Saturday, 02 December 2023
Email
Make My Homepage
RSS
Register
Hadisai 40 na Imam Ali Al-hadi (AS) Print E-mail
Written by administrator   
Sunday, 18 June 2017 12:08

Kasantuwar wannan wata mai al-barka da muke ciki wato watan Rajab,wanda a cikinsa ne aka haifi Imam Ali Al-hadi[AS] a kuma cikinsa ne shahadar sa ta kasance.A kuma jerin Hadisai 40-40 da ake kawowa wato wa]anda aka ruwaito daga Aimma na Ahlul bayt to yanzu mun kawo ga na Imam Ali Al-hadi,amma gabanin kawo wa]annan Hadisai 40 da aka ruwaito daga wajensa to ga wasu sassa na rayuwarsa mai albarka.

1-    Wiladarsa:Imam Ali al-Hadi[AS]shine Imam na goma a jerin }idaya na Imamai 12.An haife shi a wani gari kusa da Madina a na ce masa Sarya,a ran 2 ga watan Rajab a wata ruwaya kuma a ran15 ga watan Zul-hijja.shekara ta 212 bayan Hijira.

2-    Nasabarsa:Sunan mahaifiyarsa Sumanatu,amma an fi saninta da Sayyida,kuma ana yi mata kinaya da Ummul-Fadhal.kuma yazo a tarihinta cewa ta kasance mai yawan ibada,musamman ma ta ~angaren azumi.kuma ta kasance mai ta}awa da kuma zuhudu wato gudun duniya.Sunan mahaifinsa Imam Jawad[AS]

3-    Nash’a ]insa:Imam Ali al-Hadi[AS]ya tashi a madina,ya rayu a cikinta shekaru 22,ya kuma rayu tare da mahaifinsa shekara 8.{arshen rayuwarsa ta kasance a Ira} ne,domin ya zauna a cikinta shekaru 20.

4-    La}ubbansa da kinayarsa:Imam Ali al-Hadi[AS] ya kasance yana da la}ubba masu yawa,amma wa]annan biyun su suka fi fice.wato Al-Hadi da kuma Anna}iy.Haka nan anai masa kinaya da Abul-Hassanus-salis.

5-    Shekarunsa:Ya rayu a duniya shekaru 42.

6-    Muddan Imamancinsa:shekaru 33,a wata ruwaya 34.

7-    ‘ya’yansa:Yana da ‘ya’ya 5,maza 4.mace 1.

8-    Wafatinsa:Ya rasu ranar litinin 3 ga watan Rajab shekara ta 254 bayan hijira,ya rasu ne sakamakon guba da khalifan Abbasawa mai suna Mu’utazz yasa masa.

9-    {abarinsa:}abarinsa yana samarra,a }asar Ira} kusa dashi akwai }abarin ]ansa Imam Hassan al-askari[AS].

Insha Allah ga Hadisai 40 da aka ruwaito daga Imam Ali Al-hadi[AS].

          1-Imam Ali Al-hadi[AS] ya ce, “Allah Ta’ala idan yana nufin alhairi ga bawa to idan an yi mashi nasiha ya kan kar~a.”

          2-Imam Ali Al-hadi ya ce, “Ha}uri shine kafi }arfin son ranka,ka kuma ha]iye fushinka.”

          3-Imam Ali Al-hadi ya ce, “Mafi sharrin musiba shine munanan ]abi’u.”

          4-Imam Ali Al-hadi ya ce, “Mutane a gidan duniya sai da dukiya,a kuma gidan lahira sai da aiki.”

          5-Imam Ali Al-hadi ya ce, “{addara ta kan iya kasance maka da abunda baka ta~a tunaninsa ba.”

          6-Imam Ali Al-hadi ya ce, “Duniya kasuwa ce,wasu mutane sun ci riba ciki,wasu kuma sun yi hasara.”

          7-Imam Ali Al-hadi ya ce, “Jayayya da kuma gardama tana ~ata tsohuwar abokanta.”

          8-Imam Ali Al-hadi ya ce, “Idan musiba ta samu mutum to idan ya daure ta zama guda ]aya,in kuma bai daure ba to zama guda biyu.” Wato ga musibar ga kuma rashin samun lada,saboda idan musiba ta samu mutum idan ya daure yana da lada ta musamman a kai.

          9-Imam Ali Al-hadi ya ce, “Hassada tana gusar da ladar ayyuka.” Wato tana goge ladar ayyukan }warai da mutum ya aikata.

          10-Imam Ali Al-hadi ya ce, “Girman kai da kuma ta}ama yana janyo ma mutum }i daga mutane.” Wato ya kasance ba a son sa saboda wannan mummunar ]abi’a.

          11-Imam Ali Al-hadi ya ce, “Girman kai yana iya hana mutum neman ilimi ya kuma bar mutum cikin jahilci.”

          12-Imam Ali Al-hadi ya ce, “Rowa tana daga cikin mafi munin munanan ]abi’u,kwa]ayi kuma ]abi’a ce marar kyau.”

          13-Imam Ali Al-hadi ya ce, “Mu’amala ko caku]uwa da a-shararan mutane yana nuni ne ga a-shararancin wanda ya caku]u dasu.”

          13-Imam Ali Al-hadi ya ce, “Butulci ga ni’ima alama ce ta girman kai.”

          14-Imam Ali Al-hadi ya ce, “Sa~a ma iyaye yana janyo talauci da kuma }as}anci.”

          15-Imam Ali Al-hadi ya ce, “Himma ita ce amfani da fursa-dama- iyakar iyawa.” Misali wa]annan watanni masu al-barka kuma na ibada da muka shiga wato Watan Rajab,Shaaban da kuma watan Ramadan to yana da gayar muhimmanci mutum yayi iyaka iyawarsa domin yayi amfani da wannan dama da Allah ya bashi,mutum yayi tunani akwai mutane da yawa wa]anda wannan fursa ta ku~uce masu wato sun rasu,to mutum shima bai sani ba ko wannan itace }arshen fursar a rayuwarsa na wa]annan watanni masu albarka saboda haka mutum ya ribaci wa]annan lokuta ta hanyar aikata dukkan ibadodi da aka ruwaito na ayyuka a cikinsu.

          16-Imam Ali Al-hadi ya ce, “K a tuna ha]uwar ka da Mala’ikan mutuwa ta yadda wani masoyi naka ba zai iya amfanar ka ba a lokacin,haka nan wani Likita shima ba zai amfane ka ba.” Wato ba zasu iya hana mala’ikan mutuwa ba ]aukar ranka.

          17-Imam Ali Al-hadi ya ce, “Kashedinka da Hassada saboda kai zaka cutu ba zata cutar da ma}iyinka ba.” Wato zaka zauna cikin damuwa da ba}in ciki koda wane lokaci,alhali shi wanda kake yima hassadar bai ma sani ba.

          18-Imam Ali Al-hadi ya ce, “Jahilci da kuma Rowa suna daga cikin mafi munin munanan ]abi’u.”

          19-Imam Ali Al-hadi ya ce, “Duk wanda yayi ma Allah Ta’ala ]a’a to shima za a yi masa ]a’a.”

          20-Imam Ali Al-hadi ya ce, “Duk wanda yaji tsoron Allah Ta’ala to za a ji tsoronsa.”

          21-Imam Ali Al-hadi ya ce, “Allah Ta’ala ba a siffanta shi fa ce da abunda ya siffanta kansa dashi

          22-Imam Ali Al-hadi ya ce, “Duk wanda yake da ya}ini da Ubangijinsa to musibobin duniya zasu wala}anta gareshi.”

          23-Imam Ali Al-hadi ya ce, “Allah Ta’ala ya sanya duniya gidan jarrabawa,Lahira kuma gidan sakamako,ya sanya jarrabawa a gidan duniya domin samun sakamako da kuma lada a gidan Lahira.”

          24-Imam Ali Al-hadi ya ce, “Fushi akan wanda yake }ar}ashinka aibi ne.”

          25-Imam Ali Al-hadi ya ce, “Duk wanda ya tattara maka sonsa da }aunarsa gareka to kai kuma ka tattara masa ]a’arka gareshi.

          26-Imam Ali Al-hadi ya ce, “Hikima bata tasiri kan mai munanan ]abi’oi.” Wato ko da ya jita ko ya karantata to ba zata ta yi tasiri a cikin zuciyarsa ba.

          27-Imam Ali Al-hadi ya ce, “Duk wanda ya tambayi abu sama da ha}}insa to ya cancanci a hana shi.”

          28-Imam Ali Al-hadi ya ce, “Gardama da kuma jayayya suna kai mutum ga nadama.”

          29-Imam Ali Al-hadi ya ce, “Mai kwa]ayi bai da hutu a rayuwarsa.” Wato koda wane lokaci tunaninsa zai kasance kan abunda yake kwa]ayi a kai,a ta}aice dai zai kasance bai da hutun zuciya.

          30-Imam Ali Al-hadi ya ce, “Idan zamani ya kasance adalci shi yafi galaba kan zalunci,to haramun ne kayi ma wani mummunan zato har sai in ka tabbatar da haka daga gareshi.”

          31-Imam Ali Al-hadi ya ce, “Idan zamani ya kasance zalunci shi yafi galaba kan adalci to bai hau kan mutum ba yayi ma kowane mutum kyakkyawan zato ba matu}ar baka san haka daga gareshi ba.”

          32-Imam Ali Al-hadi ya ce, “Kada ka tsammaci kyakkyawan mu’amala ga wanda ka munana masa.”

          33-Imam Ali Al-hadi ya ce, “Kada ka tsammaci cika al}awari ga wanda ka yaudare shi.”

          34-Imam Ali Al-hadi ya ce, “Ku tsare ni’imar da Allah Ta’ala ya yi maku ta hanyar sarrafa ni’imar ga ]a’ar Allah.”

          35-Imam Ali Al-hadi ya ce, “Ku nemi }arin ni’imar da Allah Ta’ala ya yi maku ta hanyar gode masa kan ni’imar.”

          36-Imam Ali Al-hadi ya ce, “Yana daga cikin ru]i ga mutum tsakaninsa da Allah Ta’ala,ya kasance yana sa~a masa a lokaci guda kuma yana son Allah ya gafarta masa.”

          37-Imam Ali Al-hadi ya ce, “Allah Ta’ala yana da wasu lokuta da kuma wajaje da yake son ayi addu’oi a cikinsu kuma ya kan kar~a ma wadda yayi addu’ar.”

          38-Imam Ali Al-hadi ya ce, “Duk wanda yayi ]a’a ga Allah Ta’la to ba zai damu da fushin mutane ba.” Wato kan biyayyarsa ga Allah ma]aukaki.

          39-Imam Ali Al-hadi ya ce, “Duk wanda bai kiyaye mutuncin kansa ba to kada ka aminta da sharri daga wajensa.”

          40-Imam Ali Al-hadi[AS] ya ce, “Da a ce mutane zasu bi wata hanya,wani bawan Allah mai iklasi shi kuma yabi wata hanyar,to kabi hanyarsa shi yafi.” Wannan hadisi yayi kama da wani Hadisi da aka ruwaito daga Manzon Allah[S] ya ce ma sahabinsa Ammar ]an Yasir, “Ya Ammar idan mutane baki ]aya suka bi wata hanya,Ali ]an Abu [alib yabi wata hanya to ka bi hanyar da Ali ya bi ka bar mutanen.Wannan Hadisi yana karantar damu cewa yawan mutane ga abu bai mai dashi gaskiya,haka nan }arancin mutane ga abu bashi yake nufin ba a kan gaskiya suke a kai ba.

Insha Allah a darasi na gaba za a kawo Hadisai 40 da aka ruwaito daga Imam Hassan Al-askari[AS].

 
Home Darusan Hadisai Hadisai 40 na Imam Ali Al-hadi (AS)
Copyright © 2023. www.tambihin.net. Designed by KH