Thursday, 19 September 2024
Email
Make My Homepage
RSS
Register
Tambayoyi da Amsoshi kan Sallar Idi da kuma Zakkan fidda kai. Print E-mail
Written by administrator   
Sunday, 18 June 2017 11:57

Inna-lillah-wa-inna- ilaihi- rajiun, na tafiya da kuma rabuwa da wannan babban ba}o mai girma da kuma daraja da ya ba}uncemu, wato watan Ramadan. Domin idan mutum ya yi bincike a littafai zai ga cewa a duk watanni 12 da ake da su a musulunci,to babu wani wata da aka samu ruwayoyi daga Manzon Allah (S)da kuma A’imma na ahlul-baiti (AS) na bankwana da shi da kuma umarni da yin haka face watan Ramadan, wanda wannan ka ]ai ya isa ya nuna falala da darajan wannan watan. Misali shine ruwaya na addu’an bankwana da watan Ramadan da aka samo daga Manzon Allah (S). An samo daga Jabir ]an Abdullah al-ansariy (RA), yace: “Na shiga wajen Manzon Allah (S) a juma’ar }arshe ta watan Ramadan, lokacin da Manzon Allah (S) ya ganni sai ya ce min,ya Jabir` wannan itace juma’an }arshe ta watan Ramadan. Kayi bankwana da shi, Ka ce; YA UBANGIJI! KADA KA SA YA ZAMA AZUMIN {ARSHE A RAWUWATA. IN KASA HAKA, TO, KA SANI CIKIN RAHAMAR KA, KADA KA SAN YANI CIKIN WA[ANDA AKA HARAMTA WA RAHAMA”. Manzon Allah (S) ya ce duk wanda ya fa]i haka, zai rabauta da ]aya daga cikin kyawawa guda biyu: ko dai Allah (T) ya raya shi zuwa watan Ramadan na gaba ko kuma Allah ya gafarta masa ya yi masa rahama.

            Haka nan akwai ruwayoyi daban-daban guda biyu na bankwana da aka samo daga Imam Zainul Abidin (AS) wanda idan mutum ya karanta su, musamman ma a ce lokacin da yake karantawa zuciyarshi na halarce,wato bai tunanin kome sai abun da yake karantawa, tabbas zai samu tasirin haka a ruhinsa. Domin zai ga yadda Imam Zainul Abidin yake magana da sallama da bankwana da watan Ramadan da kuma jin zafin rabuwa da shi, kamar ka ce mutum ne yake gabansa yake bankwana da shi da kuma nuna damuwa na rabuwa da shi. Ga misali wasu daga cikin kalmomi na bankwana da ya yi ga watan Ramadan da suke a cikin addu’o’i da aka ruwaito daga wajen sa (AS). Yana cewa;”Innalillahi wa inna ilaihi rajiun saboda rabuwa da watan azumi, watan tsayuwa kuma wata na Al}ur’ani. Ya kai wannan wata namu! Muna bankwana da kai ba domin mun }osa da azumi a cikin ka ba, ba domin muna son rabuwa da kai ba. Da a ce za a iya cewa wata, Allah ya sakamaka da alheri da an ce, Allah ya saka maka da alheri ya watan Ramadan”. Awani wajen yana cewa muna bankwana da kai bankwana na ba}in ciki da kuma jin zafin rabuwa da kai”.

Akwai kuma wani sashe da ya jero sallama ga wannan wata mai albarka. Misali yana cewa;”sallama gareka ya kai wannan watan idin walliyyan Allah.Sallama gareka ya mafificin wanda ake abota dashi daga lokuta.Sallama gareka na ma}wabci,wanda zukata suka lausasa a cikinsa,kuma zunubai suka }aranta a cikinsa.Sallama gareka na mataimaki daga mataimaka akan she]an.Sallama gareka wanda kazo mana da albarkoki,ka kuma wanke mu daga dattin zunubai.Sallama gareka wanda ake bege da nema gabanin zuwansa,ake kuma ba}in ciki gabanin rabuwa dashi.Sallama gareka da kuma lailatul }adari,wadda take mafi alheri daga wata dubu.Sallama gareka a bisa falalarka,wadda aka haramta mana da kuma albarkokinka wadanda suka shu]e,wanda yanzu mun rasa su”.                                                                   

A ta}aice dai idan mutum ya biya wannan addu’a, ta Imam Zainul Abidin [AS] ta bankwana da watan Ramadan zai ga yayi wa wannan wata mai albarka sallama biye da juna, ]ai ]ai har guda 20.Haka nan Imam Sadi} [AS] an samo irin wannan addu’a ta bankwana da watan Ramadan daga wajensa.Saboda haka ana son mutum ya karanta duka wa]annan addu’oi na bankwana da aka samo daga Manzon Allah da Aimma na Ahlul bayt a daren }arshe na watan Ramadan ko a ranar }arshe ko kuma a daren Idi.

            A yanzu ibadar dake gabanmu itace Sallar Idi da kuma Zakkar fidda kai,saboda haka a wannan darasi za a gabatar da tambayoyi ne wa]anda aka yi ma Ayatullahi Sayyid Khamna’i kan mas’aloli dabam dabam da suka shafi Sallar Idi da kuma Zakkar fidda kai da kuma amsoshin da ya bayar:

SALLAR IDI

          Tambaya:Shin Sallar Idi matsayinta wajibine ko mustahabbi?

          Amsa:Sallar Idi a wannan zamani namu-wato na gaiba- matsayinta mustahabbi ne ba wajiba ba.

          Tambaya:Shin idan Sallar Idi ta ku~uce ma mutum ko kuma lokacinta ya wuce to zai rama ta?

          Amsa:Ba zai rama ta ba.

          Tambaya:Wane lokaci ne ake yin Sallar Idi?

          Amsa:Lokacin Sallar Idi shine daga lokacin da rana ta fito har ya zuwa Zawal,saboda haka babu ramuwa kan mutum in ta ku~uce bai yi ba tsakanin wannan lokaci da aka ambata.

          Tambaya:Yaya ake Sallar Idi?

          Amsa:Sallar Idi Raka’a biyu ne,amma tana da }unuti guda tara,a raka’a ta farko }unuti guda biyar,a raka’a ta biyu }unuti guda hu]u.A raka’a ta farko zai biya Fatiha da Sura amma anan an fison biya suratul A’ala wato Sabbi,bayan haka sai yayi kabbarori guda biyar bayan kowace kabbara sai yayi }unuti,bayan yayi }unuti na biyar sai yayi kabbara domin tafiya zuwa ruku’u saannan yayi sujuda.Bayan haka kuma sai ya tashi yazo da raka’a ta biyu itama ya karanta Fatiha da Sura anan an fison karanta suratu shamsi wato wasshamsi saannan yazo da kabbarori guda hu]u zai yi }unuti bayan kowace kabbara,bayan yayi }unuti na hu]u sai yayi kabbara domin tafiya zuwa ruku’u bayan haka kuma ya tafi zuwa ga sujuda bayan ya ]ago daga sujuda ta biyu sai ya zauna domin yin tashahhud-tahiya-in ya gama sai yayi sallama.

          Tambata:Shin ana kiran Sallah ko yin i}ama a sallar Idi?

          Amsa:Ba a kiran Sallah ko yin i}ama a sallar Idi-wato ita kai tsaye mutum zai yi niyya ya fara ta-amma da ace liman zai yi i}amar to bai ~ata sallarsa ba ko sallar masu binsa.

          Tambaya:Wace addu’a ce ake yi a }unutin Sallar Idi?

          Amsa:Mutum zai iya yin kowace addu’a sai dai yin wannan addu’a shi yafi falala,addu’ar tana farawa da “Allahumma ahlul kibriya’i wal azamati,wa ahlul judi wal jabaruti..............”-mutum yana iya duba addu’ar a cikin littafin mafatihul jinan-idan ma mutum bai hardace addu’ar ba to zai iya karanta ta a littafi ko takarda a cikin sallar.

          Tambaya:Shin }ari ko ragi ga }unutin sallar idi yana wajabta ~acin Sallar?

          Amsa:Haka bai ~ata Sallar.

          Tambaya:Sallar Idi mutum zai iya yinta shi ka]ai ko sai a jam’i ne zai iya yinta?

          Amsa:Mutum zai iya yinta shi ka]ai,kuma zai iya yinta cikin jam’i.

ZAKKAR FIDDA KAI

          Tambaya:Zakkar fidda kai fitar da ita wajibi ne ko mustahabbi?

          Amsa:Zakkar fidda kai ga wanda yake da halin fitar da ita wajibine ga mutum da kuma duk wa]anda suke }ar}ashinsa misali matarsa da ‘ya’yansa.

          Tambaya:Wane lokaci ne ake fitar da zakkar fidda kai?

          Amsa:Zakkar fidda kai lokacin fitar da ita yana somawa ne tun daga daren Idi har ya zuwa washe garin Sallah zuwa zawal.

          Tambaya:Minene hukuncin wanda yake da ikon fitar da ita a cikin lokaci sai ya zamanto bai fitar har lokacin ta ya fita?

          Amsa:Bata fa]i akansa ba zai fitar da ita koda ko bayan kwanaki ne,rashin fitarwar ya kasance ne akan asasin mantuwa ko jahilci ko kuma da gangan.Haka nan da zai fitar da ita amma wanda zai ba sai bai samu bashi ba har lokacin ya fita to anan zai cigaba da aje tane har ya ba da ita ga wanda zai ba.

          Tambaya:Su wanene ake baiwa Zakkar fidda kai?

          Amsa:Zakkar fidda kai ana bada ita ne ga nau’oi guda takwas na wa]anda ake baiwa Zakka misali Fa}iri,miskini,matafiyin da guzuri ya yenke masa da dai sauransu,sai dai mustahabbi ne a fifita ba da ita ga ‘yan uwa na jini da kuma ‘yan uwa na addini haka nan kuma ga ma}wabta mabu}ata.

          Tambaya:Wa]anne ababe ne ake fitar da zakkar fidda akai akansu?

          Amsa:Abubuwan da ake fitar da zakkar fidda akai sune nau’oin kayan abinci da aka fi amfani dashi a yenkin da mutum yake a zaune misali idan sun fi amfani da shinkafa ko masara ko dawa to sune mutum ake so ya fitar,amma ko da zai fitar da wani nai’in kayan abinci da basu cika amfani dashi ba to ta yi.

          Tambaya:Mutum zai iya ba da }imar ku]i maimaikon bada kayan abinci?

          Amsa:Na’am mutum zai iya ba da }imar ku]i.

          Tambaya:Minene mi}darin zakkar fidda kai?

          Amsa:Ga kowane mutum ana bada Sa’i guda ne,sa’i guda kuma yana kusan kilo ukku ne.

            Bayan haka ana son mutum ya samu isti}ama da sabati ga ayyuka na ibadodi dabam dabam da ya aikata a watan Ramadan dai dai gwargwadon iyawar sa, ya tsayu akai har ya zuwa wani watan Ramadan insha Allah.Duk da cewa mutum ba zai iya yi ba kamar watan Ramadan amma ya dage wajen tsayuwa da wani gwargwado na ayyukan ibadodi dabam-dabam.Haka nan kuma mutum yayi mujahada wajen ganin cewa tsarkakar da ya samu daga zunubai a watan Ramadan bai koma gidan jiya ba,domin in ya koma gidan jiya to misalinsa shine kamar wanda ya wanke tufafinsa kuma ya goge su,bayan haka sai ya je ya sa su a kwata.Saboda haka bayan watan Ramadan mutum na bu}atar yin mujahada da naf’s ]insa da kuma shai]an fiye da watan Ramadan,wato kasantuwar bayan watan Ramadan an saki shai]anu daga ]aurin da aka yi masu.

Daga}arshe babu abin da zamu ce face mu yi godiya ga Allah [T] daya nuna mana farkon wannan wata mai albarka,kuma ya nuna mana }arshen sa.Ayyuka na ibadodi da Allah [T] ya bamu ikon aikatawa,Allah[T]ya kar~a mana,Addu’oin da muka ro}a,Allah[T] ya bamu fiye da abinda muka ro}a.Abubuwan da muka nemi tsari na sharrori,Allah ya tsare mu fiye da abinda muka nemi tsari a kai,Allah[T] ya raya mu ya nuna mana wani watan Ramadan cikin }oshin lafiya da kuma yelwar arziki.Allah Ta’ala ya saka mu cikin wa]anda suka fita wannan wata na Ramadan da Ta}awa.

 
Home Darusan Fiqh Tambayoyi da Amsoshi kan Sallar Idi da kuma Zakkan fidda kai.
Copyright © 2024. www.tambihin.net. Designed by KH