Thursday, 27 January 2022
Email
Make My Homepage
RSS
Register
Darajoji da kuma karamomi na Sayyida Fadima[AS] Print E-mail
Written by administrator   
Friday, 17 August 2018 19:45

Insha Allah a wannan darasi bayani zai kasance ne kan wannan maudu’i na Darajoji da kuma karamomin Sayyida Fa]ima[AS] kasantuwar wannan wata da muke ciki na munasabar haihuwarta,saboda haka bayani zai gudana kan wa]annan ababe

1-Matsayin Sayyida Fa]ima wajen Allah [T]

2-Matsayin Sayyida Fadima wajen Manzon Allah[S].

3-Matsayin Sayyida Fadima wajen Aimma na Ahlul bayt[AS].

4-Matsayin Sayyida Fadima ranar lahira.

5-Karamomin Sayyida Fadima[AS].

6-Falalar son Sayyida Fadima[AS].

7-Sunayen Sayyida Fadima da kuma ma’anoninsu.

            1-Haihuwarta:An haifi Sayyida Fa]ima[AS]a Makka ranar jumma’a 20 ga watan jimada sani shekara ta biyar bayan aiko wa Manzon Allah da sa}o.2-Nasabarta:Kamar yadda aka sani mahaifin ta Manzon Allah[S]mahaifiyarta kuma Sayyida Khadija.Wani tambihi anan shine,Malaman madrsah ]in Ahlul bayt sun tafi akan cewa ‘ya’ya Manzon Allah baki ]aya an haife sune gabanin aiko masa da sa}o ne in banda Sayyida Fa]ima da kuma Ibrahim ]an Mariya wato su bayan aiko masa da sa}o ne aka haife su.3-Nash’a]inta:Sayyida Fa]ima ta tashi a makka,tana da shekara biyar mahaifiyarta ta rasu,tana da shekara takwas lokacin da aka yi hijira zuwa madina,bayan komawa madina anan ta rayu a kuma nan ta rasu.4-La}ubbanta da kuma kinayarta:Daga cikin la}ubbanta akwai Ma’asuma,Mazluma,Karima,Sabira da dai sauransu.Haka nan kuma tana da kinaya masu yawa amma wa]anda suka fi shahara sune Ummul-Aimma da kuma Ummu Abiha.5-Shekarunta: Sayyida Zahra[AS] ta rayu a duniya shekaru 18 a wata ruwaya shekaru 23 ne.6- ‘ya’yanta:Tana da ‘ya’ya biyar maza ukku mata biyu,mazan sune:Hassan,Husain,Muhsin.Matan sune Zainab da kuma Ummu Khul-sum.7-Wafatinta:Akwai ruwayoyi kusan goma akai amma ruwayar da tafi shahara kuma wadda mai littafin mafatihul jinan ya tafi akai itace ukku ga watan jimada sani shekara ta 11 bayan hijira.8-Kabarinta:Shima wannan akwai sa~ani na ainihin in da }abarinta yake amma akwai zantuka ukku akai,wasu sun ce a Ba}i’a yake,wasu sun ce }abarinta yana tsakanin kabarin Manzon Allah da minbarinsa,wasu sun ce }abarinta yana cikin ]akinta.In sha-Allah idan Imam Mahdi[AF] ya bayyana ainihin in da }abarinta yake zai bayyana.

            1-Matsayin Sayyida Fadima[AS] wajen Allah[T]:Idan mutum ya bibiyi tarihin Sayyida Fa]ima zai ga cewa komi na ta samawiy ne wato saukakke daga wajen Allah alal misali sunan ta saukakke ne daga sama Allah ta’ala ne yayo wahayi ta hanyar mala’ika Jibril cewa a sa mata wannan suna Fa]ima haka nan al’amarin ]aurin aurenta Allah ta’ala ya aiko da umarni ga Manzonsa cewa ya aurar da ita ga Imam Ali,shi yasa lokacin da wasu daga cikin sahabbai da suka nemi auren Sayyida Fa]ima basu samu ba suke ce ma Manzon Allah mun nemi auren Fa]ima baka bamu ba amma ka aura ma Ali? Sai Manzon Allah ya ce masu bani na hana ku ba Allah Ta’ala ne ya hana ku ya aura masa ita,haka ma lokacin ]aurin auren sai da aka yi a sama gabanin ayi shi a }asa kai hatta likkafaninta daga gidan Aljanna aka zo dashi.Haka nan ya zo a hadisi daga Manzon Allah ya ce, “Duk wanda Fa]ima ta yarda dashi to Allah ya yarda dashi wanda kuma take fushi dashi to Allah yana fushi dashi.” Wato dai Allah ta’ala yana fushi da fushinta yana kuma yarda da yardarta.A wani hadisi kuma Manzon Allah yana cewa, “Azaba ta tabbata ga duk wanda ya zalunce ta ko ya zalunci zuriyyar ta ko kuma ya zalunci shi’arta.”

            2-Matsayin Sayyida Fadima[AS] wajen Manzon Allah[S]:Idan mutum ya bibiyi tarihin Sayyida Fadima zai ga cewa tana da matsayi babba kuma mai girma a wajen Manzon Allah.Akwai ma wata rana Manzon Allah ya fito yana ri}e da hannun Sayyida Fa]ima sai ya ce, “Wanda ya san wannan ya santa wanda kuma bai santa ba to itace Fa]ima ‘yar Muhammad duk wanda ya cutar da ita to ha}i}a ya cutar dani wanda kuma ya zalunce ta ha}i}a ya zalunce ni.” Haka nan ya zo akan cewa duk lokacin da Sayyida Fa]ima ta je wajen Manzon Allah a gida to ya kan tashi a in da yake zaune ya ce ta zauna a wajen wato saboda girmamawa.Haka nan kuma duk lokacin da Manzon Allah zai yi tafiya wajen Madina to ba zai bar Madina ba har sai ya je yayi sallama da Sayyida Fa]ima haka nan idan ya dawo daga tafiya bai zai wuce gida kai tsaye ba har sai ya soma zuwa gidan Sayyida Fa]ima saannan ya tafi gida.Akwai ma lokacin da aka tambayi Manzon Allah akan cewa wanene yafi so? Sai ya ce Fa]ima.A wani hadisi Manzon Allah ya ce, “Fa]ima sashen jiki na ne duk wanda ya faranta mata rai ha}i}a ya faranta mini wanda kuma ya munana mata to ha}i}a ya munana mani.”

            3-Matsayin Sayyida Fa]ima wajen Aimma na Ahlul bayt:Akwai hadisai masu yawa da aka ruwaito daga Aimma na Ahlul bayt da suke nuni da matsayi da kuma darajoji na Sayyida Fa]ima alal misali ya zo a hadisi cewa itace shugaban mataye baki ]aya,a wani hadisi kuma ya zo akan cewa itace shugabar matayen Aljanna,har wala yau kuma a wani hadisi ya zo akan cewa itace za ta fara shiga Aljanna bayan Manzon Allah.Imam Musa Al-kazim ya ce, “Talauci baya shiga gidan da akwai mai sunan Fa]ima.” Haka nan akwai wani daga cikin mabiyan Imam Sadi} da aka haifa masa ‘ya mace sai ya sa mata suna Fa]ima shine Imam Sadi} ya ce masa to kada ya dake ta ko ya zage ta ko ya munana mata wato saboda girmamawa ga Sayyida Fa]ima.

            4-Matsayin Sayyida Fa]ima ranar }iyama:Ya zo a wata ruwaya cewa Sayyida Fa]ima a ranan Al-}iyama bayan ta isa }ofar Al-janna za ta waiwayo,sai Allah ta’ala ya tambaye ta miyasa ta waiwayo,sai tace ya ubangiji ina son a san daraja ta da kuma matsayi na ayau ne,sai Allah ta’ala ya ce mata ya ‘yar masoyina koma ki duba duk wani wanda yake son ki ko yake son wani daga cikin zuriyyarki ki kama hannunsa ki shigar dashi aljanna.A wata ruwaya ya zo akan cewa bayan Sayyida Fa]ima ta shiga aljanna Allah ta’ala zai ce mata ya Fa]ima ro}i duk abinda kike so zan baki sai ta ce ina ro}onka kada ka azabtar da duk wani masoyi na ko masoyin zuriyyata da wuta.

            5-Karamomin Sayyida Fa]ima:Idan mutum ya bibiyi tarihin Sayyida Fa]ima zai ga cewa tana da karamomi masu yawa wasu karamomin ma tun gabanin a haife tane suka kasance alal misali ta kasance tun tana cikin mahaifiyarta take magana da mahaifiyarta a ciki,akwai lokacin da Manzon Allah ya shigo cikin gida sai ya ji Sayyida Khadija na magana alhali ba kowa a cikin gidan shine Manzon Allah ke tambayar ta ke da wa kike magana? Sai ta ce da yaron da yake ciki na ne,sai Manzon Allah ya ce mata mace ce kuma Allah Ta’ala zai sanya zuriyyata daga gareta kuma a cikin zuriyyar tane za a samu Imaman wannan al’umma.Haka nan ya zo akan cewa lokacin da aka haife ta sai ta kasamce a }asa tana mai sujuda,haka nan lokacin da aka haife ta wani irin haske ya bayyana wanda ya haskaka garin makka baki ]aya dama sauran sassa na duniya.Haka nan kuma ya zo a kan cewa bayan haihuwarta an ji tana cewa, “Na shaida babu abun bautawa sai Allah kuma lalle baba na Manzon Allah ne kuma shugaban Annabawa miji na kuma shine shugaban wasiyyai.A ta}aice dai ayoyi da kuma karamomi masu yawa sun bayyana a lokacin haihuwar Sayyida Fa]ima.

            6-Falalar son Sayyida Fa]ima:Akwai hadisai masu yawa da aka ruwaito daga Manzon Allah kan falalar son Sayyida Fa]ima ga wasu daga cikin hadisan:1-Manzon Allah ya ce, “Duk wanda yaso Fa]ima ‘ya ta to zai kasance cikin Aljanna tare da ni.” A wani hadisi kuma Manzon Allah ya ce, “Son Fa]ima yana amfanar mutum a wajaje ]ari daga cikin wajajen akwai lokacin mutuwarsa,zamansa a }abari,ranar }iyama,kan sira]i da kuma wajen hisabi.A wata ruwaye ya zo akan cewa son Fa]ima alama ce ta imani,}inta kuma alama ce ta munafinci.A wata ruwaya kuma Manzon Allah ya ce, “An sanya ma Fa]ima suna Fa]ima domin Allah ta’ala ya yaye duk mai sonta daga wuta.” Wato ma’ana bashi ba wuta.

            7-Sunayen Sayyida Fa]ima da kuma ma’anoninsu:Ya zo a hadisi da aka ruwaito daga Imam Sadi} ya ce, “Fa]ima tana da sunaye guda tara a wajen Allah ma]aukaki sune:1-Fa]ima:Ma’anar Fa]ima ya zo da ma’anoni dabam dabam a ruwayoyi amma ma’anar da tafi shahara itace Allah ta’ala ya yayeta da shi’arta daga wuta.2-Siddi}a ma’ana mai yawan gaskiya ko mai gaskiya a dukkan zantukanta ko kuma a wata ma’ana mai yawan gasgatawa ga sa}on da mahaifinta ya zo dashi.3-Mubaraka:Ma’ana ma’abuciyar albarka.4-[ahira:Ma’ana tsarkakakkiya daga dukkan na}asa ta zahiri da ba]ini .5-Zakiyya:Ma’ana tsarkakakkiya daga dukkan munanan ]abi’u.6-Rabiyya:Ma’ana yardarta da hukunci ko }addara ta Allah Ta’ala.7-Marbiyya:Ma’ana yardaddiya a wajen Allah Ta’ala.8-Batula:Ma’ana wadda ba ta jinin al’ada na mata kamar jinin haila ko na nifasi-bi}i-wato Sayyida Fa]ima ba ta ta~a yin jinin haila ko jinin haihuwa ba a rayuwarta ita tsarkakakkiya ce daga garesu,a wata ma’ana kuma batula na nufin wadda ta yenke zuwa ga Allah ta’ala.9-Zahra:Ma’ana wadda take da haske na zahiri da ba]ini,a wata ruwaya ya zo akan cewa ana ce ma ta Zahra ne saboda idan tana ibada to haskenta yana bayyana ga ma’abuta sama wato mala’iku kamar yadda hasken taurari yake bayyana ga ma’abuta }asa wato mutane.

            Haka nan kuma a ranar haihuwar Sayyida Fa]ima 20 ga wata na jimada sani shekara ta 1320 bayan hijira aka haifi Imam Khumaini.Nan kuma wasu sassa ne na rayuwarsa a ta}aice.

1-Nasabarsa:Sunansa Ruhullah,Sunan mahaifinsa Ayatullahi Sayyid Mustafha,sunan mahaifiyarsa Sayyida Hajar ita kuma’yar Ayatullahi Mirza Ahmad, wato Imam Khumaini mahaifansa duka sadat ne,wato sharifai kuma nasabarsa tana tu}ewa ga Imam Musa Al-kazim shi yasa ake masa la}abi da Al-musawi.Yana da wata biyar a duniya mahaifinsa ya rasu ta hanyar shahada domin an kashe shine,yana kuma da shekaru 15 a duniya mahaifiyarsa ta rasu.

2-Shekarunsa: Ya rayu a duniya shekaru 93 ne.

3-Muddan da ya rayu bayan juyin musulunci:kusan shekaru 10 ne ya rayu.

4-‘Ya’yansa:yana da ‘ya’ya takwas maza ukku mata biyar,mazan sune:1-Sayyid Mustafa yayi shahada a 1977 lokacin yana da shekaru 47 kuma ya kai matsayin Ayatullahi kafin shahadarsa.2-Sayyid Ahmad ya rasu a 1995 ya rasu ne sakamakon rashin lafiya da ya yi.Kuma yana matsayin Hujjatul-Islam kafin rasuwarsa.3-Sayyid Aliy ya rasu tun yana yaro.Matan sune:1-Sayyida Farida.2-Sayyida Dr Fatima.3-Sayyida Siddi}a.4-Sayyida Sa’ida.5-Sayyida Latifa.

5- Wafatinsa:ya rasu ranar sati 3 ga watan june 1989,amma a lissafin watanni na musulunci ya rasu ne a 28 ga watan Shawwal 1409 ne.

6-{abarinsa:Yana a Tehran ne wato babban birnin }asar Iran.Imam Khumaini ya rubuta littafai masu yawa a kuma fannonin ilimi dabam dabam,haka nan ma ‘ya’yansa suma sun yi rubuce rubuce musamman ma Ayatullah Sayyid Mustafa Khumaini,akwai ma tafsiri na Al}ur’ani da ya fara rubutawa amma bai samu kammala shi ba aka kashe shi.A ta}aice dai akwai wani babban Library a birnin Qum wanda baki ]ayan littafin dake cikinsa littafan Imam Khumaini ne da kuma ‘ya’yansa da kuma littaffan da wasu Malamai suka rubuta kan tarihi da kuma rayuwar Imam Khumaini.Saboda haka duk wani littafi da Imam Khumaini ya rubuta tabbas in kaje zaka same shi a Library ]in.

 
Home Maudu'oi daban-daban Darajoji da kuma karamomi na Sayyida Fadima[AS]
Copyright © 2022. www.tambihin.net. Designed by KH