Saturday, 02 December 2023
Email
Make My Homepage
RSS
Register
Bayani kan wankan Janaba. Print E-mail
Written by administrator   
Friday, 13 October 2017 23:14

A cigaba da kawo wasu babobi da ba a yi ba a darussa na Fi}hu da suka gabata,a wannan darasi insha Allah bayani zai gudana ne a wannan babi kan wa]annan ababe:

1-Nauo’in wanka.

2-Ababe da suke sabbaba Janaba.

3-Yadda ake wankan Janaba.

4-Wajibobin wankan Janaba.

5-Ayyukan da suka haramta ga mai Janaba.

6-Hukunce-hukuncen wankan Janaba.

7-Tambayoyi da Amsa kan wankan Janaba.

          1-Nauo’in wanka:Wanka ya kasu kashi biyu akwai wanda yake wajibi akwai kuma wanda yake mustahabbi,wankan da yake wajibi akwai wanda da maza da mata sun yi tarayya a ciki misali wankan Janaba,wankan mamaci ko ta~a mamaci,akwai kuma wanda yake na wajibi ne amma ya ke~anci mata kawai misali wankan Haila ko Nifasi ko kuma Istihadha.Wankan da yake mustahabbi ya kasu kashi-kashi a}alla ukku:1-Akwai wanka zamaniyya wato na wani lokaci ayyananne misali wankan Jumma’a,wankan Idi,wanka irin na munasabobi kamar ranar Mab’as ko Ghadir ko mubahala da dai sauransu.2-Akwai wanka makaniyya wato na wajaje masu tsarki misali wanka na shiga haramin Makka ko kuma haramomi na Aimma da dai sauransu.3-Akwai wanka Fi’iliyya wato na aiki misali wanka na sa harami ko ]awafi da dai sauransu.A wankan da suke na wajibi akwai guda hu]u wa]anda dukkan mazhabobi na Sunna da Shi’a sun ha]u akai sune:Wankan Janaba,Wankan Haila da Nifasi da kuma wankan Mamaci,sauran wanka na wajibi wa]anda ba wa]annan ba to ke~antattu ne ga wasu mazhabobi misali wankan ta~a mamaci wato bayan jikinsa yayi sanyi ko gabanin a kammala masa wanka ko wankan istihada to sun ke~anta ne a mazhabar Ja’afariyya,ko kuma wanka idan mutum ya musulunta to wannan ya ke~anta ne a mazhabar Malikiyya da kuma Hanbaliyya,amma a mazhabar Ja’afariyya idan mutum ya musulunta to babu wani wanka na shiga Musulunci sai dai idan yana da Janaba ne to anan wanka ya wajaba gareshi saboda Janabar ba wai saboda shiga cikin Musuluncin ba,suma shafi’iyya sun tafi akan wannan fatawa ne wato sa~anin su kuma a mazhabar Hanafiyya su a wajensu in dai ya Musulunta to ko da yana da Janabar ne to ba wajibi bane yayi wanka.

          2-Ababen da suke sabbaba Janaba:Abubuwa ne guda biyu sune:1-Fitar Maniyyi a falke ne ko a barci da gangan ne ko ba da gangan ba,a bisa za~i ko akasin haka.2-Jima’i:Ya auku ne ta hanyar halar ko kuma ta hanyar haram maniyyi ya fito ko bai fito.

          3-Yadda ake wankan Janaba:Akwai hanyoyi biyu da ake yin wankan Janaba,na farko akwai Tar-tibi na biyu akwai Ir-timasiy,amma a nan za a kawo bayanin yinsa ta hanyar Tar-tibi ne kasantuwar ci aka fi yi kuma shi ya fi falala.Da farko mutum zai fara da wanke kansa da kuma wuyansa,a wajen wanke kan nasa wajibi ne ya wanke dukkan gashin kan nasa kuma ya tabbatar da ruwa ya ta~a fatar kansa.Na biyu ya wanke baki ]ayan rabin jikinsa na dama,Na ukku ya wanke baki ]ayan rabin jikinsa na hagu.A wajen wanke kansa da wuyan sa ana so ya shigar da saman kafa]unsa wajen wankewar,haka nan wajen wanke rabin jikinsa na dama ana so ya ]an wanke ka]an daga rabin jikinsa na hagu wato dai ya ]an gwauta rabin jikin nasa,a wajen wanke cibiya da kuma al’aura abin da yafi shine lokacin da mutum yake wanke rabin dama to ya wanke da su, haka nan ma idan mutum ya zo wankin rabin hagu ya sake wankewa da su amma idan mutum ya raba su a wajen wankin dama da hagu shi ma yayi.Wani tanbihi muhimmi anan shine da mutum zai zo da wankan janabarsa sa~anin wannan tar-tibi to wankan sa ~atacce ne,yayi haka ne akan mantuwa ko da gangan ko kuma akan jahilci,wato dai yinsu a wannan jeri guda ukku da aka ambata wajibi ne a mazhabar Ja’afariyya amma a mazhaba ta Malikiyya,Shafiyya,Hanbaliyya da kuma Hanafiyya su ba wajibi bane, a matsayin mustahabbi ne yake wato su mutum zai iya fara ta ko ina yake so.

          4-Wajibobin wankan Janaba sune:1-Niyya.2-Wanke zahirin fatar jiki wato ya kasance babu wani shamaki tsakanin fatar jikin mutum da kuma ruwan da zai zuba domin wankewa in ko akwai to wajibi ne ya ]ebe shi.3-Wajibi ne ruwan da za a yi amfani dashi wajen wankan Janaba ya kasance Mu]la} ba Mubaf ba wato ruwa tsantsa ba wanda ya gauraya da wani abu ba.4-Wajibi ne ruwan ya kasance mai tsarki.5-Wajibi ne ruwan ya kasance na halal ba na sata ba ko }wace.6-Wajibi ne ya kasance mutum ya yi wankan da kansa ba wai yi masa za a yi ba sai in da wata lalura.7-Wajibi ne ya kasance babu wata matsala da za ta hana mutum amfani da ruwan misali rashin lafiya wanda in da zai yi amfani da ruwan zata }aru ko ta haifar masa da wani ciwon.8-Wajibi ne kowace ga~a da zai wanke ya kasance tana da tsarki gabanin wanke ta,wato in akwai najasa to ya wanke najasar da farko gabanin wanke ga~ar.9-Wajibi ne idan nau’in wankan da mutum zai yi na Tar-tibi ne to ya yi akan tartibin da aka ambata wato farawa da kai sai sashen dama sannan kuma sashen hagu.

          5-Ayyukan da suka haramta ga mai janaba:Ga wasu daga ciki 1-Haramun ne idan mutum na da Janaba ya ta~a rubutun Al}ur’an ko sunayen Allah Ta’ala ko kuma sunayen Annabawa da kuma Aimma[AS].2-Haramun ne idan mutum na da Janaba ya shiga cikin masallacin Ka’aba ko masallacin Manzon Allah[S]amma sauran masallatai da ba suba mutum zai iya shiga ya wuce kamar ya shiga ta wannan kofa ya fita ta wata kofa,abunda ya haramta a gareshi shine ya zauna ko kuma ya shiga domin ya aje wani abu.Amma wannan hukunci na haramcin shiga ko zama a masallatai da aka ambata bai hau kan Husainiyyoyi ba wato misali mai janaba zai iya shiga ya zauna ko ya aje wani abu ko kuma ya ]auko wani abu a cikinsu.3-Haramun ne ga mai Janaba ya karanta wani abu daga cikin surorin Aza’im ko da ko aya ]aya ce,surorin Aza’im guda hu]u ne sune:Suratul Ala},Suratun Najam,Suratu Sajada da kuma Suratu Fussilat.4-Haramun ne idan mutum na da Janaba ya shiga Haramomi na Aimma.Bayan haka kuma akwai wasu ababe da su kuma makaruhi ne ga mai janaba ya aikata su wato ba haramun ba ne,ga misalin su makruhi ne ga mai Janaba ya ci abinci ko ya sha abin sha ko yin barci amma idan mutum yayi alwala gabanin cin abincin ko barcin to karhancin ya gushe,haka nan makruhi ne yin lalle misali ga mata alhali tana da Janaba,haka nan makruhi ne idan mutum na da janaba ya karanta sama da aya bakwai a cikin surori na Al}ur’ani mai girma da dai sauran su.

          6-Hukunce-hukuncen wankan Janaba:Wato wasu mas’aloli da suka shafi wankan Janaba ga wasu daga ciki:1-Idan mutum ya yi wankan Janaba sai ta bayyana masa cewa akwai wani sashe na jikinsa da bai wanke ba to a nan ]ayan biyu, in bai san in da bai wanken ba to wajibi ne ya sake sabon wanka,in ko ya san in da bai wanken ba to ]ayan fuskoki ukku,ko dai ya kasance a gefen hagu ne to a nan sai ya wanke wajen shike nan,ko kuma ya kasance a gefen dama ne to sai ya wanke wajen ya kuma sake wanke gefen hagu baki ]ayansa,ko kuma ya kasance in da bai wanken ba ya kasance akai ne ko a wuya to anan zai wanke wajen saannan kuma ya sake wanke gefen jikinsa na dama da kuma hagu baki ]ayansa.2-Idan mutum yana wankan Janaba sai yayi Rihi ko bawali to wannan bai ~ata wankan sa ba wato ba zai ce ya faro sabon wanka ba haka zai cigaba da wankan nasa har ya kammala kuma wankansa ya inganta,sai dai bayan ya kammala wankan in zai yi wani aiki na ibada da sai an yi alwala ake yinsa misali sallah to a nan wajibi ne yayi alwalal.3-Idan mutum yayi wanka na Janaba to ya ]auke ma mutum alwala a bayansa sai dai fa in a cikin wankan yayi wani abu da yake ~ata Alwala kamar misalan da aka bayar na rihi da bawali amma duk wani wanka wanda ba na Janaba ba to bai ]auke alwala a bayansa misali na Haila ko na Jumma’a.4-Mustahabbi ne kafin mutum yayi wankan Janaba yayi bawali,hikimar yin haka shine ko da wani danshi zai fita daga al’aurarsa bayan wankan bai zai kasance maniyyi ba da zai sabbaba masa wani sabon wankan,sa~anin idan bai yi wannan istibra’i na bawali ba to dancin zai iya kasancewa na maniyyi ne wanda kuma haka zai wajabta masa ya sake sabon wanka.5-Wanda wanka na wajibai suka hau kansa ko kuma na wajibi da mustahabbi misali mace ne wanka na Haila da kuma na Janaba suka hau kanta to anan in ta yi wankan Janabar ya ]auke mata na Hailar wato ba zata ce ta yi wankan Janabar saannan kuma ta ce tazo ta yi na Hailar ba,zata yi wanka guda ]aya ne da niyya biyu,ko kuma wani misali wanka na janaba da kuma wankan ranar Jumma’a to shima wanka ]aya mutum zai yi da niyya biyu wato wankan Janaba da kuma na Jumma’a to haka dai mutum zai yi ko da nau’oin wankan sun kai ukku kobiyar ne duk dai guda ]aya zai yi na shi Janabar sai ya gwama da niyyoyinsu.6-Idan mutum shakka ta zo masa bayan ya kammala wankan janaba kan yayi wani abun da yake ~ata alwala? To a nan alwala bata wajaba a gareshi ba sai dai kawai yana iya yin alwalar a babin ihitiya]i.7-Idan maniyyi ya motsa daga muhallinsa amma bai fito ba to anan wanka bai wajaba akan mutum ba misali a cikin barci yayi mafarki amma maniyyi bai fito masa ba to babu wanka akan sa.

          7-Tambayoyi da Amsa kan wankan Janaba:Wa]annan wasu tambayoyi ne da aka ciro daga littafin Ajwibatul istifta’at na Ayatullah Khamna’i.

1-Tambaya:Mutum ne wanda janaba ta kan kama shi kuma ya kan yi wankar Janabar sai dai yadda yake wankan ba dai dai bane,to minene hukuncin sallolinsa da yayi su da wannan ~ataccen wankan?

Amsa:Sallah da irin wannan bataccen wanka ~atacciya ce saboda haka wajibi ne ya rama sallolin.

2-Tambaya:Na kasance ina wankan janaba ta wannan fuska da farko ina wanke tsagin jikina na dama,na biyu in wanke kaina na ukku in wanke tsagin jikina na hagu,to minene hukuncin salloli na da kuma Azumomi na?

Amsa:Wanka ta wannan fuska bai yi ba saboda haka sallolin da aka yi da wannan wankan basu yi ba,amma azumin da aka yi dashi ya inganta saboda ba ka gangantar da wanzuwa da Janaba ba.

3-Tambaya:Shin ya halatta ga mai Janaba yayi taimama saboda }urewar lokacin salla wato in yace sai yayi wanka to lokacin sallar zai fita ko kuma zai yi wankan ne sallar sai ya rama ta?

Amsa:Idan lokaci ba zai yelwace shi ba har da zai iya yin wankan to sai yayi sallah da Taimama kuma wannan ya wadatar masa wato ba zai rama sallar ba idan yayi wanka.

Tambaya:Minene hukuncin wanda bai yi wankan Janaba ba saboda yin sallar Asuba maimakon haka sai ya yi taimama saboda yana da ya}inin in ya yi wankan zai kamu da rashin lafiya?

Amsa:Idan yana da ya}inin in yayi wanka zai kamu da rashin lafiya to babu laifi idan yayi taimamar kuma sallar sa ta inganta.

Tambaya:Idan mutum ya kasance da Janaba har ya zuwa ketowar alfijir saboda wasu matsaloli to zai iya halatta gareshi ya yi azumin washe-gari?

Amsa:Idan ba Azumin watan Ramadan ba ne ko na ramuwar sa to zai iya yi

 
Home Darusan Fiqh Bayani kan wankan Janaba.
Copyright © 2023. www.tambihin.net. Designed by KH