Thursday, 27 January 2022
Email
Make My Homepage
RSS
Register
Shekaru 40 cur na Harka Islamiyya Jarabawowi da kuma Nasarori. Print E-mail
Written by administrator   
Sunday, 18 June 2017 12:19

Da farko muna godiya ga Allah Ta’ala da ya nuna mana wannan lokaci na cikar wannan Harka shekaru 40 cur,idan mutum ya bibiyi tarihin wannan Harka zai ga cewa Sayyid Zakzaky[H] ya faro Da’awa siriyya ne a watan Afril 1977 wannan abu ya faru ne a garin Katsina a wata makaranta da ake cema Katsina Teachers College wato a wani IVC da aka gudanar a lokacin-Islamic Vacation Course-kamar yadda ]an uwan da ya kasance a wannan IVC ya ta~a bamu bayani wato babban yayanmu a wannan Harka ta Musulunci Sheikh Muhammad Mahmud Turi ina ce masa haka ne da yake duk wani ]an uwa da yake cikin wannan Harka a yanzu to a bayansa ya zo,yake cewa a wannan IVC Sayyid Zakzaky yayi gayyata ta musamman,Sayyid ya ce za a yi wani taro na musamman da tsakar dare lokacin da idanuwa suke barci amma yana son duk wanda zai halarta ya kasance yayi nufin ba da rayuwarsa baki ]aya a tafarkin Allah Ta’ala,lokacin da aka zo wannan taro da tsakar dare sai Sayyid Zakzaky ya ga [alibai da yawa sun zo shine har yake cewa an ya wa]annan duk sun yi nufin ba da rayuwarsu a tafarkin Allah,a ta}aice dai haka aka yi wannan taro kuma wanda ya wanzu a cikin wannan Harka na mahalarta taron shine Sheikh Muhammad Turi kuma ya ce wannan shine karon farko da ya soma ganin Sayyid Zakzaky.Ya kuma faro Da’awa Jahariyya shima a watan Afril 1980 wannan ya faru ne a garin Funtuwa.Lokacin da wannan Harka ta cika shekaru 25 akwai taro da aka yi a garin Zaria,wanda a lokacin Sayyid ya yi bayanai na tarihin wannan Harka wato yadda ta faro da kuma jarabawowi da aka fuskanta a cikin shekarun da kuma nasarori da aka samu.To a yanzu idan mutum ya lissafa daga lokacin da aka faro Da’awa Siriyya wato a watan Afril 1977 zuwa yanzu wato watan Afril na 2017 zai ga cewa shekaru 40 kenan cur.

          Idan muka dubi jarabawowin da suka auku tun daga faro wannan Da’awa zuwa yanzu zamu ga cewa suna da yawa,kuma sun auku ne ta fuskoki dabam-dabam a wajaje dabam dabam a kuma lokuta dabam dabam,saboda haka kasantuwar jarabawowin na da yawa zamu ]auki jarabawowin da Sayyid Zakzaky ya fuskanta a tsawon wa]annan shekaru 40 ta fuskacin gwamnatococi dabam dabam da aka yi tun lokacin da ya soma Da’awar zuwa yanzu.Ga wanda ya san tarihin wannan Harka zai ga cewa Sayyid ya fara Da’awa ne a zamanin mulkin soja na General Obasanjo,saboda haka kamun farko da aka yi ma Sayyid Zakzaky ya auku ne a zamanin Gwamnatin mulkin soja,}ar}ashin shugabancin Genaral Obasanjo,wannan abu ya faru ne a 1979 wato lokacin Sayyid yana ]alibi a Jami’ar Ahmadu Bello,yana ma shekarar }arshe ne na karatunsa,kai a lokacin ma yana rubuta jarabawarsa ta kammalawa ne aka kama shi,saboda haka a lokacin akwai Faifofi da bai samu rubuta su ba sai daga baya.A lokacin da aka kama shi an tsare shine a Police-Station na ‘Yan Sanda a Zaria,wani abin mamaki ma shine da suka tsare Sayyid sai da suka kwana ukku basu bashi abinci ba,bayan kwana ukku da suke fito da Sayyid cikin Cell domin su yi masa tambayoyi,su kansu Yan sandan abun ya basu mamaki domin duk tambayoyin da suka yi masa ya basu amsa,kuma suka bu}aci ya rubuta statement to sai da ya rubuta masu har shafi goma,shine har suke cewa duba rubutun sa da kyau kamar wanda bai sha yunwa ba wanda yake nuna ashe da gangan suka hana shi abincin,a kwai lokacin da Sayyid yake ba da labarin wannan al’amari yake cewa wani ikon Alah cikin wa]annan kwanaki da basu bashi abinci ba,bai ji wani abu da ake ce ma yunwa ba,ballantana ya bu}aci su bashi abinci,Allahu Akbar ‘Yan uwa mu dubi yadda wannan gwagwarmaya ta faro.Bayan haka kuma an tsare Sayyid Zakzaky a garin Sokoto a 1981,aka kai shi Kotu aka yenke masa hukunci na zuwa Kur-kukun Inugu na tsawon shekaru hu]u,saboda haka daga 1981 zuwa 1994 Sayyid Zakzaky yana kurkukun Inugu ne,kuma wannan shine karon farko na zartar ma Sayyid Zakzaky ]auri na zaman Kurkuku a tarihin wannan Harka.Wannan wa}i’a ta faru ne a zamanin Gwamnatin farar hula }ar}ashin jagorancin Alhaji Shehu Shagari.Bayan haka kuma a shekarar da Sayyid Zakzaky ya fito daga Kurkukun Inugu wato a 1984 to a }arshen shekarar aka sake kama shi,wani tarihi anan shine a cikin wannan shekara ta 1984 Sayyid Zakzaky ya yi Aure,saboda haka bayan aurensa da kimanin watanni biyar ne aka kama shi,a lokacin da aka kama shi sai aka kai shi Lagos aka tsare shi a Kiri-kiri.Wannan ya auku ne a zamanin Gwamnatin mulkin soja,}ar}ashin shugabancin General Muhammadu Buhari.Sayyid Zakzaky ya kasance a Kiri-kiri har ya zuwa 1985,shi yasa ko lokacin da aka haifa masa ]a na farko wato Sayyid Muhammad yana Kiri-kiri ne,wani tambihi anan kuma abun lura shine wannan ]a nasa na farko da baya nan aka haife shi to yanzu ma a lokacin aurensa baya nan a }ar}asin shugabancin wanda ya tsare shi a wancan lokacin.Ta yiyu wasu su tambaya kan Kiri-kiri,to kamar yadda Sayyid Zakzaky ya ta~a bayani akansa cewa waje ne da idan ana so a musguna ma mutum ko a azabtar dashi to akan kai shi wajen,har yake cewa ba a yarda mutum ya shiga wajen da riga ko wando sai dai a shigar da mutum daga shi sai Fant,to lokacin da suka kai Sayyid Zakzaky sai suka ce ya tu~e rigarsa da wando ya ce ba zai yi yu ba,haka dai akai ta ja-in-ja daga }arshe suka bar Sayyid Zakzaky ya shiga da rigarsa da wando,har ma Sayyid yake cewa yana ganin shine mutum na farko da ya shiga wajen da kayan jikinsa.,kuma ya ce yawancin ]akunansu a }ar}ashin }asa suke,saboda haka a lokacin ya ce gane lokacin Sallah yana yi masa wahala sosai musamman ma ya ce Sallar Asuba da dai sauran abubuwa na cutarwa da Sayyid Zakzaky ya fuskanta a wannan zama nasa na Kiri-kiri.

          Bayan haka kuma a shekarar 1987 aka kama Sayyid Zakzaky aka tsare daga }arshe aka kai shi Kurkuku na Porth cout ya fito daga Kurkukun a 1989,wannan wa}i’a ta faru ne a zamanin Gwamnatin mulkin soja }ar}ashin shugabancin General Ibrahim Babangida.Sai kuma a 1992 aka sake kama Sayyid Zakzaky a filin jirgin sama na Kano lokacin zai yi tafiya zuwa Ingland kan wani taro na Addinin Musulunci da aka gayyace shi,bayan an kama shi aka kai shi Lagos,kai tsaye aka wuce da shi Kiri-kiri,amma tsarewar Alhamdu-lillahi bata tsawaita ba kimanin mako guda ne,wannan shima ya auku ne a lokacin mulkin Babangida,wato dai Babangida so biyu yana kama Sayyid da kuma tsare shi.

          Bayan haka kuma sai a shekarar 1996 aka sake kama Sayyid Zakzaky aka tsare a Kurkukun Porth cout,wannan ya kasance a lokacin Gwamnatin mulkin soja }ar}ashin jagorancin General Sani Abaca,ya fito daga kurkukun ne a shekarar 1998 wato bayan mutuwar Abaca.A ta}aice dai daga shekarar 1981 zuwa shekara 1998 Sayyid Zakzaky ya kwashe sama da shekaru goma a gidajen kurkuku dabam dabam na kudanci da kuma arewacin }asar nan a }alla kurkuku sun kai guda tara da ya zauna a cikinsu.To tun daga 1998 har ya zuwa 2015 ba a sake kama Sayyid Zakzaky aka tsare ba.Amma fa a lura cewa haka ba yana nufin Gwanatocin da suka biyo bayan na Abaca sun ha}ura daga makirce-makirce ko }ullu-}ulle ga Sayyid da kuma ita Harkar bane.A’a sun lura ne cewa duk kame-kame da kuma tsare-tsare da suka yima Sayyid Zakzaky yana ha~aka da kuma tambatsa Da’awar da yake yi ne kawai saboda haka yanzu abinda suke ganin mafita garesu shine su kashe shi,shi yasa in muka duba zamu ga cewa gwamnatoci kamar irin ta Alhaji Musa ‘Yar aduwa ta yi yun}uri na kashe shi ta hanyar Bombin ]in gidansa kamar dai yadda Sayyid Zakzaky yayi bayani akai a lokacin da aka yi wannan yun}uri.Haka nan mu dubi lokacin Gwamnatin Jonasan shima an ta yun}uri kala-kala ta kuma fuskoki dabama dabam a kuma lokuta dabam dabam amma basu samu nasarar haka,in ma mutum bai san wa]ancan ba to ya dubi abinda wannan Gwamnati da muke ciki tayi masa na nufin kashe shi amma Allah Ta’ala bisa ikonsa ya kare shi ya kuma nuna ma wa]anda suka ba da umarnin haka cewa shine mai iko akan kome.Lokaci yayi da mutanan }asar nan musamman masu tafi da iko zasu fahimci cewa al’amarin wannan bawan Allah al’amari ne na Allah Ta’ala,Shehu Usman ]an Fodiyo yayi albishir da bayyanarsa,haka nan ‘yarsa mai suna Asma’u.In mutum naso ya ga wannan bushara to ya nemi littafin Shehu Usman [an Fodiyo mai suna “BUSHRAL-AHBAB” Shi wannan littafi ya }unshi bayanai na Shehu Usman kan wa]ansu bayin Allah Waliyyai da suka kasance a zamaninsa da kuma wa]anda zasu zo bayansa,amma a cikin littafin Shehu [an Fodiyo ya }arfafa bayani ne kan Imam Mahdi[AF] da kuma Sayyid Zakzaky,wani abun lura idan mutum ya karanta littafin zai ga yadda Shehu Usman [an Fodiyo ya kawo wasu bayanan dangane da Sayyid,wanda duk wanda ya san Sayyid ko ya ke tare dashi zai tabbatar dasu,ga misalan wasu ababe da ya kawo:1-Fa]in sunan Sayyid wato Ibrahim.2-Fa]in shekarar haihuwarsa,shekarar da ya fa]a itace 1370 ta Hijira.3-Fa]in cewa Sayyid zai zo daga yamma shi yasa a cikin littafin yayi masa la}abi da ‘Ibrahimul-Magribi’.4-Fa]in cewa Sayyid zai yawaito ziyarar Manzon Allah a Madina,duk wanda ya da]e a cikin wannan Harka zai ba da shaida cewa lalle a shekarun baya,baya ga aikin Hajji da Sayyid yake zuwa kowace shekara to duk watan Ramadan a birnin Madina yake yinsa wato a Masallacin Manzon Allah kuma yafi zama a Rauda kamar yadda ya ta~a fa]i.5-Fa]in kamannun Sayyid,misali yayi bayanin idanuwan Sayyid da goshinsa da dai sauransu.In ma mutum bai yarda da wa]annan ababe to karamomin da suka bayyana gareshi kuma suke bayyana sun isa su tabbatar da cewa ko shi wanene,alal misali wannan wa}i’ar da aka afkar ta Zaria Sayyid ya jima yana bayani cewa akwai plan na yin kisan kiyashi,ya kuma ce idan sun yi haka to zasu tambatsa Da’awar ta in da basu tsammani,kuma sai sun yi ba}in ciki akan haka wato ba}in cikin basu samu nasara ba,ya ce kuma zasu yi hasarar duniya da kuma lahira,to mu duba fa mu gani.A ta}aice duk wa]anda suke tare dashi zasu tabbatar maka da abubuwa masu yawa na karamomi da suka shaida daga wajensa,cikin ‘yan uwan da suka ziyarce shi kwannan yake ce min Sayyid yana tsare ba a waje ba amma yafi mu sanin abubuwa da suke faruwa a ciki da wajen }asar nan,shine nike ce masa, haka al’amarin Waliyyan Allah yake suna gani ne da hasken Allah Ta’ala,shi yasa ni koda wane lokaci in na ga wani ko wasu suna fa]a da Sayyid ko wannan Harka ta Musulunci to ina tausaya masu,saboda fa]a ne da al’amarin Allah wato dashen Allah Ta’ala,a tarihin ]an Adam kuma babu wani wanda yayi fa]a da Allah ya samu nasara in ma mutum bai san haka ba to yayi tunanin duk wa]anda suka yi fa]a dashi yadda }arshen su yake kasancewa.Kuma ma mutum ya tunani duk Gwamnatocin dabam dabam da aka ambata tun lokacin da ya faro Da’awar,matakan da suka ]auka kan Sayyid Zakzaky da mabiyansa da kuma ita kanta Da’awar domin ganin sun kauda su,to tambaya anan sun ci nasara? Kai bama kawai basu ci nasara bane sun ma taimaka wajen bun}asa Da’awar ne da kuma ]aukaka shi Sayyid Zakzaky,bari in ba da misali duk wanda ya kasance cikin wannan Da’awa ta Sayyid Zakzaky sama da shekaru 30 da suka wuce zai tabbatar maka da cewa,Da’awar nan lokacin da ta faro tafi }arfi ne a makarantu musamman ma manyan makarantu kamar Jami’oi da sauransu amma sakamakon kamun Babangida ga Sayyid Zakzaky sai Da’awar ta tambatso zuwa cikin gari wato ta soma shiga cikin birane,haka nan sakamakon kamun Abaca da matakan da ya ]auka kan D’awar sai Da’awar ta nausa ta yi cikin }auyuka kai har ma da rugage na Fulani a cikin dokar daji,in ma mutum bai fahimci haka ba to ya dubi wannan wa}i’a da muke ciki,sakamakon abubuwan da aka yi ma Sayyid da mabiyansa yanzu Da’awar ta tambatsa a sassan duniya dabam dabam,ta wani labari da na ji cewa shugaban }asar Indiya,ya ga lokaci bayan lokaci wasu daga cikin Musulmin }asarsa suna fitowa Muzahara akan a saki Zakzaky,shine yake tambaya wai waye wannan Zakzaky? Yace ina son in san wani abu dangane dashi.Haka nan wa]anda suka samu ziyara zuwa Karbala ta wannan shekara da muke ciki wato ta Arba’in ]in Imam Husain,in an ganka ba}in mutum ana tambayar ka daga wace }asa? Kana cewa daga Nigeria sai ka ji an ce Zakzaky wato sakamakon wa}i’ar sunan Sayyid Zakzaky ya tambatsa a duniya,akwai ma wani da muka ha]u dashi a Birnin Najaf a haramin Imam Ali[AS] to sai yana son ya tambaye ni cewa Zakzaky har yanzu yana tsare ne hannun hukuma ko an sake shi? To kasantuwar mutumin ba ya jin turanci ko larabci sai dai harshen }asar su na Turkiyya to sai ya kama hannu na ya matse wato yana nufin yana tsare sai na ka ]a mai kai na cewa iye,to kawai sai na ga hawaye suna zubowa daga idanuwansa,saboda haka irin wa]annan matakai da hukumomi suke ]auka na cutarwa da kuma gallazawa to suna taimaka ma Da’awar ne amma su basu sani ba,wato suna tallata Da’awar sakamakon abinda suke yi amma su basu sani ba,shi yasa cigaba da tsare Sayyid Zakzaky yana da]a fa]akar da mutane Musulmi da wa]anda ba Musulmi na cikin }asar nan dama wajen }asar nan cewa lalle abubuwan da aka yi kuma ake kanyi to akwai Lauje cikin na ]i,kuma tabbas Tarihi zai ba da shaida akai.

          Sai kuma abinda ya shafi nasarori da wannan Harka ta Musulunci ta samu a tsawon shekaru 40 da ta kwashe,wa]annan nasarori suna da yawa wato sun kai haddin La tuaddu wala tuhusa,amma ga wasu daga ciki:1-Tsayuwa da kuma wanzuwar Da’awa,wanda ko da ba a fagen addini ba a ce a fagen duniya ga wani abu ka tsaya }yam akan sa tsawon shekaru 40 ai ko za a yabe ka,to ballatana tsayuwa a fagen addini wanda yake tattare da jarabawowi masu yawa amma duk da haka mutum ya tsaya }yam tabbas wannan babbar nasara ce.2-Adadin wa]anda suke Da’awar yanzu ana maganar miliyoyi ne,mu duba fa mu gani Sayyid Zakzaky shi ka]ai ya soma wannan kira,aka fara samun ]ai-]aiku suka amsa masa,suka soma kaiwa ]aruruwa,suka soma kaiwa dubbanni yau gashi sun kai miliyoyi,a ta}aice dai wa]anda aka faro wannan Harka dasu,to yanzu suna matsayin kakanni ne,wato sun haifi ‘ya’ya a ciki,’ya’yan da suka haifa suma sun haifa duk a cikin Harkar,wanda in mutum nada tunani zai fahimci cewa lalle wannan abu ya kafu Daram kau dashi ba zai ta~a yiyuwa ba,shi yasa ko wannan kashe-kashe da aka yi to ko ]aya bisa ]ari na ‘Yan uwa ba a kashe ba wato in ka kwatanta adadin da suke cikin Harkar.3-Aikata addini a aikace ba wai a karance kawai ba,daga cikin nasarorin da wannan Harka ta samu akwai wannan wato ]abba}a addini a aikace wanda hakan kuma yayi tasiri sosai a cikin wannan }asa da muke a ciki.4-Jawo mata a fagen addini,gabanin fara Da’awar Sayyid Zakzaky a wannan }asa tamu ba a san mata a fagen addini ba,amma sakamakon Da’awar yau Harkoki na addini duk da mata ake yi,wato dai kamar yadda yake lokacin Manzon Allah[S] cewa gwagwarmayar addini tare da mata aka yi.5-Ha]a kan al’ummar Musulmi,daga cikin nasarorin da wannan Harka ta samu akwai sa’ayi wajen ha]a kan al’ummar Musulmi da kuma kusanto da wa]anda ba Musulmi ba jika wato dai kyautata ala}a dasu wanda kuma ana ganin tasirin hakan.A ta}aice dai akwai nasarori masu yawa da aka samu a tsawon wa]annan shekaru 40,ga mai bu}atar }arin bayani kan Tarihin Wannan Harka da Sayyid Zakzaky yana iya duba littafin dana rubuta a shekarun baya mai suna ‘TARIHIN SAYYID IBRAHEEM YAQOUB AL-ZAK-ZAKY DA HARKAR MUSULUNCI’.

          Daga }arshe nasiha ga masu fa]a da wannan kira na Sayyid Zakzaky[H] da ya kwashe shekaru 40 akai,mutum ya tambayi kansa in shi mai mulki ne ko jami’in tsaro shekaru 40 da suka wuce yana wane mataki ne a rayuwar sa? {ila ma wani zai ga cewa ko haihuwarsa ba a yi ba a lokacin ko kuma an haife shi amma yana firamari ne,to saboda Allah ka tausaya ma kanka kayi ma kanka adalci abinda ake tun gabinin a haife ka ko tun kana yaro yau ka zo ka ce zaka kauda shi,alhali in kan mulki mutum yake akai bayan wasu shekaru in wa’adin ya }are zai sauka ne,shi da abubuwan da ya aikata su zama tarihi,to da a ce shikanan da sau}i to {iyama tana gabanka kuma akwai hisabi a can na duk abubuwa da ka aikata a wannan gida na duniya saboda haka lahira itace abin ji,saboda haka duk abinda mutum ya shuka a wannan gida na duniya kyakkyawa ko mummuna to shi zai girba a gobe {iyama.

 
Home Maudu'oi daban-daban Shekaru 40 cur na Harka Islamiyya Jarabawowi da kuma Nasarori.
Copyright © 2022. www.tambihin.net. Designed by KH