Tuesday, 23 July 2024
Email
Make My Homepage
RSS
Register
Hadisai 40 na Imam Hassan Al-Askari (AS) Print E-mail
Written by administrator   
Sunday, 18 June 2017 12:17

Imam Hassan Al-Asakari shine Imam na 11 a jerin }idaya na Imamai 12,wato kenan mahaifi ga Imam Mahdi[AF].Imam Hassan Al-Askari[AS] shine Imamin da aka ruwaito Hadisai kadan daga wajen sa,wannan ko in mutum yayi tunani zai ga cewa bai rasa nasaba da yadda rayuwarsa ta kasance,saboda kusan rayuwarsa baki daya ta kasance ne a barikin soja,wannan ma la}abi nasa na Al-askari daga nan ne ma ya samo asali,idan mutum ya bibiyi tarihin rayuwarsa zai ga cewa mabiyansa a lokacin suna da ala}a da shine ta hanyar rubuce-rubuce,wato idan yana so ya aika masu da sa}o to ya kan aika ne ta hanyar rubutu,ko kuma mabiyansa idan suna da wasu matsaloli ko tambayoyi sukan aiko masa a rubuce shima ya basu amsa a rubuce,wato kasantuwar shi’arsa basu da ala}a dashi kai tsaye.Amma kafin kawo wa]annan Hadisai 40 da aka ruwaito daga wajensa ga wasu daga cikin sassa dabam-dabam na rayuwarsa mai albarka:

Wasu sashe na rayuwar Imam Hassan al-askari[AS]

1-    Haihuwarsa:An haife shi a madina ranar litinin 8 ga watan Rabius Sani shekara ta 232.

2-    Nasabarsa:Mahaifinsa Imam Ali al-hadi[AS] sunan mahaifiyarsa Salil.

3-    Nash’a ]insa: An haife shi a Madina,yana da shekaru 4 da watanni suka koma Ira}i shi da mahaifinsa,saboda haka a Ira}i ne yayi sauran rayuwarsa har yayi shahada.Khalifan Abbasawa a lokacin mai suna Mutawakkil shi yayi sanadiyyar komawar tasu.wanda shi mutawakil malaman tarihi suna kwatanta shi da Yazidu,domin a zamaninsa ya gallaza ma masu ziyarar Imam Husaini[AS] ta fuskoki dabam-dabam,domin a lokacinsa ne yasa dokar duk wanda aka kama ya ziyarci Imam Husain da a yanke masa hannu,in ya sake a yanke daya hannun,in ya sake a yanke masa }afa,haka yai tayi da yaga duk wannan matakin bai yi ba shine ya ]auki matakin shafe kabarin Imam Husain ta hanyar abkar da ambaliya ta ruwa da gangan,ta Allah ba tashi ba shima wannan bai yi ba,a ta}aice dai a zamaninsa ya gallaza ma mabiya Ahlul bait ba ka]an ba.Daga }arshe ma ]ansa ne ya kashe shi saboda zagin da yake ma Imam Ali[AS] da kuma Sayyida Fatima[AS]. Imam Hassan al-askari[AS] ya rayu tare da mahaifinsa shekaru 22.

4-    La}ubbansa:yana da la}ubba masu yawa amma wanda yafi shahara shine al-askari.wannan la}abi ya samo asali ne daga unguwar da ya zauna da yake sansani ne na maya}a,a wannan zamani namu kamar ace barikin soja.

5-    Shekarunsa:Ya rayu a duniya shekaru 28.

6-    Muddan Imamancinsa:Shekaru shidda ne.

7-    ‘Ya’yansa:]a ]aya shine Imam Mahdi[AS]

8-    Wafatinsa: Ya rasu ranar Jumma’a 8 ga watan Rabiul Awwal shekara ta 260 bayan hijira.

9-    Kabarinsa:Yana a Samarra ne wato a }asar Ira} tare da na mahaifinsa Imam Ali al-hadi[AS].

Ga wasu daga cikin Hadisai da aka ruwaito daga wajensa:

                                                                                                                                                                       

\

          1-Imam Hassan Al-askari[AS] ya ce, “A cikin Al-janna akwai wata }ofa ana ce mata }ofar ‘Ma’aruf’ ba mai shigar ta sai ma’abuta ma’aruf.” Wato masu umarni da kyakkyawa aiki.

          2-Imam Hassan Al-askari ya ce, “Duk wanda ya yarda da koma baya a wajen zama to Mala’iku ba zasu gushe ba suna yi masa salati har sai ya tashi daga wajen zaman.”

          3-Imam Hassan Al-askari ya ce, “Ibada ba shine yawan Sallah da Azumi ba,amma ibada itace yawan tafakkuri-tunani-dangane da al’amarin Allah.”

          4-Imam Hassan Al’askari ya ce, “Aibi ne ga Mu’umini ya kasance makwa]aici saboda haka zai dunga }as}antar dashi.” Wato abunda Hausawa suke cewa in da kwa]ayi da wala}anci.

          5-Imam Hassan Al-askari ya ce, “Yana daga cikin tawadi’u yin sallama ga duk wanda ka ha]u dashi.”

          6-Imam Hassan Al-askari ya ce, “Yana daga cikin tawadi’u zaunawa a koma bayan majalisi.” Misali ana program yana da damar da zai je ya zauna a wajen manyan ba}i ko a high-table amma sai ya zauna a akasin haka.

          7-Imam Hassan Al-askari ya ce, “Yana daga cikin abu mai ~ata rai da sosa zuciya ma}wabci wanda in yaga kyakkyawan ka ya ~oye,in kuma ya ga mummuna ya bayyana.”

          8-Imam Hassan Al-askari ya ce, “Fushi shine mabu]in dukkan sharrori.”

          9-Imam Hassan Al-askari ya ce, “Tir da bawan da ya kasance mai fuskoki guda biyu,a gabanka ya yabe ka,a bayan kuma yayi giba da kai,in Allah ya baka wata ni’ima yayi maka Hassada,in kuma jarrabawa ta sameka sai yayi watsi da kai.”

        10-Imam Hassan Al-askari ya ce, “Mafi }arancin mutane a hutun zuciya shine mai Hassada.” Wato kasantuwar mai Hassada koda wane lokaci yana cikin damuwa da ba}in ciki saboda haka zuciyarsa bata da hutu.

          11-Imam Hassan Al-askari ya ce, “Mafi tsentsenin mutane shine wanda ya tsaya gun shubuhat.”wato bai aikata duk wani abu da yake akwai shubuha a ciki.

          12-Imam Hassan Al-askari ya ce, “Wanda ya fi kowa mujahada a cikin mutane shine wanda bai aikata zunubi.”

          13-Imam Hassan Al-askari ya ce, “Babu wani ma’abucin ]aukaka da ya bar gaskiya face ya wula}anta,babu wani da bai da ]aukaka ya kuma yi ri}o da gaskiya face ya ]aukaka.”

          14-Imam Hassan Al-askari ya ce, “[abi’oi guda biyu masu daraja ne wanda babu wasu a samansu:Imani da Allah da kuma amfanar da Yan’uwa.” Wato ‘yan uwa na addini da kuma ‘yan uwa na jini.”

          15-Imam Hassan Al-askari ya ce, “Baya daga cikin ladubba bayyanar da farin ciki gun wanda yake fama da ba}in ciki.”

          16-Imam Hassan Al-askari ya ce, “An sanya munanan ]abi’u cikin ]aki guda aka sanya mabu]insu }arya.”wato yin }arya yana haifar da aikata munanan ]abi’u masu yawa.”

          17-Imam Hassan Al-askari ya ce, “Babu wata jarrabawa face akwai wata hikima ta Allah da ke kewaye da ita.”

          18-Imam Hassan Al-askari ya ce, “Duk wanda yayi ri}o da Allah Ta’ala to nisantar mutane gareshi ba zai dame shi ba.”

          19-Imam Hassan Al-askari ya ce, “Duk wanda yayi ri}o da }arya to zata saukar dashi gidan nadama.”

          20-Imam Hassan Al-askari ya ce, “Gardama da kuma jayayya yana tafida mutunci.”

          21-Imam Hassan Al-askari ya ce, “{arfin hali yaro ga mahaifansa tun yana }arami,yana janyo sa~a masu idan ya zama babba.”

          22-Imam Hassan Al-askari ya ce, “Duk wanda yayi ma ]an uwansa nasiha a ke~ance to ha}i}a ya kyautata masa,wanda kuma yayi masa a bayyane to ha}i}a ya aibanta shi.”

          23-Imam Hassan Al-askari ya ce, “Duk wanda ya kasance mai yawan kyauta da ha}uri da kuma tsentseni to masoyansa zasu yawaita da kuma yabo gareshi,zai kuma ci nasara kan ma}yansa saboda kyakkyawan yabo da yake dashi.”

          24-Imam Hassan Al-askari ya ce, “Duk wanda ya shuka sharri to zai girbi nadama.”

          25-Imam Hassan Al-askari ya ce, “Duk wanda ya shuka al-hairi to zai girbi abun farin ciki,duk abunda mutum ya shuka to shi zai girba.”

          26-Imam Hassan Al-askari ya ce, “Duk wanda aka ba al-hairi to Allah ya bashi haka nan duk wanda aka tsareshi daga sharri to Allah ne ya tsare shi

          27-Imam Hassan Al-askari ya ce, “Aibi ne ga Muumini ya kasance mai kwa]ayi da zai kai ga ya wala}anta.”

          28-Imam Hassan Al-skari ya ce, “Ku }ara gode ma Allah Ta’ala kan ni’imomin da yayi maku sai ni’imomin su }aru.”

          28-Imam Hassan Al-askari ya ce, “Shi’armu ba zasu gushe cikin matsaloli ba har sai ]ana da Manzon Allah yayi albishir dashi ya bayyana,saboda haka Shi’armu su daure.”

          29-Imam Hassan Al-askari ya ce, “Ina umarninku da sallar dare-sallar tahajjud-duk wanda bai damu da sallar tahajjud ba to baya daga cikinmu.”

          30-Imam Hassan Al-askari ya ce, “Ina horonku da taimaka ma ‘Yan uwa da kuma kai-komo wajen biya masu bu}ata a lokacin tsanani da kuma sau}i.”

          31-Imam Hassan Al-askari ya ce, “Ina umartar ku da ha]iye fushi da kuma yin afuwa da sadar da zumunci.”

          32-Imam Hassan Al-askari ya ce, “Ina umartarku da neman ilimi na Addini da kuma tabbata cikin al’amura da kuma kyawawan ]abi’oi.”

          33-Imam Hassan Al-askari ya ce, “Ina umartarku da umarni da kyakkyawa da kuma hani ga mummuna.”

          34-Imam Hassan Al-askari ya ce, “Ina umurtarku da nisantar dukkan munanan [abi’oi da kuma alfasha.”

          35-Imam Hassan Al-askari ya ce, “Ina umartar ku da tsaida Sallah da kuma ba da Zakka saboda ba a kar~ar Sallar wanda bai ba da zakka.”

          36-Imam Hassan Al-askari ya ce, “Inai maku wasiyya da ku ji tsoron Allah da kuma yin tsen-tseni cikin addinin ku.”

          37-Imam Hassan Al-askari ya ce, “Ina horonku da fa]in gaskiya da kuma ri}on Amana.”

          38-Imam Hassan Al-askari ya ce, “Ku kasance masu kyautatawa ba masu munanawa ba,ku janyo mana abunda za a somu,ku tunku]e mana abunda za a }imu.

          39-Imam Hassan Al-askari ya ce, “Ku yi Sallah a masallatansu,ku halarci jana’izarsu,ku je gaida marasa lafiyarsu,ku basu ha}}o}in su saboda idan ]ayanku ya kasance mai gaskiya da ri}on amana,ya kuma kyautata ala}arsa da mutane za a ce wannan ]an Shi’a ne,ni kuma ina farin ciki da haka.” Wannan Hadisi yana koyar da mu yadda zamu kyautata ala}a da Ahlus-Sunna.

          40-Imam Hassan Al-askari[AS] ya ce, “Ku yawaito ambaton Allah da kuma tunanin mutuwa da kuma yawaita karatun Al}ur’ani da kuma yi ma Manzon Allah[S] salati da Alayensa,ku kiyaye ababen da na yi maku umarni da kuma wasiyya dashi.” Idan muka lura zamu ga cewa yawanci Hadisai da aka ruwaito daga Imam Hassan Al-askari a rubuce ne ya aiko dasu,wato kamar yadda aka yi bayani tun farko ya kasance a tsare ne a barikin sojoji shekara da shekaru. Daga cikin dalilin da yasa khalifan Abassawa na lokacin yasa aka tsare shi a wannan waje akwai cewa suna da masaniyar cewa shine Imami ko khalifa na sha-]aya saboda haka shine mahaifin Imami na 12,kuma Imami na 12 shine wanda zai kauda zalunci da kuma azzalumai a bayan }asa,shi yasa suka tsare shi idan an haife shi sai su kashe shi,amma ta Allah ba tasu ba haka aka haifi Imam Mahdi[AF] a wannan waje har ya shekara biyar a wajen basu sani ba,basu kuma ta~a ganinsa ba.

 
Home Darusan Hadisai Hadisai 40 na Imam Hassan Al-Askari (AS)
Copyright © 2024. www.tambihin.net. Designed by KH