Saturday, 02 December 2023
Email
Make My Homepage
RSS
Register
Dabi’oin Imam Husain (AS) Print E-mail
Written by Administrator   
Tuesday, 26 March 2019 17:21

Da farko ina taya ‘yan uwa musulmi farin cikin shiga wannan sabuwar shekara ta 1440.Allah Ta’ala ya sada mu da dukkan alhairai da albarkokin dake cikinta ya kuma tsare mu daga dukkan sharrori dake cikinta,Allah Ta’ala yasa ta kasance shekara ta faraj garemu daga wannan wa}i’a da muke ciki.Bayan haka kamar yadda muka sani wannan wata da muka shiga wato na Muharram,wata na juyayi da ba}in ciki da kuma kuka ga mabiya Ahlul bayt,kamar yadda ya zo daga Imam Ridha[AS] ya ce, “Babana –wato Imam Musa Al-kazim ya kasance idan watan Muharram ya shiga,to ba a ganin dariya a fuskarsa,damuwa da juyayi aka fi gani a fuskarsa har ya zuwa ranar Ashura,ranar ta kan kasance ranar kuka da ba}in ciki gareshi,ya kan ce wannan itace ranar da aka kashe Imam Husain[AS].Sai kuma abinda ya shafi wa]ansu~angarori na rayuwar Imam Husain [AS] domin su kasance darussa a cikin rayuwarmu da zamu darastu dasu.Yana da gayar muhimmanci ya kasance duk lokacin da ake tunawa da wa]annan munasabobi na wafati ko wiladar A’imma [AS],mutum ya dinga kwatanta rayuwarsa da kuma rayuwarsu,yaga ya yake wajen kwafar su da kuma koyi dasu.Domin mustahili ne,ba zamu iya kai wa kamar suba.Amma ya hau kanmu mu yi iya kokarin mu wajen misaltuwa dasu.Kuma haka suka bukata daga wajenmu.A nan ke nan zamu iya fahimtar cewa,lallai idan muka bibiyi rayuwar Imamai [AS],sannan kuma muka zo muka kwatanta da rayuwarmu,zamu ga cewa akwai gi~i babba dake tsakani:                                                 

                1-IBADARSA

Imam Husain [AS] ya kasance mai yawan ibada da kuma mujahada.Ga misalan wasu daga cikin ibadodinsa:

  1. Sallolinsa:Imam Husain [AS] ya kasance a kowace rana yana sallar nafila raka’a dubu,to mu kwatanta wannan da rayuwarmu wajen tsayuwa da raka’a 51,kamar yadda yazo a Hadisi da aka samo daga Imam Askari [AS] cewa,daga cikin siffofin Muminai yin sallah raka’a 51 kowace rana.kwatanta raka’a 51 da kuma raka’a 1000.
  2. Karatun Alkur’ani:Imam Husain ya kasance mai yawan karatun Alkur’ani ne,ya ma zo a tarihinsa cewa a watan Ramadan kowace rana yakan sauke shi,wato kenan sauka 30 a cikin watan ya keyi.To mutum ya kwatanta da kansa,sauka nawa ya ke yi a watan Ramadan da kuma sauran watanni?
  3. Azuminsa:Imam Husain [AS] ya kasance mai yawan Azumi,yama zo a tarihi cewa mafi yawan ranaku yana Azumi ne.Akwai ma wani da yayi masa shaidar cewa,bayan da yaji an kashe shi,wallahi sun kashe shi alhali ya kasance mai yawan Azumi a ranaku,mai yawaita tsayuwa da daddare.
  4. Hajjinsa:Imam Husain [AS] yayi Hajji a rayuwar shi ]ai ]ai har guda 25,kuma dukkansu a }afa ya taka tun daga madinah har zuwa makkah,wato ba tare daya hau dabba ba.Idan Allah ya na’imta mutum ya tafi aikin Hajji yayi tunanin nisan dake tsakanin makkah da madinah,amma haka Imam Husain [AS] yake kama hanya tun daga madinah har yazo makkah,ba sau ]aya ba ko sau biyu,a’a har sau 25 ba kuma saboda ba dabbar da zai hau bane.
  5. Addu’oinsa:Imam Husain [AS] ya kasance mai yawan Addu’oi,akwai malamai da yawa daga madrsah ]in Ahlulbayt [AS] da suka tattara addu’o’insa suka mai da littafi.Alal misali,akwai sahifatul Husainiyyah,wanda baki ]aya addu’o’in Imam Husain [AS] ne,banda kuma malaman da suka yi sharhin addu’arsa ta ranar Arfa.Wanda wannan addu’ar tasa taska ce babba ta ma’arifa wanda koda ace ba wani Nusus,wato aya ko Hadis dake bayanin matsayin Imam Husain [AS],to wannan addu’ar tasa ta ranar Arfa ta isa ta bayyana matsayinsa.A ta}aice dai Imam Husain [AS] ya kasance mai yawan Ibada.Yama zo akan cewa lokacin da Umar ]an Sa’ad, shida rundunarsa su kayi yun}urin su kai masa hari a yammacin Tasu’a,wato tara ga wata,sai Imam Husain [AS] ya aika da ]an uwansa Abbas [AS] yace masa yaje wajen su domin ya shawo kansu su jinkirta zuwa gobe,saboda muyi salloli da addu’o’i da kuma Istigfari a wannan daren.Imam Husain [AS] yaci gaba da cewa; “Allah yasa ni ina son salla gare shi da kuma biya littafinsa [wato Alkur’ani] da yawaita addu’o’i da kuma Istigfari; Haka ko wannan al’amari ya auku Abbas yaje ya shawo kansu, domin sun so su yi wannan aika aikan da su kayi ranar Ashura tun a yammacin Tasu’a,saboda haka a wannan dare na Ashura kamar yadda yazo a tarihi cewa Imam Husain [AS] da sahabbansa,sun shafe daren baki ]aya ba suyi barci ba suna ibadodi wannan na salla wannan na karatun Alkur’ani,wannan na addu’o’I dadai sauran su na ibadodi, shi yasa yazo akan cewa daga cikin abubuwan da ake son yi a daren Ashura akwai raya daren da ibadodi domin koyi da Imam Husain [AS]                                                                                                                                         2. ILIMINSA.

Imam Husain [AS] ya kasance a wannan fage na ilimi a zamaninsa babu wanda yakai shi ballantana ya wuce shi.Ya mazo a tarihinsa cewa manya manyan sahabban manzon Allah [S] sukan zo gare shi dangane da tambayoyi na mas’aloli na addini ya kuma basu amsa,kuma tsawon zaman sa a madina ya kasance yana karantarwa ne a masallacin manzon Allah [S].Akwai ma wani da yazo ya sami wani yana tambayarsa ina zai ga Husain [AS] yace masa kaje masallacin manzon Allah [S] idan kaga wata hal}a ta mutanewa]anda kai kace kawukansu akwai tsuntsaye [wato saboda natsuwa a wajen karatunsu],to,zaka samu Husain anan.A ta]aice dai manyan sahabbai da ‘ya’yansu da kuma Tabi’ai sun amfana da iliminsa.                                 

3.AKHLAK [INSA.

Shima a wannan fage na Akhla}, kamar sauran fagage babu wanda ya kai shi a zamaninsa.Ga misalan wasu daga cikin Akhla}]insa:

  1. Kyautar sa:Imam Husain [AS] ya kasance mai yawan kyauta,yama zo akan cewa akwai wani ba}auye da yazo madina,sai ya tambaya a garin wa yafi kowa yawan kyauta? Sai akace masa Imam Husain [AS],sai yaje wajensa.Ko da ya isa sai ya samu yana salla,sai ba}auyen ya tsaya ya kama raira wa}o}i na yabo.Bayan da Imam Husain [AS] ya sallame salla sai ya bashi kyautar Dirhami dubu hu]u.Haka nan akwai lokacin da Imam Husain [AS] yaje gai da wani da bai da lafiya,ana ce masa Usamatu ]an Zaid.Sai Imam Husain [AS] ya same shi cikin damuwa da ba}inta~a zuwa yana so ya tambayi Imam Husain [AS] amma yana jin kunya,sai Imam Husain [AS] yace ya rubuta a takarda sai ya rubuta.Yace “Ya Aba Abdullah,wani ne yana bina bashin Dirhami 500,kuma ya matsa min in biya,sai nace masa ya saurare ni zuwa wani lokaci”.Lokacin da Imam Husain [AS] ya karanta wannan takardar sai ya shiga gida ya fito da Dirhami 1000,yace masa “Dirhami 500 ka biya bashinka,sauran kuma ka biya bu}atunka na yau da kullum”.Haka nan yazo akan cewa,bayan shahadar Imam Husain [AS] a ranar Ashura,sai aka ga kanta kanta a bayansa.Sai aka tambayi Imam Zainul Abidin [AS], sai ya ce wannan ya kasance ne saboda kayayyakin abinci da yake ]auka zuwa ga gidajen miskinai da kuma matayen da mazajen su suka rasu.
  2. AFUWARSA:Imam Husain [AS] ya kasance mai yawan afuwa.Akwai wani cikin bayinsa daya ta~a yi masa laifi,wanda ya kai ayi masa horo akai.Sai shi wannan bawan yace; “Ya shugabana! Masu ha]iye fushi [wato ya janyo ayar da tayi Magana akan haka]”.Sai Imam Husain [AS] yace,ku }yale shi.Sai kuma bawan yace “Ya shugabana masu afuwa ga mutane”.Sai Imam Husain [AS] yace “nayi maka afuwa”.Sai bawan ya sake cewa “Ya shugabana! Allah na son masu kyautatawa”.Sai Imam Husain [AS] yace “ka tafi na ‘yanta ka saboda Allah [T].Akwai wani mutumin sham daya ta~a zuwa madina sai yaga Imam Husain [AS] sai yace masa,kaine ]an Abu Turab,wato fa]i na izgili.Sai Imam Husain [AS] yace masa,na’am.Jin haka sai shi wannan mutumin sham ]in ya dinga fa]in maganganu munana na zagi da kuma cin mutunci gare shi da kuma babansa,wato Imam Ali [AS].Sai da ya gama Imam Husain [AS] ya dube shi dubi na tausayi,ya karanta masa wasu ayoyi na Alkur’ani da kuma wa]ansu Hadisai na manzon Allah [S].Bayan haka yayi masa maganganu lausasa,har ma yace masa in yana da wata bu}ata ya fa]i a biya masa,in kuma bashi da masauki yazo za’a bashi,dadai wasu maganganu kyawawa na akasin abinda shi yayi.Jin haka sai shi wannan mutumin sham,kunya da kuma nadama suka kama shi.Sai Imam Husain [AS] yace masa kada ya damu,Allah ya gafarta masa.Sai mutumin yace,sai naji }unci kamar na nutse a }}arshe yake cewa; “Duk a doron }asa ba wanda nafi so kamar kai da Babanka ”.Wannan kenan shima a ta}aice.
  3. TAWALI’UNSA:Imam Husain [AS] ya kasance mai yawan tawali’u,yazo akan cewa wata rana yana tafiya sai ya ha]u da miskinai suna cin abinci,sai yayi musu sallama,sai suka ce yazo yaci,sai yaje ya zauna.Sai yace masu,da ba domin sadaka bane da naci.Sai Imam Husain [AS] yace masu ku tashi mu tafi zuwa gidana.Da sukaje ya basu abinci da tufafi da kuma ku]a]e.
  4. TAUSAYINSA:Imam Husain [AS] ya kasance mai yawan tausayi,hatta ga wa]anda suka munana masa ko kuma suka zalunce shi.Yazo akan cewa ranar Ashura kafin shahadarsa,an ga yana hawaye aka tambaye shi dalilin hakan,yace yana tausayin wa]annan mutane ne saboda wannan mummunan aiki da zasu yi zai kai su ga shiga wuta.

4-TAKAWARSA

                Imam Husain [AS] duk da matsayin da yake dashi a wajen Allah ya kasance mai yawan tsoron Allah.Akwai ma wata rana da akace masa,me ya kai gayar tsoronka ga Ubangijinka? Sai Imam Husain [AS] yace,ba wanda zai amintu ranar }iyama sai wanda yaji tsoron Allah a gidan duniya.Ya mazo akan cewa Imam Husain [AS] idan zai yi alwala akan ga launin fuskarsa ya canza kuma ga~u~~ansa na makyarkyata.Sai aka ce masa,me yasa haka? Sai yace; “Dolene ga wanda zai tsaya gaban Allah [T] launin sa ya canza,ga~o~insa suyi makyarkyata”.

            Nan kuma wasu sassa ne na rayuwar Imam Husain[AS].

1-Haihuwarsa:An haife shi a madina 3 ga watan Shaaban.

2-Shekarunsa:Imam Husain[AS] ya rayu a duniya shekaru 57 ne.

3-Muddan Imamancinsa:Shekaru goma ne.

4-‘Ya’yansa:Imam Husain[AS] ya kasance yana da ‘ya’ya bakwai maza4 mata 3.Mazan sune,Imam Zainul-Abidin,Aliyyul Akbar,Jaafar da kuma Abdulla,Aliyyul Akbar da Abdullah sun yi shahada a karbala,ya Aba Abdullah da ake yi masa kinaya da shi ana nufin wannan Abdullah.Matan sune,Sukaina,Fatima da kuma Ru}ayya.

5-Shahadarsa:Yayi shahada a ranar jumma’a a wata ruwaya ranar asabar 10 ga watan Muharram shekara ta 61 bayan hijira.Kuma yazo a ruwayoyi na hadisai cewa a ranar da yayi shahada ne Imam Mahdi[AF] zai bayyana wato a ranar asabar ko jumma’a 10 ga muharram a shekarar da Allah ta’ala shine masani a kai.

6-{abarinsa:Yana a karbala ne tare da wa]anda suka yi shahada tare da shi.

                                                                               

Last Updated on Tuesday, 26 March 2019 17:29
 
Home Darusan Akhlaq Dabi’oin Imam Husain (AS)
Copyright © 2023. www.tambihin.net. Designed by KH