Tuesday, 09 August 2022
Email
Make My Homepage
RSS
Register
Darussa daga Aklaq din Imam Ali [AS] Print E-mail
Written by administrator   
Friday, 13 October 2017 23:04

A cikin wannan darasi insha Allah za a kawo wasu daga cikin ~angarorin ]abi’oi na Imam Ali[AS] domin su kasance madubi garemu da zamu dubi kawukanmu dasu wato mu gani mun suffa dasu,in mun siffata dasu sai mu gode ma Allah Ta’ala mu kuma }ara tabbata akansu,in kuma bamu siffata dasu to sai  mu yi }o}ari wajen ganin cewa mun siffata dasu,saboda kasantuwar mu a raye yanzu to babbar dama ce garemu wajen siffata da kuma koyi da wa]annan bayin Allah Ta’ala tsarkaka,muna mutuwa to wannan dama da kuma fursa sun ku~uce mana.

          1-HA{URINSA:Imam Ali[AS] ya kasance mai yawan ha}uri da dauriya da kauda kai da kuma afuwa, a wani Hadisi Manzon Allah[S] ya ce, “Da a ce ha}uri mutum ne to da ya kasance Ali.” Idan mutum ya bibiyi tarihin rayuwar Imam Ali to zai ga misalai masu yawa na irin ha}urinsa ga ~angarorin mutane dabam dabam wato masoyansa da kuma ma}iyansa  wanda har ma}iyansa wato wa]anda suka yi gaba da }iyayya dashi kai har ma suka ya}e shi sun tabbatar da haka ga misalan wasu daga cikin wannan ]abi’a nasa na ha}uri da kuma afuwa:A-Lokacin ya}in Jamal bayan da ya samu nasara da kuma galaba akan wa]anda suka jagoranci ya}in to baki ]ayansu haka yayi ha}uri kuma ya yafe masu wato dai kamar yadda Manzon Allah ya yi afuwa ga mushirikai a fatahu Makka.Haka nan a lokacin ya}in Siffin sojojin Mu’awiya suka zagaye kogin Furat da nufin hana Imam Ali da sojojinsa amfani da ruwan kogin,wanda sai da takai Imam Ali yayi masu magana akan su bari a yi amfani da ruwan amma suka ce a’a har ma da yin isgili suka ce masa ko ]igo ]aya ba zamu baku sai dai ku mutu da }ishi,to shine a lokacin Imam Ali ya bada umarnin a fafata dasu domin a }oce kogin furat ]in,ba a ]auki lokaci ba aka samu galaba akansu aka kore su daga wannan kogi na Furat,to shine a lokacin wasu daga cikin sojojin Imam Ali suka ce masa mu hana su amfani da ruwan kamar yadda suka hana mu sai Imam Ali ya ce masu, “Wallahi ni ba zan yi masu abinda suka yi mana ba na hana mu ruwa saboda haka ku barsu in suna da bu}ata su zo su ]iba.” Haka nan dai a wannan ya}i na Siffin lokacin da ake fafatawa shi wanda ya jagoranci ya}in a lokacin da ya ga Imam Ali ya tunkaro shi da takobi kawai sai ya tube kayansa wato yayi tsirara ganin haka sai Imam Ali ya kauda kansa ya }yale shi wato bai kashe shi ba.B-Akwai lokacin da Imam Ali ya kira wani daga cikin bayinsa sai bai amsa masa ba,shine Imam Ali yake tambayar sa mi yasa kana jin ina kiranka amma baka amsa man ba?sai bawan ya ce na san ba zaka yin komi bane shi yasa ban amsa ba,shine Imam Ali ya ce, “Ina godiya ga Allah Ta’ala da ya sanya ni halittunsa sun aminta dani-wato su yi min laifi amma ba zan yi masu komi ba-daga }arshe Imam Ali ya ce masa ka tafi na ‘yanta ka saboda Allah.” Mu dubi irin wannan gayar ha}uri da kuma kyautatawa na Imam Ali[AS].

          2-TAWADI’UNSA:Imam Ali ya kasance mai yawan tawali’u wato }as}antar da kai ga wasu misalai akan haka:Ya kasance mafi yawan lokaci shi yake yi ma kansa hidima wato aikace-aikace na yau da kullum na cikin gida haka nan ya kan taimaka ma iyalinsa a wajen ayyukan cikin gida,haka nan yazo akan cewa ko ba}i yayi to kai tsaye shi yake yi masu hidima,haka nan yazo a tarihinsa cewa ko kasuwa ya je idan ya yo sayayya to ya kanso ya ]auki abinda ya saya da kansa akan ya bayar a ]aukar masa.Haka nan ya kasance saboda gayar tawadi’unsa idan yana tafiya bai cika son ana binsa a baya ba.Imam Ali ya kasance idan ya ji wani daga cikin mabiyansa bai da lafiya ya kan je da kansa domin ya gaishe shi kuma ya kasance yana }arfafa mabiyansa akan yin haka,akwai in da yake cewa, “Duk wanda ]an uwansa Musulmi bai da lafiya sai ya tafi domin ya gaida shi to kamar yana tafiya ne cikin Aljanna,haka nan idan ya zauna wajen marar lafiyar ta rahamar Allah zata lullu~e shi.”

          3-KYAUTAR SA:Imam Ali ya kasance mai yawan kyauta musamman ma ga matalauta da kuma mabu}ata,yazo a tarihin rayuwarsa cewa duk wanda ya bu}aci wani abu daga wajensa kuma yana da abun to sai ya bashi,an ce ba a ta~a tambayarsa wani abu ya ce a’a ba, ga misalan wasu daga cikin kyaututtukansa:A-Akwai lokacin da ya raba dukiyar Baitul-Mal na Basra tsakanin maya}ansa,kowanen su ya bashi Dinare 500 shima ya ]auki Dinare 500 sai ga wani yazo ya ce shi bai halarci ya}in da aka yi ba da gangar jikinsa amma a zuciyarsa yana tare da ya}in da aka yi to sai Imam Ali ya bashi Dinare 500 na kasonsa shi ya tashi bai ]auki komi ba kasantuwar dama ragowar ku]in kenan.B-Imam Sadi}[AS] ya ce,Imam Ali ya kasance da daddare ya kan bi gidajen matalauta yana raba masu abinci da ruwan sha kuma sanyi da damuna bai hana shi wannan hidima da yake yi.C-Akwai wani da ya ta~a zuwa wajensa domin neman biyan wasu bu}atu nashi amma kuma yana ]an jin kunya shine Imam Ali ya ce masa ya rubuta bu}atun ya bashi,da yaga bu}atun nasa nan take ya bashi su har ma da }arin wasu kan abun da ya bu}ata da kuma wa]anda bai bu}ata ba.D-Akwai lokacin da Imam Ali yana da Dirhamomi guda hu]u sai ya bada kyautar guda ]aya da daddare ]aya kuma da rana ]aya a bayyane ]aya kuma a ~oye shine Allah Ta’ala ya saukar da wannan aya domin yabonsa kan wannan aiki,aya ta 274 cikin Suratul Ba}ara, “Wa]anda suke ciyar da dukiyoyinsu dare da rana a ~oye da kuma bayyane to suna da ladarsu a wajen Allah.......” E-Akwai wani fa}iri a lokacin Manzon Allah da yake zaune a wani gida }untatacce to a jikin gidan nasa akwai wata gona ta wani Musulmi mawadaci to ya kasance itacen dabinai dake cikin wannan gona wani lokaci dabinan su kan fa]o cikin wannan gida na wannan fa}iri sai ‘ya’yansa suje suna tsintar wa]annan dabinai da nufin su ci sai wannan bawan Allah fa}iri ya }wace daga hannunsu har ta kai daga }arshe ya kai }arar halin da yake ciki ga Manzon Allah,sai Manzon Allah ya bu}aci mai gonar da ya sayar masa da gonar,maimakonta Allah zai bashi gida a cikin Aljanna,amma abun mamaki sai shi mai gonar ya ce ai wannan gaibi ne shi bai yarda ba,a dai saya abashi ku]i hannu,lokacin da wannan abu ya faru Imam Ali bai wajen da ya dawo shine Manzon Allah yake bashi labarin abunda ya gudana tsakaninsa da wancan mawadacin,jin haka nan take Imam Ali yaje ya same shi suka yi cinikin gonar ya ce masa sai dai ya bashi gonarsa dake waje kaza a maimakonta nan take Imam Ali ya ce ya yarda,to shine Imam Ali da ya amshi gonar mawadacin da yake yanzu ta zama tasa to sai ya ba wancan fa}irin ya ha]a da gidansa.A cikin wannan }issa akwai darussa masu yawa da zamu koya a ciki musamman ma ga ‘yan uwanmu Musulmi da suka tafi akan ‘Wa asahabihi ajama’in’ mu duba mu gani wannan sahabi ne na Manzon Allah ya bu}aci wani abu daga wajensa maimakon haka ya lamunce masa gida acikin Aljanna amma mutumin ya ce a’a shidai ku]i hannu.Da dai sauran misalai masu yawa na irin kyaututtuka na Imam Ali[AS].

            4-ISAR:Ma’anarsa shine fifita wani akan ka wato kana da abu kana bukatarsa ko kuma kana tsananin sonsa amma ka ]auka ka ba wani kai kuma ka ha}ura,a mahanga ta Malaman Akla} matsayin Isar yafi kyauta tun da wani lokaci kana iya kyauta da abu }ila saboda baka sonsa ko yayi maka yawa ko kuma saboda ka canza wani ne,amma shi isar }ila baka da abun ko kuma iyakar shi kenan wani yazo yana bu}ata ka ]auka ka bashi,shima wannan idan mutum ya bibiyi tarihin Imam Ali zai ga cewa akwai misalai masu yawa akai kamar }issar da tazo a cikin Suratul Insan wato Hal-ata alal-insan.....na azumi da suka yi shi da Sayyida Zahra da Imam Hassan da Husain[AS] kwana ukku biye da juna ]an abunda suka tanada na bu]e baki kuma shike nan suke dashi,mabu}aci na miskini da maraya da kamamme a cikin wa]annan kwanaki haka suka ]auka suka basu.Haka nan akwai lokacin da Imam Ali ya sai wasu tufafi guda biyu,]aya akan dirhami ukku ]aya kuma akan dirhami guda biyu,to lokacin da ya sayi wannan tufafi yana tare da wani ne da yake yi masa wasu hidimomi,to sai ya ]auki tufafin na dirhami ukku yaba shi,shi kuma ya ]auki na dirhami biyu,sai ya ce ya Amiril Mu’uminin ai kai ka cancanci ka ]auki na dirhami ukku saboda kana hawa munbari ka yi khu]uba da dai sauransa,sai Imam Ali ya ce masa ai kai kuma matashi ne saboda haka kai kafi cancanta dashi kuma ina jin kunyar Allah Ta’ala in fifita kaina akanka.

          5-ADALCINSA:Idan mutum ya bibiyi tarihin Imam Ali zai ga misalai masu yawa na irin adalcinsa ga dukkan al’amuransa da kuma mu’amalarsa da mutane dabam dabam kai hatta ma ga wa]anda ba Musulmi ba,alal misali akwai lokacin da ya ga sulkensa gun wani kirista sai ya ce masa aiko wannan sulke na ne sai kiristan ya ce nashi ne,ganin haka sai Imam Ali ya ce masa to mu tafi wajen Al}ali yayi hukunci tsakannin mu,sai suka tafi wajen wani Al}ali da ake masa Shuraih,sai Imam Ali ya ce ma Al}alin wannan sulke na ne na gani a hannunsa alhali ni ban sai da shi ba kuma ban yi kyautarsa ba,sai Al}ali ya tambayi shi kiristan mi zaka ce kan abinda Amiril-Muminin ya ce? Sai ya ce to ni dai wannan sulke na ne amma Amiril muuminin ni a wajena ba ma}aryaci bane! Sai Al}alin ya dubi Imam Ali ya ce masa kana da shaida wanda zai tabbatar da cewa wannan sulken ka ne? Sai Imam Ali yayi murmushi ya ce bani da shaida!Sai Al}ali ya yanke hukunci akan cewa sulke na kiristan ne,saboda haka sai ya amsa ya tafi Imam Ali na kallonsa,mutumin bai yi nisa ba sai ya dawo ya ce lalle wannan sulke na Amiril muuminin ne,}arya nike ba nawa bane,a ta}aice dai wannan ]abi’a ta Adalci da ya gani wajen Imam Ali tayi sanadiyyar musuluntarsa har takai daga  }arshe ya kasance cikin makusantan Imam Ali.kuma wannan abu ya faru ne a lokacin yana kalifanci ne

          6-TAUSAYINSA:Imam Ali ya kasance mai yawan tausayi ga mutane shima wannan ]abi’ar idan mutum ya bibiyi tarihin rayuwarsa zai ga misalai masu yawa akan haka,kai hatta ma wakilansa na garuruwa dabam dabam daga cikin abinda ya kece masu shine cewa su zama masu tausaya ma mutane,misali wakilinsa na garin Misra a lokacin mai suna Ash-tar daga cikin abinda ya rubuta masa shine, “Kada ka kasance mai gallazama mutane saboda duk mutumin da ka gani ko dai ya kasance ]an uwanka a addini ko kuma kamar ka a halitta-wato shima mutum ne ]an uwanka- saboda haka ka kauda kai da kuma yafe masu kurakuransu kamar yadda kai ma kake so Allah ya yafe maka kuma ya gafarta maka,kuma kada kayi nadama domin kayi ma wani afuwa.

          7-IBADARSA:Imam Ali ya kasance mai yawan ibada wato ya kasance mai yawan sallah,yama zo a tarihinsa cewa kowace rana ya kan yi raka’a dubu ]aya ta nafila,to mutum ya kwatanta haka da raka’a 50 da ake so kowane muumini ya tsayu da su kowace rana,haka nan Imam Ali ya kasance mai yawan Azumi da karatun Al}ur’ani da kuma Azkar,haka nan kuma ya kasance mai yawan Addu’oi ne,in mutum ya bibiyi asalin mafi yawan addu’oi da suka shahara tsakankanin mabiya Ahlul bayt zai ga cewa asalin su daga Imam Ali ne misali Du’au Khumail,shi Khumai yana ]aya daga cikin manyan sahabban Imam Ali kuma shi ya bashi wannan Addu’ar,haka nan wata Addu’a da ake cema Du’au Shaabaniyya ita ma asalinta daga Imam Ali ne,ga mai bu}atar ganin addu’oi dabam dabam da aka samu daga Imam Ali yana iya neman littafi mai suna ‘Sahifatul-Alawiyya’baki ]ayan littafin Addu’oinsa ne.Haka nan yazo a tarihin Imam Ali cewa dararensa baki ]aya yana raya sune da ibadodi.

          8-ZUHUDUNSA:Imam Ali ya kasance mai gayar gudun Duniya duk wanda ya bibiyi tarihin rayuwarsa sanka-sanka zai tabbatar da haka,wato ya kasance mai zuhudu ne a tufafinsa da abincinsa kai hatta nama bai cika yawan cinsa ba,akwai ma in da yake cewa, “Kada ku sanya cikkunanku su zama ma}abarta ga dabbobi” Haka nan ya kasance mai zuhudu ne a wajen kayayyakin gida na amfanin yau da kullum,a lokacin da yake zaune a kufa ga wa]anda suka samu shiga cikin gidansa har kuka suke idan suka ga gidan babu wani abun aza a gani alhali gashi shine Khalifa,kuma ko yanzu mutum mutum ya tafi birnin Najaf in ya je gidan da Imam Ali ya zauna zai tabbatar da haka cewa rayuwa ce ta zuhudu,akwai ma in da Imam Ali yake cewa Duniya sai dai ki ru]i wani ba niba.

          9-SHAJA’ARSA:Shima wannan fage na jaruntaka duk wanda ya karanta tarihin Imam Ali zai tabbatar da haka,idan ma mutum ya bibiyi tarihin ya}o}in da Manzon Allah yayi zai ga cewa Imam Ali ya bada gudunmawa fiye da kowane sahabi misali mutum ya ]auki ya}i na farko da Manzon Allah ya fara yi wato ya}in Badar to in ka kasa ma}iya da aka kashe rabinsu Imam Ali ne ya kashe su,haka nan mu dubi ya}in khaibar,in kuma muka dubi wasu ya}o}i da mafi yawan sahabbai suka bada baya kamar ya}in Uhud da kuma Hunain zamu ga Imam Ali ya kasance tare da Manzon Allah domin bashi kariya daga ma}iya.Da dai sauran ]abi’oi dabam dabam na Imam Ali wa]anda ba za a iya kawo su ba saboda gudun tsawaitawa amma ga mai bu}atar ganinsu yana duba littafai kamar:Aimmatuna juz’i na ]aya,Muntahal-Amal na Shaik Abbas Al}ummiy,Tarik wa siratil }adat,A}la}un-Nabiyy-wa-ahli-baitihi da dai sauran su.Insha Allah a darasi na gaba za a kawo Darussa daga Akla} ]in Imam Hassan.

 
Home Darusan Akhlaq Darussa daga Aklaq din Imam Ali [AS]
Copyright © 2022. www.tambihin.net. Designed by KH