haife shi a makka kuma a cikin ka’aba,an kuma sare shi a cikin masallaci wanda ya zama sanadiyyar shahadarsa.

2-    Nasabarsa:Sunan mahaifiyarsa Fa]ima ‘yar Asad,kuma ta rayu har zuwa lokacin da Manzon Allah[SAAW] yayi Hijira zuwa Madina,saboda haka da ita akayi wannan hijirar,Imam Ali nema ya jagoranci hijirar tasu.Sunan mahaifinsa Abdu Manaf,anai masa kinaya da Abu [alib,da yake shine babban ]ansa namiji,bayan shi sai A}il,sai Ja’afar,sai Imam Ali wato shine ]an autansu,kuma Ja’afar ]an Abu [alib shine farkon shahidi a cikin Bani Hashim.

3-    Nash’a ]insa:Imam Ali[AS] ya tashi a makka,kuma a gidan Manzon Allah[SAAW] ya rayu tare da mahaifinsa kusan shekaru 20.Ya kuma rayu tare da Manzon Allah[SAAW] shekaru 33.}arshen rayuwarsa kuma yayi a kufa ne.

4-    La}ubbansa da Kinayarsa:Yana da la}ubba masu yawa,amma wa]anda suka fi shahara sune,Amiril-Mu’uminin,Murtadha, Haidar,Wasiyyi da dai sauransu.Haka nan kinayoyinsa suma suna da yawa,wa]anda suka fi fice sune,Abu-Turab,Abul-Hassan, Abu-sib-]ain.

5-    Shekarunsa:Ya rayu shekaru 63 a duniya.

6-    Muddan Imamancinsa:Shekaru 33.

7-    ‘Ya’yansa:Yana da ‘ya’ya 25,maza 11,mata 14.

8-    Wafatinsa:Yayi shahada 21 ga watan Ramadan shekara ta 40 bayan Hijira.

9-    {abarinsa:}abarinsa yana Birnin Najaf ne,wato a Ira}.

 
Home Maudu'oi daban-daban Darajoji da karamomin Imam Ali (AS)
Copyright © 2022. www.tambihin.net. Designed by KH