Friday, 28 January 2022
Email
Make My Homepage
RSS
Register
Darussa daga waki’ar Karbala Print E-mail
Written by administrator   
Friday, 13 October 2017 23:18

A wannan darasi insha Allah bayani dai-dai gwargwadon iko zai kasance ne kan wani sashe daga cikin sassa dabam dabam na darussa daga cikin wa}i’ar Karbala,wannan darasi ko shine bayani dangane da }arshen wa]anda suka afkar da wannan wa}i’a ta Karbala wato }arshen wa]anda suka ba da umarni da kuma wa]anda suka aiwatar da umarnin a wannan gida na duniya kafin ranar Lahira.Idan mutum ya bibiyi tarihin wa]anda suka afkar da wannan wa}i’a ]aya bayan ]aya misali Yazidu[LA] Ibn Ziyad[LA] Ibn Saad[LA]  mutum zai ga cewa kowannensu ya yi mummunan }arshe a wannan gida na duniya wanda wannan darasi ne babba ga azzalumai da kuma masu goyon bayansu wato dai abunda ba-haushe yake cewa gani ga wane ya isa wane tsoron Allah.Bayanin zai gudana ne kan wa]annan ababe:

1-Mummunan sakamako ko u}uba kan wa]anda suka afkar da wannan wa}i’a a dun}ule.

2-Mummunan sakamako ko u}uba kan wa]anda suka afkar da wannan wa}i’a a warware.

3-Wa]anda Imam Husain[AS] ya yi addu’a akansu ranar Ashura.

4-Abun da ya samu wannan al’umma sakamakon wannan wa}i’a ta Karbala.

          1-Mummunan sakamako ko u}uba kan wa]anda suka afkar da wannan wa}i’a ta Karbala a warware wato }arshen da kowannan su ya yi a matsayin su na ]ai-]aiku ga misalan wasu daga cikinsu:1-Yazidu[LA]Idan mutum ya bibiyi tarihin Yazidu zai ga cewa tun bayan da wannan wa}i’a ta Karbla ta auku to komi nasa ya lalace kuma ya ta~ar~are wato dai matsaloli dabam dabam ta kuma fuskoki dabam dabam suka taso masa har takai daga }arshe ya yi mummunan cikawa,}abarinsa ma bola wato wajen zuba shara ya zama daga baya.2-Ibn Ziyad[LA] Shima idan mutum ya dubi }arshen rayuwarsa zai ga cewa kashe shi aka yi aka kuma sare kansa kamar yadda yasa a sare kan Imam Husain[AS] da sahabbansa bayan an sare kansa aka kaima Muktar assa}afi a lokacin yana cin abinci shine yake cewa ina godiya ga Allah Ta’ala cewa an kai kan Imam Husain gaban ibn Ziyad yana cin abinci ni kuma gashi an kawo mani kan ibn Ziyad ina cin abinci,a lokacin da aka kawo kan shi ibn Ziyad to akwai wasu kawuka na wasu daga cikin makusantansa wa]anda suma aka kashe su aka kuma sare kawukansu,to wa]annan kawuka suna zube gaban Muktar kawai sai ga maciji ya bayyana ya hawo kan wa]annan kawuka sai aka ga ya shiga cikin hancin ibn Ziyad ya fita ta cikin kunnensa saaannan kuma ya sake shiga ta kunnensa ya fita ta cikin hancinsa,lokacin da Muktar ya gama cin abinci sai ya tashi ya tattaka fuskar ibn Ziyad da takalminsa,bayan haka sai ya tu~e takalminsa yaba wani bawansa akan yaje ya wanke masa shi ya ce saboda wannan najasar da ya taka dashi.Bayan haka kuma ya aika da wannan kai na ibn Ziyad da sauran kawuka ga Imam Zainul Abidin lokacin yana Makka,Ikon Allah lokacin da aka kai wannan kai na ibn Ziyad gaban Imam to yana cin abinci ne,shine Imam Zainul Abidin yake cewa, “An kaini da kuma kan mahaifina gaban ibn Ziyad yana cin abinci shine na ro}i Allah kada ya kar~i rai na har sai na ga kan ibn Ziyad ina cin abinci saboda haka ina godiya ga Allah Ta’ala da ya amsa mani wannan addu’a.” To wannan shine }arshen ibn Ziyad a wannan gida na duniya.3-Umar ]an Saad:Shima idan mutum ya bibiyi tarihinsa zai ga cewa yayi mummunan }arshe ne daman Imam Husain ya fa]a masa cewa duk al}awurar da aka yi masa misali na zama gwamna a garin Rayyi da sauransu to ba wanda zai samu kuma daga }arshe za a kashe shine a kuma sare kansa,yara kuma a kufa zasu yi ta }ollo da kan nasa,tabbas kuma haka abun ya auku wato na babu wani abu da ya samu na al}awuran da aka yi masa kuma daga }arshe kashe shi aka yi aka sare kan bayan an gama tangaliliya da kansa a garin Kufa aka aika ma Imam Zainul Abidin,lokacin da aka kai kan ibn Saad gaban sai ya yi sujuda ta godiya ga Allah Ta’ala ya ce, “Godiya ta tabbata ga Allah da ya ]aukan man fansa daga ma}iyanmu, Allah kuma ya saka ma Muktar da alhairi.”4-Shimru[LA]Shine ainihin wanda ya kashe Imam Husain shima in mutum ya bibiyi tarihin }arshen rayuwar sa zai ga cewa bacin matsaloli da yai ta fuskanta bayan wannan wa}i’a daga }arshe Muktar yasa a farauto masa shi,lokacin da Shimru yaji cewa ana nemansa sai ya gudu ya tafi wani }auye aka jin labarin in da yake nan ma aka bishi,sai ya sake gudu shi da wasu da suka yi musharaka a wannan wa}i’a ta Karbala suka je daji suka zauna,haka sojojin Muktar suka same su in da suka ~oye,da yake dare yayi lokacin har sun yi barci sai kawai suka ga an zagaye su a ta}aice dai anan take aka kashe Shimru aka sare kansa tare da wa]anda aka kashe tare dashi aka kawo kan ga Muktar shi kuma ya aika kawukan ga Imam Zainul Abidin.Mu dubi yadda }arshen wannan laanannan ya kasance zama cikin garin Kufa ya gagare shi ya gudu yaje }auye can ma ya gagare shi daga }arshe ya }arata a daji.5-Harmala:Shi Harmala shine wanda ya kashe ]an Imam Husain mai suna Abdullah jariri ]an wata shidda wato wanda Imam Husain ya ]aga gaban su ma}iya ya ce masu idan kuna ganin ni na yi maku wani abu to shi wannan jaririn fa bakwa bashi ruwa ya sha ba kawai sai Harmala ya harbo kibau sai ga wuyan wannan jariri! Akwai wani mutumin Kufa da yazo wajen Imam Zainul Abidin a Madina sai Imam Zainul Abidin yake tambayarsa dangane da Harmala sai ya ce na barshi a Kufa a raye,sai Imam Zainul Abidin ya ]aga hannunsa masu albarka sama ya yi addu’a ya ce, “Ya Allah ka ]an]ana masa zafin wu}a ka ]an]ana masa zafin wuta.” Wannan mutumi ya ce da na koma Kufa na samu Muktar ya soma ]aukar fansa na duk wa]anda suka ya}i Imam Husain,da muka ha]u dashi yake ce man kwana biyu bamu ha]u ba sai ya ce masa ai na yi tafiya ne ban jima da dawowa ba,sai wannan mutumin ya ce muna cikin magana da Muktar sai ga wani yazo wajensa yake ce masa sun gano in da Harmala yake sai Muktar ya aika wasu maya}a akan suje su kamo shi,ba a jima ba sai gashi an kamo Harmala aka kawo shi gaban Muktar.Muktar ya dubi Harmala ya ce masa na gode ma Allah da ya bani iko akanka,shine Muktar ya ce a nema masa mahauci kuma yazo da wu}a,da mahaucin yazo sai ya ce masa yenke min hannuwansa ya yenke,sai ya sake ce masa yenke min }afafuwansa aka yenke,sai Muktar ya ce a hura huta aka hura sai ya ce ku jefa shi a ciki,sai abokin shi Muktar ya ce Subhanallah,sai Muktar ya ce masa tasbihi abu ne mai kyau amma mi yasa kayi,sai ya ce masa wannan tafiyar da na yi zuwa Makka naje wajen Imam Zainul Abidin sai yake tambaya ta dangane da Harmala na ce masa aiko na barshi a Kufa yana raye nan take sai ya ]aga hannu yai addu’a Allah ya ]an]ana masa zafin wu}a da kuma wuta,sai Muktar ya ce masa tabbas kaji Imam Zainul Abidin yana wannan addu’a,sai mutumin ya ce masa wallahi na jishi yana fa]in haka nan take sai Muktar ya yi sallah raka’a biyu ta godiya ga Allah Ta’ala kuma ya tsawaita sujuda, kafin ya gama sallar Harmala ya }one }urmus cikin wutar,bayan haka sai shi wannan mutumi ya bu}aci Muktar da suje gidansa su ci abinci,sai Muktar ya ce masa haba wane ka fa]a min ga addu’ar da Imam Zainul Abidin ya yi kuma Allah ya amsa masa wannan Addu’a da yayi ta hannuna saannan kace in ci abinci? Ai yau azumi zan yi saboda godiya ga Allah kan wannan ni’ima da yayi mani.To mu duba mu gani wannan shine }arshen Harmala a gidan Duniya ballantana kuma a ranar Lahira,Harmala yayi munanan abubuwa da yawa a wannan wa}i’a ta Karbala bilhasali ma shine ya ]auki kan Imam Husain daga Karbala zuwa Kufa.To haka in mutum ya bibiyi tarihinsu ]aya bayan ]aya zai ga cewa dukkansu sun yi mummunan }arshe ne.Idan kuma muka juya ga wa]anda suka ]ebe kayan jikin Imam Husain bayan shahadarsa shima zamu ga cewa babu wanninsu wanda haka bai zamar masa wani bala’i da musiba ba a wannan gida na duniya ga misalan haka:Wanda ya ]auki rigar Imam Husain yana sata a jikinsa sai ciwon kuturta ya kama jikinsa baki ]aya nan take kuma aka ga fuskar sa ta canza,wanda kuma ya ]auki wandon Imam Husain to da yasa sai ya zamo bai iya tafiya sai dai zama,wanda ya ]auki rawanin Imam Husain to da yasa nan take gashin kansa ya ~ace wato ya zamo bai da }wayar gashi akansa,wanda kuma ya ]auki alkyabbar Imam Husain da ya isa da ita gida matarsa tace masa ka sani bani baka har abada kuma Allah ya jefa masa mummunan talauci daga }arshe ma hannayensa suka shanye,wanda kuma ya ]auki Zoben Imam Husain saboda sha}awar wannan laananne da yazo ]ebe zoben  har sare yatsun Imam Husain yayi,shi yasa lokacin da Muktar ya kamo shi sai ya sa ake yanyanka shi gudun-guduwa daga }arshe aka barshi nan jininsa ya tsiyaye ya mutu a haka,haka nan kuma wa]anda suka tattaka Imam Husain da dawakansu Muktar da ya kama su an ce su goma ne yasa aka ]aure hannayensu da }afafuwansu yasa a hau dawakai ai ta sukuwa akansu har sai sun mutu.  

          2-Mummunan sakamako ko u}uba kan wa]anda suka afkar da wannan wa}i’a ta Karbala gobe }iyama:Idan muka juya ga mummunan sakamako ko u}uba ranar }iyama zamu ga cewa mai tsanani ne.Allah Ta’ala yana cewa a cikin littafinsa a suratun-Nisa’i aya ta 93, “Duk wanda ya kashe Mu’umini da gangan to sakamakon sa Jahannama ne kuma zai tabbata a cikinta kuma Allah yayi fushi dashi kuma ya tsine masa kuma yai masa tattalin azaba mai girma.” Mu dubi irin wannan mummunan sakamako ]aya bayan ]aya:1-Shiga wutar Jahannama.2-Tabbata har abada a cikin wutar.3-Fushin Allah akansa.4-Tsinewar Allah akansu.5-Fuskantar azabobi dabam dabam ranar }iyama.To mu duba fa mu gani sun yi hasarar duniya da lahira,tarkace duniyar da aka yi masu al}awari basu same shi ba kai koda ma sun samu to sai me! Ko da a ce sun samu ababen da aka yi masu al}awarin na dukiya da matsayi to yau ina dukiyar? Ina kuma matsayin? Saboda haka mummunan sakamakon dasu ka fuskanta na wa]anda suka afkar da wannan wa}i’a a wannan gida na duniya babban darasi ne ga dukkan azzalumai na kowane zamani a kuma kowane waje.Kuma mutum ya tambayi tarihi ya bashi amsa akan cewa shin Yazidu da ibn Ziyad sun samu nasara na bice hasken Ahlul bayt ko ko akasin haka suka samu? Tabbas in mutum ya bincika zai ga cewa sakamakon wannan mummunan abun da suka yi na afkar da ita wa}i’ar sai suka tambatsa fahimta ta Ahlul bayt a lokacin musammam ga mutanen Sham tun dasu da yawansu basu san su waye Ahlul bayt ba ballantana kuma sanin matsayinsu sa~anin ko mutanen kufa sun san su waye Ahlul bayt kuma sun san matsayinsu,shi yasa in mutum ya bibiyi jawabin da Sayyida Zainab ta yi a Kufa yana da banbancin kan wanda ta yi a Sham saboda su mutanen Kufa sun san ko su su waye amma mutanen Sham basu sansu ba,shi yasa lokacin da wani a cikin fadar Yazidu ya ce ma Yazidu ya bashi wa’iyazu billahi Sayyida Fa]ima ]iyar Imam Husain yayi sa ]aka da ita daga }arshe da ya fahimci cewa wace ce ita nan take ya ce Yazidu Allah ya tsine maka ni ai na ]auka wa]annan kamammun ya}i daga Rum ne aka zo dasu shine Yazidu ya ce a je akashe shi, a ta}aice abun da Yazidu ya yi a lokacin sai ya zama sanadiyyar tambatsar shi’anci saboda a lokacin da yawa sai suka yi masa tawaye musamman a Madina da kuma Makka wanda sakamako hakan ya aika da maya}a zuwa ga wa]annan birane masu tsarki suka yi munanan abubuwan da suka yi wanda tarihi shaida ne akan haka.Dawowa kan mummunan sakamako na lahira daga ciki akwai cewa ba zasu samu ceto na Manzon Allah[S]ba wato ceto na amma da kuma kassa,haka nan kuma yazo akan cewa Sayyida Zahra[AS] zata nemi ha}}in jini na Imam Husain wajen Allah Ta’ala ranar }iyama,duk ko wanda Ma’asumi zai yi husuma dashi ranar }iyama to tabbas ya shiga ukku,yama zo a Hadisi cewa wanda yafi kowa tsananin azaba ranar lahira shine wanda ya ya}i ma’asumi ko ya kashe Ma’asumi ko kuma wanda Ma’asumi ya ya}e shi ko ya kashe shi.

          3-Wa]anda Imam Husain[AS] ya yi addu’a a kansu ranar Ashura:Idan mutum ya bibiyi abubuwan da suka auku a ranar ashura zai ga cewa akwai wa]anda Imam Husain yayi addu’a akansu a ranar ashura sakamakon mummunan abunda suka fa]a masa na isgili ko mummunar magana kuma a ranar  addu’ar da yayi a kansu ta kama su ga misalan wasu daga cikinsu:1-Kamar yadda yazo a tarihi cewa a ranar ashura Imam Husain yasa an ha}a ramuka a bayan hemomin da suke ciki bayan an gama ha}ar ramukan yasa a zuba itatuwa a cikinsu a kuma kunna masu wuta,hikimar yin haka shine saboda su zama shamaki daga ma}iya koda zasu yi tunanin su ~ullo ta baya, to bayan an yi hakan sai wani laananne daga ciki ma}iya mai suna ibn Jauzata ya bu]e baki ya ce ya Husain ina yi maka albishir cewa ka hura wutar da zaka soma shiga a duniya gabanin kaje ka shiga ta lahira,sai Imam Husain ya ce masa kaitonka ni kake ce ma haka? Ya ce iye,nan take Imam Husain ya yi addu’a akansa ya ce, “Ya Allah ka jashi zuwa wuta ka ]an]ana masa zafinta a duniya gabanin ya shige ta ranar Lahira.” Daman mutumin yana kan dokine  aka ce haka dokin ya zuba dashi a guje bai tsaya koina ba sai kusa da ramin wuta yana zuwa yayi tutsu dashi cikin wutar haka ya }one cikin wutar,ganin haka aka ce Imam Husain ya yi sujuda ta godiya ga Allah Ta’ala.2-Yazo akan cewa a ranar ashura Imam Husain yayi addu’oi to daga cikin addu’in da yayi akwai in da yake cewa, “Ya Ubngiji lalle mune iyalan gidan Annabinka zuriyyarsa kuma makusantansa.....jin haka sai wani tsinanne daga cikin ma}iya ya ce wane kusanci kake dashi da Muhammadu,sai Imam Husain yayi addu’a akansa ya ce, “Ya Ubangiji ina ro}onka ka nuna mani }as}antar wannan mutumi da gaggawa a wannan rana.” Bayan haka sai wannan mutumi ya tafi yayi ga’i]i-kashi- ya tsugunna yana yi sai ko kunama ta harbe shi a zakarinsa nan dai ya dunga kururuwa yana kuma birgima akan kashinsa.3-Akwai wani mutum a ranar ashura da ya harbi Imam Husain da kibiya sai ta ma}ale a kumatunsa sai Imam Husain yayi addu’a akansa da cewa , “Ya Allah kada ka }osar dashi da ruwa.” Nan take ciwon }ishin ruwa ya kama shi ta yadda ko ya sha bai }oshi.4-Haka nan a ranar ashura akwai wanda ya kira sunan Imam Husain ya ce ya Husain ba zaka ta~a ]an]anar ruwa ba ko da ko ]igo ne sai dai ka mutu a haka ko kayi bai’a ga Yazidu[LA] shima Imam Husain yayi addu’a akansa ya ce, “Ya Ubangiji ka kashe shi da }ishi kada ka gafarta masa har abada.” Haka ko abin ya faru da }ishi ya mutu koda wane lokaci sai dai aji yane cewa ruwa-ruwa ko yasha kuma bai }oshi kai daga }arshe ma a jikin kogi ya mutu wajen shan ruwa.5-Yazo a tarihi cewa lokacin da aka kashe Imam Husain sararin sama ya janza yayi jajajur,wani ba}in duhu ya lullu~e wajen, ta yadda su ma}iyan basu ganin junansu har suka yi zaton cewa lalle azaba ta sauka akansu to bayan wani lokaci yanayin ya yaye.Da dai sauran ayoyi masu yawa da suka afku a ranar ashura gasu wa]annan ma}iya Allah da kuma iyalan gidan Manzon Allah.

4-Abunda ya samu wannan al’umma sakamakon wannan wa}i’a ta Karbala:Idan mutum ya bibiyi wasu Hadisai da aka ruwaito daga Aimma na Ahlul bayt zai ga cewa akwai wasu ababe da suka bi wannan al’umma tun daga ran da aka kashe Imam Husain har ya zuwa yau kuma zasu cigaba da bibiyar al’umma har ya zuwa bayyanar Imam Mahdi[AF] daga cikinsu akwai ru]amin ko rikir-kicewa na lissafin watan Azumi da kuma Sallah {arama da kuma sallah Babba.An ruwaito Hadisi daga Imam Sadi}[AS] ya ce, “Lokacin da aka kashe Imam Husain aka kuma sare kansa sai wani Mala’ika da yake }ar}ashin al’arshi ya ce, “Ya ke wannan al’umma mai faganniya wadda kuma ta zalunci kanta bayan Annabinta kada Allah yayi maki muwafa}a da Idin }aramar sallah da kuma idin babbar sallah,sai Imam Sadi} ya ce ba mamaki wallahi basu samu muwafa}ar ba ko, kuma ba zasu ta~a samun muwafa}ar ba har sai mai ]aukar fansan Imam Husain ya bayyana.A wani Hadisi kuma da aka ruwaito daga Imam Jawad wani yake tambayarsa dangane da Hadisin da aka ruwaito cewa ba zasu samu muwafa}ar azumi ba,sai Imam Jawad ya ce, “Lokacin da ma}iya suka kashe Imam Husain sai wani Mala’ika yayi addu’ar cewa kada su samu muwafa}ar ganin watan Azumi ko na Sallah.” Haka nan ko wannan yawan sa~ani dake tsakankanin ‘yan wannan al’umma daga cikin musabbabinsa akwai kisan Imam Husain[AS]kamar yadda ya zo a ruwayar wani Hadisi.  

Last Updated on Friday, 13 October 2017 23:24
 
Home Maudu'oi daban-daban Darussa daga waki’ar Karbala
Copyright © 2022. www.tambihin.net. Designed by KH