Bayani kan jinin Haila, Nifasi, da Istihadha |
Written by administrator | |||
Sunday, 28 January 2018 19:34 | |||
Insha Allah wannan shine babi na }arshe a cikin babobin da ba a kawo ba a wannan darasi na fi}hu wato a shekarun baya,kuma bayani zai kasance akan wa]annan fasaloli: 1-Jinin Haila. 2-Jinin Nifasi. 3-Jinin Istihadha. 1-Jinin Haila:Sassan da bayani zai gudana akai sune:A-Ma’anar Haila.B-Alamomin Jinin Haila.C-Muddan kwanukan Haila.D-Shekarun Haila.E-{arancin kwanukan tsarki.F-Rabe-raben Haila.G-Abubuwan da suka Haramta ko karhanta ga mai Haila da kuma ababen da suke mustahabbi gareta.H-Yadda ake wankan Haila.I-Hukunce-hukuncen Haila. A-Ma’anar Haila:Jinin Haila shine jini wanda yake fita daga mahaifar mace kowane wata na wasu kwanuka. B-Alamomin jinin Haila:Jinin Haila ja ne wani lokaci yakan sauya zuwa ba}i ko ya yi jajur,kuma yana da tunku]a wajen fitowa da kuma zafi. C-Muddan kwanukan Haila:Mafi }arancin kwanukan Haila kwana ukku ne saboda haka idan ya kasance }asa da kwanaki ukku ne to ba Haila bane,haka nan wa]annan kwanaki ukku dole su kasance biye da juna,mafi yawan kwanukan Haila kwana goma ne. D-Shekarun Haila:Jinin Haila yana farawa ne da cikar ‘ya mace shekara tara saboda haka duk jinin da yarinya }arama za ta gani ya fito mata kafin ta cika shekaru tara,to ba Haila ba ne,ko da kuwa yana da siffofi hailar.Haka nan jinin da mace ta gani bayan shekarun daina Haila –Shekarun daina Haila shekaru sittin ne ga wadda take Ba}uraishiya,in kuma wadda ba ita ba bane daga sauran }abilu shekaru hamsin ne – Wato dai shekarun soma Haila shine shekara tara,abinda ake nufi da shekara tara anan shine lokacin da yarinya ta cika shekara tara cif-cif wato ba mujarradin shigar ta shekara tara ba a’a sai ta cika shekara tara ]in cif-cif,haka nan ita ma wadda ta kai shekarun daina Hailar sai ta cika shekaru hamsin cif-cif ba mujarradin shigar ta shekaru hamsin ba. E-{arancin kwanukan tsarki:Mafi }arancin kwanuka tsarki wato tsakanin wannan Haila da wannan Haila kwanaki goma ne,saboda haka zai iya yiwuwa mace ta iya yin jinin Haila sau biyu a wata amma fa da shara]in a samu tazaran kwana goma tsakanin Haila ta farko da kuma Haila ta biyu.Amma mafi yawan kwanukan tsarki to shi bai da iyaka wato a ce kwana kaza ne. F-Rabe-raben Haila:Mai Haila imma ta kasance wadda take ma’abuciyar al’ada ko kuma wadda take ba ma’abuciyar al’ada ba,wadda take ma’abuciyar al’ada itace wadda ta maimaita Haila sau biyu kuma biye da juna haka nan kuma ya kasance an samu dacewa a lokacin da kuma adadin kwanakin,ko kuma ya kasance a samu dacewa a cikin lokutan ka]ai ko kuma a adadin kwanakin ka]ai,to da wannan ne mace za ta zama ma’abuciyar al’ada mai lokaci tsayayye ko ma’abuciyar al’ada mai adadi tsayayye ko kuma ma’abuciyar al’adi mai lokaci da kuma adadi tsayayye.Ita kuma wadda take ba ma’abuciyar al’ada ba ta kasu zuwa kashi ukku wato imma ta kasance yanzu ta fara wato ba ta ta~a ganin hailar ba ko sauya ]aya,ko kuma ta zamo wadda al’adarta ba tsayayya ba wato tana rawa,ko kuma ta zamo ta manta al’adarta,ita ma wannan wato wadda ta manta al’adarta ta kasu gida ukku ko dai ya kasance ta manta lokacin Hailar ta ko kuma ta manta adadin kwanakin Hailar ta ko kuma da adadin kwanakin da kuma lokacin duk ta manta.To duka bayanai sanka-sanka na wa]annan rabe-raben Haila ga mai bu}atar bayani ana iya komawa ga littafan Fi}hu misali littafin Zubda ko Tahrirul wasila na Imam Khumaini. G-Abubuwan da suka haramta da kuma karhanta ga mai Haila:Daga cikin ababen da suka haramta a gareta akwai yin Sallah,Azumi, [awafi,Iitikafi da kuma dukkan ababen da suka haramta ga mai janaba kamar ta~a sunan Allah da na Annabawa da kuma Aimma na Ahlul bayt ko kuma zama cikin masallaci.Haka nan haramun ne ga mijinta saduwa da ita.Wasu kuma daga cikin abubuwan da suke aikata su makruhi ne gareta akwai karatun Al}ur’ani mai girma ko kuma ]aukar Al}ur’ani haka nan kuma makruhi ne gareta lokacin da take Haila ta yi }unshi wato lalle,haka nan kuma makruhi ne ga mai Haila ta ]auki Turba ta karbala.Mustahabbi ne ga mace mai Haila ta ri}a sauya audugar ta,haka nan mustabbine gareta ta yi alwala lokacin kowace Sallah,bayan haka sai ta zauna tana mai fuskantar al-}ibla da kuma yin Azkar na ]an wani lokaci gwargwadon yadda take ]auka wajen yin sallah,zikirin da za ta yi shine misali istigfari ko hailala ko salati ga Manzon Allah da dai sauransu. H-Yadda ake wankan Haila:Yadda ake wankan janaba to haka ake wankan Haila banbanci kawai shine wajen niyya wato maimakon yin niyyar wankan janaba to za ta yi niyyar wankan Haila ne,wani tambihi kuma shine wankan Haila bai ]auke Alwala wato idan mace ta yi wankan Haila to idan za ta yi sallah to dole sai ta yi alwala sa~anin ko in da wankan janaba ne ta yi shi za ta yin sallah kai tsaye bayan yin sa ba tare da ta yi alwala ba sai dai idan ta yi wani abu da yake ~ata alwala a lokacin wankan ko bayan wankan. I-Hukunce-hukuncen Haila:Mas’ala 1:Sakin da aka yi shi cikin Haila bai inganta ba wato bai yi ba a mazhaba ta Ja’afariyya amma akwai wasu fuskoki da yake inganta misali idan bai yi dukuli da ita ko kuma yana wani waje da bai san halin da matar tasa take ciki ba kuma ba zai iya yiyuwa masa ba ya bincika.Mas’ala 2:Idan Haila ta ]auke misali }arshen yini gabanin fitar lokacin Sallah to idan har za ta iya yin wanka kuma ta yi alwala ta samu ko da raka’a guda ne to wajibi ne ta yi hakan in ko ba ta yi haka ba to za ta rama sallar la’asar ]in,in ko da za ta iya samun raka’a biyar to wajibi ne ta yi sallar zuhur da kuma asar.Mas’ala 3:Salloli na khusufi idan sun auku misali khusufin wata ko rana alhali mace tana Haila to bayan ta yi tsarki wajibi ne sai ta biya sallar amma salloli wajibai na yini guda biyar su ba za ta biya su ba,sai dai azumi na Ramadan da ta sha shima zata rama shi.Mas’ala ta 4:Yadda ake istibra’in jinin Haila wato gane ya yenke ko bai yenke ba shine ta hanyar sa auduga a gabanta sai ta dakata na ]an wani lokaci bayan haka sai ta fitar da audugar in ya fito da jini to alama ce ta jinin Hailan bai yenke ba amma idan ya fito babu alamar jini to alama ce ta jinin ya ]auke.5-Idan Haila ta zo ma mace alhali tana Sallah ko Azumi to sallar ko azumin sun ~aci ko da ko gab da bu]e baki ne abin ya faru. 2-Jinin Nifasi:Jinin Nifasi shine jinin da mace take gani lokacin haihuwa ko kuma bayan haihuwa saboda haka jinin da ya kasance gabanin haihuwa to bana Nifasi ba ne.Jinin Nifasi bai da haddi na }aranci amma mafi yawan kwanakinsa kwana goma ne saboda haka dukkan jinin da mace za ta gani bayan ta haihu har zuwa kwanaki goma to duk na Nifasi ne amma in ya wuce kwanaki goma to ya fita daga hukuncin Nifasi.Mas’ala :Idan jinin Nifasin ya wuce kwanaki goma to yanzu hukuncinta ya koma na mai istihadha ne misali a ce jinin ya kai har kwanaki sha-biyu to idan ta kiyaye kwanakin al’adarta kamar a ce tana kwanaki bakwai ne to wa]annan kwanaki bakwai sune na nifasi sauran kwanakin kuma na istihadha ne,amma idan ba ta da al’ada zaunanna ko kuma ta manta kwanakin da take yin al’ada to anan sai ta ]ebe kwanaki goma cikin sha-biyun sauran kwanaki sun koma na istihadha.Mas’ala:Hukunce-hukunce mai jinin Nifasi ]aya yake da na mai jinin Haila misali bai halatta a sake ta ba ko a take ta ko kuma ta yi sallah ko Azumi da dai sauransu.Mas’ala:Bayan yenkewar jinin Nifasi to wajibi ne ta yi wanka shima shigen na janaba ne wato yadda take wankan janaba haka za ta yi banbanci kawai shine wajen niyya,shima wankan nifasi bai ]auke alwala wato in ta yi shi kuma za ta yi sallah to dole ne sai ta yi alwala. 3-Istihadha:Sassan da bayani zai gudana akai sune:A-Ma’anar Istihadha.B-Alamomin Istihadha.C-Muddan Istihadha.D-Rabe-raben Istihadha.E-Hukunce-hukunce Istihadha. A-Ma’anar Istihadha:Istihadha a is]ilahi na Fu}aha shine Jinin da mace take gani ba a lokacin Haila ba ko Nifasi.Jinin da yake fita a mahaifar mata guda ukku sune:Jinin Haila,jinin Nifasi da kuma jinin istihadha. B-Alamomin jinin Istihadha:Jinin Istihadha a mafi yawan lokaci fatsi ne,mai sanyi ne haka nan kuma siriri ne,ya kan kuma fito ba da }arfi ko zafi ba wani lokaci ma yana iya kasancewa da siffofi na Haila. C-Muddan Istihadha:Shi jinin Istihadha babu iyaka a }arancinsa ko a yawansa. D-Rabe-raben istihadha:Ya kasu kashi ukku,akwai mai ka]an da kuma matsakaiciya da kuma mai yawa.Yadda ake gane mai ka]an shine idan tasa auduga za ta audugar ta gur~ata da jinin ba tare da ya huda ta ba ya bayyana a ta ]aya ~angaren.Yadda ake gane matsakaiciya shine jinin zai huda audugar har ya bayyana ta ]aya ~angaren,amma dai ba zai kwarara ba ya kai ga }yellen da yake kan audugar ba.Yadda ake gane mai yawa shine jinin zai kwarara har ya iske }yellen da yake kan audugar. E-Hukunce-hukunce istihadha:Hukuncin mai ka]an shine wajabcin yin alwala don yin kowace sallah da kuma wanke gabanta idan ya gur~ata da jini.Hukuncin matsakaiciya shine }ari akan abinda ya gabata za ta yi wanka guda ]aya domin yin sallar Asuba,kai a kowace sallah ma in dai jinin istihadha ya auku gabanin sallar ko a lokacin da take sallar.Hukuncin na mai yawa shine }ari akan abunda aka ambata shine za ta yi wani wanka dabam domin yin Zuhuraini idan ha]a sallolin za ta yi,da kuma wani wankan domin yin sallar Isha’aini idan suma ha]a su ]in za ta yi.Amma idan ya kasance Istihadhar ta faru ne bayan sallar Asuba,to wajibi ne akanta a ranar ta yi wanka sau biyu:na farko don yi zuhraini na biyu kuma don yin Isha’aini.In da a ce Istihadhar ta faru ne bayan ta yi Zuhraini,to wanka ]aya ne ya wajaba akan ta a ranar wato domin yin Isha’aini.Wani tambihi anan shine in da a ce ba ha]a sallah za ta yi ba misali za ta yi sallar zuhur yanzu bayan wani lokaci kuma ta yi sallar asar to a nan wajibine ta yi wanka ga kowace sallah,saboda haka ha]a sallar domin sau}i ne ba wajibi ba.Kuma yadda ake wannan wanka shine shigen yadda ake wankan janaba.Insha Allah a darasi na gaba za soma babobi na Mu’amalat kasantuwar an kammala babobi na Ibadat a wannan darasi.
|
|||
Last Updated on Sunday, 28 January 2018 19:38 |