Dabi’oin Imam Hassan (AS) |
![]() |
![]() |
Written by administrator | |||
Friday, 10 November 2017 19:33 | |||
Insha Allah a wannan darasi za a kawo wasu daga cikin Akla} ]in Imam Hassan[AS] domin su zama darussa garemu da zamu darastu dasu.Idan mutum ya bibiyi tarihin Imam Hassan zai ga cewa a cikin watan Safar ne wafatin shi ya kasance,banbancin da aka samu a wajen Malamai na Tarihi shine a nawa ga watan ne ya rasu,wasu Malamai sun tafi akan cewa yayi shahada ne a 7 ga watan Safar wasu kuma sun tafi akan cewa a ranar 28 ga watan Safar ne.Sanadiyyar wafatinsa ko shine sakamkon guba da Mu’awiya ya bayar asa masa a abinci,wato dai kamar yadda Yazidu ]an Mu’awiya ya ba da umarnin a kashe Imam Husain da takobi shi kuma Mu’awiya ya ba da umarnin a kashe Imam Hassan da guba,haka nan baban Mu’awiya wato kaka ga Yazidu Abu Sufyan duk ya}o}in da ma}iya suka yi da Manzon Allah tun daga ya}in Badar,Uhud da dai sauransu har ya zuwa na Fatahu Makka to Abu Sufyan ne ya jagorance shi,shi yasa in mutum ya duba kuma yayi tunani zai ga cewa gidan Bani Umayya gida ne wanda tun asalinsa ya ginu ne kan fa]a da addini da kuma ma’abuta addini ne.Gabanin kawo darussan Akla} daga rayuwar Imam Hassan ga wasu sassa na rayuwarsa mai albarka: 1- Haihuwarsa: An haife shi ranar talata 15 ga watan Ramadan,shekara ta 3 bayan hijira. 2- Nasabarsa: Mahaifinsa Imam Ali[AS] mahaifiyarsa Sayyida Fatima[AS]kakansa ta wajen mahaifiya Manzon Allah[SAAW].kakansa ta wajen mahaifi Abu Dalib.kakarsa ta wajen mahaifiya Sayyida Khadija.kakarsa ta wajen mahaifi Fadimatu ‘yar Asad. 3- Nash’a ]insa: Imam Hassan[AS]kamar yadda aka haife shi a madina anan ya rayu kuma ya rasu,face kusan shekaru shidda da yayi a kufa,lokacin da Imam Ali[AS] yana zaune a kufa.Bayan shahadar Imam Ali[AS] da wata shidda Imam Hassan[AS] ya bar kufa ya dawo madina.Ya rayu tare da kakansa wato Manzon Allah[SAAW] shekaru bakwai da watanni.Ya rayu tare da Mahaifinsa Imam Ali[AS] shekaru 37.Bayan shahadar Imam Ali[AS] ya rayu shekaru 10.Imam Hassan[AS] ya halarci duk ya}o}in da Imam Ali[AS] yayi wato ya}in Jamal,siffin da kuma ya}in Nahrawan. 4- La}ubbansa: Yana da la}ubba masu yawa amma wanda yafi fice shine “Assib]i” kuma anai masa kinaya da Abu Muhammad wannan kinaya yazo akan cewa Manzon Allah ne yasa masa ita. 5- Shekarunsa: Imam Hassan[AS] ya rayu a duniya shekaru 47. 6- Muddan Imamancinsa: Shekaru 10 ne. 7- ‘Ya’yansa: Imam Hassan[AS] yana ‘ya’ya 15,maza 8,mata 7. 8- Wafatinsa: Imam Hassan[AS] ya rasu ranar Alhamis 7 ga watan safar a wata ruwaya kuma 28,shekara ta 50 bayan hijira. 9- Kabarinsa: Yana madina ne a Ba}i’a,kusa da kabarin kakarsa Fatima ‘yar Asad wato mahaifiyar Imam Ali[AS]. 1-HAKURINSA:Imam Hassan ya kasance mai yawan ha}uri hatta ma}iyansa dama wa]anda suka ya}e shi sun tabbatar da haka ga misalan wasu daga cikin ha}urinsa:A-Ha}urinsa ga mabiyansa idan mutum ya bibiyi tarihin Imamai zai ga cewa babu wani Imami da ya sha wahala da mabiyansa ta fuskoki dabam dabam kamar Imam Hassan misali ya samu matsalar ‘yan tawayiyya wato wa]anda suka yi masa tawaye musamman bayan sulhu da Mu’awiya,haka nan a cikin mabiyansa an samu wa]anda suka dunga fa]a masa ba}a}en maganganu alal misali a cikinsu akwai wanda suka ha]u amma sallamar da yayi masa itace, Assalamu Alaika ya muzillal Mu’uminin,kai akwai wa]anda har hari sai da suka kai masa har suka raunata shi amma haka Imam Hassan yai ta ha}uri da irin wa]annan munanan halaye nasu har ya koma ga Allah Ta’ala.B-Akwai wata rana Imam Hassan cikin dabbobinsa na gida sai ya ga wata akuya }afarta a karye alamu kuma ya nuna kamar karyata aka yi da gangan sai ya tambayi wani bawansa waye yayi wannan abu? Sai bawan nasa ya ce nine,sai ya ce masa don me kayi haka? Sai bawan ya ce don in baka haushi,sai Imam Hassan yayi murmushi ya ce to ni ko zan faranta maka rai,shine Imam Hassan ya ‘yan ta shi kuma yayi masa kyauta mai yawa.C-Akwai wani mutumin Sham da ya zo Madina –Mutanan Sham a lokacin Mu’awiya ya gina su akan }iyayya da Ahlul bayt da kuma la’antarsu da zaginsu-lokacin da wannan mutumi ya ha]u da Imam Hassan akan hanya kawai sai ya fara zagin Imam Hassan da kuma la’antar Imam Ali,Imam Hasan dai bai ce masa komi ba sai da ya gama Imam Hassan ya dube shi yayi masa sallama ya ce ya kai wannan dattijo ina tsammani kai ba}o ne,idan kana da bu}ata ta abinci ko tufafi ko ku]i zan baka,idan kuma in da zaka je baka san wajen ba muje zan kai ka,idan kuma baka da in da zaka sauka to ka zo gidana ka sauka,jin haka sai wannan mutumi na Sham ya fashe da kuka,ya ce lalle na shaida kai khalifan Allah ne a bayan }asa,ya ce kuma a da kai da babanka babu wasu da nafi }i kamar ku,amma yanzu babu wanda nafi so yanzu a duniya nan kamar ka,ya ce a wajen ka zan sauka,haka ya zauna wajen Imam Hassan a Madina har sai da zai koma Sham,kuma ya zo akan cewa tun daga lokacin mutumin ya zama ]an Shia,to mu dubi yadda kyakkyawar ]abi’a take canza ma}iyi ya zama masoyi. 2-KYAUTARSA:Imam Hassan ya kasance mai yawan kyauta saboda ma yawan kyautarsa ya zo a tarihinsa cewa a garin Madina a lokacin duk wanda aka je wajensa neman wata biyan bu}ata in har ba zai iya ba to sai ya ce aje wajen Imam Hassan,idan aka je wajensa to zai ko biya bu}atarsa ga misalan wasu daga cikin kyautarsa:A-Akwai lokacin da Imam Hassan ya ji wani mutumi yana ya Allah ka bani dirhami dubu goma,nan take Imam Hassan ya koma gida ya aiko masa da dirhami dubu goman.B-Ya zo akan cewa wata rana Imam Hassan yana tafiya sai ya ga wani ba}in mutum yana zaune jikin wata gona yana cin abinci,lokacin da yake cin abincin akwai kare kusa dashi,to sai ya kasance in ya ci loma guda sai ya jefa ma karen loma guda,sai Imam Hassan ya tambaye shi mi yasa kake yin haka? Sai mutumin ya ce ina jin kunya ni ina cin abinci yana kallo na ban bashi ba,jin haka sai Imam Hassan ya ce masa ya zauna ya jira shi yana zuwa,sai Imam Hassan ya je ya samu mai wannan bawa da kuma gonar, ya sai bawan da kuma gonar bayan haka sai ya koma wajen wancan mutumin ya ce yanzu ya ‘yanta shi kuma ya mallaka masa gonar.Mu duba mu gani sakamakon wannan ]abi’a mai kyau tasa Imam Hassan ya yi masa wannan saayi da kuma ihsani.C-Akwai wani mutumin }auye da yazo wajen Imam Hassan da wata bu}ata to tun kafin ya fa]i bu}atarsa sai Imam Hassan ya bashi dirhami dubu goma ganin haka sai ba}auyen abin ya bashi mamaki ya ce, ya shugabana ban fa]i bu}atata ba har ka biya man ita sai Imam Hassan ya ce, “Muna kyauta tun gabanin a tambaya saboda kiyaye mutunci.D-Yazo a tarihin Imam Hassan cewa kusan koda wane lokaci a }ofar gidansa akwai masu zuwa neman taimako kuma yana taimaka masu haka nan kuma ana dafa abinci domin aba wa]anda basu dashi a lokacin har la}abi ake yi masa da Mai kyautar-Ahlul Bayt.E-Akwai lokacin da aka tambayi Imam Hassan mi yasa duk lokacin da aka tambaye ka wani abu baka cewa a’a face ka bayar? Sai ya ba da amsa da cewa, “Ni ma ina ro}on Allah kuma yana bani saboda haka ina jin kunya ina ro}on Allah ya kuma bani wani kuma ya ro}eni ni kuma ban bashi ba.” 3-TAWADI’UNSA:Imam Hassan ya kasance mai gayar tawali’u ga misalan wasu daga ciki:A-Wata rana Imam Hassan yana tafiya sai ya ha]u da wasu miskinai sun zauna suna cin abinci sai suka yi masa tayi,dama yana kan dabba ne sai ya sauka ya ce, “Allah baya son masu girman kai” sai ya ci abincin bayan haka ya ce masu yana gayyatar su liyafa a gidansa,da suka je bayan ya basu abinci ya yi masu kyaututtuka na tufafi da ku]i.B-Haka nan makamancin haka ya ta~a faruwa shi kuma yara ne matasa suna cin abinci suka gayyace shi domin yayi musharaka dasu wajen cin abinci ya amsa masu saboda tawadi’unsa bayan haka suma ya gayyace su zuwa gidansa da suka je ya basu kyaututtuka dabam dabam.C-Daga cikin Tawadi’un Imam Hassan akwai lokacin da yana zaune zai tashi kenan sai ga wani fa}iri yazo wajensa yai masa maraba da zuwa,ya ce masa gashi ka zo lokacin da ni kuma zan tashi,ka yi man izini da in tafi,mu dubi irin wannan tawadi’u na Imam Hasssan. 4-IBADARSA: Imam Hassan ya kasance mai yawan ibada,an ruwaito daga Imam Sadi}[AS] ya ce, “Imam Hassan a zamaninsa babu wanda ya kai shi yawan ibada.” Ga misalan wasu daga cikin ibadodinsa:A-Hajjinsa:Imam Hassan ya yi aikin Hajji a rayuwarsa ]ai-]ai har guda ashirin da biyar kuma baki ]ayan wa]annan Hajjin- 25 – ya yi sune ta hanyar tattaki wato a }asa yake takawa tun daga Madina har ya zuwa Makka,akwai ma lokacin da ka tambaye shi mi yasa idan zai tafi aikin Hajji yake tafiya a }afa maimakon ya hau abin hawa wato dabba? Amsar da ya bayar itace, “Ina jin kunyar Allah Ta’ala in kama hanya zuwa ]akinsa ba akan }afafuwa na ba.” Wata ruwaya ta nuna cewa wani lokaci ya kan yi tafiyar a }afa bama tare da takalmi ba.Akwai wani aikin Hajji da yayi shi da Imam Husain,sun taso daga Madina zuwa Makka to akan hanya mahajjata da ke kan abun hawa wato dabbobi misali ra}uma da kuma doki sai kowa yana jin kunyar ya wuce su Imam Hassan da Imam Husain kasantuwar suna tafiya a }afa ne,sai wani daga cikin mahajjatan ya samu Imam Hassan akan ko zasu hau dabba saboda ga matsalar da ake ciki,Imam Hassan ya ce lalle niyyar da suka yi shine zasu taka da }afa ne har ya zuwa Makka,to shine Imam Hassan suka canza hanya wadda ba a cika bi ba.B-Karatun-Al}ur’an:Imam Hassan ya kasance mai yawan karatun Al}u’ani ya zo a tarihin sa cewa a kowane dare ya kan karanta Suratul-Khahafi.C-Sallah:Imam Hassan ya kasance mai yawan salloli ya zo a tarihinsa cewa idan ya yi sallar Asuba to ya kan zauna in da yayi sallar ba tare da yayi magana da kowa ba yana ibadodi har ya zuwa rana ta keto,idan kuma rana ta fito ya kan tashi yayi sallah ta nafila raka’a hu]u,wannan sallah ana ce mata salatul-ish’ra} tana da falala,in ma mutum ba zai samu yin raka’a hu]un ba to sai ya yi raka’a biyu.An ruwaito Hadisi daga Imam Ali[AS] ya ce, “Duk wanda ya yi sallar Asuba sai ya zauna anan in da yayi sallar yana Azkar har rana ta fito to wannan zai kasance masa shamaki daga shiga wuta.” D-Zikiri:Imam Hassan ya kasance mai yawan zikiri ne ya zo a tarihinsa cewa koda wane lokaci harshensa cikin zikiri yake kamar tasbihi,tahmidi,hailala da dai sauransu. 5-KUKANSA:Imam Hassan ya kasance mai yawan kuka saboda tsoron Allah,ya zo a tarihinsa cewa idan ya zo yin Al-wala akan ga canji a jikin shi,aka tambaye shi mi yasa haka yake faruwa? Ya ce “Dole ne ga duk wanda zai tsaya gaban Allah haka ya faru da shi.” Haka nan idan ya tsaya zai yi Sallah akan ga jikinsa na makyarkyata wato saboda tsoron Allah.Haka nan kuma idan ya tuna mutuwa ko }abari ko ranar }iyama ko tsalleke sira]i ya kan yi kuka.A ta}aice dai Imam Hassan ya kasance mai yawan kuka,mu duba mu gani duk da cewa shi Ma’asumi ne to ina ga mu.Ya zo a Hadisi cewa, “Bushewar ido –rashin yin kuka saboda tsoron Allah –bushewar zuciya yake haifar dashi,bushewar zuciya kuma yawan zunubi yake sabbaba shi.” Ashe kenan idan muna so mu siffata da wannan ]abi’a ta kuka saboda tsoron Allah to munisanci aikata zunubi . 6-ZUHUDUNSA:Wato gudun duniyarsa Imam Hassan ya kasance mai yawan gudun duniya,akwai ma wani malami mai suna Muhammad ibn Babawaihi Al}ummiy da ya rubuta littafi khususan kan zuhudun Imam Hassan yasa ma littafin suna “Zuhudul-Hassan” Imam Sadi} yana cewa, “A lokacin Imam Hassan babu wani da ya kai shi zuhudu a zamanin sa.” Imam Hassan yana yawan cewa, “Ya ma’abuta jin da]in duniya wadda ba zata wanzu ba,ru]uwa da abunda ba zai wanzu ba rashin tunani ne.” Ya zo a tarihin Imam Hassan cewa sau biyu yana bada duk wani abunda ya mallaka na abun duniya ga matalauta. 7-MAKARIMUL-AKLA{:Zan kammala wannan rubutu da wani Hadisi da aka ruwaito daga Imam Hassan[AS] da ya ce, “Makarimul-Akla} guda goma ne sune:1-Fa]in gaskiya.2- Bayarwa ga wanda ya ro}e ka.3-Kyakkywar ]abi’a.4-Yin tukwiyci ga kyautatawar da aka yi maka.5-Sadar da zumunci.6- Kyautata ma ma}wabci.7- Kiyaye ha}}in abokantaka.8-Kula da ba}o.9-Kunya.10-Nisantar dukkan munanan ]abi’u.A wani Hadisi kuma Imam Hassan ya ce, “Halakar mutane tana ga abu ukku sune:1-Girman kai.2-Kwa]ayi.3-Hassada.Insha Allah a darasi na gaba zai kasance ne kan [abi’oin Imam Husain[AS].
|